Showing 99001 words to 102000 words out of 407268 words
/>
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
👉🏻
2
⃣
6
⃣
..........Da kuka na farka, duk da naji dad'in jikinna kuwa, dan banajin azabar kamar jiya, tashi
nayi zuwa toilet danna d'auro alwala, na tuna labarin da wata k'awarmu ta ta6a bamu akan yanda taita ciwon jiki, saida mijinta yata mata ruwan zafi a ranar, ruwan mai d'an zafi na had'a na shiga ciki, nasha zafi kuma naji dad'i, amma inajina kamar ba a da
i-daiba maganar gaskiya, haka dai nasamu nayi sallar asubahi, ina tsaka da sallar yashigo da nufin tadani, ganin na tashi ma saiya juya yafice abinsa zuwa masallaci shima.
Koda na idar kwanciya nayi saman abin sallar nacigaba da kuka na, ina kuma tu
nano abinda yafaru a jiya tamkar a films ko novels ko mafarki, babu abinda zuciyata keyi sai tsinemar, a yau d'inan dolene saiya bani Sakina natafi gidanmu, nafasa auren Contract d'in ma, da dai na zauna da mugunnan gwamma nakoma gidanmu nacigaba da rayuwa
dasu innaro yafimin....
Tun d'azun yana tsaye a kaina, tausayina yakamashi, dan yasan shine silar kukan mawa, bayason zalunci ko kad'an, amma saigashi shine da aikatawa kuma, zama yayi a bakin gadon, cikin muryar nan tasa mai kama da anmasa
tilas yace “tashi zaune muyi magana”.
“baza na masa, a zuciyata nace bazan tashiba mugu kawai, bakada abinda zaka fad'amin na yarda, azzalumi, dama abinda ka shiryawa rayuwata kenan? Dan kaganni d'iyar talakawa banida k'arfin gogayya da kai, tab
bas nayi kuskuren yadda da Wanda shikansa ma bai gama yadda da kansaba, ALLAH ya Isa wlhy tunda ka ketamin mutunci har abada bazan yafe makaba, kullum cikin sallata saina sakoka da neman sakkaya ga mahaliccina akan zalincin dakami.........
A fili k
uma nace, “kagama zalintata kazo kanamin mazurai da mulki, ank'i tashin”. a hankali nake maganar banyi tunanin yana jinaba, sai tsawa kawai naji ya dakamin
“k!!!!!”.
Yafad'a cikin daka tsawa, Ashe tunda nafara maganar ya rumtse idanu saboda ya
nda Kalmar zaluncin suke sukarsa a zicciya, ban ta6a ganinsa a wannan yanayinba, a cikin fad'a yace, “Niba azzalumi baneba, zina nayi dakene!? dazaki dunga aibantani damun duk furucin dayazo bakinki? to bara na tuna miki idan kin manta, SADAKI na biya na a
uroki! tun jiya kike fad'an magana amma na shareki, ni sa'an kine? wlhy idan bakiyi wasaba zan koya miki hankali! danaso muyi magana ki saurareni mana kiji mizance?.........”
Zumbur namik'e zaune, duk da azabar da k'asana kemin, na kallesa ido cik
in ido ina zubda kwalla nace, “bakada abin fad'a shiyyasa bazan saurarekaba, bar ganina 'Yar talaka bana d'aukar raini wlhy, mina maka ne? miye had'ina da kai kaketa bibiyar rayuwata da bala'i, tunda na had'u da kai ban kuma samun nishad'iba, wlhy bazan ya
fe makab.......
Jikake bamm! ya make bakina da bayan hannunsa, cikin zazzaromin ido yace bazaki nutsuba Ashe?”.
Naji zafi sosai, dan haka nafashe dawani marayan kuka mai ban tausayi, ga wani bala'in tsoronsa daya kuma shigata, maganar ma a t
sorace dama nayita, Dan tsabar bala'i na hango cikin idonsa Dana kallesa.
Kansa ya dafe da hannu, jiyake tamkar ya tariyo jiya a rayuwarsa ya goge dukkanin abinda yafaru
Ganin bazan sauraresan ba da gaske saiya tashi ya fice yabarmin d'akin.
Nakuma 6arkewa da kuka.
