Showing 372001 words to 375000 words out of 407268 words

Chapter 125 - Raina Kama COMPLETE

/>
Kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru yana kallon Munayar da kanta ke a duk'e tana kuka har yanzu.....

“Ba kallonta nace kayiba, amsar tambayata nake buk'ata”.

Zamansa ya gyara a sanyaye yace, “Momma

ku gafarceni, dama nasan duk daren dad'ewa wannan ranar saitazo, nasan nayi kuskuren aikata abinda Addinina bai koyar daniba, hakama al'adata idan taji zata k'yamaci hakan, saidai wlhy a wancan lokacin banida za6in daya wuce hakan, ban ta6a tunanin son wat

aba, damuwar mahaifina da ciwonsane kawai agabana, banta6a kallon mace dawata siga ta soyyayaba balle tunanin aure, dukda fad'a da kukemin akan nayi aure a kullum. Bayan jaridar nan ta fita saina shiga rud'ani da zargin an aikotane dama gareni, wannan dali

line yasani tunani sakawa a satomin ita Na ajiyeta harsai ta sanarmin wanene ya sata, amma sai Muftahu ya nunamin Sam hakan ba mafita baneba, dama kawai Na aureta, maganarsa ta sakani d'aukarsa mahaukaci, Dan haka namasa gargad'in karma ya kuma yinta, nida

i kawai a d'akkomin ita Na tuhumeta. Shikuma yace Sam bazai bani goyon baya bisaga wannan gangancinba, k'yalesa nayi da nufin zan nemo Wanda zaimin aikin. Saidai kuma Nureddin kawai gareni, shikuma a time d'in yana Italy. Kwatsam sai wani tunani yazomin a

zuciya da gamsuwa da shawarar Muftahu, Dan gaskiya yafad'amin, inhar wani yasan tana hannuna duniya zata d'auka abinda yafaru a jaridar nan gaskiyane Na aikata d'in, amma idan aurenta nayi bakin kowa zai mutu, inada kuma ikon sata tayi komai takuma sanarm

in Wanda ya sata. Wannan ne dalilin dayasani bincike akanta, har nasamu aka d'akkomin ita Na sanar mata buk'atata. Da farko k'in abincewa tayi, amma daga baya bansan dalilinta Na amincewarba. Wlhy Momma kinji Na rantse ban aureta dannaci zarafinta ba, kuma

harga ALLAH banso kutse cikin mutuncintaba, wlhy Muftahu ne ya zuba mana pills a hollandia muka sha, ALLAH kuma ya k'addara zuwan yarannan ta wannan silar, tundaga randa Na aikata mata abinda babushi acikin yarjejeniyarmu nayi nadama, nakuma gane kuskuren

a, tunkuma a lokacin nafara tausayinta, tsakanina da ALLAH badan Na amfanu da itaba Na aureta, saidai nasan koda fad'a mata nayi bazata aminceba, zata d'auka bisa wancan dalilinne nace ina sonta, amma nasha nuna mata inason nata, saita dunga sharewa, bansa

niba ta fahimcenine kokuwa bata fahimtaba, wlhy Momma tsakanina da ALLAH nakeso Munaya, kuma nayi nadamar aikata abinda Na aikata, na tabbatar bazanma ALLAH wayoba, ikonsane ya aikata yanda yaso a lokacin dayaso d'in”.

Momma tayi murmushinsu na m

anya tana kallon Munaya, “Na fahimceka Muh'd, amma adalci d'aya zan maka bisaga wannan gangancin naka, adalcin kuwa shine ka saki Munaya a warware auren Contract, saika koma ka kuma Neman aurenta na gaskiya ga iyayenta, ka kuma sanar musu mika aikata musu

a farko, kanemi afuwarsu, shima takawa da mai martaba kaje ka sanar musu abinda ka aikata, nikuma namaka alk'awarin zan tsaya maka wajen ganin dawowar Munaya gareka”.

Kasak'e yay yana kallon Momma da wannan tsarin nata, toshi mahaukacine dazaiyi wan

nan gangancin? Ai kowane irin hukunci zai d'auka amma banda na saki wlhy.

