Showing 165001 words to 168000 words out of 407268 words

Chapter 56 - Raina Kama COMPLETE

Sameer”.

Murmus

hi kawai Galadima yayi, amma baice uffanba.

Knocking akayi, Nuren ya kalli k'ofar yana bada izinin a shigo, Sauban ya shigo da sallama, su duka idonsu a kansa, Nuren yace “lafiya kuwa?”.

Zama Sauban yayi yana sauke Numfashi da k'yar, cikin m

agana d'ai-d'ai da alamar a birkice yake yace, “wlhy Yaya binmu aka ringayi da wata bak'ar Jeep, da k'yar mukasha wlhy, ni dai yau zanbar k'asarnan gaskiya”. Sauban ya fad'a tamkar zaiyi kuka’.

Gani kawai sukai Galadima yana dariya, saida yayi mai

isarsa sannan ya tsagaita.

Nuren da Sauban suka tsaya kawai suna kallonsa.

Tashi yayi tsaye yana takawa cikin izzar k'asaita, ya dafa bango yana lek'en waje ta window d'in office d'in, yakai wasu adadin lokuta a wajen, sai kuma ya juyo yana kal

lon Nuren d'in da Sauban da suma suka zuba masa idanu.

“my dear brother! daka tsaya sun kamaka ai, tabbas da wannan shine kuskuren da zasuyi Wanda bazasu ta6a mantawa da waye Muhammad Sameer Saifudden ba a tarihin rayuwarsu. Waya gaya maka kana yawo

cikin 9ja ne batareda idon Sameer ba a kanka?”.

Sauban ya sauke ajiyar zuciya yana share gumin daya jik'a fuskarsa, “wlhy yaa Sam daka fad'amin da bazan tsorata ba”.

Daga Galadima har Nuren dariya suka kwashe da shi, Nuren ya dafa kafad'ar Sau

ban yana fad'in “matsoracin banza”.

“uhm-uhm yaa Nuren bazaka ganeba wlhy, tsoro halak ne fa”..

Galadima dai baice komaiba ya koma ya zauna yana murmushi.



)))*(((



)))*(((



)))*(((



)))*(((



Ganin har anyi sallar Magriba

babu baba k'arami balle Dady ya saka Innaro d'aukar gyale ta fito, lokacin gwaggo Safiyya tana salla, shiyyasa batasan innaro ta fitaba, habiba da Naja'atu dake tsakar gida suna tattare kaya saboda hadari na farkon damina dayake nuna alamar zai zubda ruwa.

suka kalli juna, Naja'atu tace “yaya habiba tsohuwarnan fa bata da dama wlhy”.

Dariya habiba tayi, “ai kad'anma kika gani Naja'atu, yanzu dai zataje ta tadama baiwar ALLAH hankali”.

“to ALLAH ya k'yauta”. ‘cewar Naja'atu tana rik'e ha6a’.

Lokacin da Innaro ta shigo gidan d'akin Innarsu Munaya ta nufa kai tsaye, sai dai ta iskeshi rufe, kwala kiran sunanta ta shigayi cikin masifa, “Ai'sha!! Ai'sha!! Nasan kina jina, wlhy ki fito kafin yau d'innan igiyar aurenki ta tsinke”.

Mam

ansu yaa Hameed da gwaggon Haleematu ne suka fito, mamansu yaa hameed tace “aiko tafita fa inna, dan gab da magribar nan naga Fadeel ya shigo sun fita, bansan mike faruwa ba dai”.

“yaza'ayi kusan mike faruwa tunda anyi k'ulle-k'ullen munafunci, lall

ai jafaru, wai yau da kaine za'a muzantani hannun mak'iyana, to nikuma naga ta yanda Ai'sha zataje wata k'asa jiyyar Auwalu da raina”........ haka taita zuba banbamin masifa matan gida na saurarenta, daga daddy har baba k'arami suna gidan amma sukak'i fito

wa. Jarabar Innaro ta saka kowa na gidan fahimtar mi ake ciki, nanfa hassada da bak'in ciki suka kume zukatansu, dukda kuwa sunsan tafiyar bata dad'i baceba, maman fauziyyace kawai hakan yamata dad'i, koba komai inna ta huta da cin zarafin Innaro koyayane.



Sai da Gwaggo Safiyya ta shigo tama Innaro magana sannan ta tafi gida, su matan gidanma sai yanzu suka San da zuwa gwaggo Safiyya d'in.

Amma sunso ace innarsu munaya na gida Innaro tayi wannan rashin mutuncin.



Hummm

😕

.



****************************

Bayan fitowar su Galadima daga birnin gayu, sun wuce gidane, Nuren kuma yakoma hotel d'in daya sauka.

