Showing 24001 words to 27000 words out of 407268 words

Chapter 9 - Raina Kama COMPLETE

/>
Komawa yayi 6angarensa yashiga wanka, kusan mintina 40 sannan yafito sanye da bathrobe fara k'al, bai wani d'au dogon lokaciba y

ay shiri cikin k'ananun kaya, yayi k'yau sosai, ya feshe jikinsa da turarensa masu matuk'ar k'amshi.

Wayarsa ce tashiga ringing, baibi takantaba yacigaba da hidimarsa, dama tun yana bathroom yakejin ana kiransa.

ta baya yabi inda bayi bazasu

isheshi da gaisuwa gaisuwa d'innanba, dayake sarki yana gida, yau ana hutun zaman fada saboda tunawa da abinda yafaru da tsohon sarki (mahaifin Galadima Sameer) duk ranar litinin tana zama ranar daba'a zaman fadane...



.



.



.



.



.



.



.



.



.



Ko

wa ya ganmu yasan muna cikin rud'ani, da k'yar aka samu innarmu ta farfad'o, sai dai an hanamu mushiga mu ganta.

Gidanmu kam abin nema yasamu, hakama cikin anguwa, saboda yad'uwar labarin a social Media.

Muna zaune a falo duk mun zabga uban tag

umi dagani har munubiya, idanunmu duksun kunbura saboda kuka, Ni ba abinda yafaru a jaridar ne yafi damunaba, halin da mahaifiyarmu ke ciki shine babbar matsalata, bamuda kamarta duk duniya, bazanso wani Abu ya sameta asanadinmu ba, bayan bak'incikin datak

e k'unsa agidanmu kuma.

Kamar anjeho mama Rabi'a itada ya Marwan suka shigo falon. mun tsorata kwarai da gaske, cikin daka tsawa mama Rabi'a take tambayarmu innarmu.

Hakanne ya tabbatar mana da suma labarin yaje musu. munubiya ce tabata amsa ci

kin kuka, sannan tace “wlhy mama sharrine, ba abinda yafaruba kenan n......”.

Saukar marin datajine yasakata rufe bakinta 6am, kafin na tantance mai Marin nima naji saukar nawa.

Ko kad'an yaa Marwan baiji tausayinmu ba, saida yamana lik'is da d

uka, dak'yar Dady ya kar6emu a hannunsa, amma baba k'arami da Abbanmu casukai yama k'ara mana.

'Yan gidanmu duk sunfito cirko-cirko a tsakar gida, kowa na tofa albarkacin bakinsa, gashi akwai sauran 'yan biki dabasu gama tafiyaba.

Iyayenmu da y

ayinmu duksun taru akanmu, ana tambayarmu wacece daga cikinmu.

Kafin Munubiya tayi magana nayi saurin cewa “kuyi hak'uri iyayena, nice munaya a gaba d'aya hotunan, wlhy kuma tsautsayine, amma ba ainahin abinda yafaruba kenan”.

Munubiya zatayi

magana nayi sarin rik'e hannunta alamar kartace komai, “karki d'aurama kanki abinda ba laifinkiba Munubiya, nice Munaya na aikata....”

Itama cikin kuka tace “wlhy bake baceba, nice, wlhy nice”.

Nima nace “wlhy nice”.. ....

Tsawa Abbanmu y

adaka mana, atare mukayi shiru yace “nasan dama Munaya kece, Munubiya bazata aikata wad'annan abubuwan ba, dukda kema d'in nayarda da tarbiyyar dana baki, amma bansan miya kaiki ga aikata hakanba, shiyyasa ranar idi mukaita nemanki, Ashe kinacan kina d'akk

o mana magana, tunda aure kikeso zan miki, nabaki nanda sati 2 kacal, inbaki kawomin mijiba zan had'aki dadu Wanda nayi niya”.

Yana gama fad'ar haka yatashi ya fice, baba k'arami ma ficewarsa yayi.

