Showing 192001 words to 195000 words out of 407268 words

Chapter 65 - Raina Kama COMPLETE

“miyasa kake kokwanto? inhar zaka kasa gaskatani a nan bai kamata ka aminta da zancena Na farkoba kenan?”.

Ya murmusa yana fad'in “kozaki gaji Abba ne?”.

Nace, “akan me?”.

“jaridanci mana, naga kin shahara waje

n iya bincike”.

Mik'ewa nayi saboda k'afata tafara yaamm alamar jinina yana buk'atar motsawa, nafara d'an takawa. hannaye kawai ya hard'e a k'irji yana bina da kallo, saida nad'an zagaya d'akin kafin nabashi amsa da fad'in “yalla6ai kasan wani Abu kuw

a?”.

Kansa ya girgizamin kawai.

Nace, “humm nifa nan daka gani, kwakwalwata tana aiki fiyeda yanda kake aiki da agogo”.

“really?”.

“baka buk'atar jayayya”.

Ya d'aga kafad'a yana ta6e baki, “hakane kuma”.



Sha

resa nayi na zauna a bakin gadon danna d'an mik'e, a haka najawo filo na kwanta k'afafuna a k'asa.

Tasowa yayi ya dawo ya zauna saman k'aramin table d'in gaban sofa, jinai kawai ya kama k'afata ya d'ora saman cinyarsa yana matsamin a hankali.



Da mamaki na d'ago kai na kallesa.

Ido d'aya ya kannemin yana d'an ta6e gefen bakinsa, ya maida kallonsa ga k'afar.

Sabon salo, na fad'a a raina. a fili kuma nace, “yalla6ai kaine......”

Bai bari na k'arasa ba yay saurin fad'in, “ba dole

na taimaki lafiyar abin cikin kwan ba”.

Harara na dalla masa ina janye k'afata, ya kalleni da mamaki, “ya haka? ko haushi kikajine?”.

“miye zai Sani jin haushin? saika bari idan yafito duniya ka matsa tashi k'afar”.

“oh ni Sameer na

ga ta kaina”.

“zama kaga ta k'afa bata kaiba, Sunan nakama bazaka iya fad'arshi da r ba”.

“oh nan kuma kika dawo?”.

Matsawa nayi baya saman gadon sosai batareda na bashi amsaba. shima saiya taso ya hawo gadon, hakan yasani yunk'urawa

zan sauka na bar masa, fan nasan hawan nasa bazai haifar da d'a mai ido ba, yasa hannu ya rik'eni, “yalla6iya ai saikin maimaita mikika fad'a dalla-dalla”.

“lah wasafa nake maka, kaga rigar wankace a jikinka kaje ka cire kar mura ta kama ka”.



“Ai kinga dai-dai kenan”. Yay maganar yana k'ok'arin kwance igiyar rigar.

Hannunsa nayi azamar rik'ewa ina marairaice face alamar yaji tausayina.

Baki ya ta6e yana ture hannuna, na kuma k'ank'ame nasa nak'i bari. Murmusawa yayi, ya kwanto

gefena tareda sakani jikinsa ya rungume.

“Nace please wankama zanyifa, zafi nakeji”.

Maidani yayi ya kwantar, cikin kunnena yace, “kedai fad'i gaskiya, ko kina son a.......”.

Rufe bakinsa nayi da tafin hannuna ina kukan shagwa6a, ya s

higa k'ok'arin cirewa amma nak'i bari, shi dariyama na bashi, irin wannan hak'ilo haka. duk yanda yaso na barsa k'i nayi, saida barci yafara fisgata hannun ya zame.

Kansa ya girgiza kawai yana murmushi, a fili ya furta “mai bakin tsiwa”. Ya k'are ma

ganar da sumbatar goshinta yana gyaramata kwanciya a jikinsa.

Ya tsira mata idanu yana kallon yanda take fidda numfashi a hankali, a zahiri idonsa a kanta, amma zuciyarsa maganganunta taketa cud'awa, shi baima ta6a ganin mace yarinya k'arama mara

tsoro da shiga rikita-rikita irinta ba, bata gudunma shiga had'ari? ya sauke ajiyar zuciya yana tashi zaune, k'afafunta

yashiga mammatsa mata a hankali, aikam harda gyara kwanciya su madam munaya, yad'an murmusa, yasan ko'a d'azun tanaso fa, amma iyayi ya

sata hanashi ya mata. Ya d'auki tsawon lokaci yana mammatsa mata jikinma gaba d'aya, yayinda zuciyarsa kuma ke tattance bayananta dalla-dalla, daga k'arshe sauka yay daga gadon ya fice zuwa d'akin sirrinsa, duk abinda tafad'a yasamu sabon file ya bud'e mas

a, baya wasa da evidence komai k'ank'artarsa, balle ma nata ya wuce Na wasa, ya dad'e yana rubuce-rubucensa kafin ya koma kan Computers, sunan SD kawai ta ambata masa, dan haka yafara searching gameda SD d'in kawai, babu abinda ya fahimta akan hakan, dama

baiyi tunanin fahimtarba, waya ya d'auka ya kira Nuren, bayan sun gaisa yace, “Nureddin acikin yaransu Tanderu kasan SD?”.

