Showing 186001 words to 189000 words out of 407268 words
Hakeem (Wambai) amma sai Harun
da Muftahu sukace zasumin rakiya, ba rakkiyarce ta sani Ankara a kansuba, yanayinsu ya nusar dani kowanne akwai manufarsa, ban kulaba mukaje muka halacci d'aurin auren, anatashi Hakeem yace shi zai wuce, Dan yanada wajen zuwa, banbi ta kansaba Dan bana d'
aukar raini, karramawar da aka shirya yima mai martaba sai ta juye kaina, aka karramamu sosai, ni bammaci abincinba, sai Harun da Muftahu ne sukaci, suna tsaka da cin abincin sai aka kira Harun, bai d'aga wayar a gabanmu ba ya tashi ya fice, ko alama ban k
awo komai a rainaba, muka cigaba da hira ni da Muftahu, abinda na lura da shi rabin hankalin Muftahu akan Harun yake, dan yanayinshi ya nuna, zuwa can sai shima ya mik'e ya fice, yacemin yana zuwa, fitarsa babu dad'ewa d'ayar wayar Harun tayi ring, ni mutu
mne dabai damu da shiga abinda babu ruwansa ba, amma a ranar saina tsinci kaina da duba wayar, bansan Number d'inba, amma nasan fuskar wadda take jikin hoton da Number ta bayyana, ba kowa bace face d'aya daga cikin matan Abie na”.
“Matan Abie kuma?”
.
“kwarai kuwa, wannan shine abinda na gani, Wanda ya zaunamin a rai, koda Harun ya dawo yaga wayarsa kusa dani sainaga kamar baiji dad'iba, na bashi ina fad'in hajia ta kiraka, kinga kuwa yanda yanemi zubewa? humm saida Muftahu ya taimaka masa, dan
a tambayesa se cewa yayi wai tunkan mu taho dama kansa na ciwo, nasan ba haka baneba amma na sharesa. tunda muka taho na lura ana kallon kallo tsakanina Muftahu da Harun, kuma duk sanda hakan tafaru, Muftahu kanyi wani murmushi mai tattare da ma'anoni masu
yawa, Wanda har yanzu nakasa fasarasu”.
Huci na fidda daga bakina, na koma Inda na taso na kuma zama, shima saiya tako zuwa inda nake, ya durk'usa a gabana tare da d'ora hannayensa bisa Gwiwoyina, idanu na d'ago a hankali na sakasu cikin nashi,
k'ok'arin janyewa na farayi, saboda wasu abubuwa danake hangowa cikin idanunsa. Amma saiya hanani wannan damar, yay wani sassanyan murmushi yana fad'in.............
🤫
✍
🏼
Barkanmu da dawowa sister's
😄🤝🏻
🥰🥰🥰
.
*_ALLAH k'a ga
fartama iyayenmu
😭🙏🏻
_*
*_typing
📲
_*
💡
*_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_
♦
RAINA KAMA.....!!
♦
_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
~Book 2~
👉🏻
1
⃣
6
⃣
.................“Kin shirya
taimakon Mijinkine Munaya?”.
A salon da yay maganar saida tsigar jikina ta tashi, nad'an lumshe idanu sannan na bud'e a kansa, muryata na rawa nace, “ni bansan komaiba. kuma ina ganin a wajen Abie yakamata ka k'ara samun haske ai, tunda yanzu yana
magana”.
Murmushin takaici yayi, sannan ya kamo hannuna cikin nashi, “Kinsan miyasa nabaki dukkan wannan labarin daba kowanne mahaluki ya sansu baki d'aya ba?”.
Kaina na girgiza masa a sanyaye.