“wai kobaka jini bane?”. Momma ta katse masa tunani.

Narke mata fuska yayi tamkar zaiyi kuka, “Haba Momma Dan ALLAH, yanzunan dakanki kike fad'ar haka? Nidai kimin du

kkan hukunci dakikeso amma wlhy banda na saki, bazan iya aikata wannan gangancinba, nayi kuskuren farko amma na biyu kam yana dai-dai daku rasani baki d'aya, wlhy inason matata ina k'aunarta har cikin raina, ni na amince zanje nasami su Abba da papi na san

ar musu, nakuma nemi afuwarsu amma banda maganar saki please ”.

Shiru Momma tayi tak'i tanka masa, saikuma yabama Munaya tausayi, ita dama burinta ya amince yayi kuskurenne.

Haka yaytama Momma magiya amma tak'i tanka masa, shikuma ya nace.



Saida Momma ta tabbatar yayi ligif sannan tace, “To ga adalci na biyu tunda ka nace, idan Munaya ta amince ni banida matsala ai, nabaka minti goma kacal zanje na dawo”.

Tashi Momma tayi ta fita tana gumtse dariya, saida ta fita tayita sosai, dama

akwai randa Muh'd d'inta zai risina irin haka akan mace, Muh'd dazai aikata laifi bada hak'uri ya gagaresa koma yafi Wanda yayma laifin zuciya da fusata, itakam babu abinda zatace da ALLAH sai godiya, Munaya tagama mata komai data zama sanadin canjawar yar

onta mai masifar tauri da tsauri.

A d'aki kam Momma na fita Galadima ya sakko k'asa wajen Munaya, matsawa tayi baya, ya bita, takuma matsawa, yasake binta, sai kawai ta saka masa sabon kuka.

Kansa ya dafe yana fad'in “O ALLAH, Munaya ple

ase and Please kiyi hak'uri, nasan nimai laifine amma ki gafarceni, wlhy tun kwananki biyar kacal dakikayi a gidana nayi nadamar aurenki ta sigar yarjejeniya”.

Cikin kuka Munaya tace, “saboda kashiga mutuncina ba”.

Huci Galadima ya furzar, “

Haba Munaya yakike fad'ar haka? Ke shaidace dagani har ke babu mai nutsuwar banbance wani Abu a waccan ranar, sai wahaltuwa da mukayi muduka, wlhy kinji namiki rantsuwa badan na lashi zumarkiba nafara sonki, a lokacin nadamar auren contract da mukayi nayi,

amma soyayyarki tafara tsiro da yad'one a zuciyata tamar yanda tushiyar bishiya keyi, wasu k'yawawan halayyarkine suka jani a k'aunarki, rashin tsoronki da d'aukar raini, dukda kasantuwata a gidan dana fito baki amince na takaki yanda nasoba, hakan ya tab

batar min bak'ya cikin mata masu kwad'ayi dason wani Dan d'aukakarsa ko dukiyarsa, yawan ibadarki ya tabbatar min da tarbiyyarki, babbar mallakata da kikayi shine damuwa da ciwon mahaifina, wannan Ce babbar hanyar dakika cusan k'aunarki cikin sauk'i, Munay

a kin bada gudunmawa a arayuwata wadda bazan ta6a mantawa da itaba, aduk lokacin da raina ya 6aci kafin shigowarki rayuwata nakan azabtu da motsawar ciwona, na fita hayyacina, bana sauraren kowa sai damuwata, amma kece kika canja wannan matsalar tawa ta k'

yak'yk'yawar siga, cikin hikimarki da ilimin da ALLAH yabaki, da kasancewarki mai tarbiya, Dan kowanne tsuntsu da gaske kukan gidansu yakeyi, nasha gwadaki akan abubuwa daban-daban amma kina cinye wannan gwajin nawa saboda zuciyarki a tsarkake take, please

ina rok'onki a karon farko ki yafemin, kiyi hak'uri kiyi hak'uri kiyi hak'uri, nimai laifine amma mai nadama, tabbas zanji ciwon wani ya k'ulla alak'ar aure da Samha ma ba Amaturrahman ba ta sigar dana k'ulla dake, amma wlhy inhar kince naje gabansu Abba

na sanar dasu komai zanje, nidai karki bari aurenmu ya girgiza koda da igiya d'ayane, namiki alk'awarin samuna fiyema da yanda kike tsammani matata”.