Koda yafita a falona ya zauna, ya dafe kansa daya koma masa ciwo k'asa-k'asa yau, tunaninsa yafara komawa baya daga jiya zuwa yau, shin miya sakashi wannan matsananciyar sha'awar ne wai? dan bai ta6a jin makamancin
feelings irin na jiya ba, da sauri yamik'e yanufi sashensa, a falo ya tsaya, ya d'auki kwalin hollandia fresh milk d'in jiya yana dubawa, shi dai yasan shine last abu daya sha a jiya, to kenan koma miye daga cikinsa yake?. to amma ai ba yaune yafara shan f
resh milk ba a gidannan balle yace kuma shine. kwalin ya ajiye yakuma dafe kansa, gaba d'aya tunaninsa ya kulle, dama shi indai yana cikin 6acinrai to komai nasa birkicewa yakeyi, dolene saiya kwantar da hankalinsa zai iya kamo bakin zaren. a kujerar Yakom
a ya kwanta, ko azkar yakasayi yau, babu dad'ewa barci yakuma kwasheshi anan.
Itama Munaya daga kuka barci yay awon gaba da ita a wajen.
Har Samha suka kawo abinci duk barci suka Tatar sunayi, tasan halin Uncle Sam shiyasa bata tadasu ba, kad
'an daga aikinsa ya mammaketa a safiyarnan.
Su duka sai wajajen 12 suka farka, kowanne yatashi da damuwarsa.
Tunda nayi takun farko nakuma tabbatar da akwai matsala, dan ruwan zafin da yaymin jiya kad'ai ya isa na daina jin zafinnan irin haka,
balle kuma nima nayima kaina da safennan, amma maimakon k'asana yabar zafin saima zugi yake k'arawa, gashi idan nashiga ruwan, zafi nakeji sosai.
Yanda nake takawar ina hawayene yabashi mamaki, dan aganinsa yakamata nasamu sukuni saboda yanda y
amin jiya. bansan yashigoba, maganarsa kawai naji..
“Wai mike faruwane? Ko dai kinji ciwone?”.
Wata uwar harara dataso bashi dariya na zuba masa, amma saiya danne baiyiba, takowa yayi har inda nake yakama hannuna na fisge, ya d'aure fuska
shima yana hararata, “k! Wlhy kinutsu kafin na canja miki kamanni”.
“yo kammani na yaushe kuma zaka canja min? bayan Wanda ka canja min yanzu? dama haka kake? a fuska kamar babu ruwanka amma sai zalunci taf zuciyarka”.
Idonsa ya runtse dan ba
yason Kalmar zaluncin nan danake jifansa dashi, jinai kawai an fusgoni an zaunar a bakin gadon, nakuwa fashe da kuka ina fad'in “wayyo zafi, munubiya Azalumin nan zai kashe miki ni”.
Ko kallona baiyiba yafice, ina nan ina kuka saigashi yadawo da wa
yarsa a hannu, ya zauna saman sofa batareda ya kalleninba, bashida mafita saita kiran Akash, dan yanason sanin minene matsalar datake sakani wannan kukan da complain d'in zafin, yasan koya tambayeni ba fad'a masa zanyiba..
Da turanci suka gaisa
, amma da zaiyi tambayar saiya canja harshe zuwa yaren daban saniba.
Akash yace saidai idan ciwo taji, dan bai kamata ace tana Complain zafi irin haka ba, zataji ciwo kam amma bawai yanda yake nuna masa yanzun ba.
Galadima ya gyara zamansa sos
ai yace “to ai na sanar maka fyad'e akama yarinyar fa”.
Akash yace “zata iya kai shekara nawa yarinyar?”.
'Dago ido yayi ya kalleni kafin ya janye yana fad'in “Maybe 19years ko 20 kawai”.
“ai bama yarinya baceba can sosai, inaga taji c
iwone gaskiya, yakamata doctor ya dubata gudun samun matsala, amma kabada gudunmawa a hukunta Wanda yay abunnan my man, please ka kwatarma yarinyar hak'k'inta wajen azzalumin nan”.
lips d'insa kawai ya cije maganar Akash na sukar zuciyarsa, da Aka
sh yasan shine yay aika-aikar dabai ce hakaba. sallama sukayi ya yanke wayar, saikuma yafara tunanin doctor d'in dazai nemo ya dubani, dan bashida damar fita dani a gidan yanzun.
Can doctor Hafsat ta fad'o masa a rai, ita kad'ai zai iya aminta tasan
matsalarsa, dan ya yarda da ita sosai, yasan zata masa k'yak'yk'yawar fahimta.
Kiranta yayi bayan sun gaisa cikin mutunci ya fad'a mata matsalar ta yanda zai iya, dukda ya 6oye mata wacece keda matsalar ta fahimcesa, d'an murmushi kawai tayi tana gir
giza kai da tausayin yarinyarnan data shiga hannun Galadima, duk abinda zata buk'ata tagama had'ashi sannan ta fito, matsalar gidansu data Sani yasakata yin shiri tamkar ba doctor ba.
