Showing 207001 words to 210000 words out of 407268 words
Idona harya fara tara kwalla cikin marairaicewa nace, “dan ALLAH kabani, wlhy yunwa nakeji bata wasaba”.
Rasa ma mizaicemin yayi, ya zubamin ido kawai yana kallona. a mama
kinsa saiyaga ma ina hawaye, abincin ya tura min yana fad'in “wannan cin naki yayi yawa, gama muje wajen Akash ya dubaki”.
Uffan bance masaba, shima bai sake tankawa ba yanufi bathroom, yaja wasu mintuna saigashi ya fito d'aure da towel, kallo d'aya
namasa na janye idona, wannan abun nasa yafara damuna, yanzu baijin kunyar yafitomin a duk yanda yaso, ko yana mantawa bashi kad'ai bane a d'akin oho.
Shima dai kallonta kawai yakeyi, dan nacinye abincin plate d'in tas, a ransa yace shiyyasa taketa za
ma k'atuwa, irin wannan ci haka.
Oho bansan yanayiba, nidai mik'ewa nayi nashige bathroom abuna, nasamu nai wanka da ruwa mai sanyi dan naji dad'i. lokacin dana fito yagama shiryawa cikin ainahin kayan malam bahaushe, blue d'in shaddace akaima d'inkin
wando da 'yar shara, saidai tasha aikin sarauta d'an asali da d'aukar hankali, ya kawo bak'ar hularsa ya d'ora, itama dai irin ta mutanen dace *dara* (irin wadda su ibro suke sawa), saidai wannan batakai waccan tsawoba, dai-dai take kamar sauran huluna. h
arga ALLAH kwalliyar tasa tamin k'yau, dan yafito a cikakken bahaushensa, turare yake fesawa amma nakasa d'auke idona daga kansa.
Duk kallon k'urillar datake masa yana kallonta ta gefen ido, wani miskilin murmushi yayi Na gefen baki, ya juyo muka h
ad'a ido, saurin janyewa nayi cike da basarwa.
Shikuma ya ta6e baki yana takowa inda nake. tuni zuciyata harta fara tsitstsinkewa, dan ayanzu babu abinda nake gudu kuma irin yace zai ra6u jikina koya nunan buk'atar wani abu, shima inaga fahimtar haka
nne yasa a kwanakinnan bai cika takurani kamar abaya danake kawo kaina ba.
Ganin yanda ta tsorata sai abin yabashi mamaki, waskewa yay yafasa zuwa gareta, ganin ya canja hanya Na sauke ajiyar zuciya wadda har fitar sautinta saida yaji.
Kansa
kawai ya girgiza ya zauna a bakin gado yana fad'in “kishirya mana”.
Bance komaiba nawuce Na d'auki Arabian gown da zan saka, dan yanzu sune kawai kayan dakemin dad'in sakawa, bathroom nakoma Na saka, Na fito Na iskeshi yana waya da Akash dake fad'a
masa inda zamu iskeshi. wucewa nayi nad'an gyara fuskata, inason shafa mai a k'afa amma ina tunanin yanda zan sunkuya.
Lura da yay da hakan yasashi mik'ewa, wajen takalmanmu yanufa ya d'aukamin masu taushi cikin wad'anda ya siyamin saboda naji sauk'
in tafiya.
Kafad'una ya kama ya zaunar dani ga stool d'in mirror, sannan ya d'auki man ya duk'a k'asa a gabana yakamo k'afata yana shafamin, nidai kallonsa kawai nakeyi, harya gama yasakamin takalman ya d'auran igiyar yana fad'in “yakamata ma mufara
fita kina motsa jiki, dan k'afarnan kamar tana d'anyi fushi a kwanakin nan”.
Nace, “ai bata ciwo”.
Baice komaiba yamik'e yana kama hannuna ya mik'ar dani.
A falo muka iske jakadiya tana kallo, tamin sannu sannan ta gaida Galadima.
yafad'a mata zamu fita, tabimu da addu'ar dawowa lafiya.
Tafiyar tamu takasance shiru kamar yanda muka saba inhar ta had'amu mu biyu, maimakon muje asibiti sai gamu awani gida mai k'yau da tsari, kafin nasamu damar tambayarsa saiga Akash yafi
to yana zabga murmushi, rungume juna sukayi da Galadima, kafin ya d'ago yanamin sannu da zuwa.
Fuskata da murmushi Na amsa masa tareda gaishesa.
A tsararren falon gidan muka yada zango, komai ya birgrni dan an tsarashi yanda ya kamata. dandana
n Akash ya tara mana kaya a gaba, sannan ya zauna muka sake sabuwar gaisuwa. Suka d'ora da barkwancinsu irin Na abokan da suka shak'u. A firar tasune nakejin Auren Akash d'in ya matso, dan zasuyi baiko next week da wadda zai aura, Na tayashi murna da fatan
kaiwa da rai. ya amsamin bakinsa har kunne.
