Showing 381001 words to 384000 words out of 407268 words
Wata y'ar dariya yayi, wadda tafi kud'i tsada awajensa. Yace, “My Heartbeat ALLAH kin iya haihuwa”.
Ba k'aramar dariya maganarsa tabaniba, aiko nashiga k'yalk'yalawa. Shiko ya shagala da kallonta saboda birgeshi da dariyar tata tayi, burinsa dama yaganta cikin farinciki.
Bayan na tsagaita da dariyar na kallesa Ina d'aga kai da kashe masa ido alamar
kallonfa?.
Mik'ewa yay tsaye ya dawo inda nake tareda rank'wafowa kaina yana dafa hannayensa biyu asaman gadon gefe da gefena. Kusancin namu yasakani d'anyin baya kad'an ina kallon cikin idonsa, yakuma matsowa, na matsa, yakuma again, Nina still na
matsa, saida na haye gadon sosai shima yay balance yanda yake buk'ata sannan ya kwanto gefena kusan Rabin jikinsa a nawa, har lokacin idonsa na sark'e da nawa. Galadima yay bala'in Sanin sirrin kallo, inhar ya sark'e idanunsa da nawa duk wani hope d'ina n
emansa nakeyi na rasa, yatsansa kawai naji saman la66ana yana zagayawa ahankali, santsin hannunsa Dana lips gloss d'in Dana sanya sunayin kamar susa, kasa jurewa nayi na lumshe idanuna a hankali.
Galadima ya murmusa da bud'e baki da k'yar yana fad'i
n, “Kin cancanta, kin cancanta zama matar Muhammad Sameer Munaya, ked'inki da dukkan halayyarki irinta Muhammad Sameer ke buk'ata ga matarsa, ko ayarda ko kar ayarda nasan nama sauran maza zarra, dan matata tafi ta kowa, kinzama fitila mai hake gabana da b
ayana, kinzamarmin bango abin jingina lokacin danawa yanemi rushewa, shigowarki rayuwata na dai-dai da farkawata daga nannauyan barci mai cikeda rud'ani, nabaki dukkan zuciyata ki jani a sannu danna cigaba da ribantuwa da ni'imomin da ALLAH ya azurtaki das
u, I love you so much Munaya, I love you har a aljanna matsayin uwargidan matana”.
Bansan lokacinda hawayen farinciki suka fara zirarominba, na bud'e idanuna dakai hannu saman kwantaccen sajensa ina shafawa a hankali, cikin wani yanayi nace, “Ka ca
ncanci fiye da haka mijina, dan kanada zinariyar zuciya, kaimai tarin tsoron ALLAH ne dabin dokokinsa, a wannan zamanin samin matashin saurayi mai kud'ad'e da mulki a hannunsa dabaya wata masha'a abune mai wahala, baka kasance mazinaci ba, baka kasance mai
shaye-shaye ba, ko sigari wannan bakasha, kulum cikin Neman halalinka kake Dason k'yautatama iyayenka dana k'asa da kai, kaimai ibadane, salla bata wuceka, mai yawan tsayuwar dare, mai yawan bitar littafi mai girma dake d'auke da zancen ALLAH ne, mai yawa
n sadaka da taimakon mutanen da bakuma had'a addiniba, bakada wata majalissa ta abokai daza'ace gaka cikin jerin masu cin naman wani ko zind'en wani, abinda ke gabanka da Wanda ALLAH ya halatta maka kawai kakeyi, mijina tayaya bazaka samu nasaroriba a rayu
warka? Ubangiji mai ni'imane ga dukkan Wanda ya ra6u samun ni'imar, babu wani Bawa dazai tsinci kansa a ta6ewa inhar yabi dokokin Ubangiji da koyi da manzon tsira, babu cuta mafi rad'ad'i da ciwo kamar bijirema Umarnin ALLAH Wanda ayanzu shike wahal da mat
asan duniya irinka, burunsu kawai su hole su mori k'uruciyarsu, sun manta babu tagomashi mafi k'yak'yk'yawan farashi irin morar k'uruciya bisa ga Umarnin ALLAH, yadda da k'addara, samu ko rashi, tsayawa matsayin da ALLAH ya ajiyeka, kaucema dukkan wata bad
