Showing 270001 words to 273000 words out of 407268 words
Na 6atan y'an uku, dan labarine daya zagaye kowacce kafa ta yad'a labarai da socia media Na k'asar nan, (kunsan dai abin manya duk k'ank'antarsa saiya fita, balle wannan da yazamo mai girma).
Bay
an Munaya da aunty Mimi sun zauna a k'asan lallausar darduma can gefe suka kwashi gaisuwa, dogarai suka amsa da yawun Sarki, sannan suka kuma gaisheda fadawa.
Daga nanan aka amshi su Abdurrahman, y'an majalissar Sarki sukaita d'auka d'ai-d'ai suna sak
a musu albarka, da addu'ar fatan alkairi.
Bayan fitowarsu sai sashin iyalan mai martaba, yau ma dai gimbiya zulfa bata fasa nunama Munaya da yaranta soyayyaba, daga Munaya har aunty Mimi basu San komaiba, dan haka sukaji dad'i da sakin jikinsu fiye
da sauran matan sarki.
Daga nanan sai sashen Mama Fulani, (kaga manya, Sarautar gagara badau a hannunku take, mama fulaninmu ta mutunci
🤸🏻
♀
😂
, ga irin naku manyan mata
👍🏻
)
To kunsan dai mutuniyar taku, yauma dai cikin izzar mulkinta suka i
sketa, ita dama Aunty Mimi babu ruwanta, tana mata yanda takeso, shiyyasa babu y'ar habaici ko bak'ar magana tsakaninsu kamar Galadima, hakanne yasaka munaya samun tsira daga samun nata rabon, amma mama Fulani bata d'auki yaro ko d'aya ba, a hannun kuyangi
n ta gansu tana ta6e baki.
Daga Munaya dai har aunty Mimi babu Wanda yay ko tari, to balle kuyangi dasuka zama takalmin takawarta, basu jimaba suka fito, haka sukaita zuwa sashe-sashe, basu sami Kansu ba saida suka Shiga ko ina .
Sun dawo kusanda
awanni biyu aka gama loda kayansu a mota Samha da Sauban suka shige gaba aka kai gidansu Munaya. Ita kuma sai zuwa yamma za'a mata rakiya.
************
Gidansu Munaya dai tunda kaya suka isa aka tsaya kallon-kallo, daga Sauban kam har Samha babu
Wanda yamusu kallon arzik'i, yo sunaji da hayak'in girma dana mulki, innarsu Munaya da Munubiya da tuni tana gida kawai suka kula, harda sakin jiki dasu sukaita hira, sunmayi zamansu anan sai ankawo Munaya zasu koma.
Nanfa matan gidan suka fara
k'ananun magana, saidai babu mai yunk'urin d'aga murya saboda tsaro
🤣
.
Oho innarsu Munu ma batasan sunayiba, balle Munubiya da yanzu saita ma gadama suke ganinta, ko yaushe tana d'akinsu, da anyi magana tace jego, dukda gasu Fiddausi a gidan duk suna
wankan suma, Fauziyyace kan shigo susha hirarsu ta zuminci, amma sauran saidai idan an had'u a gaisa, kowa uwarsa Na kitsa masa munafurci a d'aki (
🤦🏻
♀
gaskiya iyaye mata munada gyara babba ta wannan fannin, inhar zaka rayu gidan yawa sai kayi gamo da ir
in wad'annan matsalolin kuwa, ALLAH ya ganar damu baki d'aya dai).
******************
Su gadima Na shigowa masarauta ana kiran salla, hakanne ya sakasu yada zango a massalaci, saida aka idar sannan suka k'arasa sashensa, Duk agajiye yake, d
'akinsa daret ya nufa, yashiga zame kayansa tun a falonsa, yana shiga ciki k'arasawa kawai yayi yashige bayi.
Ya dad'e aciki kafin ya fito, baiko cire rigar wankanba yasha wani Magani ya kwanta, dan kansa ciwo yake masa. Cikin mintuna k'alilan barci
yay gaba dashi.