Shiru d'akin yayi, sai kukana dayake fita a hankali, shikam ya
zubamin idanu yana kallona k'asan ido, zaune yake k'afa d'aya akan d'aya, ya jingina da kujera, saika rantse idonsa a rufe yake, amma yana kallonane ahaka.
Bayan doctor Hafsat tazo k'ofar fada saita kirashi, dan baza'a barta kai tsaye tashigaba.
Ina kallonsa ya fice bayan ya yanke wayar daban San dawa yakeyinta ba.
Kusan mintun 20 saigasu sunshigo dawata mace, ba yarinya baceba can gaskiya, zasu iya zama sa'anni da Galadima d'in, dan haka na tashi zaune na gaidata cikin girmamawa.
Ita kuma ta amsa cikeda fara'a.
Kallon Galadima tayi dayake tsaye yana kallonmu, “ranka ya dad'a kozaka bamu wajene”.
Murmushi yad'anyi yana fad'in babu damuwa.
Yana fita matar ta zauna kusa dani a bakin gadon, fuskarta d'auke da murm
ushi tace, “sunana doctor Hafsat Abu, friend d'in Galadima ce tun a primary school”.
Murmushi nayi mata na yak'e kawai.
Takuma gyara zamanta tana kallona, please dear karkiji nauyina, ki fad'amin matsalarki kai tsaye, dan ba'a wasa da wannan m
atsalar, takan zama babban Abu anan gaba ga d'iya mace”.
Kai na jinjina mata ina hawaye, sannan nace “inajin zafin wajen sosai”.
“ok kozaki iya kwanciya nagani”.
Ido na waro waje a tsorace, sai kuma nayi k'asa da kaina saboda kunya.
Tayi murmushi tana kama hannuna, “karkiji kunya akan lafiyarki dear, please ki daure kinji”.
Kai kawai na gyad'a mata sannan na kwanta, babu yanda zanyi dole na yarda ta duba, kanta kawai ta girgiza da mamakin Galadima, saikace Wanda ya kusance
ni da k'arfin tuwo?, ai wannan kam da wani doctor d'inne saiya yima Galadima fad'ama wlhy, dan ko kad'an bai bini a hankaliba, amma ciwon daya jimin bazai zama mai cutarwa ba insha ALLAH.
da kanta yanzu ta had'amin ruwan zafi tazuba wasu magani, sa
nnan ta taimakamin har zuwa bayin ta nunamin yanda zanyi. ban cutar da kainaba na nutsu nayi komai yanda tace, dukda inajin zafi kuwa, bayan nafito saina sameta zaune ta gyara gadon tsaf, gakuma abinci a ajiye, da alama Galadima ne ya kawo, tsareni tayi da
lallashi naci abincin ma yanzun, sannan tabani magunguna nasha, ta kalleni da murmushi, “ALLAH yak'ara lafiya gimbiyarmu, indai zaki cigaba da kulawa kamar yanda na nuna miki insha ALLAH nan da 2days zaki dawo normal, ga drugs d'inan saikina sha, shima wa
nnan cream d'in kina matsi dashi awajen a koda yaushe”.
Kaina na jinjina mata sannan nace “ nagode Aunty”.
Sallama tamin tafice.
A falo ta iske Galadima, bayan tamasa bayanin yanda yakamata a kula dani saita kallesa cikin tsokana, “r
anka ya dad'e kafayi 6arna gaskiya, Shifa wajenan ba a nuna masa k'arfi, please a kiyaye”.
Murmushi kawai yayi baice mata komaiba.
rakiya yamata tareda mata alkairi sannan yadawo.
A kwancen data barni ya iskeni, zama yayi gefen gadon ya
d'an kalleni ya janye idonsa “yaya kikeji yanzun?”.
Baki na turo masa, amma ban tankaba. shima bai damu da amsawar tawaba, ya basar kawai ya d'akko wata maganar.
“nasan babu abinda zan fad'a ki yarda dani tabbas, sai dai zankuma maimaita m
iki SAMEER BAYA ZALUNCI, koda wasa ban ta6a kawo zan aikata hakan agarekiba har kibar k'ark'ashin kulawata, bansan miya shiga kainaba a jiya”.
Kallonsa nayi ina hawaye da takaicin maganarsa, nace “bakasan miya Shiga kankaba ka d'auki fresh milk k
abani? bayan kasan mika zuba”.
Shima kansa ya d'ago yana kallona, cikeda k'asaitarsa yace “ban fahinceki ba, mikike nufi? dan ina son na kusance ki sainayi amfani da wani abu? da hakan naso daret zanzo gareki tunda nasan nabiya sadaki ai, tunda ba
tsoranki zanjiba ko?”.
