Showing 204001 words to 207000 words out of 407268 words

Chapter 69 - Raina Kama COMPLETE

Munaya bata fahimceshiba, dan yayi maganane da yaren dabat

a ji, dan haka saitayi murmushi ta tambayesa yanajin English?.

Yaron ya d'aga mata kai alamar eh.

Ta kuma murmusawa, duk abinda ke faruwa a idon Galadima ne.

Da turanci munaya tace, “yarona kai kata6a irin wannan game d'inne?”.

Mu

rmushi yamata shima, yace “aunty akwai dad'i ma sosai, ranar saida na cinye kharan a gidansu ma”.

“da gaske?”. munaya tafad'a tana dafa kafad'arsa.

Kansa ya d'aga mata, cike da d'oki yace, “Aunty na koya miki?”.

Munaya ta d'aga masa kai.

Game d'in ya d'ora a cinyarta, ya danna wasu Number, sai kuma ya zubasu cikin d'aya, duk suka shige. Cikin mamaki munaya tace “mikenan to?”.

Shima dariyarsu ta yara yayi, yace “Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'ayane, amma sainayi ammafani da

numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacal”.

Sosai abun ya birge munaya, tayi dariy

a har hak'oranta na bayyana, jawo yaron tayi a jikinta ta rungume.

Iyayensa dake tsaye suna kallonsu tun d'azun duk sukayi dariya suma, sannan suka matsa kusada munaya suna bata hannu alamar gaisuwa. itama ta mik'a musu suka gaisa, d'aya tace sunanta

Radha, d'ayar kuma tace Anjali, munaya ta fad'a musu nata suna itama, sannan takamo hannun saran yaran tana tambayarsu suma, d'aya yace vanish, d'ayan kuma Anjun, duk kumatunsu ta sumbata tana sakama rayuwarsu albarka.

Wadda tace sunanta Radha tace

“kiyi hak'uri da surutun Vishnu shi baya gajiyane ko kad'an”.

Munaya tace babu komai.

Daganan sukai gaba, munaya tana binsu da kallo tana murmushi, yaran sai waigenta suke suna d'aga mata hannu.

Sunje wajen biyan kud'i akace subar kud'

insu inji mai shagon, da mamaki suka tambayi wanene? Mikuma yasa ya barmusu.

Mai kar6ar kud'i ya murmusawa yana fad'in mijin matarcan da kuka gaisane mai shagon ai.

Munaya batasan mike faruwaba taga sun dawo, godiya suka shiga yimata, ta t

ambayesu akan me?.

Suka bata amsa da cewar mijinta bai kar6i kud'in kayansu ba. Murmushi tayi, k'asan ranta tana mamakin dama shagon na Galadima ne?.

Sun katse mata tunani da tambayar kozasu samu number ta, babu musu tabasu sukayi sallama suk

a tafi.

Maida kallonta tayi ga Galadima dake zaune yanata latse-latsen laptop tamkar baisan mike faruwaba, da alama yana duba kayane ko wani Abu, dan time to time Wanda yake gefensa yakan nuna masa wani yanki na kayan dake shagon, shikuma ya waiga y

a kalla, idan bai hango sosaiba saiya kalla ta cikin Computer d'in dake tareda cctv cameras d'in shagon.

Munaya tace kai mutuminnan akwai son kud'in tsiya, kai komai kana saidawa, wata zuciya tace idan bai nemi kud'iba dame zai kula da mahaifinsa?

. “hakane kuma”. ta fad'a a fili tana sauke ajiyar zuciya.

Kusan mintuna 15 saitaga ya taso ya nufota. Zama yay kujerar kusa da ita yana fad'in “sorry friend na barki ke kad'ai. kin gaji mu tafi ko?”.

Munaya tad'an yamutsa fuska tace “ba

sosaiba”.

Ya d'an murmusa, “ok tunda baki gajiba kozaki d'an mana taimako ni da abin cikin kwan?”.

Hararsa tad'anyi, itafa haushin wannan abin cikin kwan dayake fad'a takeji.

Hannu yasa ya dafe bakinsa yana fad'in “maida wuk'ar”.

A tare suka dinga zagayawa cikin shagon, dayake babbane sosai, kayan yarane kuma zalla a wajen, komai bibbiyu take d'auka, baice komaiba, dan yasan dai bai wuce tana had'awa da cikin 'Yar uwarta Munubiya bane. Sund'an d'iba kaya babu laifi, ya

bada ATM d'insa aka d'auka harda na wad'ancan matan, yaran shagonne suka kai musu har cikin mota.

