Showing 117001 words to 120000 words out of 407268 words

Chapter 40 - Raina Kama COMPLETE

samha ta fad'amin d'azun a asibiti ta dawomin a rai, Ashe mahaifinsu ya rasu suma shekara 2 kenan, itace d'iyar Aunty Mimi ta farko, sai Hakim da suka rasu tareda babansu, saikuma khaleel auta. Suma a Nigeria da suke zaune, ba

yan rasuwar mahaifin nasune suka dawo nan india, duk da dangin mahaifinsu sunso kar6arsu papi yahana, babansu tsohon Governor ne shima, mutuwar tasa kuma akwai lauje cikin nad'i shima, dan ya tsananta akan binciken ciwon surukinsa Abie sosai, shiyyasama ak

e zargin an kasheshine saboda wani Abu daya gani.

Har muka Isa gida bansan hirar dasukeba a baya, dan shima Galadima baya cewa uffan.

Shine ya kar6i khaleel a hannuna, ya sa6ashi a kafad'a muka shiga ciki, har d'akinsa ya kaisa. ni lokacinma ha

rna haye saman..........



🏼

Barkanku da juma'a.

Zanyi last page gobe idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya



🏻

‍♀⛹

🏻

‍♀

.

Network yanata min iskanci tun jiya shiyyasa kuka jini shiru



*_YA ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

😭🙏🏻

*_Typin

g

📲

_*

*_HASKE WRITERS ASSO...

💡

_*

_(Home of expert and perfect writer's)_

*_



RAINA KAMA......!!



_*

_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

👉🏻

3



0



..................Da sall

ama ciki-ciki ya shigo, nayi saurin maida zip d'in rigata sama nafasa cirewa, a sace ya kalleni yawuce bakin gadon ya zaune tareda dafe kansa.

Kallonsa nayi Na kauda idona nima, kusan mintuna 3 kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa. d'agowa y

ayi yakuma kallona, kamar an masa dole yake maganar cikeda k'asaita, “k! Wai bazakima Momma magana ba kikoma d'akinki?”.

Kamar bazanyi maganaba saikuma nayi batare da Na kallesaba, “inaga kaine yakamata kamata maganar ai, dan nima zanfi son haka,

duk nabi Na takura zama da Namiji d'aki d'aya”.

Banza yamin bai sake tankawa ba, saima yamik'e yana jan k'aramin tsaki, nikam Na ta6e baki a zuciyata ina fad'in ka iya fad'ar R kafin kamin mazurai.

Baima san ina yiba, yaje wajen wardrobe d'ins

a ya d'auki kayan barci yanufi bathroom.

Murmushi kawai nayi, danni rayuwar mutuminnan mamaki take bani, ina dad'i kabi ka k'untata kanka irin haka? baka hira da kowa, baka dariya, shifa ko kallo inba labaraiba ban ta6a ganin yanayiba, hakama wak'a b

anta6a jin yana jiba, koranar dana duba wayarsa karatun Qur'an kawai nagani da Tafseer. nakai dubana gawata 'Yar kanta dakecan gefe a bedroom d'in nasa, mafi yawanci littatafan addini ne awajen, sai English Novels. (To yayi karatun addinine? tunda naji Mom

ma tace anan India ya girma

🤔

). Wata zuciya tacemin su India basuda musulmai ne?. “hakane kumafa” nafad'a a fili ina mik'ewa.

Ganinaima bara nacire kayana kafin yafito, daya fito saina shiga nima.

Har ga ALLAH banyi tunanin fitowarsa ba yanzun,

dan haka hankalina kwance na zuge zip d'in rigar, na cireta gaba d'aya, shima sket d'in nayi k'asa dashi yafad'i k'asa.

Juyowarnan da zanyi da nufin d'aukar towel dana ajiye saman akwatina sai kawai naga mutum tsaye a k'ofar bathroom, hannunsa rik'e

da k'aramin towel yayi tsaye yana kallona.

Bansan Na kwalla k'araba wlhy, Na rarumi towel d'in nayi saurin kare jikina, ALLAH ma yaso k'ofar a rufe take, dan dawuya su Aunty Mimi sujini.

K'arata tadawo dashi daga sumar tsayen dayayi, yawani ka

uda kansa cikeda basarwa yana ta6e baki, saikuma yaja guntun tsaki yaje bakin gadon ya zauna yana cigaba da goge fuskarsa, dan har yayi shirin barcinsa a ciki.

Jinayi tamkar na makesa, d'an rainin hankali yagama kalleni zai wani miskile fuska asfa

baiga abin kalloba. hijjabin sallata na janyo Na saka, sannan nawuce bayi ina hararsa.

Ina shiga yamik'e yana wani munafukin murmushi, abin salla ya shinfid'a ya kabbara shafa'i da wutiri.

Nadad'e abayin nak'i fitowa, saida nabar jin motsinsa

duka sannan Na fito, dayake nayi shirina a bayin nima, nazata ya kwanta, amma saina iskeshi zaune a kujerar dake gefen kantar littatafan nan ya bud'e laptop yana danne-danne, gefensa kofine yanata turiri, da alama coffee ne aciki.