“SD! SD! kai anya kuwa? amma dai ina zuwa bani mintuna 30”.

“ok saina jika”.

Galadima Na yanke wayar ya nemo numb

er d'in Abba da bakowa ya sani d'innanba yafara aiki a kansa, dukkan Contact d'in ciki suka bayyana, d'aya bayan d'aya ya dinga binsu yana nazarin adadin kiran da aka ta6ayi, sau nawa aka kira Abba sau nawa ya kira shima? Mafi yawa ma kiransu yafi yawa, ya

d'an murmusa yana wasa da tsinken hannunsa a kan la66a da nazarin yanda zai 6ullo musu, dan duk hanyar daya kamata yayi bincike an d'auki mataki a kanta, tsawon lokaci bai fahimci komaiba, sai zuwacan wata dabara tafad'o masa, nutsuwa yay yana sarrafa Comp

uter's d'in cikin tsantsar kwarewa da gwaninta, ya kafa musu tarko ne a wayar innarsu Munaya, dan ya tabbata watan watarana zasu iya kira ko sak'o, amma abinma haushin saiya iske wayar inna a kashe, ya dafe kansa, saifa da yacema dady aringa barin wayar a

kunne.

Babu shiri ya d'auki waya ya kira daddy, bayan sun gaisa yaymasa maganar kunna wayar innar. cikin mamaki Dady yace, “ai a kunne take koda yaushe, Change ma baya k'arewa nake kuma sakata, idankuma zan zo nan nakan sanarma Jafar shima ya kula, a

mma ina zuwa dai”.

Galadima ya amsa da to, amma k'asan zuciyarsa tana mamaki. babu dad'ewa Abba ya sake kiransa, “Ashe Change ne ya k'are babu dad'ewarnan ban lura ba, amma gashinan Na sakata”.

“to Dady, Na gode sosai”.

Sunayin sallama da

Dady Kiran Nuren Na shigowa, d'agawa yayi, Nuren yace, “inagafa brother hanya d'ayace dazata saka musan shi wanene SD d'in, dan abinda Na lura dashi baya amfani da hakan ta kowanne fanin yanar gizo, maybe da full name yake amfani. yanzu zan sayi ticket in

sha ALLAH zanje domin bincika a wajen Malam Saminu, nasan ya magantu yanzu, zai amsa mana dukkan tambayarmu”.

“ok hakan yayi, idan ka fahimci bai saniba karka takurashi, ka binciki yarinyarnan itama, koma ka fara bincikarta dan ita bama wayo ta cikab

a sosai, k'ila kafi samu cikin sauk'i a wajenta, abinda yasa Malam saminu baison fad'ar komai, babbar 'yarsa cikin 'ya'yan Alhaji balala wani ya mata ciki, kuma sun dai-daita akan idan ta haihu za'ama yaran aure, wannanne yasakashi tsoron fad'ar komai, da

n karya lalata waccan alak'ar, dan tabbas yasan yana fad'a auren bazai yuwuba, to nima banason shiga hak'in kowanne ahali akan aikina, shiyyasa nabashi dama kaga bankuma waiwayarsa ba, yanzu haka yarinyar ta haihu kwana hud'u kenan, amma shi yaron ya kawot

a nan Dubai ta haihu ne, a nufinsu bayan haihuwar da sati d'aya zasu dawo Nigeria a d'aura musu aure sannan su dawo Dubai d'in, dan Alhaji balala baya son abinda zai 6ata record d'insa, kuma

mamar yaronce ta Dage sai anyi auren dan ita mutuniyar kirkice, d

an haka mu bama Malam Saminu wannan damar”.

Ajiyar zuciya Nuren ya sauke, cikin mamaki yace, “duk ya akayi kasan wannan brother? ”.

galadima ya murmusa, yana fadin “Nuren kenan, to bara nayi copy d'in my mata, kwakwalwata tana aiki fiyeda

yanda kake aiki da agogo, nasha fad'a maka bada kwanji kawai ake yak'i ba, sai anhad'a da dabarun tunani dana nazari, so kad'an nafad'a maka daga abinda ya shafi Malam Saminu, kaidai saina jika kawai, a time d'in da zakuyi maganar ka tabbatar ka had'a Comm

unication dani ok?”.

