Showing 384001 words to 387000 words out of 407268 words
Erfan Fahad yanata murmushinsa.
A k'ofar falo ya tsaida Galadima, tareda fidda handkerchief a aljihunsa yace Galadima ya rufe idonsa.
Da mamaki Galadima ke kallonsa, amma yagaza furta komai.
Dr Erfan Fahad
ya jinjina masa kai da had'e hannayensa alamar rok'o.
Ruf Galadima ya rife idonsa, Dr Erfan Fahad ya saka handkerchief d'insa ya d'aure masa ido, sannan ya kama hannunsa suka shiga ciki.
A tsakkiyar falon ya tsaidashi, ahankali yace, “my fri
end are you ready?”.
Cikin sauke numfashi Galadima ya d'aga masa kai.
Dr Erfan Fahad ya murmusa yana kwance masa handkerchief d'in sannan yace, “Bud'e idonka”.
A hankali Galadima ya shiga bud'e idanu, harya bud'esu gaba d'aya akan k'yak'y
k'yawan dattijo zaune bisa kujera, fuskarsa ta k'awatu da murmushi, yasha gyaran fuska mai k'ayatarwa, sai gashi kad'an mai adon furfura da aka bari ya zagaye fuskarsa.
Wata zabura Galadima yay mai kama da firgita, Dr Erfan Fahad yay saurin tarosa, Da
n kad'an yarage ya zube a k'asa.
Cikin rawar baki data jiki yake kallon dattijon, dak'yar ya iya fusgo numfashi da magana mai cike da in'ina daga bakinsa “A..b..ie k..ai.ne?”.
Abie ya share hawayen da shima suke ziraro masa, cikin tsantsa
r so da k'aunar d'an nasa yabashi amsa da fad'in “Tabbas nine Muhammad Sameer sanyin idaniya, Abie d'inka ne zaune yau agabanka, Wanda ya tashi cike da hukuncin Ubangiji gagara misali”.
Galadima ya maida kallonsa ga Dr Erfan Fahad.
Murmushi D
r Erfan Fahad yayi, “Karkayi kokwanto da ikon ALLAH Sameer, shike kwantar da Wanda yaso, Yakuma tasheshi a lokacin da yaso, dama ba'a yankema rayuwa hukunci, mai jiyya saiyayi rayuwa mai tsayi amma mai lafiya a wayi gari yazama gawa, ciwo bashi bane mutuwa
, kwanaki 10 kacal Na d'auka ina treatment d'in Abie ga66ansa suka fara aiki, a sauran sati uku danayi tare dashi muna koya masa yanda zaiyi tafiyane, da zama, d'aukar Abu, da sauransu, Dan duk ga66ansa sun manta, kamar yanda ka sanarmin addu'ar da kukaita
masa lallai itace babban magani daya zama mai tasiri a garesa, domin nikam abinda ba'a rasaba Na k'arasa, duk Wanda yabar addu'a lallai dole matsala tazama ma'abociyar rayuwarsa, a yanzu haka ina mai tabbatar maka Abie zai iya tafiya dayima kansa wasu abu
buwa, amma bamasu yawaba, tafiyarma bamai tsaho ba, Dan yawanyin ne zai bama ga66ansa kwari da sabo, shekara 26 mutun Na kwance sai na'urori ke sarrafashi ba k'aramin Abu bane Sameer, Dan dolene akira Abie d'an baiwa, masu irin nasarorinsa kad'anne a cikin
al'umma wlhy, kaje ga Abie, domin kuna buk'atar juna”.
Tamkar Dr Erfan Fahad yama Galadima allura ne, cikeda sasaarfa ya k'arasa ga Abie, a gabansa ya zube yana sakin wani kuka maiban tausayi tamkar mace”.