Yanzuma haka suka taho tamkar kurame.

Kowa da abinda yake sak'awa....

Danja data tsayar damune yasakashi juyowa yad'an kalleni, ganin ha

nkalina nakan wasu yara 'yan makaranta dake mota yace, “dama haka kike da son yara?”.

Juyowa nayi Na kalleshi, amma saiya d'auke kai tamkar bashine yay maganarba ma.

Nima maida kaina nayi ga yaran, a kuma time d'inne muka sami damar barin wa

jen.

Saida muka fara tafiya nabashi amsa da “yalla6ai kenan, waye zaice baison yaro, a duniya babu abinda yafi k'uruciya dad'i”.

Kad'an ya juyo yad'an kalleni yana fad'in “really?”.

Nima kallon nasa nayi ina fad'in “na tabbata amsarn

an kowama zai baka idan ka tambayesa”.

Bai kalleniba yanzun kam, hankalinsa naga tuk'insa, yace, “ALLAH ya kawoka duniya lafiya abin cikin kwan”.

“shiru namasa bance uffanba”.

Har muka isa gida kuma babu Wanda ya sake magana a cikinmu.

Saida yay parking motar a harabar gidan sannan ya juyo gareni, ina niyyar bud'ewa Na fita ya ruk'o hannuna. kallonsa nayi da mamaki, yawani ci magani irin babu raininnan, kamar zanyi magana saikuma nayi shiru muka zubama juna ido,

kowannenmu zuciyarsa Na

bugawa da sauri-sauri. Cikin k'asaitarnan tasa yace, “Addu'a nayi amma jan aji yahanaki amsamin da amin”.

Ni dariyama ya bani wai jan aji, hakanne yasakani murmusawa kad'an ina k'ok'arin janye idona daga cikin nasa, amma saiya hanani hakan, nace, “

na amsa ai, bakaji bane kawai”.

“aiba kurma kika auraba”.

Uhm wannan aure ana tak'ama dashi, Na fad'a a raina, a fili kuma nace, “a zuciya Na amsa”.

“k'arya haramun, banji wannan sak'onba a tawa zuciyar”.

Da mamaki Na waro ida

nu waje ina fad'in “ban fahimceka ba”.

Lips d'insa yad'an ciza da hak'ora yana matsoda fuskarsa dab da tawa, gashi ya sark'eni da idanu nakasa matsawa, d'an yatsansa ya d'ora saitin zuciyata, muryarsa k'asa-k'asa tamkar mai rad'a yace, “zuciyoyi amin

an juna sukan kar6i sak'on juna alokacinda d'aya ya aikashi ga d'aya, karki jahilci kanki har yanzu akwai sauran dama”.....

Yana gama fad'a ya saki hannuna, tareda bud'e motar ya fice.

Galala nabisa da kallo tamkar wata sokuwa, nakasa motsi nak

asa fassara zantukansa da ma'anarsu.

Tsawon mintunan dahar bayin gidan sungama kwashe kayan da mukazo dasu ban fitoba, bud'ewa naji anyi, hannunsa kawai ya mik'omin alamar nakama Na fito. tamkar sokuwa haka Na d'ora hannun cikin nasa, ya kamoni ahanka

li Na fito, maimakon ya sakeni saiya jawoni Na shige jikinsa, ya d'ora kansa a dokin wuyana, cikin kunnena yace “wasu bayanan basa buk'atar fassara, ayanda sukazo ahaka ake barinsu, karki zurfafa tunani, dan yana kawo ciwon kai da hana Hutu”.

Ya d'ag

o kaina tareda janye jikinsa yana d'agamin gira da salute d'ina, ya juya zuwa cikin gida.

Binsa kawai nakeyi a baya tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki.

A falo muka iske duka ahalin gidan, har Momma dazata kwana yau a gida, Abba ne kawai

babu, muduka sun birgemu, Dan hira suke ta nishad'i da girmama juna.

Dagani harshi gaishesu mukayi, Sauban da Samha dasuka k'arasa da kayanda da bayi suka shigo dasu suka sakko daga samanmu suna mana sannu da zuwa.

Ni kad'ai Na amsa, Galadima ha

nnu kawai ya d'aga musu.

Momma tace, “kuje ku huta mana”.

mik'ewa mukayi duk a kunyace, ina gaba a yanzu yana baya, suduka da kallon sha'awa suka bimu, dad'i da farinciki Na ratsa zukatansu, innarmu harda kwalla suka cika idonta, Wanda ita k

ad'ai tasan fasaarar kayanta.