Munaya batasan ya dawoba, d'okin zuwa gida ya hanata barcin ranarma ita, sai yawan duba lokaci takeyi
😂👍🏻
.
*_3:35pm_* Galadima ya tashi, saboda kiran wayarsa da akayi, idonsa a lumahe ya d'aga, a haka suka gaisa da Momma, ya ta
mbayi Abie tace barci yakeyi, sunyi wayar kusan mintuna 15 haryaso makara fita sallar la'asar.
Bayan yadawoma papi ya kira suka tattauna, sannan yakuma sabon shiri cikin Orange d'in yadi anmasa kwalliyar bak'i kad'an, yayi k'yau sosai, sai tashin k'
amshi yakeyi, saidai fusakar kam babu alamun yasan miye dariya.
A haka ya iso sashen Munaya, babu kowa daga ita sai yaranta da Khaleel dake barci a gefensu, itako wayama take latsawa, da alama game takeyi Kodai wani Abu.
Sallamarsa ciki-cik
i da k'amshin turarensa ya sakata d'ago ido suka kalli juna, yawani Basar yana shan k'amshi, hakanne yasaka Munaya sake kama kanta, ta gaisheshi, sau d'aya ya amsa ya zauna a bakin gadon yana shafa kan yaran d'ai-d'ai harda Khaleel.
Handbag d'inta da
mayafi dake ajiye alamar lokaci take jira kawai ya kalla, baki ya ta6e ya d'auke kai.
Key d'in mota guda biyu ya fiddo a aljihu ya jefa min akan cinya.
Ni harma Na tsorata na kalli keys d'in sannan Na d'ago na kallesa.
d'auke Kansa yay
daga inda nake, cike da k'asaitarnan tasa yace, bak'in kibama Abba, d'ayan kuma ki ajiye a wajenki, motar tana can, saboda ko wani abu yataso musamman kai yara asibiti sai wani ya kaiki cikin yayyenki, ki kulamin da yara, kuskure d'aya kikayi a kansu zand'
au mataki mai tsaurine, duk abinda zuciyarki batayi na'am dashiba ki gaggauta kirana na sani, ki kula da Abdurraheem sosai, banda barinsa yana dogon kuka saboda doctor ya sanar mana yana d'auke da ciwon......”.
Saikuma yay shiru yana furzar da iska
r bakinsa.
Masifar tsura masa ido nayi zuciyata Na bugu tamkar zata fad'o dan tsoro, sai tsuma nakeyi, babu shiri na taso na dawo inda yake, durk'ushewa nayi gabansa tamkar mai neman gafara, “Yalla6ai ciwon mi? Please ka k'arasa fad'an dan ALLAH”.
lumshe idanunsa yayi yana cizar lips, “Ba abin tada hankali baneba ai, domin ALLAH daya d'ora mana yafimu sanin hikimar hakan, bagashi ni nakai lokacin da Magauta basuyi tunaniba”.
Maganganunsa ya nuna minta cewar Abduraheem Na d'auke da Ciwon
zuciya? kenan shima yayo gadon mahaifinsa?”.
Matsowa nayi na fad'a jikinsa na sanya kuka, bashida za6i saina kar6ata shima ya rungumeni cikin yima Ubangiji tasbihin Neman dauriya da kar6ar jarabawa a duk yanda tazo. Bai hanani kukanba saida nayi mai
isarta sannan na share hawayenna. d'agowa nayi daga jikinsa zan tashi amma saiya hanani hakan, cikin kunnenna yace, “Baki da kunya gaskiya, ban ta6a ganin uwa mara kawaici akan y'ay'an fariba saike”.
Kunyace ta kamani, na 6oye kaina a jikinsa ina
murmushi.
Galadima ma murmushin yake yana shafa bayanta.
Sun dad'e a haka sannan na tashi daga jikin nasa gudun kar khalel ya farka ya ganmu a haka, shima ya fahimceni, dan haka bai hanani ba.