Abie ya sakko daga kujerar ya rungu
me jarumin d'ansa shima yana hawaye, sun dad'e a haka, jisuke tamkar karsu saki juna, a tunaninsu Kodai mafarki sukeyi, suna tsoron rabuwa su farka suga ba haka baneba.
Shi kansa Dr Erfan Fahad hawayen tausayinsu yake sharewa.
Ni kaina masu kara
tu wannan lamari yasani hawaye Na gaske
😭
, da zaka k'iyasta hakan a kanka wane farinciki kake hangowa yayinda waraka ta riskeka?.
😭
Wad'annan bayin ALLAH yau lallai suna cikin tsantsar farin ciki, ko kad'an Galadima ya kasa gusawa daga jikin Abi
e, Yakuma k'i kiran kowa, burinsa shima yabasu mamaki tamkar yanda Dr Erfan Fahad yabashi. A yau yay niyyar su juya amma Dr Erfan Fahad ya hana hakan saidai gobe, Dan dare yayi kam a yau.
A gado d'aya Galadima da Abie suka kwana, dukda sunma cinye
rabin daren da fira
😁
.
**********
Hankalin Munaya duk a tashe yake, saboda tanata kiran Galadima yak'iyin picking, tun tana daurewa harta gaza tafara kuka da shiga tsantsar tashin hankali.
Momma Ce ta lura da canjawarta, ta tambayeta lafiy
a?.
Kasa magana tayi saboda kunya, saida Momma ta kuma maimaitawa sannan tace, “Momma inata kiran Number Abbansu ne yak'i yin picking tun d'azun”.
Ita kanta Momma ta kirashi baiyi picking ba, amma ta d'auka ko wani uzirine yasha kansa, sai y
anzumefa hankalinta ya fara tashi itama, waya ta d'auka tashiga kiransa amma babu amsa, kusan kira 10. Cikin firgici ta kalli Munaya da aunty Mimi da itama take kan gwada kiran nasa, amma itama ba'ayi picking.
“Kinga Munaya tura masa massage mu gani
”.
Jiki a sanyaye Munaya ta tura massege, amma kusan 30minutes babu reply.
Hankalinsu fa yakai k'ololuwar tashi, amma sun rasa mafita.
*********
Shikam Galadima baima San sunaiba, wayarma kanta baisan inane ya jefar da itaba, gabaki
d'aya hankalinsa ya tattarane ga Abie, harkuma suka kwanta barci bai nemi wayarba.
***********
Yau kam inhar wani yay barci a cikinsu to bana kwanciyar hankali baneba, dan kowa damuwa tamasa katutu, dai-dai da Hadiman gidan suma duk a damuwa su
ke, sai dai tamkar yanda suka saba yauma sun mik'a lamarinsu ga Ubangijin talikai.
*_Washe gari_*
Tunda safe Momma ta nemi Number Dr Akash da Dr Ajey akan rashin jin Galadima, duk sun amsa mata da zasu bincika.
Can kuma su Galadima su
n wayi garine da shirin dawowa New Dhalhi, cikin tsantsar farin ciki irin Wanda misaltashi ma 6ata lokacine.................
✍
🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*
😭👏🏻
[8/21, 8:44 PM] 0mmer Farouk: *_Typing
📲
_*
*_
💡
HASKE WRITERS ASSO
...._*
*_
♦
RAINA KAMA...!!
♦
_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
*_BOOK 3_*
👉🏻
2
⃣
9
⃣
.................Gaba d'aya sun kasa yin breakfast, suna cikin zaman jigum-jigum suka jiyo bud'e gate da shigowar mota.
Samha ta fita da hanzarinta danson ganin wanene, fitowar tata tayi dai-dai da fitowar Galadima daga cikin mota fuskarsa d'auke da wani irin k'ayataccen murmushi daya fidda sirrin k'yawunsa.
Da gudu ta taho garesa, yakan mata fad'a akan son rungumars
a ko Sauban amma yau saigashi ya bud'e mata hannu dakansa tazo ta shige jikinsa.