★★★★★★★

Da daddare Galadima Na zaune akan sofa ya d'aura k'afafunsa saman teble yana latsa laptop, yayinda Munaya ke zaune a tsakkiyar gado tana karatun wani English novel na Galadima, buk d'in love story ne d

an haka taketa faman zabga murmushi, lokaci-lokaci yakan d'ago ido ya kalleta, saboda idan tayi murmushi yakan jiyo sautinsa.

Maida kansa yayi, yacigaba da aikinsa dayakeyi akan numbers d'in layin Abba na sirri, kwatsam sai maganar yaron d'azu na sha

go mai suna Vishnu ta fad'o masa a rai.

*_Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'aya ne, amma sainayi amfani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da a

ikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacal._*

Saida yakuma maimaita maganar kusan sau uku a ransa, kafin ya kalli Munaya da dukkan hankalinta ke kan Novel,

“Friend!”.

Ya kirata a nutse.

Da “na'am” Na

amsa ina kallonsa, saikuma Na janye saboda wandon jikinsa baiko rufe masa cinyaba, sai k'aramar riga mara hannu.

Yace, “mikika fahimta ga zancen abokinki na shago?”.

“abokina? waye abokina?”.

Tasowa yayi dagashi har laptop d'in da coff

ee d'insa ya hawo gadon, nima saina tashi zaune sosai.

Ya zauna ta gefe tareda ajiye mug d'in hannunsa a drowa d'in gefen gadon, laptop d'in kuma a saman gadon d'ayan gefensa. hannu ya mik'amin alamar nazo.

Ban musa masaba Na matso, ya kamoni

ya sakani a jikinsa, dan tsakkiyar k'afafunsa ya sakani, saina zame Na kwanta na d'ora kaina a cinyarsa, (dama wajen lak'ewa nake nema

🤪

).

Ya kar6i buk d'in hannuna ya ajiye gefe, ya d'ora hannunsa a saman cikina.

Kuma maimaita masa tambayar na

yi.

Ya shafa sajensa yana cije lips, “miyasa wataran kike da basarwa”..

“ni d'in?”. ‘nafad'a ina nuna kaina da kallonsa’.

Bai bani amsaba yace “ina nufin yaron d'azun”.

“Oh sorry”. nafad'a ina gyara kwanciyat.

Nace, “wai

Vishnu? ”.

Kansa ya d'aga min

“to amma wace maganace tasa? tazama abin nazari yalla6ai?”.

“game”.

“game! game!” nashiga fad'a ina k'ok'arin tunanowa.

“okay, wai yanda yafad'i yaci game d'in?”.

“Uhhm”. ya fad'a a tak'aice.

.

Nikuma saina murmusa, “to dukda dai bansan ma'anar d'aukar maganar da muhimmanciba amma anawa tunanin yana nufin _abinnan mabanbantane, amma saiyayi amfani dasu cikin Abu d'aya, kuma sukai masa aiki iri d'aya, sannan duk shi kad'ai ya sarrafas

u akan Abu d'aya bawai yayi tarayyar da wasu mutane da yawa bane ko aikinsa had'aka,_ wannan itace fahimta ta ga zancen nasa”.

Lumshe ido Galadima yayi, ya duk'o a hankali ya mannamin Sumba mai k'au a goshi. Sannan ya d'akko novel d'in ya damk'amin a

hannu, yajawo laptop d'insa yacigaba da aikinsa.

Kallon mamaki kawai na zuba masa, kokad'an ban fahimci muhallin maganar tasaba da son fashin bak'i.

Batareda ya kalleni ba, idonsa akan system d'insa yace, “kallonfa?”.

Janye idona nayi

ina ta6e baki.

Shima saiya ta6e nasa alamar yaganni kenan. karatuna nacigaba shima yacigaba da aikinsa yana shan coffee time to time.

Yayi aiki mai tsawo kafin yasaki wani murmushi da ajiyar zuciya, ya kalli munaya da barci ya kwashe, fuskart

a ya shafa yana kuma sakin wani murmushin, “tabbas gaskiya Vishnu ya fad'a, mutum d'ayane ke amfani da Numbers daban-daban wajen kiran Abba munaya, duk wadda yagama da ita bazai sakeba, tagama aikinta, a wannan karon lallai kunyi aiki da basira, wadda hart

a birkita tunanin Sameer, kuna kiran Abba da mabanbanta Numbers wad'anda kunrigada kun gama shirya matakan da kowacce number bazata sake aikiba, shima kansa ya d'auka mutane daban-dabanne ke kiransa. O ALLAH wannan shine bada k'afa, to ai inkunsan wata bak

usan wataba kuma, Muhammad Sameer ruwane, idan bakasha yanzuba zakasha anjima, idan kak'i kuma k'ishirwa ta kasheka. Inhar tarkon dazan d'ana zai d'annu dai-dai, tabbas zan cafke kurayen daji mai duhuwa a wannan karon”. ‘Ya k'are maganar da jan hancin muna

ya yana kuma sumbatar goshinta’.