Idanu Munaya ta d'ago tana kallonsa, ya jinjina mata kai da lumshe idanu alamar tabbatarwa.



Batace komaiba ta maida kanta k'asa.

Hanunta ya saka anashi yana matsawa, a marairaice yace, “Kokinason Muhammad Sameer yamiki kukane Munaya? Sannan ki yarda nayi nadama? Wlhy nayi nadama da gaske”.

Jikinsa kawai ta fad'a takuma sanya masa wani

kukan, shima ya rungumeta yana sakin wasu mugayen ajiyar zuciya, jiyake kamarma ya had'iyeta gaba d'aya ya huta, suzama abu guda d'aya kawai.

Momma dake bayansu tashiga tafi tana takowa cikin d'akin. Da sauri Munaya tabar jikinsa tana 6oye fuska, s

hikansa Galadima yaji kunya, yay k'asa da ido tana murmushi.

Momma ta zauna tana fad'in “Alhmdllh ya Ubangijin talikai na gode maka, ALLAH ka d'orar da wannan zama har'a aljanna”.

A saman la66a Galadima ya amsa da amin. Munaya dai kunya ta hana

ta kallon kowa.

Momma tace, “Nima yau zan sanar muku abinda baku saniba”.

Daga Galadima har Munaya kallonta duk sukayi.

Ta gyara zamanta tana murmushi. Tace, “Tun farkon Aurenku nasan komai”.

Da mamaki duk suka kalli juna sannan

suka maida kallonsu ga Momma.

Murmusawa takumayi, “Lokacin da Muh'd ya yarda zai auri Munaya amatsayin auren contract Muftahu ya sameni ya sanarmin komai, danshi burinsa Muh'd ya Auri Munaya ne aure na gaskiya tamkar kowa, a lokacin kuma yasan cewa

r Gimbiya Zulfa itace ta saka aka muku wannan 6atancin, domin 6atama Muh'd suna, abinda yasa Munaya ta shiga matsalar ranar da kuka had'u a filin idine, shikuma Erfan dayazo miki da suna Fu'ad an sakashi sakama Muh'd idone, saikuma ya ganku tare, duk zaton

sa akwai alak'a a tsakaninku shiyyasa yayta bibiyar lamarinki harya kaiku plaza, saidai kuma ya rikice yagaza banbanceku lokacin daya fahimci sewar Ku y'an biyune, shi Muftahu a lokacin bazai iya tunkarar Muh'd da ainahin gaskiyar abinda ya saniba gameda G

imbiya Zulfa da Harun, shiyyasa yayta cusamasa ak'idar aurenki a zuciyarsa, Dan aganinsa hakan zai girgiza zuciyarsu gimbiya zulfa, maybe su aikata abinda Muh'd zai iya farga dasu, ammashi sai rashin yardarsa ta tsiya ta hanashi aminta dake kanki. Gudun ka

rta kwa6e agaba yasaka Muftahu zuwa ya sanarmin komai, yakuma fad'amin nagartarki data ahalinki, ya tabbatar min sai kowa yayi alfahari dake acikin masarautarnan, dansu suna ganin idan Muh'd ya auri y'ar talaka zai k'ask'anta bazaiyi sarauta ba, sun manta

ALLAH shine mai komai da kowa. Muh'd yanada tausayi sosai Na tabbata inhar wani Abu ya shiga tsakaninku bazai ta6a sakinki ba, wannan dalilin ya sakani bama Muftahu pills ya saka muku, Dan ta wannan hanyar ne kawai zaku iya zama Abu guda”.

Munaya d

a Galadima duk suka kalli Momma da mamaki, saikuma sukayi k'asa da kai saboda kunya.