Ihun murnartace tasaka su Momma fitowa da hanzari suma
Ganin Galadima ai sai duk sukayo kansa itada aunty Mimi, itadai munaya gefe ta tsaya tana sharar hawayen fari
n ciki.
Abie dake kallonsu daga cikin mota ya saki murmushi yana share hawaye, yana k'asa d'aya da iyalansa amma bai ta6a sanin muhallinsu ba sai yau, dukda bai shigaba gidan yamasa k'yau.
Galadima ya ture Samha daga jikinsa ya rungume Momma da
aunty Mimi yana sakin wani irin kuka daya matuk'ar tada hankalinsu.
Da sauri suka d'agosa hankali tashe suna tambayarsa mike faruwa? Kodai ALLAH yayima Abie rasuwane?.
Cikin kuka da dariya yace kowa ya rufe idonsa .
Babu musu sukab
i Umarninsa, har Munaya dake gefe.
Yace, “kun tabbatar kowa ya rufe?”.
A tare suka amsa masa da eh.
Ya murmusa da goge sauran hawayensa sannan ya juya ga motar ya bud'e, hannun Abie ya kama da taimakonsa ya fito rik'eda sandarsa mai k
'yau dazata dinga taimaka masa wajen tafiya, Dan har yanzu tafiyar batai kwariba.
Saida Abie ya jingina jikin Mota ya tsaya da k'yau sannan Galadima yace, “Kowa ya bud'e idonsa”.
Har rige-rigen bud'ewa suke.
Akusan tare Aunty Mimi da Muna
ya da Samba suka kwalla k'ara, Momma kam sai tayi luuu sai gata a k'asa kawai ta sume.
Abie da Galadima dasu Munaya duk kanta sukai suna kiran sunanta, shima Abie ya tuzgud'e zai fad'i, Dr Ajay daya kawosu yay hanzari rik'esa yana fad'in “A sannu da
i Sir, k'afafunka basukai k'warin wannan hanzarinba”.
Da gudu Munaya takoma ciki sai gata da ruwa, ta zuba a hannu tana shafama Momma, da k'arfi takawo Numfashi.
Bin yaran nata tayi da kallo tana fad'in “mafarki nakeyi ko yarana? Nasan irin
mafarkin dana sabane dama, ba takawa Na bane ba”.
Cikin dariya da kuka Aunty Mimi tace, “Wlhy shine Momma, shine agabanki ba mafarki kikeba, Momma Abie d'inmune wlhy tallahi kinji Na rantse”.
Zumbur Momma ta tashi daga jikin Aunty Mimi, Abi
e dake tsaye har yanzu bisa taimakon su Galadima ya murmusa yana fad'in “Zeenah ki cire kokwanto, da gaske wannan Saifudden d'inkine ba Wanda yasaba zuwa miki a mafarkiba kinji”.
Tasowa Momma tayi garesa, ta shafa fuskarsa domin tabbatarwa, takuma
binsa da kallo tundaga sama har k'asa, lallai da gaske wannan Saifudden d'intane bana mafarkiba, Ai sai kawai ta rungumeshi babu kunya ko tunawa dasu Galadima a wajen.
Sai duk'ar da Kansu duk sukai suna Murmushi.
Gaba d'ayansu kowanne so
yake ya nuna ajintarsa ga Abie domin nuna masa gamsuwa da farincikin samun lafiyarsa, aka kawo masa y'an Uku ya had'a duka ya rungume yana maijin k'aunarsu har cikin jininsa, Khaleel ma yana nanik'e dashi.
Munaya dai nadaga gefe bata zak'eba.
Idon Abie ya sauka akanta, Murmushi yamata yana fad'in “'Diyata zo mana”.
Takowa tai cikeda jin kunya tazo gabansa ta durk'usa, cikin girmamawa ta gaisheshi da masa addu'ar k'arin samun lafiya mai d'orewa.