'ala, matasa sune k'ashin bayan al'umma, lalacewarmu ta saka al'ummar tafiya a karkace a halin yanzu, da'ace zamu gyara da kowa ya mik'e, dolene Momma da Abie suyi alfaharin samun d'a irinka, dolene Aunty Mimi da Yaa Sauban suyi alfaharin samun d'an uwa ir
inka, dolene su Samha dasu Amaturrahman suyi alfaharin samun Uba irinka, dolene k'asarka da addininka yayi alfaharin samunka, saidai duk nice nafisu sa'a da alfaharin samunka a matsayin miji uban y'ay'ana, inaji inama y'ay'yana su gaji k'yawawan hallaya da
d'abi'u irinna mahaifinsu, saidai kash ina cike da fargabar tsoron kalmarnan ta bahaushe dakance *Bakowanne tauntsu bane ke raira kukan gidansu* wani tun a koyan tashi yake canja salo. Mijina ka more, ka matuk'ar morewa da k'yawawan hallaya, irinku kunada
tsadar samu a cikin al'umma, da mutane zasu gane dasun fuskanci ba k'yawun fuska dana jiki bane abin alfahari, zinariyar zuciya da hallaya shine abin alfahari da d'agawa, saidai kash, burin samarin yanzu da y'ammata k'yawun fuska dana halitta, nauyin alji
hun wayewa, basa tunanin mika tara mizaka taras, sannan mika barma bayanka da ahalinka Wanda ko bayan shekaru aru-aru tarihi bai Isa mantawa da kai ba, da inada dama sainabi matasan mata da maza dukna musu allura sunzama kamarka mijina, inasonka, ina sonka
, zan fad'a a hankali, nafad'a da k'arfi, na fad'a da kuwwa, na fad'a da ihu agaban kowa kuma, Kaine duniyar Munaya, Kaine farincikin Munaya, zanta k'aunarka har randa nufashina zaibar gangar jikina, nakumayi fatan ganina a cikin matanka dake aljanna Muham
mad Sameer”.
Kasa magana Galadima yayi, sai bakinsa ke motsi alamar buk'ar firta wani Abu amma yakasa, idonsa yacika taf da kwalla, lallai hikimar zancema baiwace ga mace tagari, dashi kawai zata iya mallakar mijita babu boka babu Malam, dan gashi Mu
naya tasamu dukkan nasarori, ya rungumeni tsam a jikinsa tareda d'ora bakinsa saman la66ana, hawayen dayake rik'ewa suka gangaro saman fuskata. Banyi yunk'urin ko motsawa ba nabashi wuk'a da nama yayi yanda yakeso ni halalinsace..........
😘👍🏻
*_Hummmm, lallai matar kwarai rabin addini, ya ALLAH kabamu damar zama matan kwarai ga mazajenmu
😢🙏🏼
_*.
*******
Bayan shud'ewar wani lokaci muka dawo daga duniyar da muka tafi, kunya duk sai ta kamani, nakasa had'a ido dashi.
Galadi
ma ya murmusa yana kama hannuna zuwa hanyar bayi, banida za6in daya wuce na bisa kawai. Yauma dai tare mukayi wankan, nad'an sake dashi fiyeda d'azun da safe. Muka fito na taimaka masa da shafa mai, yasaka kaya marasa nauyi. Nima da taimakonsa na kimtsa sa
nnan na sauka nemo masa abinda zaici dukda magrib ta gabato. Babu kowa a falon sai Khaleel dake homework. Sannu namasa shikuma ya gaisheni, nace, “Ina Samha my boy?”.
Yace, “Aunty yanzu aunty Dhibiya tazo suka fita”.
Agogon falon na kalla da
mamakin fita a yanzun? Halan batasan Uncle d'inta ya dawoba?.
Bance komaiba na wuce kitchen.
Da taimakon kuku na shirya masa Abu mara nauyi, na had'o saman tire ina fitowa. Samha data shigo tad'an kalleni a firgice, nima kallon mamaki nake mata
da tuhuma.