Bayanin yawan cin abincina Galadima yamasa, Akash yay dariya, “to inbanda abinka Sameer ai dole taci abinci fiyeda da, karka manta yanzu ba ita kad'ai bace, kuma saitaci abin cikinta zai samu shima, kunk'
i yarda ayi scanning muga adadin 'ya'yan namu ko jinsun su”.
galadima ya murmusa kawai, karka damu, miye Na zazzari, kwana nawane insha ALLAH zaizo ko zatazo duniya, yanzu dai tunda ba Matsala bane cin abincin ai Alhamdllh”.
“no babu wata M
atsala, abindama yasa zakuga yanzu takanyi saurin jin yunwa cikinta ya tsufa, shima yak'ara girma abin cikin nata, dan zama ta dingajin idan bataciba ana motsi da harbe-harbe a cikin, idan da zaka kalli cikin a time d'in datakejin yunwar sosai har yanda ya
ke wuntsilniya saika gani kaima, Madam ko hakan baya faruwa?”.
Nace, “yana faruwa sosai, amma da zaran naci abincin sai a nutsu”.
Akash yay dariya, “Alamun yana cikin k'oshin lafiya kenan, abincinne kawai buk'atarsa”.
Galadima ya juyo
muka kalli juna, gira ya d'agamin nikuma nayi murmushi ina kauda idona gefe.
Daga nan wata hirar suka koma, wadda nake zargin akan Abba nane, dan naji Akash Na fad'in doctor Johnson yabama Abba glasses d'in amatsayin medical glasses, kuma ya gargad'e
sa karyayi wasa dashi saboda jijiyar idonsa nason samun Matsala, to sunason glasses d'in yazama riga kafine, dayake da turanci suke magana sai yazam inaji nima.
Murmushi Galadima yayi yana jinjina kai.
A raina nace mikuma Galadima ya shiryama Ab
ban?. banida mai bani amsa, dan haka nayi gum.
Muna niyyar tashi Akash yace bamu isaba, bazamu tafi bamuci komai a gidansa ba, kodan munga bashida matane.
Badan munsoba mukad'anci abinda zamu iya, sannan yayo mana rakiya har wajen mota.
Saida munaya tashiga mota sannan Galadima ke fad'ama Akash yayi mantuwa.
Akash yace “tami?”.
Babu kunya Galadima yad'an ciza lips yana tambayar Akash wai miyasa yanzu take gudunsa?.
Akash yabashi amsa da maybe salon cikine, danshi bab
u yanda baya zuwa ma mace, wani yasata sha'awa wani kuma akasin hakan, amma idan na haihu zan iya komawa normal. Galadima ya basa hannu sukai musabaha sannan ya shigo mota yana masa godiya.
Tunda muka fara tafiya saina kasa jurewa, na jeho masa ta
mbaya muryata a sanyaye.
Kad'an ya juyo ya kalleni ya maida kansa ga tuk'i, saida yaja wasu mintuna kafin yasaki ajiyar zuciya tareda cizar lips nashi, batareda Yakuma kallonna ba yace, “Friend! Wani karatun baya buk'atar fashin bak'i, akan karantash
ine a barsa a yanda yazo”.
Murmushi nayi ina maida hankalina gareshi, nace “yalla6ai koda shi wannan karatun zai iya fita a jarabawa?”.
“Humm” yafad'a yana rage gudun motar, yanzunma bai kalleniba, yad'an zakud'a jikin sitiyarin sosai, “some
times akanyi burin cin jarabawane domin canjin aji ko gama makaranta ko shiga, saidai awannan karon ni nawa jarabawar da banbance-banbance tazo, dan bana buk'atar cin jarabawar kai tsaye, har sai harsashina ya isa ga zukatan malaman”.
“to amma yall
a6ai karka manta Hasashefa ba shi bane yak'ini”.
“wannan gaskiyane yalla6iya. Saidai yak'ini kuma baya amsa sunan tabbaci, daga lokacinda kika shiga fili wasa kika saka aranki bazakiyi nasara ba, to da kamar wahala kiyi nasarar, duk abinda zanyi n
akan rok'i ubangiji nasara Kafin yinsa, sannan na cika zuciyata da kwad'aituwar samun wannan abin, lokuta da dama mutane kan Gaza tsarkake zuciya kafin su cikata da buruka, shiyyasa kikaga duk gudun jirgi a samaniya wataran gaggawa nasakashi tarwatsa a fil
inda ba muhallin saukarsaba, kiringa zama mai yak'ini saikiga kin tabbata a jerin masu samu”.