Ya murmusa, tareda d'ora hannunsa sam
an cikina, hannun nasa na kalla, shima idonsa na a wajen, yace, “saboda kece wadda zata zama uwar d'ana ko 'yata, ina fatan koda nabar duniya ban cimma burina ba kibama duk abinda kika haifa labarinnan domin ya ida cimma manufata, wannan wasiyyace ga abind
a zaki haifamin, dan inaji a jikina komi zaki haifamin insha ALLAH ba zai zama ragoba, sannan kuma tabbas kin cancanta, domin kece mutum ta farko dana ta6a yarda bazataci amanata ba bayan Mahaifiyata da kakannina da yayata da k'anina. daga k'arshe ina rok'
onki girman ALLAH ki sanarmin da abinda kika Sani game dani, dan tabbas nasan kinsan wani Abu, nasha auna fik'irarki a ma'auni kuma ina samunta dai-dai, dan haka batun 6oyemin ma kibarsa zuwa yanzu, kinga Abba jibine zasu koma, to lallai rayukansu tana ci
kin had'ari kuma komai zai iya faruwa, saboda a yanzu mak'iyansa sunyi shirin dayafi na farko ma, a zatonsu Abbanki yasanar dani komai ne. ni kuma ban ta6a wannan maganar dashiba, sannan Abie da kike magana likitoci sunyi gargad'in kar'a tuna masa da abind
a ya wuce yanzun, saboda gudun dawo da hannun agogo baya, kuma kodama na tambayesa zai iya dakatar dani yace ya yafe, ni kuma nariga nataso da BURIN 'DAUKAR FANSA, a cikin zuciyata da kwanjina, Ni nasan Yaya nayi
jiyana, yau d'ina ma a wahale take kasantuw
a, dan haka nakeson gyara gobena da goben 'ya'yana da dukkan ahalina, inason sanin dalilinsu nama mahaifina hakan, inba hakaba bazan ta6a samun kwanciyar hankaliba”.
Nad'an muskuta domin gyara zamana, ina fad'in “shikenan, amma kabani lokacin please”
.
“Nabaki”. yafad'a yana mik'ewa tsaye.
Binsa kawai nayi da kallo, saiya kuma bani tausayi, dukda kasantuwar rayuwarsa cikin Rud'ani, hakan bai habashi zama kamilin mutum mai tarin Nutsuwa ba, gashi da sauk'in kai, saidai idan baka fahimceshi ba
neba, kamar yanda na kasa fahimtarsa a farko, saika masa kallon mai girman kai.
A gaba d'aya yinin wannan ranar cikin nazarin maganganun galadima na yisu, tabbas abotar Alhaji Mamman kurfe da Senator Halluru da Abbana abin dubawace, na shiga tunano
wasu abubuwa danaita karo dasu a d'akin Abbana ni da Munubiya, a wani time d'in da Innarmu ta sakamu masa wani gyaran d'aki, Wanda shine sanadin shigowarmu wannan cakwakiyar kuma, na dafe kaina saboda saramin d'in da yakeyi, motsin da d'an cikina yayine y
a sakani dafe cikin ina lumshe idanu, gaba d'aya kaina yana Neman kullewa, har a washe garin ranar haka naita fama da tunani, danma yana hanani, amma danaga ya matsa zan d'ora daga inda na tsaya, yanzu ma dazai fita aiki saida yamin gargad'i, yace na sauka
k'asa wajensu innarmu nayi hira, to kawai nace masa, amma yana fita ban fasaba, ganin lokaci na k'ara k'urewa saina d'auki waya na shiga rubuta massage mai tsawo dazan turama Munubiya.
Duk abinda takeyi a idon Galadima ne, tun d'azun yana lura da
dukkan motsita ta camera d'in daya ajiye a d'akin wadda koda wasa Munaya batasan da zamanta ba, ya murmusa tareda godema ALLAH, dan yasamu damar kamata a hannu, ta wannan hanyarce kawai zaiyi amfani da ita wajen samun abinda yake buk'ata ga Abbanta, dan Ab
ba yak'i bashi kowacce k'ofa dazai san wani abinda ya sakashi shiga wannan halin, alhalin yaga tarin damuwoyi a idanunsa, masu kuma matuk'ar muhimmanci a aikinsa.