Murmushi Momma tayi. Tace, “Yes nice nabashi danna kafeku a waje d'aya, nakuma san Munaya zata iya bore akan ka saketa, shiyyasa a washe garin faruwar abin nasaka k

a tilas ku taho nan, wannan shine mataki na biyu, mataki na uku saka Munaya tak'i kwantar maka dakai dannasan halinka da bak'in rashin yarda Muh'd, wannan na kula itakuma bata d'aukar saita kwana, shiyyasa abin yamin dai-dai, nadad'e da fahimtar son dakake

mata, amma na shareka harsai ka gano dakanka ka fad'a mata. Cikin Munaya shine babbar ribar danaci, wadda nakema ALLAH godiya akowace dak'ik'a ta rayuwata, nake kuma jin k'aunarta har cikin jinina, badan na rabaku na rik'e Munaya ba, nayine dama danna tab

batar da nadamarka, itama ta kuma tabbatar da lallai da gaske kana k'aunarta, ta daina kokwanto a ranta, ALLAH yayi muku albarka, ya k'ara baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba, yabama Sauban mace tagari shima irin Munaya, itama Haneefa yabata miji nagari k

amar mijinta daya bar duniya koma Wanda ya fishi, jikata Samha itama ALLAH yabata miji nagari Wanda zai rik'e mana ita”.

Atare muka amsa da amin.

Galadima zaiyi magana Momma tace, “kaga d'auka matarka ku tafi dare yayi, da safe ma k'arasa, ni

kam barci nakeji”.

Kunya ta kama Galadima da Munaya, amma Momma saitayi tamkar batasan sunaiba.

Tamkar munafukai haka suka mik'e sum-sum suka fice a d'akin, yanda basuyi yink'urin d'aukar yaro ko d'ayaba haka Momma bata tuna musuba itama

🤣👍

🏻

...................



🏻

*_Masoyan Raina kama amin afuwa dajina shiru, wlhy abubuwane sukaimin yawa, amma Alhmdllh yanzu nafara daidaita, kuma zanyi k'ok'arin gamawa nan kusa da izinin ALLAH, ina muku barka da salla baki d'aya, inakuma jiran naman layy

a

😅🤸🏻

‍♀

🤸🏻

‍♀

._*

_wad'anda suka tura hoto kuma Na yafe muku wlhy har zuciyata, wancan write up nayisane lokacin raina a matuk'ar 6ace, yanzu kuma Na huce

😅

, nayi HAK'URI bisa koyarwar manzon ALLAH, Maman Haneefa ngd kema sosai ALLAH yabar zu

minci, yakuma yafe mana baki d'aya, dama raina ya 6acine saboda bansan iya inda hotunan zasu kaiba, idan wani ya gani da k'yak'yk'yawar zuciya wani zai iya munanani ta mummunar hanyar dabanjiba ban ganiba, duk mace tagari bazataso pictures nata suke yawo a

social media ba, musamman ma mai aure, kobaka da aure mace darajane da ita, saikuma mutunta kanka ALLAH zai kareka, masu ganin Abu kuna yad'awa jikinku Na rawa kubari wlhy, kokad'an hakan bashida k'yau, Dan kuma bazakuso hakanba, ALLAH ya k'ara mana hak'u

ri baki d'aya._

👏🏻😘😘

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*

😭👏🏻

*_typing

📲

_*



💡

*_HASKE WRITERS ASSO....._*

*_



RAINA KAMA.....!!



_*

_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*



~Book 2~

👉🏻

2



8



............A yanda Na kula har yanzu bayajin dad'in jikinsa, dan komai a d'an wahalce yakeyinsa, koda ya fiddo kayan daga wardrobe saiya dawo bakin gadon ya zauna ya dafe Kansa, kallonsa nayi cikin damuwa nima, Na cire Abdurraheem

Na kwantar, sannan Na mik'e zuwa garesa, durk'usawa nayi Na d'ora hannayena akan gwiwarsa, “yalla6ai lafiya?”.

Shiru yamin kusan minti 1, harna fidda ran samun amsa ma na yunk'ura na mik'e da nufin barin masa d'akinma duka.

Hannuna ya rik'o,

na juyo na kallesa, har yanzu yana yanda yake baiko d'ago motsa ba.