Nace, “Daga ina haka?”.
Kame-kame tafara na lalubo amsar dazata bani, wadda alamunta ke nuna k'aryace kawai zata fad'a.
Girgiza kai nayi kawai nai gaba abina ina fad'in “Zanso sanin mike tsakaninki da Dhibya Samha? wannan abotar
taku k'arfinta yafara tsoratani”.
Banjira amsarta ba na haye saman benen.
Gudun karya fahimci wani Abu na daidaita kaina tunkan na shiga, nasan inhar yasan raina ya6aci akan Samha ne sai taci k'aniyarta, nikam ba buk'atata ba kenan, nafison sa
nin tsakaninsu da k'awartata kafin na rabasu.
Tsaye na iskeshi rik'e da abin salla, na ajiye tiren saman table d'in gaban sofa sannan na kalli agogo. Yanda banyi magana ba shima baiyiba, na nufi bayi nayo alwala nima, tsaye na kuma iskeshi yana jiran
a.
Bayan mun idar da sallah na kallesa ina fad'in “Abinci yalla6ai”.
Harara ya zubamin da rankwashi, na dafe wajen ina kwa6e fuska zanyi kuka.
Yace, “Yalla6ai d'inan bazai bar bakinkiba ko?”.
Dariya namasa da gwalo inaja ba
ya, “Yo ba sunanka baneba”.
“Da kika rad'amin ko? Zan kamakine ai”.
Sanin halinsa yasani fad'in, “Toyi hak'uri bazan sakeba”.
“Harkin karaya kenan?”.
“Ba doleba, kamun nakane ai bamai sauk'iba”.
Dariya sosai tabashi, amma
ya had'iye abunsa kawai yayi murmushi yana cizar lips.
Munaya tace, “Wato a rayuwa duk d'an Adam zaka sameshi dawata d'abi'a data zame masa jiki”.
Kallona yayi da alamar tambaya, amma baice komaiba.
Mik'ewa nayi tsaye ina cire hijjab
da fad'in, “Cizon lips yazama maka jiki, harya zama d'abi'ar dake yawan birgeni agareka”.
Lips d'in nasa ya ciza sannan ya saki wani k'asaitaccen murmushi da girgiza kai, Munaya kenan sarkin k'uruciya. Yafad'a a zuciyarsa yana mik'ewa shima.
Saman sofa ya zauna yana d'aukar system ya d'ora a cinyarsa, ganin haka saina sauke tiren Dana ajiye a saman table na tura masa gabansa, nasansa akwai son d'ora k'afa, abinka da jinin mulki.
Aiko saiya maida k'afafunsa duk biyu akai yana fad'in “tha
nks”.
Bance komaiba sai murmushi dana d'anyi, na zuba abincin ina zama kusa dashi, tunda ya d'auki lap-top d'inan hanyar zamewa cin abincin yake Neman k'irk'ira, kuma saiya cishi.
Nace, “to yanzu ya za'ayi? Ga abinci”.
Batareda ya k
alleniba yace, “Kici da nawa kawai ya wadatar”.
Ni dariyama ya bani, amma na daure banyiba, “Nikam ina mamakin yanda kake k'in abinci saikace wani Khaleel”.
Murmusawa yayi hankalinsa nakan aikinsa. Yace, bazaki ganebane, nifa wlhy abinci takur
amin yakeyi, shiyyasa ko sau d'aya nacisa a rana ya watar dani”.
Nace, “Nikam dai ban wadatuba, bud'e baki wannan bashida nauyi, nasandai gudun k'aton ciki kake kawai”.
Dariya ya sanya kawai.
Nima nad'an dara ina kai abincin bakinsa.
ALLAH yanzu saikaga mutun nata hora kansa da yunwa wai karyayi k'iba, shikuma ALLAH ba ruwansa, idan haka yayoka ko ruwane kawai abincinka sai kayita”.
Abincin ya shiga taunawa da murmushi saman fuskarsa hankalinsa nakan system d'in.