Galadima kawai ne ya shiga sashensu, amma Sauban 6angaren mai martaba ya nufa neman yarima Mahfuz.



Munaya na zaune a falon farko tareda sabbin kuyanginta guda uku, (dan bata amince su shiga falonta ba, saita gama tantance su sannan) ba wani hira

sukeyiba, d'ayace a cikinsu ke sak'a shine abin ya birge Munaya take kallo, tana kwance cikin d

oguwar kujera ne, yayinda su kuma su ke zaune a k'asan lallausan carpet d'in falon.

Dogarai biyune suka fara shigowa hannunsu d'auke da ledoji, sai kuma mai gayya mai aiki Galadima.

Da sauri bayin suka mik'e tsaye, saida ya ida shigowa sannan

suka d'urk'ushe a k'asa suna kwasar gaisuwa.

A la66ansa ya amsa yana d'aga musu hannu, yayinda idanunsa ke kan munaya da itama ke satar kallonsa

Duk d'insu kowa janyewa yayi, yayinda bayin da dogaran suka fice bayan sunkai ledojin falon Galadi

ma.

Baice da ita uffanba yafara takawa zai shige, tamkar mai tsoron fad'a tace, “sannu da zuwa”.

Ysayawa yayi cak, sannan ya juyo da kansa tamkar mai ciwon wuya ya kalleta, bata yarda sun kuma had'a idoba takuma fad'in “nagode sosai”.

“for

what?”. ‘ya fad'a cikin isa’.

Shiru munaya tayi, ta kasa cewa komai.

Shima bai sake cewa komai ba ya taka ya shige abinsa.

Harara munaya ta raka bayansa da shi, sai kuma ta sauke numfashi tana tashi itama, bedroom d'inta ta koma, a sama

n sofa ta zauna tana dafe kai, sosai take buk'atar zuwa sake duba mahaifinta, amma ta kula Galadima bashida niyyar cemata taje, kai itako wannan wane irin abune haka? shi dama gidan Sarautar haka yake bakada 'yancin kanka?, komai saida k'a'ida. tun d'azu k

uma take kiran number inna bata d'agaba, tadai kira baba k'arami da daddy sun gaisa ta tambayi jikin Abba, shine ma har suke kuma sanar mata k'ok'arin da galadiman keyi. tabbas hakan da yayi yasata jin farin ciki, koba komai tasan shi adaline, ko anan gaba

ragamar shugabanci ta riskesa zaiyima na k'asa da shi adalci.

Galadima daya shiga tun a falo yafara k'ok'arin cire navy blue d'in jacket d'insa, ya wullata saman kujera, sassauta belt d'in yayi shima amma bai cireba, ya zauna cikin tsantsar nu

na gajiya yana furzo iskar bakinsa, remote ya d'auka ya kunna tv, tamkar ya saita lokaci saiga hoton d'iyar minister mai amsa sunan Farhat ana nunawa, an saka 2.5 millions ga dukkan wanda ya kawota koya bada bayanan sirri akan wanda yasan wani Abu akan 6at

anta.

Wani mugun tsaki Galadima yaja a zuciyarsa yana fad'in wawaye, saiku k'ara yakai 100millions ba 2 ba, idan ubanta ya shirya kawo kansa gareni nima a shirye nake nabashi shashashar 'yarsa mai zubin ta6arya, ya kashe TV d'in kawai ya mik'e ya shig

e ciki.

Ko ina fes da shi, yasan baida Matsala da Sauban a 6angaren tsafta dama. kayan jikinsa ya ida cirewa ya shiga wanka.

Bayan ya fito samu yay yad'an kwanta, dan ya samu Hutu kona 2hours ne, dan yanzu akayi sallar zuhur. aiko kwanciyarsa ba

bu dad'ewa barci yay gaba dashi.

Munaya ta jawo wayarta da nufin kuma kiran inna, amma sai taga Ashe credit d'inta yama k'are, kanta ta dafe dan haushi, zuwa can tamik'e domin bin shawarar zuciyarta. turare ta kuma fesama jikinta ta d'auki gyale ta

yafa.

Ta d'an dad'e a k'ofar d'akin tana tunanin idan kuma ta shiga hasashenta bai zama gaskiyaba ya kenan?, wata zuciya tace kije abinki k'ilama wanka yake.

Da sand'a na ida shiga tamkar wata 6arauniya, sai kuma na tuna ai yanada CCTV cam

era, nutsuwa nayi na daidaita kaina, na koma normal saboda tsaro. Ganin babu abinda naje nema d'in a falo saina zarce bedroom ina wani ciccijewa.

Mamaki ya kamani ganinsa kwance a kan gado yana shak'ar barci hankali kwance, hakan yamin dad'i kam.