Wani kuka mai tsuma rai muka kuma fashewa da s

hi, musamman ma ni danasan nasaka kaina a tarko, amma hakan shine dai-dai, bazan amince naga 'Yar uwata cikin bak'in cikiba, insha ALLAH koma minene zan jureshi, muniya tanada hak'urin dazai iya cutar da ita akan wannan lamarin, gashi baba yafurta in ban f

iddo da mijiba zai auramin Wanda yaso, to idan hakan ta kasance kan Munubiya wane hali kuke tunanin zata shiga? Musamna dabamusan gidan dazamu iya fad'awaba tunda nasan abinda Abba yafad'a tabbataccene, dan shi baya magana biyu.

Dady ne yashiga lalla

shinmu, tareda mana nasiha da nuna mana illar abinda muka aikata, musaman ma ni. ya Marwan kam sai antayamin harara yakeyi shida yaa hameed.

Yinin yau kam kuka muncishi harmun godema ALLAH, mu duka kwance muke rijif da zazza6i, har akayi isha'i bamu

kumajin motsin kowaba, mukuma muna d'aki kwance mu duka k'udundune a bargo.

Su Aryaan sunacan nanuk'e da innarmu dake 6angaren Abbanmu har yanzun, dan haka 6angarenmu saiya kasance tsitt. a ranar dai haka muka kwana babu lafiya nida Munubiya, babu ma

i iya taimakon wani acikinmu, ga yunwa ga damuwa ga ciwo.

Zuwa asubahi ko salla kasa gashi muyita mukayi, dan k'arfinmu yagama k'arewa...

😭



.



.



.



.



.



.



.



.



.



.



Ya isa sassan mai martaba, bayan masu tsaron k'ofa sun gama kwasar gai

suwa suka masa iso.

Izinin shiga mai martaba yabashi.

Falone k'aton gaske, Wanda nikaina banmasan yanda zan musalta k'yansa da girmansaba, ga kujeru rukuni-rukuni, ko ina yagama d'umamewa da sanyin AC, gawani k'amshi na musamman.

daga ca

n gefe na hango mai martaba kishingid'e bisa wani lallausan carpet da aka k'awata da tarin tum-tum, gabansa tirene dake d'auke da jug na glass cikeda zo6o, sai wani k'aramin kwano na tangaram Wanda bansan miye acikiba, saikuma k'aramar butar shayi awani ti

ren daban, da mug guda d'aya.

Fuskarsa d'aure take tamau alamar yana cikin 6acin rai, ga jarida a hannunsa.

Cikeda girmamawa Galadima ya zauna a gefen dardumar, ya tankwashe k'afafunsa sannan ya risina yana fad'in “barka da rana ranka ya da

d'e”.

Mai martaba bai amsaba, sai ma cilla masa jaridar hannunsa dayayi.

Galadima yabi jaridar da kallo batareda ya d'aukaba.

“ka d'auka ka duba mana, dan inason sanin gaskiyar zancen”.

Kan galadima a k'asa yace, “takawa nima

yanzu Muftahu yakawo min nagani, nama fito zanje ga gidan jayidayne kiyanka ya isomin, amma wlhy Abba ba gaskiya baneba, ka.......”

Da sauri mai martaba ya d'aga masa hannu cikin 6acin rai “mi kakeson fad'amin? kana nufin zasu buga abinda baka aik

ata bane? ai sunsan gidan daka fito, haka kawai bazasu maka sharri ba kodan gudun abinda zaije ya dawo. Sameer yanzun nan da mutuncinmu kaje ka aikata wannan son zuciyar domin ka 6atama wannan masarautar suna? Lallai kacika d'an halak, kuma kayi dai-dai, t

abbas ka kafa tarihin dawani bai ta6a yin irinsaba a wannan masarautar, Dama Ashe kabud'e waccan plaza d'inne domin son zuciyarka? Yanzu da ace lafiyar Yaya k'alau wane irin hali kake tunanin zai tsinci kansa? Ina ganinka shiru-shiru Ashe kaid'in shaid'ani

ne”.

