Showing 195001 words to 198000 words out of 407268 words
nan bara na gwada, ALLAH ya saka da alkairi, ina alfahari da d'iyata”.
Samha ta fita tana dariya, nikuma na warware kayan, masha ALLAH sarin ya had'u gaskiya, farine anmasa kwalliya da pink and silv
er kad'an-kad'an. Na saka rigar, sai dariya ta kamani, saikace wata bafulatana
🤭🤣
.
Warware zanin nayi, tofa anan akeyinta, dan ban iya nad'awaba, na tsaya gaban mirror inata gwadawa amma na kasa, dariya ta kamani, yau naga takaina, Samha ta had'a
ni da aiki.
Tunda ta fara k'ok'arin d'aura zanin sarin yana tsaye a k'ofa, ya hard'e hannayensa ak'irji kawai yana kallonta, kamar zaiyi dariya saboda yanda taketa murd'e-murd'en d'aurawa.
A hankali ya taka zuwa inda take, jinai kawai an
dafa min kafad'u ta baya, na d'ago a tsorace muka had'a ido ta cikin mirror, fuskarsa babu walwala, ya d'agamin gira d'aya, maida idona k'asa nayi, yayinda shikuma ya juyo dani ina fuskantarsa.
Gwiwarsa d'aya ya saka a k'asa ya dogare d'aya, nidai
kallonsa nake mizaiyi?. Batareda ya kalleni ko min magana ba ya zare zanin dake tattare a hannuna, nikam kamar wata sokuwa saina sakar masa.
Yiyay kamar zai warware zanin, nayi saurin rik'ewa, ya d'ago fararen idanunsa yanamin alamar na saki, ban
iya musa masaba na sakar masa.
Shima sai bai yaye dukaba ya dai-daitashi, ammakina sainaga yana nad'amin, babbar magana Galadima da nad'a sari.
Dazai saka wanda a ke sokewa a gefen kugu sai yayi dawani salon daya sakani zabira saboda sak'ons
a yajemin har kwalwar kai, ya d'ago ya kalleni yana wani miskilin murmushi da d'agamin gira. Sai kawai na lumshe ido dan naji kunya wlhy. Ya mik'e tsaye yana daidaitamin na kafad'ar shima, nidai harya gama ban bud'e idoba. baiyi magana ba ya warware reborn
d'in kaina, da sauri na bud'e idon, yanda yawani tsareni da idanu sai nakasa jurewa na maida na rufe.
Cumb ya d'auka yahau gyaran kai, to nikma naga abinda yafi k'arfina yau d'innan, wai dama guy d'innan ya iya abin mata ne?. Bai barni ba saida ya
gama yanda yakeso dani, ya zubamin ido kawai batareda yace komai ba. nikuma nakasa bud'e idona na kallesa, ahankali yafara busamin iskar bakinsa saman idona, dole nafara marmar da idanu, dainawa yayi, na bud'e idon ahankali a kansa, kuma matsoni yayi muka
Zuba juna ido ko k'yaftawa bamayi, gashin dake neman shigarmin ido ya saka d'an yatsa ya matsar, na maida idanun na lumshe ina sauke k'aramar ajiyar zuciya.
Shima nannauyan numfashi ya sauke kafin yaja da baya, wardrobe d'insa ya nufa, jin yabar w
ajen saina bud'e idona, duk jikina ya saki, kallo d'aya namasa na d'auke kaina na juya ga mirror Dan naga yanda ya maidani, murmushi nayi ina saka hannu na gyara gashina, nima na yarda da gaske nayi kyau.
Nakuma d'ago ido da nufin sake kallon kaina s
ainaganshi a bayana, sark'a ya ziro a ya sakamin tareda gyara zamanta ta zauna sosai a k'irjina, ya janye gashina ta baya yana sak'ala sark'ar, nidai nawa idone, ya gama ya cire d'an kunen dake
kunnena ya sakamin na sark'ar, sannan ya mannani da jikinsa ya
na zagayo hannunsa duk biyu saman matashin cikina, hannuna ya kama yana sakamin bangles, cikin k'asaitacciyar muryarnan tasa yake magana cikin kunnena, “haka dama sari kema Afirikawa k'yau?”.
Murmushi nayi, na d'ago idona muna kallon juna ta cikin
mirror, haryanzu hannayena na cikin nasa yana saka bangles d'in da guda d'ai-d'ai.
Ya lumshe idanu yana shanshanar wuyana, jikina yafara rawa, babu shiri na saka hannuna d'aya daya gama saka bangles d'in na shafo gefen kumatunsa, cikin rawar murya na
ce “please kabari yalla6ai”.
Batareda ya dainaba cikin sark'ewar harshe yace “mizaisa na daina? yalla6iya”.