Wayarsa tai 'Yar k'ara alamar Munaya na sarrafa wayarta, saurin saita abinda ya saka
mata a wayarta bata saniba yayi, harta gama typing ta tura sak'on akan idonsa, shiga yayi ya duba, saiyaga Munubiya ta turama sak'on, yay hanzarin bud'ewa. (Galadima ya had'a wani tarko a wayar Munaya batareda ta saniba, dukkan wani Abu dazai shiga wayart
a ko fita saiya gansa a wayarsa, ta wannan hanyarne yaga na yanzu, saimu bishi muga abinda Munayar ta rubuta to).
_“ ‘Yar uwata, tabbas Allurafa na shirin to no galma, anzo ga6ar da lallai yakamata mu sanarma Galadima komai akan abinda muka Sani,
danna fahimci lallai zatonmu yazama gaskiya, wannan sunedai ahalinnan da mukaga bayanai a Kansu, dukda nakula Abbanmu nasan basarwa, saidai bansan manufarsa tayin hakanba, bayan wannan itace damarsa ta k'arshe dazai yadda kwallon mangwaro ya huta da k'uda
, sweetheart minene shawararki? dan burina dana haife cikinnan auren contract ya k'are a tsakaninmu, domin babu alak'a kuma kenan, kinga nima na samu 'yancin kaina, nayin auren din din din kamar kowacce mace”._
Babu shiri Galadima ya mik'e tsaye, j
ikinsa har wani tsuma yakeyi, lallai anzo ga6ar Ashe, hasashensa yazama gaskiya kenan kokuma zai zama, tomi wad'annan yaran suka sani? kenan Munaya Nada dalilinta na yarda da auren su na Contract? Mi Muftahu ya Sani gameda Munaya dahar ya d'anata a gareshi
a matsayin tarko?, bayan shi yana nan yana ik'irarin yima Muftahu tarko da auren Munayar. Lallai kan yakula itama Munaya da 'Yar uwarta da Muftahu suna Neman zame masa RAINA KAMA.
Baifi mintuna 15 ba da tura sak'on da Munaya tayi, saiga Munu
biya ta kirata, duk Galadima yana kallo daga camera d'insa da kuma saitin wayarsa, dukda kuwa yana office ne, Munaya bata d'aga kiranba, saida ya katse sannan ita ta kirata, munubiya na d'agawa Munaya race, “Sweetheart kinga sak'ona kuwa?”.
“Na gans
a sweetheart, amma fa ni duk kin rikitani, kinga wata alamace data tabbatar miki ahalin Galadima ne?”.
“Munu, tabbas alamomi da yawa sun nunamin hakan, sannanfa shima yasan Alhaji Mamman k'afur fa, kuma kinga ai a takardarnan munga sunan Alhaji Mam
man k'fur d'in, gashi abokin Abbanmu sosai, nifa yau wlhy abubuwa masu yawa ya fad'amin game da sirrinsa, dukda kasancewarsa mutum mara yarda, duk dai da inaji a raina kamar ya fad'amin wani yankin sirrinsane danya bigi cikina be, amma ni wlhy tausayi guy
d'innan yake bani da gaske”.
Munubiya tayi murmushi daga can, cikin tsokana tace, “to ALLAH yabar k'auna dai, sweetheart”.
“ban ganeba, k'aunar mi zai bari?”.
“keda Galadima mana, ai soyayya kan fara da tausayine”.
“Mtsoow da
n ALLAH muyi magana mai amfani Munu, yanzu ya kika gani, danya rok'eni ALLAH akan nafad'a masa mina Sani, nikuma ina tsoron koba akansa d'in baneba Abbanmu yake cikin damuwar, karmuzo kuma muyi aikin Baban giwa”.
Ajiyar zuciya Munubiya ta sauke, ta g
yara kwanciyarta tana fad'in Munaya kodai mu sanar da innarmu ne kozata bamu shawara?”.
“kai amma bakida hankali yasin, sokike innarmu taci k'aniyarmu Ashe, zatace miyasa tun a farkon lamarin bamu sanar mataba, k'ilama tayi fushi, Dan nima wlhy ayanz
u ina ganin munyi wauta fa”.