Runtse idanu Galadima yayi zuciyarsa na k'una da kalaman mai martaba k'anin mahaifin nasa, amma yagaza furta komai, sai idanunsa daketa k'are rinewa zuwa jajazur.

Har mai martaba yak'araci fad'ansa yagama Galadima bai iya furta komaiba, ka

nsa ak'asa ko motsi baiyiba.

“katashi kabani waje, k'arfe 8:30pm akwai meeting, saika jira hukunci daga mama Fulani ”.

Rissinar da kai Galadima yayi yace, “ALLAH ya huci zuciyayka, na bayka lafiya”.

Banza mai martaba yay masa, yatash

i yafice shikuma cikin k'unar zuciya.



Yana fita wayarsa ta fara ringing, ransa adagule yacirota da nufin kashewa gaba d'aya, saiyaga *_My dear Momma_* rintse idanunsa yayi ransa nakuma suya, yasan tabbas labari ya Isa gareta kenan, wannan wace

irin masiface, mahaifiyarsa dake wata k'asa har ankirata an Sanar mata, ko halin datake ciki baza'a kallaba?. Kasa d'aga wayar yayi harta tsinke.

Tabbas duk Wanda yake gidan jaridarnan saiyayi Dana sanin saninsa arayuwa.

Kiran Momma ne yakuma sh

igowa, yanzuma bai d'agaba harya k'arasa sashinsa.

Sai da ya zauna sannan yafara k'ok'arin nemanta cikin suyar zuciya data ruhi...............



🏼

To masu karatu, ko wanene da wannan aika-aikar? tabbas yau Munaya tabani matuk'ar tausayi daga

ita har munubiya, kai harma Galadima.

🤦🏻

‍♀

Kumuje zuwa danjin Yaya kuma zata kasance

🙆🏻

?.

Yanzufa aka fara wasan

👌🏻



🏻

‍♀⛹

🏻

‍♀⛹

🏻

‍♀

🤾🏻

‍♀

*_YA ALLAH ka gafartama iyayenmu

😭👏🏻

_*

[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing

📲

_*

*_HASKE WRITERS ASSO...

💡

_*

_(Home of expert and perfect writer's)_

*_



RAINA KAMA......!!



_*

_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

👉🏻🔟

.......Maman Fauziyya ce taga

shirun yayi yawa narashin gittawarmu ta aiko Kamal yagani muna nan, dan ita azatonta ko mama Rabi'a tawuce damu gidanta ne.

Da gudu yakoma ya sanar mata gamucan babu lafiya a d'akinmu.

ai bata tsaya jin k'arshen zancenba ta garzayo, halin data i

skemu aciki itama hankalinta yakai k'ololuwar tashi, takira baba k'arami a waya tana Sanar masa, duk da haushinmu dayakeji hakan bai hanashi shiga tashin hankaliba shima. atare suka shigo da dady, shima abbanmu sai gashi yashigo.

Duk kuma jikinsu sai

yayi sanyi, aganinsu yakamata su sauraremu ajiyan, amma duk da haka babu iyayen dazasuga wannan abun hankalinsu bai tsashiba, garashi d'an manyan mutanene, nashi mai sauk'ine, amma mune awahale.

Haka aka kira doctor yaduba mu, yace damuwace ta hadda

sa mana zazza6in, sai kuma yunwa.

Da k'yar maman fauziyya ta taimaka mana mukayi wanka da ruwa mai d'umi, sannan mukayi sallar asubahi. tea ma dak'yar muka shashi sannan mukasha magani, still kwanciya muka k'arayi, nan barci ya kwashemu.