Yanda yake min akan dokin wiya da yanda hannunsa d'aya ke canja salo a jikina sainayi k'ok'arin juyowa garesa, ko hakan zaisa y
abari d'in. Ashe dama ma na sake bashi, gaba d'aya yawani rikice kamar ba Galadiman Dana saniba. Hannunsa ya sak'alo kuguna yana kuma matsoni jikinsa sosai, yasaka d'ayan hannun ya tallafo kaina tareda d'ora la66ansa akan nawa.
Kasa jurewa nayi, na
mik'a masa wuya kawai, harda bada gunmawa nima........
Tofa munga idi, daga gyaran sari
🙆🏽😹
.
Samha tataho da karsashinta dantaga ko Munaya ta saka, daga nan ta nuna mata yanda zata nad'a zanin sarin, tunda tasan bata iyaba, ko k
ad'an babu Wanda yaga shigowar Galadima, Dan babu kowa a falon, jakadiya ta tafi asibiti itada Sauban da innarsu munaya, aunty Mimi kuma barci takeyi, Dady kam yanacan baya inda ya maida lambun tunaninsa, itako Samha tana bama Munaya sari takoma d'aki dant
a bata lokaci ta shirya a tsanake. Sallama d'aya kawai tayi ta turo k'ofar tana kwala kiran “Aunty gimbiyarmu kin saka?”.
Galadima dayake Neman fara zirmawa yay hanzarin sakin Munaya, da sauri naja baya nima, dan kamar a sama mukaji muryar Samha.
Itama Samha baya ta koma da sauri gabanta na fad'uwa, Dan ganin Wanda batayi zatoba a d'akin. ALLAH ma yaso bataga komaiba, lokacin datake sako k'afarta a d'akin Galadima ya janye bakinsa yana k'ok'arin matsawane baya.
Wata uwar harara mai ka
d'a hanji da hanta ya zubama Samha, hakanne yasakata yin baya da sauri ta koma.
Nikam kasama d'aga ido nayi balle na kalleshi dagashi har Samhar, saima wani yaam nakejin jikina tamkar zan fad'i.
Lura da hakan da yayine yasakashi azamar rik'o
hannuna, na shige jikinsa ina sauke tagwayen ajiyar zuciya, dagani harshi idanu kowa ya lumshe, tsawon lokaci muna a haka munkasa sakin juna, ahankali na shiga k'ok'arin janye jikina, bai hananiba yabani damar barin jikinsa, ra6awa nayi ta gefensa na wuce,
na koma saman sofa na zauna ina dafe kai, juyowa yayi yana kallona, kafin yatako shima zuwa bakin gado ya kwanta, k'afafunsa na k'asa duka, yayinda yay filo da hannayensa yana lumshe idanu.
Duk munyi shiru d'akin tamkar babu wata halitta mai numfa
shi a cikinsa, kowannenmu shiyasan mi yake sak'ama zuciyarsa.
K'arar wayarsace ta sakamu d'an firgita mu duka, duk sai muka zubama wayar ido tamkar wani ojuju. harta tsinke bai d'aukaba, saida aka sake kira sannan ya cirota daga aljihun wandonsa yay
picking.
Muryarsa vary low yace, “Nuren Yaya dai?”.
Mamaki da al'ajabi ya cika Nuren, yakuma Ciro wayar daga kunnensa ya duba Dan tabbatar da Galadima ne kuwa?, lallai shine, maida wayar yayi a kunne yana fad'in “brother lafiyarka kuwa
?”.
Taune lips nashi yayi, ya yanke wayar, dan indai ahaka zasuyi wayarnan bazai fahimci komaiba, ajiye wayar yayi yatashi ya shige bathroom.
Da kallo k'asa-k'asa kawai na iya binsa, amma nakasa ko kwakwkwaran numfashi.
Daga can kuwa N
uren kwashewa yayi da dariya saboda tuno wani Abu, (to su Nuren dai dama bariki sune manyanta
🤣
), dariya yakeyi iya iyawa yana dukan kansa, daya fara tsagaitawa saiya kuma saka wata, saida yayi ta ishesa sannan ya daina, ya rik'e ha6a yana fad'in “oh ni su
brother ansan takan tsiya, ina ganinsa lab-lab Ashe d'anba sauk'ine, toma uwar miye na d'agamin wayar tunda yasan yafara sauka a network
🤣
, yakuma saka dariya saikace wani sabon kamu.
😬
Galadima kam ruwa ya sakarma kansa kawai, ya dafe bango da
hannu biyu ruwan na kwarara saman kansa, sai faman taune lips yakeyi shi kad'ai, yayi da zuciyarsa ke sak'awa da kwancewa, saida ya ji k'arfi-k'arfi sannan ya kashe shower d'in yaja bathrobe d'in ya saka yana faman sauke 6oyayyar ajiyar zuciya.