Yace, “Addu'arki yake buk'ata da taka tsant
san, dukda ba wayonmune zai hana Ubangiji ikonsa ba idan yaso, sai yakai watanni 6 zai fara ganin doctor insha ALLAH, ya mik'a mamin ATM d'insa, ga wannan dukdai abinda yataso saiki cira, amma a bimin kud'i a sannu ni talakane mai yawan buk'atu, ga Abdurra
heem ya k'aru shima, to idan bawa bai nema kud'iba ai yagama shiga uku a wannan zamanin daba kowa ya damu da damuwarka ba, inadai kuma gargad'inki ki kula min da yara, yau zamu koma India, amma kwanaki uku zanyi insha ALLAH na dawo”.
Nace, “ALLAH
yabashi lafiya da dukkan al'ummar ANNABI, nagode sosai, saidai kuma inason kawai idan na tafi shi.......”
Hannu ya d'aga min, “karki damu nasan maganar Aurenmu ne, kamar yanda na alk'awarin inhar komai ya fito kan shekara zamu rabu, inkuma ba a samu
yanda akesoba shekara biyu inakan Sani, sauran bayani kibani lokaci zuwa kammala abinda ke gabana OK?”. ‘yay maganar yana kallonna’.
Kaina kawai na d'aga masa ina had'iye abinda ya tokare mak'oshinna.
Bai sake cewa komaiba ya mik'e yana kallon
agogon hannunsa bak'i, “ku fito”. yafad'a yana ficewarsa.
Da kallo kawai nabisa idonna yana cika da k'wallan dabasan na minene ba.
**************
Munaya tasamu rakkiyar wasu daga masarautar, bisaga jagorancin Galadima da suke zaune a mo
ta d'aya, daga ita har shi babu Wanda ya tankama wani koya kalli wani, shi tundama suka fito latse-latsen System yakeyi hankalinsa kwance, itama ta basar gefe tana kallon waje dukda glass d'in mai duhune.
Sun Isa k'ofar gidan k'arfe 5:24pm, bay
an su Aunty Mimi sun fita duk suka shige cikin gidan tareda Kuyangi.
Munaya tayi yunk'urin fita amma sai taji motar a kulle, Sarkin Mota ta kalla sai taga harya fice, ta dawo da kallonta ga Galadima daketa aikinsa tamkar ya manta a mota yake.
Shareshi nayi kamar nima bazanyi magana ba kamar yanda ya basar, amma saina kasa, na kuma kallonsa murya a sanyaye nace, “ka bud'emin mana, miye ma'anar zaman namu? Wanima saiya zargi wani Abu ai?”.
Banza yay mani tamkar bazai tankaba, kusan mintu
na biyu sannan yace, “idan sun zarga laifine? Naga Sadaki na biya”.
“Hummm”. Munaya ta fad'a kawai tana d'auke kai.
Saida ya gama shan k'amshinsa sannan ya ajiye lap-top d'in gaban motar yana matsoni. da mamaki na kallesa, “yalla6ai lafiya?”.
“ita ta kawo haka”. ‘yafad'a yana wani ciccijewa da jawoni jikinsa’.
Tamkar zan tsala kuka haka naji, dan naji zafi, mukaima juna kallon ido cikin ido, idona da kwalla tafara taruwa sai wani marmar yakeyi, matso da fuskarta yay sosai, cikin
magana rad'a yace, “kin fara kewata ne?”.
Baya naja da kaina ina tura baki da yamutse fuska, amma sai hannunsa daya sa ya tokareni ya dakatar dani daga matsawar, yakuma matsowa gaf, numfashin junanslmu na sauka a fusakar juna, a hankali yafara hura
min iskar bakinsa saman ido, babu shiri na lumshesu, hawayen da suka taru suka zubo, sai kawai ya shiga sumbata ta.