Saida nabi ko'ina na bedroom d'in da kallo, ganin babu alamar akwai camera a nan saina ida shiga, wayoyinsa biyu na ajiye gefen filon dayake kwance, rabin hannun damarsa ma nakan d'aya ya d'ora cikin barci halan?.

Dole saina hau saman gadon, dan

haka na tsaya tunanin yanda zanyi, banida wata mafita dan haka nahau a hankali, kai kace wata hawainiya ce.

Cikin rintse ido da cije la66a nakai hannu zan d'auki wayar d'aya.

Caraf aka rik'emin hannu, babu Shiri na bud'e idona zuciyata nawani

tsitstsinkewa.

Fisgoni yayi na fad'o jikinsa, zafin danaji ya sakani sakin k'aramar k'ara.

Ya matseni a jikinsa batare da ya kula miya aikata ba. nikam jikina sai rawa yakeyi, tsorona karya d'auka ko cutar da shi zanyi ma........ maganarsa

cikin yanayin barci ta Sani kallonsa.

Kad'an ya bud'e idonsa dake jajir, alamar da gaske barci yakeyi, muryarsa a sark'e irinta barci yace, “sata kika koma?”.

Baki na tunzuro ina marmar da idanu da suka cika da kwalla, nace “ALLAH ya kiyaye, a

rafa zanyi”.

Kuma matseni yayi har saida na rik'e hannunsa,, yace “wannan ba aro bane sata ce yalla6iya, dan haka dolene ki kar6i punishment”.

Jin ya ambaci punishment saina kuma rikicewa, nahau k'yarma ina rantse-rantae da matso kwallan idona

.

Bai wani saurareni ba ya hau sumbatar wuyana, tureshi nafarayi amma saina gaza, dan haka na koma mintsini, shima a banza man kare

😩

.

Dukna d'auka wasa yakeyi kawai farfaganda Ce danna tsorata, amma saina tsinci ya fara sakin layi, iya yina

da rok'o, yakushi, mintsini, ban samu ku6uta ba, saima salonsa yafara tasiri a kaina, nima nai luf harda k'ok'arin maida murtani. saida naji zai kama wata tashar nai azamar tsaidashi ta hanyar fad'in “please yalla6ai camera”.

Maganinki ai bab

y

😝

, su Galadima akwai bak'in wayo dai

🤥😂

, idan ta gaskiya za'abi ni banga abin punishment anan ba

🤣

, dama yadawo 'Yar matsalarsa dai tsautsayi ya kawo mai karanbani dason banza ta fad'a tarko

😜

🥳

😆

.

**********



********

Koda inna ta dawo sa

ita had'ama su Aryaan kayansu, da nufin su koma wajen mamansu yaa hameed harta dawo.

Amma suka tibire akan bazasu jeba, su Uncle yace zaizo ya kaisu wajen Auntynsu.

Tun inna na lallashinsu harta kai ga mammakesu suka fara kuka, daga nan sukai ba

rcin dole.

Bata fasa had'a kayanba, tagama tsaf ta d'auki akwatin zuwa d'akin mamansu yaa hameed.

Su Bintu kawai ta iske a falo suna kallo, Aminu ne yace “innar 'yan 2 ina zaki da daddare?”.

Murmushi inna tamasa tana fad'in “kayansu Aryaan n

e Aminu........”

Bata gama rufe bakiba mamansu yaa hameed ta fito. ganin innarsu munubiya da kaya saita had'e fuska. Inna bata damuba tace “ga kayansu Aiyaan, saisu dawo nan da zama kafin na dawo”.

“to”. Kawai mamansu yaa hameed tace tana kauda k

ai gefe.

Ran inna ya sosu, amma sai batace komai ba ta ajiye ta fice jiki a sanyaye.

Da murnar Haneeff ya tashi zai d'au jakar yakai d'akinsu, amma sai Maman ta watsa masa harara. babu shiri ya koma ya zauna. Jakkar dai sai anan ta kwana, bata d'a

uka ba, bata bar 'ya'yanta sun d'auka ba saboda bak'incikin inna zataje jiyyar Abba ba itaba.

ALLAH ya k'yauta

😡

.

****************************

Dakatawa yay daga abinda yakeyi, ya bud'e idanu a hankali akan fuskata, murya k'asa-k'as

a ya furta “camera?”.

Kaina na d'aga masa batareda na bud'e idoba.

Bai kuma cewa komai ba ya koma ya kwanta yana furzar da huci mai zafi daga bakinsa, sai kuma ya cije lips yana gyara kwanciya da sake rungumeni kawai.

Idona na bud'e a tsor

ace, azatona zai cigaba ne, sainaga ba haka bane.

A cikin kunnene ya furta “barci please”.

Kallonsa nayi ta gefen ido sai naga idonsa a rufe, nima banida za6in daya wuce na rufe nawan, dan haka na lumshe kawai.