Dadyn

e ya kalli 'yan uwansa, cikin damuwa yace, “yaya Auwal yanzu bazamuyi wani yunk'urin bincike akan lamarinnan ba? ni dai sainake ganin kamar yarannan bazasu aikata hakaba, tsawon shekaru muna tare dasu, bamu ta6a jin makamancin abinan ba daga garesu, sainak

e ganin bai kamata mu yanke hunci ba akan abinda bamuda tabbas kuma cikin fushi”.

“Hameesu karka goyi bayansu akan wannan lamarin, babu yanda za'ayi abuga labarinan alhalin bai faruba, kaduba fa shi yaron d'ane ga Sarki, shinema Galadima, kodan tso

ron abinda zaije yadawo ai nasan gidan jaridarnan saji tsoron buga labarin”.

“hakane yaya, amma baka ganin mak'iyanshi zasu iya amfani da wannan damar domin 6ata sunansa? maybe kuma su yaranmu tsautsayine ya gitta akansu”.

“maganarka gaski

yane Jafaru, nima wlhy hakan nake tunani, amma yakamata mujira muji daga gidan Sarki, Dan inhar Dan 6ata sunan yaron akayi nasan bazasu k'yaleba, kuma zasu nememu”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauke yace, “nidai koma minene gsky aure yakamata ayima Munaya,

Dan nikam banta6a cin karo da abinda ya rud'ar daniba irin wannan, mahaifiyar yarannan wlhy batayi barciba jiya, kwana tayi kuka, kuna ganin dai irin cin zarafin da inna tadinga mata jiya a tsakar gida gaban kowa, shin minene laifin A'isha akan wannan lam

arin? zata aiki su Munubiya ne akan suje su aikata hakan?”.

“kayi hak'uri yaya, lamarin inna sai hak'uri, kasan dai halinta ai”.

Haka sukaita tattauna yanda zasu 6ulloma lamarin.



.



.



.



.



.



.



.



.



.



.



.



Jiki a sanyaye ya d

anna kiran Momma, bugu biyu ta d'aga, cikin girmamawa ya gaidata, ta amsa itama cikeda kulawa kamar yanda ta saba. hakanne yad'an sakashi jin sanyi a zuciya, ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in “Momma ya jikin Abie?”.

“Alhmdllh Moh'd. wani mummunan l

abari yanzu Ummu Erfaan takirani take sanarmin?, sai kuma ga mama Fulani ma takira tanata fad'a. yanzu kuma Sauban ya nunamin wasu pictures wai an turo masane”.

Rintse idanunsa yayi cikin k'unar zuciya, murya a sark'e yace, “Momma nima haka kawai

nagani”.

“ban gane kaima haka kaganiba Moh'd, kagayamin gaskiya please, wannan ba k'aramin Abu bane bafa”.

Da k'arfi ya cije lips d'insa tamkar zai hudashi da hak'ori, cikin wata murya dake nuna k'ololuwar 6acin ransa yace, “Momma wlhy b

ansan komaiba, yanay idi tabbas munyi kayo da wata yayinya hay wayata tafad'i ta fashe, jiya kuma yayinya takusan fad'uwa a plaza nayi yink'uyin taimakon ta saima ALLAH yasa bata fad'iba, kuma ko ta6a banyiba, shine kawai yau gidan jayiday nan suka maida p

ictures d'in haka fa”.

Ajiyar zuciya Momma ta sauke, (dan tarigada tasan halin d'an NATA, duk da ba'a shaidar d'an yau musamman idan yabar gaban idonka) “Muh'd tabbas wannan k'ulline, amma kuma yarinya d'ayace ai”.

“haka nagani nima Momma”.

“yanzu mi sarki yace?”.

“Momma wlhy maganay babu dad'inji, hayma sun shiyya meeting a kaina”.

“Humm Muh'd wannan maganace mai girma, kuma tabbas domin 6ata sunanka ne da namu akayi, akwai kuma dalilinsu nayin hakan, ita wannan yariny

ar kodai da saninta kokuma an shigo da itane saboda cikar manufarsu”.

“Momma su waye to?”.