Yad'an juyamin bay

a kad'an, dan haka cikin sand'a Na rufe k'ofar, nakuma tako a hankali har zuwa wajen sofa Na kwanta, duk zatona baya ganina, Ashe yana kallon duk abinda nakeyi ta gefen idonsa.

A ransa yace munafunci. cigaba yay da aikinsa hankaki kwance, bai bar wa

jenba har kusan 1:30pm, maimakon ya kwanta sainaga yashiga bayi ya d'auro alwala.

Nima har time d'in barci yakasa d'aukata, maganar Momma tanata min yawo a zuciyata, tunanin ta inda zan taimaki Galadima kawai nakeyi.

Ina kallonsa ya kabbara sal

la. saida yay kusan raka'a 6 yanayi yana sallamewa, daganan ya d'auki alku'ani yafara karatu k'asa-k'asa.

Masha ALLAH nafad'a a raina, danjin yanda muryarsa ke fita cikin karatun littafi mai tsarki, gashi yana fidda kowane harafi cikin tsantseni

da kwarewa. Tun

ina saurarensa har wani barci mai dad'i ya saceni, bansan lokacin daya kammala ba yazo ya kwanta.

Muduka makara mukayi sallar asuba yau, dan haka shima yau a gida yayi.

Bayan ya idar waya ya d'auka naga yayi kira.

Bayan an

d'aga daga can sukayi gaisuwa, jin ya tambayi ya Nigeria Na gane da 'yan can yake wayar. yacigaba da fad'in.

“Nuren naga ka turomin hotonsa, shin a inane yake haka?”.

Bansan mi akace masaba daga can, naga dai yayi kwafa, sai yace “ya magan

ar Minister? dan nagansa wajen d'urin aurena, ban kuma yi zaton zai zoba”.

Canma aka kuma yin wata maganar.

Zamansa yagyara, yakuma jingina da bangon, dayake yana kan abin salla har yanzun. “kayi k'ok'ari Nuren, yanzu abinda nakeso dakai shine, a

kwai yarinyarsa d'inan datake karatu a nan jami'ar Abuja, inason a sacemin ita k'arshen watannan, yanzu ka saka ana bibiyarmin komai nata, Shikuma Alhaji Balala driver n sa zaku d'aukemin, dan bincikena ya ganomin shekarunsa 30 dawani Abu yana masa aiki, k

uma randa su Alhaji balala sukayi zama da Abie shine ya kaisa masarautar mu, inada tabbacin zai San wani Abu koda kad'anne, kuyi aikinku da kulawa Nuren, banason asami matsala kamar wancan time d'in, gobe kashiga birnin gayu plaza kuyi zama Na musamman da

Saleem akan maganar CCTV camera data daina aiki randa abinnan ya faru, ni naso Na zauna dashi, amma kaga Momma tamatsa akan dawowata”.

bayan nacan yagama magana.

Yace “ok babu damuwa, zan turo maka number yarinyar, saiku bibiyeta tanan. sai anj

ima, ka gaidamin Mom d'ina”.

Koda ya ajiye wayar saiya koma gado ya kwanta abinsa, nikam ina zaune sai cud'awa da kwancewa nakeyi, ban fahimci wayar tasaba gaba d'aya, shin wanene kuma NUREN!? shikuma miye alak'arsa da Galadima kuma?.

Tabbas aik

ina bazai yuwuba saina San wanene NUREN, wane kuma aiki yakema Galadima a sirrence, su waye wad'annan mutanen biyu daya ambata Minister da Alhaji balala? suna cikin wancan case d'in Na Abie ne? kokuwa tasu dabance?.

Kwanciya ta na juya yanda zanji

dad'in tunanin da k'yau, saikuma naga ai ba sanin waye Nuren bane matsalata yanzu, kamata yayi nafara sanin shi kansa Galadima d'in da rayuwarsa, na tuna maganar Momma da tece “shi mutumne dabashi da yadda”. Mutum mara yarda kuwa yanada wuyar sha'ani, kad'

an na juyo na kallesa, idonsa a rufe yake, amma ban yarda barci yakeba, na janye idona nima na maida lumshe, barcine mai nauyi ya kwasheni, harya fita bamma saniba inata barci, babu kuma Wanda yazo ya tadani.

Sai around 11:30 na tashi, wani masifar

ciwo kaina yakemin, haka dai na tak'ark'ara nayi wanka, nagyara d'akin sannan na sako k'asa, gidan shiru tamkar babu kowa, sai television daketa aiki, zama nayi bisa kujera dafe da kaina.

“ranki ya dad'e lafiya dai?”.

Bud'e idona nayi a hankal

i, sai naga jakadiya ce, namata murmushi tareda yunk'urin tashi zaune, “wlhy kaina ke ciwo jakadiya, halanma ke kad'aice ma a gidan?”.