“babu damuwa aljanin munaya”.

Dariya sosai Galadima ya shiga tuntsurawa da iskancin Nuren, wato shima ya maida Aljani yau, wlhy yaronnan yagama rainashi, wai Aljanin Munaya, d'an iska zan kamaka ai.

Kashe ko

mai yayi ya fito daga d'akin, bai koma cikiba saiya sakko k'asa, ya iske Sauban kad'ai a falo, shima shigowarsa kenan daga asibiti yake.

Galadima ya zauna yana fad'in “jirgi sarkin tashi daga ina?”.

Dariya sauban yayi, yace, “kai Yaya, nine

kuma jirgin?”.

“Kamafi jirgi ai. Wane shiri kakeyi gameda zuwa bautar k'asarka Nigeria”.

Sauban ya 6ata fuska kamar zai fasa ihu “yaya yanzu fa ca za'ayi saina koma 9ja har zaman 1year?”.

Hararsa Galadima yayi, “to zakayi anan k'asa

r ne?”.

“Ni Yaya ALLAH da anayi da nayi, a manta da bautar k'asar kawai mana, nayi joining masters d'ina”.

K'aramin tsaki Galadima yayi, yay crossing k'afarsa yanama Sauban wani kallon bammasan amsar dazan bakaba, saida ya d'auki wasu mi

ntuna sannan yace, “rashin yin ai bazai zama matsalar kowaba sai taka, bakuma zaka gane hakanba sai nan gaba idan ALLAH ya kaika inda bakayi zatoba, idan kace bazakayiba it's better, nidai ai nayi nawa ko. tashi kabani waje”.

Ganin ransa ya 6aci Saub

an ya marairaice fuska zaiyi magana, amma sai Galadima ya d'aga masa hannu, sannan yamasa nuni da k'ofa alamar ya fice masa.

Fita Sauban yayi yabarsa, shifa tsakani da ALLAH zaman masarautar ne baya son yi shi kad'ai.

Galadima ya girgiza ka

i kawai yana fad'in “ALLAH ya shiryeka, gata kasamu tunda katashi kaga komai basai ka nema ba”.

Jakadiya data fito ta rissina tana fad'in “Ashe ka shigo magajin gari, barka da dawowa”.

Murmushi Galadima yayi, yanason matarnan saboda halacci

n datake wa rayuwarsu, “yauwa jakadiya, ya gidan?”.

“lafiya lau Ranka ya dad'e, a shirya abinci ko?”.

Agogon dake tsintsiyar hannunsa ya kalla, sai kuma ya maida ga jakadiya, “bar abincinan jakadiya, akwai Inda zanje”.

“to ALLAH

ya dawo dakai lafiya”.

Hannu ya d'aga mata kawai sannan ya tashi ya fice. mashin ya hau yafita.

Abba dake can gefe a harabar gidan tsakanin wasu flowers yana hutawa ya sauke ajiyar zuciya, tundaga fitowar Galadima har hawansa mashin da fitars

a akan idonsane, rufe idanunsa yayi yacigaba da tunaninsa da tun d'azun yake zaune a wajen yanayi.

Asibiti Galadima ya nufa, yay kici6us da Aunty Mimi Na shirin tahowa gida ta huta, ta kalleshi da mamaki, “my k'ani dawowa kayi?”.

Gefen

girarsa yad'an shafa da d'an yatsa d'aya, “eh , ina zakije k?”.

“gida zanje nad'anyi wasu abubuwa”.

“ok sai kin dawo”. yafad'a yana ida shigewa, ita kuma ta fice.

Momma Na zaune tana waya da papi, ya zauna d'aya a kujerun yana kallon

ta cikeda sha'awa, uba da 'Yar sun birgeshi, juyawa yay ya kalli gadon Abie, barci yakeyi, har Momma ta gama wayar ison Galadima Na kan Abiensa ko k'yaftawa bayayi, shi kad'ai yasan mi zuciyarsa take sak'awa.

“Muh'd daga ina haka?”. Maganar Momma

ta katse masa tunani.

Janye idonsa yayi daga kan abie ya maido ga Momma, “Daga gida Momma, har yanzu barcin Abie yakeyi?”.

“eh tunda ka Fita bai farkaba, mike faruwa naganka cikin damuwa?”.

Huci ya furzo daga bakinsa, zaiyi magana sai

kuma yayi shiru.