Na cije lips ina had'iye kukan dakeson zubomin, rayuwar nan tasa bana sonta wlhy, ni y'ar dangi Ce, nariga natashi gidan yawa, dukda gidanmu bahagon gidane mukanyi hira koyayane, amma

shifa magana ma idan bai ra'ayiba wahala take masa, Abu na damunsa a rai amma bazai iya fiddashi yaji sauk'iba, Momma ta had'ani da aiki, a watannin baya kad'an kamar yafara canjawa, amma gashi yakuma birkicewa yanzu, tayaya Momma take tunanin zan iya can

ja Galadima? murd'ad'd'en mutumne shi mai wahalar sha'ani, ga tsantsar mulki da k'asaita da suka zama jinin jikinsa, s.........

Tunanina ya katse lokacin danaji an jawoni, nai firgigit saboda fad'awa danayi jikinsa, shikuma yay baya ya fad'a kan g

adon, kad'an ya rage mu danne Amaturrahman, yad'an kauce kad'an yana sauke ajiyar zuciya.

Uffan bai ceminba ya maida idonsa ya lumshe.

Mamakin wannan lamari ya kamani, hannu yasaka ya kwantar da kaina a k'irjinsa yana d'an buga bayana da d'ayan

hannun, zanyi magana ya d'ora yatsunsa hannunsa uku na tsakkiya akan bakin alamar nayi shiru. banida za6in daya wuce yin shirun, nabisa yanda yakeso.

Yanayin da zuciyarsa ke bugawa sai yabani tsoro, na saka hannuna na danne wajen sannan na d'ora

kaina bisa hannun, ajiyar zuciya yayi yana cizar lips..

Tsawon mintuna 3 muna a haka, har knocking d'in k'ofa akayi amma baiko motsaba bai barni na motsaba, na yunk'ura zan tashi ya maidani.

Munkai mintuna 7 sannan ya zameni ya kwantar ya mi

k'e zaune, batareda ya kalleni ba ya sauka daga gadon, bathroom ya Shiga, babu dad'ewa ya fito, nidai kallonsa kawai nake da mamaki, Dan fuskarnan amatuk'ar d'aure take tamkar baisan minene dariyaba a rayuwarsa, ya shinfid'a abin salla, domin rama sallolin

da suka riskesa yana barci.

6oyayyar ajiyar zuciya na sauke, na tashi zaune idona akan yaran, duk sun koma barci, na tsurama Abdurraheem ido, saboda fitar numfashinsa ta banbanta dana y'an uwansa, tunani nai ko yanayin nasa barcin kenan shikuma, s

aboda wahalar da suka sha,

d'aukar ledar kayan da mom ta kawo nayi, na fiddasu na saka, ban jira ya idarba na fice abina.

Nayi mamakin da yanzu babu kowa, harsu Munubiya sun tafi, haushi ya kamani kamar zanyi kuka, aidai sa jira na fito mu

gaisa ko? hawayen da suka zubomin a kumatu na share, namafi jin haushin Munubiya wlhy.

Sallamar da akeyi na amsa da k'yar, sannan na bada izinin shigowa, cikin bayina ne guda biyu, zubewa k'asa sukayi suna gaisheni.

Cikin girmamawa d'ay

a tace, “dama ance mu gani idan kin fitone”.

Nace, “Hummm”.

Fahinmatar iya amsar dazan iya basu kenan ya sakasu mik'ewa suka fita, zamewa nai na kwanta cikin kujerar ina cigaba da zirar da hawaye.

Kusan mintuna 5 saiga Samha ta shigo, ta

durk'usa gaban kujera tana sharemin hawayena, d'ago ido nayi na kalleta, namata murmushin k'arfin hali ina tashi zaune.

Muryarta da alamun tasha kuka itama tace, “Aunty Uncle Sam na kiranki”.

Kai na jinjina mata kawai, na tashi gaba d'aya na d'

auki mayafi muka tafi tare.

Koda mukaje k'ofar falon bata Shigaba, nikad'ai na Shiga ita kuma ta juya ta fice daga sashen gaba d'aya.



A falo na iskeshi cikin doguwar kujera a kwance, ya kifa yaron d'aya a k'irjinsa Wanda nake k'yautata z

aton Abdurraheem ne, wayace manne a kunnensa, amma a hankali yake

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login