Tuni nabashi had'inkai babu wani gardama, saida yay yanda yakeso da ni sannan kowa yakoma gefe, wata y'ar k'aramar souvenir bag y
a d'ora mani a cinya, sannan ya cire luck d'in motar, saida naja wasu Seconds nasamu dai-daita sannan ta bud'e na fice rik'eda bag d'in daya bani, ban yarda nasake koda kallonsa ba.
Shima harta fice bai kuma kallon nata ba.
Jiki a sanyaye
nashiga gidan, matan gidanmu duk suna falon innarmu gaida bak'i, ina shiga muka rungume juna nida Munubiya muna hawayen da ita Munubiya tana tayani ne, nikuma bansan dalilin yinsuba
🤣
.
Kowa dai da kallon mamaki ya bimu kawai.
Su Aunty Mimi
basu dad'eba sosai suka tafi, anbar laraba anan zata zauna damu.
Samha da khaleel harda kukansu.
**************
Bayan komawar su Galadima masarautane yakejin wai ba'aga Harun ba, k'ala bai tofa ba balle nuna alamun damuwa ko jimama
.
Saima shirinsa Na tafiya ya fara hankali kwance, yaje yayma mai martaba sallama. Suka wuce airport abinsu, dan jirgin 7:30pm zasubi.............
✍
🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu
😭👏🏻
_*
*_typing
📲
_*
💡
*_HASKE WRITERS
ASSO....._*
*_
♦
RAINA KAMA.....!!
♦
_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
~BOOK 3~
👉🏻
7
⃣
& 8
⃣
...............Galadima ya shigo murmushi d'auke a fuskarsa, dattijon dake zaune a falon
ya d'ago ido yana kallonsa shima fuskarsa d'auke da murmushin, k'arawa Galadima yayi garesa, ya zauna kusa dashi yana fad'in “Baffina kanata jirana ko?”.
Kafad'arsa dattijon ya dafa, yace “karka damu d'an baffinsa, nasan aiki mai muhimmanci ne ya t
saidaka. ya k'ok'ari?”.
“Alhmdllh baffi, munata fama”.
“ALLAH ya dafa mana, yanzu ina shi Darma?”.
“Gashi a waje tareda ma'aikata, zamu jira zuwan Sir Isa ne, dan asan miya kamata, bazai yuwu mu had'ashi da su Harun ba”.
“Uhm ha
kan shine dai-dai kam, amma yakamata suma bayanansu kagama tattarasu waje d'aya ka kawomin, kasan abubuwa zasu cud'e mana a tsakaninnan, dan fatana insha ALLAH wannan shine case Na k'arshe dazan fuskanta a rayuwar aikina, shekara 1 kacal ya ragemin cika ta
latin a matsayin lauya, insha ALLAH kuma zan cikasune bisa alk'awarin gurfanar da dukkan mai hannu akan mai martaba”.
Murmushi Galadima yay, idonsa cike da kwalla, ya had'iye Abu mai d'aci yana fad'in “ALLAH ya cika maka wannan buri baffi, lallai
ina alfahari dakai amatsayin uba, Kaine ka nunamin hanya alokacin da k'ofa ta rufe min, Kaine ka tsallakar dani a lokacin da gada ta karye ina tsaka da tafiya, ga kuma gagarumin hadad'i mai cike da tarnak'in iska ya taso, badan kaid'in ba da jajircewarka d
a yanzu ruwan daya zuba ya shafe da tarihina dana ahalina, da ace wani zai saurari labarina saiya d'auka labarin film ne ko novel, ni karan kaina nakanyi zaman yin tunanin anya akwai mai irin rayuwata a k'asarnan? Dan mafi yawa a tatsuniyoyi da hikayoyi ak
ejinsa, saikuma abin mamaki ga nawa a zahiri, a yankin k'asar hausa, yanki mai tsananin ruk'on addini da Al'ada, yanki mai mutunta ahali da zuminci, inhar a shekaru 26 baya za'a iya samun masu irin ayyukan su tanderu lallai akwai abin tsoro kenan a k'arni
nagaba da y'ay'anmu zasu mu'amulanta, Baffi da ace d'an Adam Na iya za6ama kansa rayuwa da banzo cikin ahalin jinin sarauta ba, amma Alhmdllh, ina godiya da Ubangiji daya halicceni yakuma San cancantar fitowa daga cikinsu.......”. kukane ya sark'e Galadima
, Baffi ya mik'a masa handkerchief yana girgiza masa kai alamar kar yayi.