“dama ai bazaka fahimceni ba tunda Kasan ka aikata ai, kuma ai alk'awarin zama tamkar abokai kamin ba irin wannan ba”, na had'e hannuna alamar roko
🙏🏻
ina kuka nace “dan girman ALLAH ina rok'onka kabani Sakina a yau natafi
gidanmu, wlhy nafasa auren Contract d'in, koma waye yayi abun ni na yafe masama, kawai ka sallameni”.
Yama rasa mizai cemin shi, ajiyar zuciya yad'an sauke, kafin ya cije lips nashi, “shikenan, zan miki yanda kikeso, amma kibari ki warke, bai kam
ata ki koma gida ahakaba”. ‘yana gama fad'ar haka yatashi yafice batareda yaji amsa taba.
Duk da naso yabani sakina a yau, amma zanyi hak'uri na warke d'in kwana nawane.
******
Yinin yau haka mukayishi duk zukatanmu babu dad'i, Ga
ladima kam ai ciwon mara saiya nemi dawo masa sabo, jiyayi kawai yana sake buk'atar kasancewa dani, haka yayta dannewa har zuwa dare, dan bazai kuma yarda yin gangancin nanba. ganin yana neman mutuwa yay shiri a gaggauce yafito domin zuwa hospital.
Tunda yafito suke zubewa gaisheshi, hannuna kawai yake iya d'aga musu, dan kallo d'aya zaka masa ka tabbatar yanada damuwa, da sauri sarkin mota yazo yabud'e masa ya shiga, suma dogaran dakan bisa idan zai fita sai duk suka taso.
Tundaga fitarsu g
idan Muftahu na kallonsu, yad'an murmusa kawai abinsa. (
🙄
wlhy Reader's suka kamaka zaka gane bakada wayo
😡
)
Shi kad'ai yasan azabar dayakeji a jikinsa, yana kwance cikin kujerar ne sai faman cije lips yakeyi.
Tunkan sarkin mota ya tamb
ayama ya sanar masa asibitin da zasuje.
Sarkin mota ya amsa cike da girmamawa da tausayin shugabansa, dama shi tunda yaga yafito ya fahimci akwai matsala.
Tun amota yakira wata number yana tambayarsa ko yana asibiti?. Dr Jalal ya amsa da eh
yana nan.
Yanke wayar yayi kawai baisake cewa komaiba. Dr jalal yabi wayar da kallo yana mamakin Galadima da halinsa, kiransa yakuma yi shi dan bai fahimci inda maganar tasa ta dosaba. sai dai harta yanke bai d'aukaba, yana k'ok'arin sake kira yaji
ana Knocking d'in k'ofar.
Amsawa yay da yes tareda izinin shigowa.
Wani dogari ya bud'ema Galadima k'ofar yashiga, da hanzari Dr Jalal yamik'e yana murmushi da masa welcome.
Hannu kawai ya iya d'aga masa ya zauna kujerar gaban decks d
'in.
Shima Dr jalal saiya zauna, “ranka ya dad'e lafiya dai ko?”.
Saida yaja wasu Seconds sannan yafara ma Dr jalal bayanin damuwarsa, ya sanar masa mararsa namasa ciwo tun jiya, kuma ada bata masa kamar hakan.
Shiru Dr jalal yay ya
na nazarin maganar tasa, saida yakai aya sannan yace “ranka yadad'e kokasha pills ne?”.
Kallonsa Galadima yayi, “pills kuma? wane irin tambaya kakemin haka?”.
“afuwa ranka ya dad'e, matsalar taka tayi kama da wanda yasha tablet ne, mikaci
na k'arshe jiya?”.
cikeda nazarin maganar Jalal yace “fresh milk ne last abinda nasha jiya da daddare”.
“to amma bayan shi kafara jin matsalar?”.
“kusan haka gaskiya”.
Dr jalal dai shiru yayi, dan ya tabbatar wannan aikin
desire tablets ne, amma koya fad'a dawuya Galadima ya yarda, sai kawai yashare ya had'a masa drugs da injection yamasa, yace yad'an kwanta na kamar 20 minutes a office d'in. bai musa masaba ya shiga inda jalal kan huta idan yaso, saiya kwanta kawai, dan s
hima bazai iya tafiyarba, d'akin ma da taimakon jalal d'in yashigo.
Ni bansan hidimar da akeyiba, dan rabona dashi tun bayan munyi maganar saki, abinci ma tun Wanda doctor tabanine a cikina, sai kusan 8 Samha takawo min kayan fruits dawani Abu mai
dad'i daban san mineneba
😝
.
Ta zauna mund'anyi hira kafin tafice. a bakin ta nakejin wai jibi Friday zasu koma India.