Haka nacigaba da bashi abincin da janye hankalinsa da hira, yayinda yake aikinsa da saurarena, idan na murmushine ya murmusa, Wanda zaiyi magana ya amsamin a tak'aice, Wanda tuni na fahimci al'adarsace tak'aita magana yabaka a dunk'ule kawai ka fassara sau
ran.
'Dagowa yay fuska a marairaice, “My mata ki tausayamin hakanan cikina karya fashe”.
Dariya nayi da nuna masa plate d'in daya koma empty.
Ya waro idonsa waje yana shafa ciki, “Dan ALLAH da gaske kike dukni na cinye?”.
Nakuma tun
tsurewa da dariyar danake dannewa, “Yo dawa kukaci? Wlhy duk kai kacinye harma d'an k'arawa nayi”.
“Chiii yarinyarnan kin gama dani, amma gama dariyar muguntar ai kanki zata k'are wlhy, ke zakiji nak'ara miki nauyi”.
Dukda na fahimci inda ya
dosa saina shareshi ina cigaba da dariyata, nama mik'e daga kusa dashi.
“Humyim zaki gane kuranki ne”.
Yay maganar yana cije lips.
Da lokacin isha'i ma yayi shine ya jamana jam'i, ya kuma komawa kan aikinsa, ganin aikin ya d'auke dukk
an hankalinsa saina d'auka wayarsa Na kira su Zuhuriyya y'an Niger, muka gaisa dad'an ta6a hirar zuminci cikeda nishad'i. Sannan Na kira aunty Salamah itama nasha labari.
Ganin harna gama wayoyina yana aikin still saina d'auka Novel d'insa d'aya nai
zaman karatu.
Sai wajen 10 ya dafe kai yana sauke ajiyar zuciya.
Kallonsa nayi da tausayawa. Nace, “Ka huta haka nan mana my king”.
Huci yakuma furzarwa yana k'aramin tsaki, ya taso daga gaban tebir d'in ya dawo bakin gadon ya zauna.
Han
nunsa Na kamo, Na kwanto kansa bisa cinyata inad'an shata goshinsa, idonsa a lumshe yace, “wlhy sonake naga na had'a kud'in jirgi da abubuwan buk'atar mu idan zamu wuce Nigeria, Dan Dr Erfan Fahad yamin albishir da k'arshen watannan insha ALLAH zai sallami
Abie, gashi ina cikin matsalar kud'i Munaya, narasa yanda zanyi, bazai yuwu Na kwashe kud'in kasuwa Na narkarba kuma”.
Ajiyar zuciya Nima nayi cikin damuwa, ganin ya bud'e idonsa saina murmusa ina d'an matsa masa kafad'unsa. Nace “ga shawara to”.
“Ina saurarenki”. Yafad'a cikin maida hankali gareni tareda hard'e hannayensa a k'irji.
Yatsana d'aya Na d'ora saman girarsa ina kwantar da gashin a hankali, “My King mizai hana gifts d'in dana samu Na aure da haihuwar yarannan kayi amfani da kud
'ad'en ciki, abinda ya kasance Na kud'i a siyar dashi Dan banga amfanin ajiyesuba ai”.
'Dan Murmushin gefen baki yayi yana lumshe ido, sannan ya bud'e a kaina, “Munaya duk abinda aka baki ko yarana halalinkine, idan Na kar6a nazama mai handama kenan
, ta wani faninma zaluncine, nine yakamata Na baki domin sauke wasu nauye-nauyenki Na y'an uwa da makamantansu, saikuma Na amsa Dan nine baba rodo sarkin babakere”.
Na 6ata fuska ina janye hannuna daga saman girarsa dukda dariyar da furucinsa Na k'ar
she ya bani, “Shikenan tunda baka d'aukeni yanda Na d'aukeka ba, yanzu tsakani da ALLAH idan kabarni dasu mizanyi dasud'in? Ashe abuna ba naka baneba?”. Nai maganar cikin matso hawaye.