Murmushin takaici Galadima yayi, sannan ya kar6a handkerchief d'in ya tsane k'ananun hawayensa.
Baffi yace, “Muhammad Sameer akwai labarai da tarihin mutanen da yafi naka
sark'ak'iya da hargitsi wlhy, sometimes abinda mukan gani a films ko hikayoyin marubuta akwaishi azahiri, saidai inhar bai faru akanka ba ko waninka saikaga tamkar k'anzon kuregene, kasan su mutane sunfi amfani da abinda suka gani da ido wato zahiri, ko su
ka San Wanda ya Sani wato tabbaci, a shekarun da nayi INA aiki nahad'u da cases da dama masu sark'ak'iya da ban tsoro, nakuma halarci kotuna da Dama domin ganin wasu cases d'in, idan ka samu wani case kai kanka saika ringa kokwanton anya kuwa wannan da gas
ke ya faru d'in? Amma daka tsananta bincikema saikaga abinda yafi Na farko mamaki, lallai a ranar gobe kiyama wasu zasu kasance cikin bayi masu tsananin kunyata agaban Ubangiji, Dan wata shari'a Ubangijine kawai mai iya mata, mu kammu acikin lauyoyi da alk
'alai hummmm”. Baffi ya d'an bubbuga kafad'ar Galadima yana murmushi cikin takaici.
Bai samu damar k'arasa magana ba akayi sallama, izinin shigowa ya bada, wani matashin dattijo da shekarunsa bazasu gaza 45 ba ya shigo, baikai girman baffi ba, sannan
ya girmi Galadima sosai.
Mik'ewa Galadima yayi yay salute nashi, dattijo ya murmusa yana kama hannun Galadima ya zaunar da fad'in “ni da kai adai bincika mai sarama wani”.
Baffi yay dariya, “kudai kuka Sani da gardamarku wacce kullum bata k'ar
ewa inhar kun had'u”.
Bak'o mai amsa Sir Isa yace, “wai Yaya naga alhaji Rabilu zaune a waje suna sa'insa da banzan can?”.
Nanma dai baffi ne Yakuma darawa, yace, “duk cikin aikine, dukkan wata magana dazai takalesa ya fad'a ai itama hujjace
, kasanfa halin Alhaji Rabilu ai, shiyyasa nace masa da irin aikinku ya dace ba siyasa ba”.
Sir Isa da yay dariya shima, yayinda Galadima ke murmushi, “Ai yalla6ai yanzu ma aikin dayake mana bashi da banbanci damu d'in, danya bamu damar sanin abinda
tsawon shekaru muketa wahala da kaikawon sani”.
“Wannan gaskiyane kam Isa, yanzu Yaya za'ayi da Darma kenan?”.
Sir Isa ya gyara zamansa, yana saka d'an yatsa a baki alamar tunani, zuwa can yace, “inaga kam saidai mu nema wajen ajiyes
a ko yalla6ai ya Adana mana shi, dan yakamata saimun kammala tattara komai a hannunmu bayan yalla6ai Galadiman mu ya dunk'ule kifaye a ragaya, idan sun mik'a wuya shima sai a sakashi a ayari ko?”.
Baffi yace, “shawararka tayi kam, inaga yanzu abinda
kasaba za'ayi, dan aiki da ilimi yafi aiki da agogo, kaike 6oyewa, kuma kaine akesa kanemo 6oyayye”.
Murmushi Galadima ya sakeyi baice komaiba sai jinjina kai. Duk d'insu