Inda
yabarta anan ya fito ya isketa, kallo d'aya yamata ya d'aukekai, bakin gadon ya zauna yana goge kansa da k'aramin towel, yajawo wayar da d'ayan hannun ya danna kiran Nuren.
Bugu d'aya Nuren d'in ya d'aga, da k'yar yasamu ya danne dariyarsa, “brother
wai miya farune naji muryarka haka? nifa ka tadamin hankali”.
“Ba komai, shin kajene?”.
Nuren ya toshe bakinsa gudun kar dariya ta kufce masa, Sameer d'an rainin wayone ALLAH, wai babu komai, to naji babu komai aje a haka.
“wai k
ana jina kuwa?”. Galadima yafad'a.
“Oh sorry brother network nayin wasa, gani a gidan, amma bankai ga shiga inda takebane”.
“ok tom kaje, amma kabar wayar a kunne, inason naji komai”.
Nuren yace “to”.
Da sallama ya shiga d'akin, sai
wani ciccin magani yake.
Farhat dake zaune bakin gadon d'akin ta zabga tagumi ta d'ago kai tana kallonsa, yayin da wasu hawaye ke shirin zubo mata.
Kujera guda d'aya dake d'akin ya jawo ya zauna.
Farhat ta share hawayen kumatunta, mu
rya a sanyaye tace, “yayana dan ALLAH kayi hak'uri, wlhy ina missing d'in families d'ina da karatuna, dan ALLAH idan kasheni zakayi ka kasheni kawai na hutama rayuwa ma ni gaba d'aya”.
Murmushi Nuren yayi, idonsa a kanta yace, “bazan kashekiba Farha
t, dan bakimin komaiba, kamar yanda na sanarmiki mahaifinkine yaja miki, ki kwantar da hankalinki, insha ALLAH zaki koma gidanku kwana kusa, yanzuma dukba wannanba, wata tambaya nazo yimiki, ALLAH yasa zaki bani had'in kai?”.
Kanta ta jinjina masa
tana kuma share sauran hawayen, “insha ALLAH inhar nasani zan fad'a maka”.
“good girl ”. ‘cewar Nuren yana gyara zama’.
“Farhat nasan kinsan duk yaran Abbanki ko?, ina nufin masu masa hidima a office ko a gida?”.
“Eh nasan mafi yawa
nsu, dan ina zuwa wajensa a Office, kuma wasu acikinsu sukanzo gidanma”.
“Masha ALLAH, kokin san SD?”.
“SD!?”.
“eh shi”.
“gaskiya a yaran Abbana dana sani babu wani mai suna SD”.
“okay, amma ko wani mai Something sunan dazai iy
a kasancewa full name bazaki iya hasasowa ba?”.
Shiru tayi ta lula duniyar nazari, shidai Nuren ya zauna mata idanu yana kuma jinjina ma ubangiji akan yin k'yak'yk'yawar hallita, dan Farhat black beauty ce masha ALLAH.
A jiyar zuciya ta sauke,
“yaya inaga kamar dai akwai wani Sagir dauda dana Sani, amma bansan aikin da yake a k'ark'ashin Abbanmu ba, sai kuma ya Shareffudden k'anin Aunty Umma, sai Steven Daniel”.
“shi Steven d'in wanene shi a gidanku, itama Aunty Umman haka?”.
“Dr
iver d'insu Mom ne, shike kaisu anguwa, ita kuma Aunty Umma matar Abbanmu ce ai, itace amaryarsa”.
“Uhyim”. Nuren yafad'a yana jinjina kai.
“Dan ALLAH yayana in tambayeka mana?”.
“ina saurarenki”.
“laifin mi Abbana yamuku hakane?”.
murmushi Nuren yayi, “karki damu nangaba kad'an komai zai wuce, kuma bashi yay laifinba, wanine yayi na kusa dashi”.
“to ALLAH yasa Ku kamashi, amma dan ALLAH karkuma Abbana komai”.
“insha ALLAH babie”.
Murmushi Farhat tayi, Nur
en kuma ya mik'e tsaye idonsa a kanta. “babu dai wata Matsala ko?”.
Cikin shagwa6ar data saba tace, “please ko TV ka samin, banajin dad'in zaman hakanan”.
“Am sorry to say dear, har kibar gidannan dokace, babu television, babu phones, amma wa
y not nakawo miki irin Hausa novels d'innan danaga mata na karantawa?”.
Idonta ya cika da kwalla, “ayya yayana wlhy ban iya karatun hausaba sosai, yana bani wahala”.