Ya amsa yana mai k'ara jin far
in cikin kadancewarta suruka agaresa uwa ga jikokinsa.
Galadima ma yakasa d'auke ido daga gareta, sai yaga tamasa y'ar rama tsakanin jiya da yau.
Breakfast d'in dabai samu shigaba d'azun aka baje domin ci, amma shi Abie kasancewar an hanashi
cin wasu Abubuwan Kuku yay azamar tanada masa Wanda yake buk'ata.
Daka gansu kasan suna tareda matsanancin farin ciki .
Koda suka kammala Galadima ya taimakawa Abie shiga d'akin Momma, shima ya haye sama shida matarsa.
Tun'a falo ya d'auketa
cak yana juyi da ita cikin hajijiya, babu shiri Munaya tahau k'yalk'yata dariya da k'an k'ame wuyansa da hannayensa tana cusa kanta cikin k'irjinsa.
A haka suka k'arasa cikin bedroom, ya jefa abarsa saman gado yabita tareda jan bargo yay musu runfa
.
An hanani ganin abinda akeyi
🤨
, sauk'inma inada mijin Nima
😏🙄
.
Farin cikin da wannan ahali suka tsinci Kansu wlhy 6ata lokacine, Momma kam sai ko ganinta bama ayi
🤭🙈
.
A gurguke please
🥺
😔
.
Walwala da farin cikin wann
an gida tadawo kam, ga nutsuwa mai saka zukata samun damar yawan ibada, ko yaushe suna manne da Abie, sai idan time d'in hutunsa ne yayi, Galadima yayma kowa gargad'i akan sanarda tashin Abie, burinsa kowa yaga abin mamaki, 100% Momma ta yarda da shawarar
sa, hakama Abie.
Yanzu dai kam sun yanke shawarar Isa k'asarsu ta haihuwa ranar salla k'arama, zasu azumi na kwanaki 20 a india, su biya Saudiyya suyi Umrah ta kwana goma su isa Nigeria a ranar salla ayi idi dasu.
Gaba d'aya azumi saura kwanaki
6 a farashi.
******************
*_AZUMI_*
Alhmdllh kowanne musulmi yau ya tashi da azumin watan Ramadan mai mai albarka, saidai irin masu ak'idar saimun gani da suka kasance k'alilan acikin wasu k'asashe irin namu Na yankin Africa.
Duk da shayarwa hakan bai hana ni zama cikin jerin masuyiba, dan raino dai bani nakeba, tsakanina da yarannan idan sunji yunwa, koyaushe suna tare dasu Momma, sunyi 6ul-6ul dasu tamkar y'an watanni 6, amma har yanzu suna cikin wata Na hud'une ma kacal.
Tunda safe Galadima ya fice, Na d'an tashi nai gyaran saman sannan Na sakko, yau babu maganar shiga kitchen, Dan tunda Abie ya dawo nakoma nike mishi girkin abinda zaici, wataranma nakan had'a da namu muma, babu abinda zan cema wad'annan mutane sai
godiya, soyayya dai mai cike da k'auna ina samunta a garesu, ni da mijina kam ai sai hamdala, yana tattalina da tarairayata, saidai d'an sa6ani Na yau da gobe Wanda baka Isa raba ma'autara da Shiba, shima kuwa bai wuce wasu awanni muke shiryawa ba, inko M
omma ta lura ma takan kiramu tamana Nasiha, hakama Aunty Mimi.
A falo Na iske Abie daga can gefen falon inda wasu kujeru biyu suke da kanta mai d'aukeda buks Na karatu, tundaga kan Na addini har zuwa Na makaranta dadai sauransu, zaune yake yana nazar
in wani littafi da banga sunansa ba saboda tazarar dake a tsakaninmu.