Da Sauri ya tashai zaune yana rik'oni amma saina kwace ina niyyar
sauka ma gaba d'aya daga gadon. Gaba d'aya yasani a jikinsa yana fad'in, “Sorry tsaya muyi magana to kinji my sweetness, ya kikeso ayi yanzun?”.
Hawayen nakuma sharewa nace, “Ka kar6a kawai”.
Shiru yay yana kallona da nazarin maganar, saikum
a yad'an numfasa yana gyara zama. Yace, “to ai naga suna Nigeria? ”.
“A'a suna nan, Dan dukna had'osu Na taho dasu wannan karon”.
“Ok babu damuwa, da safe zamuyi magana, shirya yara nakaisu wajen Momma dare nayi nafara jin barci”.
Naj
i dad'i daya amince zai kar6a, Dan haka Na rungumeshi ina dariya.
Bayana yad'an bubbuga kawai yana cewa “jeki shiryasu”.
'Dagowa nayi ina kallonsa, “Amma my King zamuke takura mata itama ai, ka barsu kawai”.
“Babu wani takurawa, bazaki g
ane bane y'ammatana”.
Babu yanda Na iya, dan babu jayayya a tsakaninmu, shiryasu nayi Na shayar dasu kowanne yay d'if, ya d'auka biyu yakai yadawo ya d'auki d'ayan shima. Nikamdai wannan Abu ya girmeni, amma babu damar magana.
Ya dawo yana da
riya da bani labarin gargad'in da momma tamasa akan wlhy mu tashi da wuri, kokuma da anyi sallar asuba yazo ya d'aukesu, Dan bazai yuwu ake barinsu da yunwaba.
Sai Na k'arajin duk kunya ta lullu6eni, amma shi ko'a kwalar rigarsa, saima wata tashar d
aya kamo.
A gurguje please
😊
.
************************
Washe gari ya koma Kashmir, yaso mu tafi tare amma Na nuna masa Momma yakamata ta fara zuwa, Dan tunda aka kai Abie babu Wanda yaje saishi kad'ai.
Daga baya dai sai muka tsaid
a shawara akan zaije yafara ganin halin da ake ciki a yanzu, da wannan shawarar yatafi.
Ba k'aramin abin mamaki Dr Erfan ya shiryama Galadima ba, shiyyasa gaba d'aya ya hanashi ganin Abie.
Da yamma lik'is Galadima ya isa Kashmir, saboda bai
tafi da wuriba, kai tsaye asibiti ya nufa dukda yana tunanin mawuyacine ya samu Dr Erfan Fahad a can, saboda lokacin tashinsa aiki yayi, saidai idan wani muhimmin aiki ya tsaidashi ko Emergency ya riskeshi.
Ilai kuwa a harabar asibitin Galadima yaci
karo da Dr Erfan Fahad ya fito zai wuce gida, sosai Dr Erfan Fahad yay mamakin ganin Galadima, Dan basuyi waya yana hanyaba. Ya bashi hannu sukayi musabaha da rungume juna, “wai my friend dama kana hanya?”.
Galadima ya murmusa da shafa kansa, “Kabar
i kawai, ya aikin?”.
“Alhmdllh”.
“To inaga kawai muwuce gida. Dan wlhy nagaji sosai, yau nayi aikin daya wuce kima”.
Galadima yay d'an jim alamar tunani.
Murmushi Dr Erfan Fahad yayi yana dafa kafad'ar Galadima, “Sameer nasan kana tsana
nin buk'atar son ganin Abie ko? Karka damu, kaidai muje gida kawai abokina”.
Galadima baice komaiba ya bisa suka wuce, Dr Erfan Fahad nata jansa da hira, amma shi iyakarsa murmushi ko eh da a'a.
Ko kad'an Dr Erfan Fahad bai damuba, danya fahimci
halin Galadima Na rashin son hayaniya tsaf, dama tun a baya bashida yawan magana, Ashe halin Na nan bai canjaba, saima k'aruwa dayay.
Shikam Dr Erfan Fahad mutum ne faran-faran, ko jama'ar dake jiyya namasa wannan shaidar ta yawan tsokana.
Aha
ka dai suka isa gida, shidai Dr