Ni sai barcin ya d'aukeni

, amma shi ya k'auracema idonsa, mamakin furicina ya dami zuciyarsa, dama yadad'e yana zargin akwai camera a d'akin nan nasa, sai dai bawai ya tabbatar bane, kuma bai ta6a yunk'urin dubawa ba. da wad'annan tunanin ya cinye lokacin barcinsa har aka kwala ki

ran sallar la'asar.

Bud'e idanunsa yayi akan fuskata, yad'an tsuramin ido nawasu time's, sai yaga barcin yamin k'yau, kauda idonsa yayi cikeda basarwa, saikuma ya janyeni daga jikinsa yana yunk'urin tashi, hakanne ya sakani farkawar nima, na tashi da

hanzarina ina gyara rigata, sai kuma na sauka na fice batareda nako waiwayoshi ba.

Bina yay da kallo harna fice sannan ya janye yana ta6e baki.

Ban kuma jin labarin Galadima ba har dare yayi, nafito wanka ina shirin barci ya shigo, yau dai

babu laptop d'in kaddara, dagashi sai phone guda d'aya ma, yana sanye da kayan barci kalar gwaiduwar kwai masu duhu.

Zama yay a kujerar dake cikin d'akin, yayinda ni kuma na k'arasa saka hijjab d'in dana jawo, babu walwala ko alamar wasa kwata-kwat

a a face nashi, dan haka nima saina kama kaina.

cikin k'asaitarsa yace “muyi magana mana”.

Kallonsa na d'anyi, saikuma na amsa da “ina jinka”.

d'ago ido yay muka kalli juna, da ido yay min nuni da bakin gadon.

Ban musaba nazo na zau

na, amma sai nayi k'asa da kaina ina wasa da zoben hannuna.

Maida kallonsa yayi ga zoben danake jujjuyawa, kusan mintuna 4 harna d'auka ya ma fasa maganar, na d'ago na kalleshi.

Ya kauda kai gefe yana fad'in, “waya fad'a miki da CCTV camera

a d'akina?”.

Nima ban kalleshi ba na bashi amsa a tak'aice, “bakai ka saka kayarka ba danni?”.

Da mamaki ya kalleni, sai kuma ya kausasa muryarsa, “Munaayaa seriously nake miki magana!”.

nad'an razana, amma saina dake, nace “kana nufin

bakasan da itaba?”.

“idan nasan da ita mizai sani aikata wani Abu na sirrina a d'akin”.

da mamaki na kalleshi domin tabbatarwa, tsantsar gaskiya na hanga a idonsa, dan haka na danna yatsun hannuna da k'arfi suka bada sautin “k'asss!, k'asan z

uciyata na tunanin minene sirrin nasa?”.

Idonsa a kaina ko k'yaftawa bayayi, nima na d'ago mukaima juna kallon ido cikin ido, dukda tsorata danai da hango masifa cikinsu ban janyeba, nafara fad'in “tabbas naga camera a falonka, tana nan saitin hoton

ku kaidasu momma, inda flower d'in nan take, hakanne yasani zargin kai ka saka kayarka saboda tsaro”.

“hummm”. kawai yafad'a yana janye idanunsa, sai kuma ya taso ya dawo inda nake zaune, ganinai kawai ya rungumoni jikinsa, na waro idanu dan mamaki,

shikuma ya lumshe nasa tareda sumbatar goshina a hankali, shigar sumbarce tasakani lumshe nawa idanun nima tareda k'ank'ameshi.

Cikin kunnena ya furta “i'm proud of you my friend”.

Da sauri na waro idanu ina kallonsa, saiya d'agamin gira d'a

ya yana wani miskilin murmushi, sannan ya tadani zaune shima ya tashi ya fita.

Baki da idanu da hanci duk na saki ina binsa da kallo, a k'asan raina ina tambayar mike damun guy d'innan ne wai?.

Banida mai bani amsa, dan haka na mik'e na cire

hijjab d'in nai kwanciyata.

d'akinsa ya koma ya d'akko wani Abu kamar k'aramar ball

🎱

ya ajiye saman table d'in gaban gadon, sannan ya manna wani dogon Abu a jikin 'Yar ball d'in, ya d'akko laptop d'insa ya kunna. shiru na kusan mintuna uku ya k

'urama abinnan ido, zuwa can yafara wata k'aramar k'ara d'i! d'i! d'i!, sai kuma k'aramar danja ajikin abinda ya manna d'in shima tana kawo haske jaa da d'aukewa.

Murmushin takaici kawai yayi, a zuciyarsa yanama ALLAH godiya dabai ta6a kusantar Muna

ya a d'akin nanba. dan tabbas ga CCTV camera ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login