Sai Samha dake falon kwance a kujera tana kallon film, zaman gyalena Na gyara, Na taka a nutse zuwa garesa, saida Na durk'usa a gabansa sanann nace “Barka da safiya Abie”.
'Dago k'yawawan idanunsa da Galadima ya gado yay yana kallona, ya zare medical eyeglasses d'in idonsa yana Murmushi, “'Diyata barka dai, kin tashi lafiya?”.
Kaina a k'asa ina murnushi nace, “Lafiya lau Abie, ya ibada da k'arin k'arfin jiki?”.
“Alhmdllh d'iyata, ai jiki kam sai godiyar Ubangiji, Muhammad fa?”.
“Ya fita tunda safe”. Na fad'a cikin kuma duk'ar dakai.
Murmushi Abie yayi, ya maida eyeglasses d'insa yana fad'in “ALLAH ya dawo dashi lafiya to”.
A saman la66a Na amsa,
sannan Na mik'e da k'yar zuwa d'akin Momma.
Abie ya bita kallo zuciyarsa cikeda k'aunar wannan yarinya, irinta yaytama y'ay'ansa addu'ar samu amatsayin abokiyar rayuwa, Alhmdlh Ubangiji ya amsa masa, saura Sauban kuma.
Nidai nashiga Na gaid
a Momma, Na iske tanama su Amaturrahman shiri, da alama wanka tamusu, Na gaisheta cikeda girmamawa kamar yanda Na saba, itama ta amsamin da kulawa tareda d'an jana da hira tamkar yanda ta saba, nad'an jima a d'akin, harta fito tabarni Na gyarashi tsaf kama
r yanda nakeyi tun bayan dawowarmu, Dan tuni Na dakatar da Samha ni nakeyi.
Na fito da nufin shiga Na gaida aunty Mimi saina isketa tama fito falo, anan muka gaisa Na zauna muka d'ora da hira tamkar yanda muka saba, mafi yawama firar ta Sauban Ce, Da
n kowa yayi missing d'insa, yace azumi da kwana 3 zai zo sai salla zai koma, Galadima bai hanashiba, dukda yana tareda tattalar kud'i a tsakaninnan saboda sun masa k'aranci, to saima papi ya d'auki nauyin zuwan Na Sauban da komawarsa.
Mund'an ja lokac
i Muna hira barci yafara rinjayata, mik'ewa nayi Na gudu sama, nad'an rage kayan jikina Na haye gado sai barci.
Kusan 10am saiga Galadima ya dawo, bai iske kowa a falonba, da alama barci suke kokuma suna harkokin gabansu a ciki, kai tsaye d'a
kin su Momma ya nufa, yay knocking aka bashi izinin shiga.
Abie Na zaune saman abin salla ya idar da sallar walha, yayinda Momma ke zaune bakin gado tana bama Abdurraheem Magani saboda zazza6in dake jikinsa.
Galadima ya zauna a saman sofa y
ana gaidata da tambayar miya sami Abdurraheem d'in?.
Cikeda kulawa ta amsa masa tana gogema yaron inda maganin ya 6ata masa a wuya da fuska.
“Tunda muka tashi yau Na kula bayajin dad'i yaronnan, inagafa yakamata ka kaishi a bincikasa, basai mu
n zauna wata 6 ta cikaba, tunda kasan ciwon yana zama iri daban-daban, karmuyi tunanin ko irin nakane azo ba hakaba, Dan Na kula yafika yawan laulayi shikam, Abdurraheem baya had'a sati biyu da isashsshiyar lafiya”.
Jin jina kai Galadima yayi, tausa
yin d'an nasa Na ratsashi, ya had'iye abinda ya tsaya masa a mak'oshi da k'yar yana amsar Abdurraheem d'in daga hannunta.
Abie daya shafa addu'a ya maido hankali garesu.
Mik'ewa Galadima yay yakoma inda yake yana gaisheshi, Abie ya shafa kansa h
akama Abdurraheem, cikeda tsokana