“to komadai miye munrigada mun aikata. Yanzu mafita zamu nema, mizai hana ki rok'eshi inhar bashi bane kokin fad'a Dan girman ALLAH karya tada zancen kawai, yakuma rik'e mana sirrinmu, idan kuma zai taimakemune akan Wa
nda kema Abbanmu barazana da mutuwa ai kingani munsamu madafa muma, kinga dai yanda sukaso cin galaba wajen kashesa, wlhy Munaya jinake kamar kar Abbanmu su dawo k'asarnan”.
“Ni kaina tsoron dawowar tasa nakeji, musamman da jiya Yakuma maimaitamin,
shiyyasa kawai na Yanke shawarar mu fad'a masa, idanma ba shi bane saiya taimakemu wajen gano wanene”.
“to shikenan, sai naji yanda kukayi kenan, Yaya unborn d'inmu?”.
“gashi nan ya isheni da motse-motse wlhy, na k'agara ma ya fito na huta,
kema Yaya namu da lafiyarki?”.
Cikin tsokana Munubiya tayi dariya, “aikoya fito nanda wata shekarar Munafata wani ya Shiga sweetheart”.
“wlhy na kula bakida man kai Munubiya, sai anjima”. Munaya tafad'a tana yanke wayar.
Gala
dima daga can yay wani k'asaitaccen murmushi yana shafa Kansa da cije lips, ya koma jikin kujera ya lafe yanamai lumshe idanu.
👭
🤣
Galadima Kodai-kodai
🤫
************
Muna gama waya da Munubiya na sakko k'asa, babu kowa gidan dagani
sai su innarmu sai jakadiya, a falon k'asa na iskesu suna hira.
Jakadiya tace, “ranki ya dad'e kin fito?”.
Murmushi namata, ina fad'in “na fito jakadiya, ya k'ok'ari?”.
Tai 'yar dariya tana cewa “kuke fama da k'ok'ari ai, ALLAH dai ya
raba lafiya”.
Bance komaiba na zauna ina gaida Innarmu ta amsa tana tambayata ya jikin.
“da sauk'i” na fad'a kaina a k'asa, nace, “innarmu Abba fa? ko barci yakeyi?”.
“A'a sun fita ai shida Sauban tunda safe, zasuga likitansa daga nan sud
'an zaga gari”.
“Oh ALLAH ya dawo dasu lafiya to, zaisha yawo kam indai fita da Yaa Sauban ne”.
Dariya jakadiya tayi, tace, “ai mai sunan manya sai a hankaki, shibama ya gajiya”.
Inna tace, “a baya gajiya kam, ni ai birgeni yakeyi, b
abu ruwansa, sai tsokana da barkwanci”.
“Ai tamkar gadone abin nasu, dan mai martaba lokacin yanada lafiya, dukda kasancewarsa shugaba hakan baya hanashi barkwanci da mutane lokaci-lokaci, to hakama magajin gari yake, daga bayane shi sai nasa halay
yar suka canja, yazama shiru-shiru, amma shi mai sunan manya saibai canjaba kuma”.
Ina jinsu nidai bance komaiba, sai murmushi danake tayasu dashi kawai.
Mun dad'e a falon har su Abba suka dawo, masaukinsu ya wuce, Sauban kuma ya zauna muka cig
aba da hira, tashi innarmu tayi tabi bayan Abba.
Sauban ya mik'e yana cewa zaije ya watsa ruwa, itama sai jakadiya tashiga domin nunawa kuku abinda zai dafa, ganin haka natashi na nufi masaukin su innarmu.