Ido yad'an zaro waje, yace, “saboda mi? Keba bahaushiya bacene?”.
“b
ahausa mana”. ‘tafad'a cikin turo bani irinnan ta6ararru’.
Baki ya ta6e yana kama hanyar fita, “zaki cigaba da kad'aicinki ashe kuwa”.
Ganin zai fice da sauri tace, “please ka siyo zan fara koya to”.
“it's better”. ‘yafad'a yana ficewa
rsa’.
Saman gadon ta fad'a ta fashe da kuma mai ban tausayi.
Duk abinda ke faruwa Galadima najin komai ta waya, Munaya ma na zauna a sofa har yanzu tana satar kallonsa, amma batajin miyake saurare da ya nutsu haka.
Cire wayar yafara k
'ok'arin yi ya jiyo muryar Nuren na fad'in “hello brother kana jina?”.
Galadima yace, “eh”.
“okay duk kaji aimi ta fad'a ko?”.
“duk najiku, saika samin ido akan duk d'unsu, a bincikomin komai daya shafesu”.
“indai wannanne insha
ALLAH angama, amma ni a ganina banda wannan Shareffuden d'in datace, domin babu wani kamanni a cikin nashi sunan, ballema tace k'anin step mom natane”.
“Humm Nuredeen kenan, shifa mak'iyi ba'a rainashi, mutane da yawa sukan d'auki cinnaka ba komaib
a, amma idan yacijesu sukan ji cizon har a ransu, dan haka karka ta6a d'aukar mage mafi sauk'i akan kare, itama idan taga nama citakeyi”.
“wannan gaskiyane brother, ALLAH yabamu sa'a”.
“amin ya rabbi, naji kuna maganar buks da ita, kaje ka sa
mo mata dukkan Wanda take buk'ata, har English novels d'in, sannan ak'ara tanadar mata dukkan abinci mai k'yau datake so”.
“insha ALLAH angon Munaya”.
Girgiza kai kawai Galadima yayi ya yanke wayar.
Kallon Munaya yayi suka had'a ido
, saita janye cikeda basarwa. Shima tashi yayi ya koma gaban mirror, duk uzirinsa yayi ya gama sannan yamatsa ga wardrobe ya ciro kayan dayake buk'ata.
Ganin haka Munaya tazame ta kwanta cikin kujerar yandama bazata gansaba.
Baki kawai ya ta6e
yacigaba da saka kayansa.
Bayan yagama yamatsa kusada ita, “tashi ki canja kaya ki rakani wani waje”.
Fuska Munaya tad'an yatsina, kamar zatace wani Abu saikuma ta yunk'ura zata tashi kawai, hannunta ya kama ya taimaka mata ta tashi zaune
. fita yayi abinsa. Hakan yasata fahimtar zai jirata a falo kenan.
Bata 6ata lokaciba ta canja kayanta da atanfa skt da riga, takawo after dress ta saka sannan ta nad'a Vail d'in rigar, d'as ta fito itada cikinta, kamar ka saceta ka gudu abinka.
Tunda ta fito ya zuba mata idanu, ko k'yaftawa bayayi, saida yaga tana gabda k'arasowa garesa ya basar yana mik'ewa. Gaba yayi tabisa abaya, yandama yake taka steps d'in benen dolene ya birgeka, duk takunsa nakan idonta, yayinda itama take binsa dak
i-daki a hankali.
Babu kowa a falon, dan haka suka fice basu nemi kowanba.
A mota yana tuk'i da sauraren karatu itakuma tana latsa waya suna charts a families group d'insu. Sai murmushi take zubawa, duk abinda take yana kallonta ta gefen
ido. Sun isa wani k'aton shagon saida kayan babies, duk abinda kake buk'ata zaka sameshi indai na yarane daga 1year zuwa 15. Itadai mamaki ya ishi Munaya, miye nawani kawota nan? yabari a haihun mana ma.
Tarba ta musamman aka musu, hakan ya tabb
atar ma Munaya yasan mai shagon kenan, dan yanda aketa girmamasu sai abin ke bata mamaki. gashi indiyanci sukeyi bata fahimtar maganganunsu. Itadai tana zaune hankalinta ya rabu gida biyu, wajensu Galadima da kuma wasu mata biyu da yaransu uku dabazasu wuc
e 7-7years ba, yaran k'yawawa masha ALLAH, ga wayo.
Galadima ya juyo zai mata magana saiya lura da inda ta zubama idanu, shima shagala yay a kallon yaran, iyayensu na za6ar kaya amma su suna tibirewa sai Wanda sukeso za'a d'auka. Munaya sai zuba m
urmushi takeyi, dan suntafi da