“Masusan ganin bayanmu mana, sun biyo wannan hanyarne domin dak'ileka da ragema kaifi”.

Wani naushi ya kaima k'aramin teble d'in gabansa na g

lass, nan take ya tarwatse. bai damu da ciwon dayajiba, cikin k'araji yace, “tabbas kafin suga bayana nizanga nasu!!! rayuwar mahaifina bazata salwanta abanzaba!! Saina wulak'anta dukkan masu hannu aciki kosu waye su wlhy billahi Momma! numfashina fansa ak

an mahaifina!!”.

Dole Momma tacire wayar daga kunnenta saboda yanda Galadima ke magana cikin matsananciyar tsawa.

Saman kujera ya wurga wayar, batareda ya katse kiranba, afusace yafito daga 6angaren nasa, tsawa ya dakama dogaransa.

G

aba d'ayansu cikin rawar jiki suka nufi motocin da ke fake a wajen, ko jira abud'e masa baiyiba yabud'e yashiga.

Hankalinsu a tashe yake daganin yanayin shugaban nasu, sunsan tabbas ran 'yan maza ya 6aci yau, Dan kowa yasan rashin son hayaniya irinta

Galadima a masarautar nan.

Saida suka fito daga masarautar a d'arare sarkin mota yace, “ranka ya dad'e ina muka dosa?”.

Tamkar bazai tankaba, sai kuma can afusace yace, “plaza!”.

“angama Ranka ya dad'e, ALLAH ya huci zuciyarka ya

shugabana”.

Banza yamasa bai tanka masaba, sai huci yakeyi yanna karkad'a k'afafu da taunar lips, idonsa yayi zajur saboda masifar 6acin rai.

A plaza ma tunda yashigo kowa ya fahimci yanda cikin 6acin rai, Dan ko kallon masu gaisheshi baya

yi, mutane masu siyayya sai kallonshi sukeyi, dama wasu gulmace takawosu dansu k'ara ganema idonsu akan labarin da ayau yazaga ko'ina da ina. kai tsaye wani Office yashiga.

Cikin hanzari Wanda yake a office d'in yamik'e domin kwasar gaisuwa, sai da

i yanayin ogan NASA yayi masifar rikitashi.

Bai saurari gaisuwarba yace, “inason ganin abinda yafayu a CCTV tundaga safiyay jiya hay daye”.

Jiki Na rawa guy d'in yace “angama ranka ya dad'e”.

Kujera ya jawoma Galadima ya zauna, sannan yag

yra zaman computers d'in wajen sosai, tariyo wa yafarayi cikin nutsuwa, saida yadawo Sunday morning 6pm sannan ya saki, tundaga bud'e plaza har zuwa masu share-share da goge-goge dasukayi aikinsu, har lokacin da masu sayayya suka fara Shiga da fita a plaza

d'in, har an wuce yace “dawo baya kad'an”.

A slowly yadawo bayan kad'an, har zuwa kan wasu samari biyu d'aya sanye da jallabiya d'ayan wandon Jeans da farar t-shirt.

“kayo zooming d'in yayannan dake tsaye sunan waige-waige”.

Zooming d

'insu yayi, sannan yasanya play yanna tafiya a slow.

Samarin sunata 'yan kalle-kallene, saikuma zuwa can d'aya yasaka waya a kunne yana magana da kallon cctv camera d'in dake hasko tsakkiyar plaza d'in Inda motoci ke Parking, saikuma ya janye idonsa

ya maida kan motocin dakeJere a wajen. da ganin Kasan yana maganane, Dan d'ayan dasuke tare yanata gyad'a Kansa alamar gamsuwa da abinda d'an uwansa yake fad'a.

Galadima Na zaune shiru, idonsa nakan computers d'in yana nazarin gayun har aka wuce Kans

u, baice uffanba yacigaba da kallon shigi da ficin jama har zuwa 8:11pm, daga nan Computer tayi d'iff.

Da Sauri

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login