Nakama handle d'in k'ofar zan mur
d'a tareda yunk'urin sallana sainaji muryar innarmu kamar tana kuka, “Haba Abbansu dan ALLAH ka sanarmin damuwarka, Yaya kana cikin matsala amma ka gaza fad'ama kowa?, tunda tafiyarnan tamu ta gabato ina lura dakai baka ko barcin kirki, sannan inajinka kan
a sambatu cikin mafarki jiya da asuba akan kozasu kasheka bazaka bayarba, shin wai minene? kuma su waye?, nidai tun bayan haihuwar su Munubiya na fuskanci kana cikin wata damuwa, amma kullum cikin k'ok'arin 6oyewa kake, bansan minene kake 6oyewarba, haba A
uwal, a tunanina yanzu munzama irin d'ayan da bazaka 6oyemin matsalaba kowacce irice, a nawa tunanin munkai bigiren raba farinciki ko sa6aninsa, ko kasan ranar da muka fita da dasu Samha naga lokacin da wani bak'in mutum yazo kuka ke6e gefe, kana kuma maga
na tsakaninka dashi cikin fushi”......
A rikice naji Abba ya katseta da fad'in Ai'sha kenan ido kike sakamin ban saniba?, dan kawai kin ganni da mutum saiki fassara da wani Abu, Toni banma sanshiba, dan kawai ya ganni bak'in fatane shine yake t
ambayata, amma daga hakan babu komai, tunba yanzuba kikemin tambayar mike faruwa ina baki amsa
babu komai, miyasa bazaki yarda babu komai d'inba, ni nama matso da tafiyar tamu baya, dan doctor yakuma tabbatarmin da babu wata sauran matsala, ki sanarma Muna
ya ta sanar da mijinta gobe zamu koma kawai”.
“gobe kuma Abbansu?”..
A fusace yace “eh!”.
Ni kaina saida na razana da tsawarsa naja baya daga jikin k'ofar, da sauri nabar wajen jin alamun za'a bud'e k'ofar, tabbas akwai abinda Abbanmu
ke 6oyewa da gaske, to wanene bak'in fatar da innarmu tagani tare da Abba ranar? a ranar tare dasu muka fita, saidai sun rigamu tafiya, saboda ni da Galadima mun biya asibiti wajen awo, saida akamin sannan mukabi bayansu, kenan kafin muje abin ya faru? da
n tabbas na tarar Abba baya cikin walwalarsa, harna tanbayesa ko jikinsa ne? Amma yacemin a'a kansane kawai ked'an ciwo.
Bansan na iso bedroom d'inmu ba saboda zirfi danayi a tunani, ko hawan benen ma bansan nayoba, juyowa nayi da sauri saboda jin
an kama hannuna. ganin Galadima saina rajaza zanyi baya, da sauri ya rik'oni da k'yau yana fad'in “Nutsu mana”.
Da k'yar na tattaro nitsuwa ta, shikuma ya zaunar dani gefensa, hawayrne suka shiga ziraromin a kumatu, Abbana yana cikin matsala, amm
a wani dalili ya hanashi fad'a, takai har inda yake jiyya ana bibiyar rayuwarsa kenan?.
Ido Galadima shidai ya zubamin, bai hanani kukanba baikuma tambayeni dalilin yinsa ba, kusan 5minutes sannan ya kwanto da kaina jikinsa, jina a k'irjinsa saina f
ashe da sabon kuka, nanma k'ala bai ceminba, yadai cigaba da bubbuga bayana alamar lallashi, saida nayi mai isata nayi shiru sannan ya d'agomin kaina, dukkan kumatuna ya rik'e cikin tafin hannunsa, Kafin yay k'ok'arin saka idanunsa cikin nawa, cikin k'asai
tacciyar muryarnan tasa mai kama da anmasa dole yace, “Haba yalla6iya, sokike ki haifamin abin cikin kwan mai saurin kuka irinkine wai shin?”.
Bansan Sanda murmushi ya su6ucema fuskata ba, na lumshe idanuna saboda bana da jimirin jure kallon da yake
min, shima murmusawa yayi, sannan yakai fuskarsa dab da tawa yana huramin iskar bakinsa a saman ido.
Ban iya hanashiba kusan mintuna 2 sannan ya daina, bud'e idona nayi nad'an kallesa, ya d'agamin gira yana fad'in, “ya dai?”.
Cikin tunzuro bak
i nace, “babu komai”.
“To miye abin jin haushi daga tambaya”. ‘yay maganar yana sakin kumatuna’.
Binsa nayi da kallo, ganin zai