“Nifa tsiyata dakai kenan Muh'd, Yaya Abu nacin ran mutum bazai iya fad'ama kowa a taimakeshi da shawara ko addu'a ba, kaga yanda jijiyar kanka ta tashi kuwa? Haba Muh'd Sameer d'ina, kaifa yanzu ubane, girmanka ya k'aru, aringa r

age damuwarnan da miskilanci mana, ni ALLAH ma yasa ba haka kakema d'iyar tawaba?”.

“kai Momma”. ya fad'a amarairaice cikin 'Yar shagwa6a.

Murmushi tayi tace “to fad'amin mike faruwa?”.

Yay d'an tsaki, “Ni ai Momma bammasan ta in

a zan fara baneba”.

“kafara ta sama kawai”. Momma ta fad'a tana dariya.

Shima dariyar yayi kad'an sannan ya gyara zama, kuma maida muryarsa k'asa-k'asa yayi yana maganar ahankali, tsaf ya zayyanema Momma yanda sukayi da Munaya, ya d'ora da fad

'in “Amma kinsan wani Abu kuwa Momma?”.

“a'a saina fad'a dear”.

“uhm gani nake kamar bakomai ta fad'a minba, ta 6oye wasu abubuwan dai kamar, saidai bansan dalilinta ba.

Momma ta jinjina kai tana murmushi, “To Muh'd mizai hana kac

igaba da binta a hankali, nasan zata fad'ama sauranma, ni aganina kamar tana ganin kaima ka kasa yarda da itane shiyyasa tafad'i wasu tak'i fad'in wani, idan har ka yaba da hankalin matarka yakamata ka fara sakin jiki da ita wajen Neman shawararta da sakat

a cikin wasu al'amura naka Na tabbata itama zata fara fad'a maka nata”.

“gaskiya kika fad'a Momma, dan naga fa'idar hakan kwarai da gaske, zan kula insha ALLAH. ya addu'oin Abie akwai saura?”.

“saura kad'an, gashi bakuyi wasuba”.

“mai

k'arfin yince tazama sai a hankali, daga barci sai barci take yini”.

“ALLAH Sarki d'iyata, ai tanama k'ok'ari, dama idan ciki ya fara tsufa hakane, ALLAH dai ya sauketa lafiya”.

“To amin Momma”.

Sun cigaba da 'yan hirarrakinsu har zuwa

lokacin da Abie ya farka..................



🏻

*_inata gaisheku da yawa da yawa, comments naku Na sakani nishad'i over

🥰🥰🥰🥰🥰

😍😍😍😘😘😘

_*.

I love you wijiga-wijiga sister's

🥰🥰🥰🥰

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*

😭🤚

🏻



🏻

*_typing

📲

_*



💡

*_HASKE WRITERS ASSO....._*

*_



RAINA KAMA.....!!



_*

_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

~Book 2~

👉🏻

1



8





1



9



.................Na dad'e ina barci kafin

Na tashi, nayi mamakin ganina ni kad'ai, bansan time d'in da Galadima ya ficeba, sakkowa nayi daga gadon Na nufi Na watsa ruwa.

Ina tsaka da shafa mai Samha ta shigo, saida tayi sallama nabata izinin shigowa sannan, ledar hannunta Na kalla ina fad

'in “mikika samo mana 'Yar Uncle?”.

Cikin dariya ta zauna kan sofa tana cewa “kayan dad'i ne Aunty gimbiyarmu, alfarma nazo nema wajenki keda Uncle”.

Hankalina gaba d'aya Na maido kanta, “Alfarmar mi kuma?”.

“Aunty gimbiya ple

ase ki lalla6a Uncle ya barki muje birthday d'in k'awata Dhibya, ALLAH yarinyarnan tana sonki sosai, kullum hirarki”.

Nad'an zaro ido “kai Samha yaza ai naje wani birthday da wannan cikin? kuma kema kinsan bazai bariba tunda Na 'yammatane”.



“kai aunty, cikin saikace Wanda yayi wani k'ato, kumafa a cikin gida za'ayi wlhy, iyamu goma ne kawai”.

“to naji, ALLAH yasa ya bari, mikika kawo mana a ledar?”.

“yes my sweet aunty, wannan wani sari ne yamin k'yau a wani shagon da muk

e zuwa siyan kaya, shine nayi alk'awarin siya miki, Uncle Sauban ya cikamin na siya, yanzu Na kar6o please ki gwada muga”.

Dariya nayi, nace, “inye kaga 'Yar Uncle Anfara jink'an iyaye, to amma ni ina na iya saka sari?”.

“kowama koya yayi

nidai ki saka muga dan ALLAH”.

“to shike

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login