Murmushi nayi har hak'orana na bayya, nace, “dakai kanarine danace kafi dukkan halittar kanari iya raira zance, dakuwa mawak'ine saina saka a jerin ma
su zak'ak'an murya, inkuwa a Marubuci kazo to tabbas kai Kanada yawan fik'ira, domin hikayarka zata yawaita saye zukatan mabiyanka ne”.
Gefen hanya ya gangara, ya kashe motarma baki d'aya ya maido hankalisa gareni.
“Munaaya!” yakirani cikin
wani yanayi kuma murya ahankali.
nima saina amsa masa a sanyaye.
Hannuna ya kamo cikin nasa yana mirza yatsun a hankali, yaci gaba da fad'in “A shekarun baya ni mutumne mai ra'ayin Kansa, ma'ana murd'ad'd'e mai wahalar sha'ani, sannan mai za
ma a bisa tsarinsa, kece mutum ta farko dana fara doguwar magana da ita koda bana so, nakanyi mamaki a duk lokacin da kika taya nazamo mai sallama miki, anya kuwa bakizo da wani Siddabaru ba?”.
Idanu nad'an fiddo waje, nace “siddabaru kuma yalla6ai?
to ai awajena ni har gobe kana akan wad'annan ra'ayoyin naka, dan banga canjin dakake hasashen kasamu ba, amma miyasa kace hakan?”.
Numfashi ya sauke ahankali, kafin ya ciji gefen lips nashi yana Sosa girarsa d'aya da d'an yatsa “wannan sak'on zu
ciyane, kibata dama, zata tabbatar miki da cewar wannan Muhammad Sameer d'in yasha banban dana shekarun baya”.
“sak'on zuciya kuma?”. nafad'a cikin hasashe, dan nikam Yakuma dilmiyar dani.
Mortar ya tada yana fad'in “well basai kin zurfafa ba,
dan haryanzu akwai sauran dama”.
Baki na d'an ta6e ina gyara zama, “har walau zancen “dama! dama! dai again?, bana son saka baki a hurumin daba nawaba, amma abinda nasani dama dai duk damace, sannan mai ita yakan tanadar mata dukkan muhalin daya tad
ace da ita, damarmu ce mu damata takowane
hanya mukaso”.
Idanunsa ya lumshe yana sakin wani k'asaitaccen murmushi daba koyaushe yake irinsaba.
Jin Sautin murmushin ya sakani juyawa na kallesa, ya d'agamin gira yana maida hankalinsa ga tuk'
insa.
Babu Wanda yasake yin magana har muka Isa gida. har yanzu babu Wanda ya dawo, dan haka muka haye sama kai tsaye. dama na k'agara na cire rigar jikina
saboda azababbiyar zufar danakeji, danma ya tausaya min yad'an saka AC a mota, ban iya zama b
a saida na watsa ruwa, nifa abubuwan sunmin yawa, nice jin zafi nice ci kamar gara, harda alwala nayo, Dan magriba tayi.
Ina fitowa shima yashiga yayo alwala. Koda yafito saiya wuce masallaci.
Ina jiyo hayaniyar su Samha dasuka dawo a
mma nakasa sauka, ina kwance abina, hawa da saukarnan bak'aramin wahal dani yakeba yanzu, ahaka Galadima yadawo ya iskeni, sallamarsa kawai na amsa, amma ban iya d'agowa na kalleshiba. Saida ya sauya kayan jikinsa zuwa marasa nauyi kafin yazo ya zauna kan
sofa yana fad'in “lafiya dai?”.
d'ago ido nai namasa d'an murmushi, nace, “babu komai, gajiya ce kawai”.
Shima murmushin yamin, cikin lumshe ido yace, “Sorry friend, saura k'iris insha ALLAH”.
“Humm” kawai nafad'a batare da nace m
asa komaiba.
Daga nan muka d'anyi shiru, kusan mintuna 3 yanata latse-latsen wayarsa, batareda ya kalleni ba yace, “Abba kuwa yana saka zobe?”.
Kallonsa nayi, amma hakan baisa ya kalleniba, a d'arare nace, “eh yana sakawa amma miyasa kamin
wannan tambayar?”.
Wayar ya ajiye yana sauke ajiyar zuciya, ya saka d'an yatsansa yana bubbuga la66ansa ahankali, yayinda idonsa yake a kaina tamkar mai nazari, “kina ganin idan kika bashi zai saka?”.
Yunk'urawa nai na tashi zaune sosai
, “dan sakawa zai saka, amma kana ganin bazai zargi wani abuba kuwa?”.
“miyasa kikace haka?”.
Shiru nad'anyi, dan ganin ina neman zirma kaina, saina d'an murmusa kawai cikin basarwa, nace, “waynot abashi ba kai tsayeba”..