Kwanciya ya gyara mata sosai, ya ja bargo ya lullu6a mata sannan yaje bayi ya d'auro alwala, kamar yanda ya saba ya raya wannan dare da nafilfili da godiyar ALLAH, kafin yazo ya kwanta gefen munaya zuciyarsa na cike d

a annashuwa da farinciki, kaikace komai yayi done ne.

Addu'a ya musu sannan yasakata jikinsa barci ya Lula dashi shima.

Nima mai d'aukar rahoto bara nad'an rintsa my sweet sisters

😉🤩

......................



🏻

Duk Wanda yaga

ban amsa massage nashiba yamin afuwa, nayi up date WhatsApp d'inane

🥰🥰🥰

🤝🏻

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu

👏🏻😭

_*

*_typing

📲

_*

*_typing

📲

_*



💡

*_HASKE WRITERS ASSO....._*

*_



RAINA KAMA.....!!



_*



_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

___________________________

_jinjinar gaisuwa a gareku da fatan alkairi, Bilyn Abdull ta gaisheku, gaisuwa irin ta musamman d'innan my lovely sister's

🥰🥰🥰🥰🥰

🤝🏻

_

*_Ays

ha Manshart (Ummu zunnur

😍

), Hafsa abdulaziz, mmn fukaihat, Hannah A Ali, marnona, Mmn Al'ameen, Sumee waziri, Ummu walid, Yar tulluwa, Khadija Aliyu Sa'id, Umm Abdul, Umm Yusuf, Mrs Ahmad, zubby abdullahi, Hajara Ismail shatu, Ummu barakat, maryam haruna

, Ummu sulaym, Ummu Ahmad, Haizarana halliru._*

I love you mazga-mazga

😂🤸🏻

‍♀

____________________________

~Book 2~

👉🏻

2



0





2



1



................Tafiyar su Abba dai ta kankama, dan Abba ya matsa ainun, dole Galadima ya musu dukkan shi

rin daya kamata, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu jirginsu zai d'aga.

Da yake yau Saturday ce babu aiki, amma hakan bai hana zama gidan shiru ba, su Sauban da innarmu sun fitane, nikad'aice a gidan sai jakadiya, nima barci nake suka gudu suka barni a

gidan.

Yunwar dana farka da ita ta tilastamin sakkowa k'asa neman abinci, dan a 'yan kwanakinnan nazama wata acici, danaci abinci danaji sabuwar yunwa, narasa wannan dalili.

Bannemi kukun gidanba ma ko cikin bayi, nahau dafa abinda zaimin

saurin dahuwa, kafin ya dahunma saida na d'umama madara nad'ansha sannan 'yar nutsuwa tazomin. ina sauke abincin kuwa Na juyoshi a plate na koma sama. tun a hanya naji k'amshin turarensa, ban kawo yashigo gidan bane nidai na ida hawa. ban tsaya faloba na s

hige bedroom.

Galadima dake zaune a sofa yana kwance igiyar takalminsa ya d'ago ido yana kallona da amsamin sallamar danayi.

Sandunan wasan Golf d'insa daya shigo dasu ya zube a carpet d'in gaban gadon na janye gefe na zauna, dan nafiji

n dad'in xaman k'asan yanzu.

Shidai bai fasa kallona ba baikuma bar cire takalman ba, dan abincin dayaga ta zubo yakema kallon mamaki, kafinfa yafita harda kukanta ta farka wai yunwa takeji, haka dole yafita yasaka kuku dafa mata abinci, baibar gida

nba saida taci takoma barci, da fitarsa kuwa baifi 3hours ba, amma jita yanzu dawani abincin.

Ya janye takalaman daya gama cirewa a gefe ya zubamin ido kawai, dukda abincin nada zafi haka nakecinsa da sauri-sauri.

Janye plate d'in yayi daga

gabana, fuskarsa babu walwala yace, “waike mike damunki hakane?”.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login