Murmushi
n gefen baki yayi, yace, “y'ar tsuntsuwata wai mikike tunanine? da har kiketa kwana-kwana haka?”.
Baki na tunzuro gaba, ina fad'in “nidai ba tsuntsuwa bace ba”.
Dariyace ta kufce masa babu shiri, yasaka hannu yana rufe bakinsa.
Haushi y
a kamani na d'auki filon dana kwanta na jefa masa. da sauri ya cafe yana cigaba da dariyarsa, hakan yasa najawo na kujerar ina cigaba da kai masa duka yana karewa da wancan. daga k'arshe sakkowa yay yahad'a nida filon ya rik'e yana fad'in “sorry sorry na b
ari, ba 'yar tsuntsuwa ba giwar mata”.
Hararsa nayi nafara kukan shagwa6a kuma.
dariya Yakuma sakawa yana fad'in “toni bansan mikikeso nace mikiba kuma?”.
“ni banaso duka”.
“to shikenan nabari, yanzu dai yaza'ayi Ring yaje yatsan
Abbanmu to?”. ‘yay maganar yana d'ora kaina jikin kafad'arsa’.
“saika fad'amin sirrin sannan zan fad'a nima”.
Ya murmusa yana jan hancina, “kin cika wayo yarinyarnan wlhy”.
K'aramar dariya nayi nace, “ai awajenka na koya”.
Murm
ushi kawai yay baice komaiba, ya jawo wata 'yar k'aramar bag mai k'yau fara ya mik'omin.
Kar6a nayi ina tashi zaune sosai na bud'e jakkar ina fiddo kayan ciki, agogone mai masifar k'yau da tsari, na azurfa 'yar asali mai tsada, sai wani d'an akwati
da ring mai k'yau na azurfa shima, an masa ado da farin stone mai garai-garai tamkar diamond, na jujjuya zoben kafin na d'ago mu kalli juna ni da Galadima, ido d'aya ya kashemin
😉
.
Janye idanuna nayi nakuma maidawa ga zoben ina k'ok'arin sakashi a
yatsana, saidai yamin yawa sosai, na cire ina fad'in “amma gaskiya zobenan ya had'u sosai yalla6ai”.
“duk haduwarsa bai kaikiba ai”. ‘yay maganar acikin kunnena’.
Kallonsa nayi, amma saiya basar tamkar bashi yay maganar ba.
Lips na
cije na d'an hararesa.
Shikuma ya ta6e baki.
Na maida kayan duk a cikin bag d'in dad'an hanzari ina rik'e cikina dayay wata wuntsulawa.
“lafiya?”. ya fad'a yana rik'o hannuna.
'Dagowa nayi na kallesa da k'yar, da hannu na nuna mas
a cikina dake juyamin, jinake kamar numfashine zai bar jikina.
Babu shiri ya dire wayar hannunsa ya rik'oni jikinsa da k'yau.
Sosai na fara murk'ususu ina kuka da k'ank'amesa, dukya rikice, yama rasa mi zaiyi?.
Ana cikin haka saiga salla
mar Aunty Mimi dataga shirun yayi yawa sun dawo ban sakkoba, saitai tunanin kobana jin dad'ine, sallama tayi Galadima ya amsa murya a rikice, hakanne yasakata shigowa batareda jiran isoba.
Da hanzarinta ta k'araso tana tambayar miya faru?. nidai kuka
kawai nake ina kuma k'ank'ame Galadima.
Shine yasamu damar mata bayani sama-sama, yak'are maganar da fad'in “Aunty mutafi asibiti please, maybe haihuwa Ce?”.
Da sauri tace, “badai haihuwaba Sameer, cikin dake wata takwas, kaga ina zuwa
”. Ta fita a hanzarce.
Babu dad'ewa sai gata tadawo da innarmu da jakadiya, dak'yar innarmu ta amince ta hawo, danma taga tsantsar rikicewar da aunty Mimi tayine. har yanzu dai kukan nake ina jikin Galadima dashima dukya koma kalar tausayi kamar zaiy
i kukan.
Ganinsu a haka yasaka innarsu munaya k'ok'arin komawa da baya, dan saitaji kunya ta kamata, dukda tasan suma bada son ransuba ne. ita kanta jakadiya taji kunya. ganin innarsu munaya zata gudu Aunty Mimi tayi azamar rik'o hannunta. “please i
nna karki duba ta kunya, halen datake cikine abin dubawa, kowa yasan dai ba haihuwa baceba tunda da saura”.
Ajiyar zuciya inna ta sauke, batare da ta motsa daga inda takeba takuma musu kallo d'aya ta d'auke kanta, tace, “inaga juyine ai, zai lafa i
nsha ALLAH”. ‘tana gama fad'a ta fice abinta’.
Jakadiya da aunty Mimi suka kalli juna,