“subahanalla, sannu ranki ya dad'e, bara na samo miki abinci saikisha magani, eh ni kad'aice ranki ya dad'e su Sau

ban sun tafi makaranta. Gimbiya Mimi kuma tana asibiti itama, taga kina barcine shiyyasa tahana a tadaki”.

Nace “ALLAH sarki”.

Wucewa tayi zuwa kitchen, babu dad'ewa saigata tadawo da tire, a gabana ta ajiye tana fad'in “gashi ranki ya dad'e

, kici saikisha magani kafin Magajin gari yadawo saikuje asibiti”.

Kallonta nayi da mamaki, “jakadiya waye magajin gari kuma?”.

Tayi 'Yar dariya, “ranki ya dad'e ina nufin mai gidanki, ai magajin gari nake cemasa”.

Murmushi nayi ina girg

iza kai kawai, na had'a tea nasha, sannan nasha maganin, anan falon na kuma kwantawa, barci yakuma kwasheni.

Jakadiya na zaune tana gadina.

Da sallama ya shigo, jakadiya ta amsa tareda mik'ewa da sauri ta kar6i kayan hannunsa tana masa sannu d

a zuwa, yad'an saki fuska yana amsawa. d'aya acikin kujerun ya zauna, sai lokacin idonsa ya sauka kaina.....

maganar da jakadiya take masa ce yasakashi janye ido daga kaina ya maida kanta.

“ranka ya dad'e akai kayan samane?”.

“no jakad

iya kibari zan hau dasu, ai sunmiki nauyi, ita wannan mike damunta tayi barci anan?”. ‘yay maganar yana maido idonsa kaina’.

“kanta ke ciwo ranka ya dad'e, amma tasha magani ma, shine barcin ya kwashe a wajen”.

Ido yad'an tsuramin, kafin ya

cije lips d'insa kad'an.

Jakadiya tajuya zuwa kitchen, babu dad'ewa tadawo da ruwa ta ajiye masa.

Sannu yamata sannan yad'auka yana sha, itakuma tabar wajen.

Kofin da yasha ruwan ya ajiye, ya maida kansa jikin kujerar ya jingina kansa,

tareda maida k'afarsa d'aya kan d'aya, lumshe idonsa yayi, ta k'asan ido yake kallona, tsawon lokaci yana a haka, yayinda nikuma nake barci bansan yana yibama.

Kamar an tasheni saina bud'e idona a hankali, dashi na fara tozali, dan haka namik'e zaune

da sauri, tareda warware d'an kwalina na yafa, dan gown d'in material ce a jikina, gashi irin mai santsinan, kuma rigar takamani sosai, a raina nace dukma yagama kalleni, wama yasan tun yaushe yake anan?.

Duk abinda nakeyi yana kallona, sometimes

yarinyar nan takan bashi dariya, a d'an zaman dayayi da ita yalura tanada kunya, saidai batason raini, bakuma tada tsoro ko kad'an, ganin ina Neman mik'ewa saiya bud'e idonsa.

Harna fara tafiya saina juyo, danjin kamar ana kallona. idonsa a kaina,

amma saiya wani basar tareda janyewa.

Kaina kawai na girgiza, harzan cigaba da tafiya saina tuna nemanfa kusanci nake dashi domin cika alk'awarin Momma da zanyi, baya na dawo nakoma na zauna, muryata a sanyaye nace, “sannu da dawowa”.

Sosai na

bashi mamaki, dan haka ya kalleni da k'yau, kamar zaiyi magana saikuma ya fasa, kusan minti 1 dawasu Second's sannan yace “mike damunki kika kwanta anan?”.

“kainane ke ciwo amma yama daina”. maganar dayayice tabani mamaki.

Mik'ewa yayi yana

fad'in “ba gulma tasaki k'inyin barci jiyaba, dole ai kitashi da ciwon kai”.

Galala nabishi da kallo, kai wannan guy d'in yafara bani tsoro, dama yasan banyi barciba jiya kenan? Anya guy d'innan baya gani har hanji

🤨

? nabishi da kallo yayinda yak

e taka step d'in benen cikeda izza, hanunsa d'aukeda ledojin daya kwashe a falon, saida ya 6acema ganina sannan na sauke ajiyar zuciya.





*



*



*



*



*



*





*_Nigeria_*

Tun bayan zuwanmu sallama da tafiyarmu 'yan gidanmu sai suka

dainama innarmu magana, musamman yanda sukaga anata fita da abubuwan dana bari a baiwa mutane, innarmu ko'a kwalar rigarta itakam, bata damu da rashin mata maganar dasukeba, harkokin gabanta kawai takeyi hankali kwance.

Innaro kam kud'in da Galadima

yabata suka sakata d'agama innarmu k'afa, ko gaidata tayi cikin salama take amsa mata, a jiya harda siyoma su Aryaan sllifas, wai taganine a hanya sun mata k'yau ta siya musu, murmushi kawai innarmu tayi damata godiya ta kar6a.

Wannan k'yauta tasak

a mamansu yaa Hameed kasa hak'uri taita sakin habaici, daga nan sauran matan gidanmu suka d'auka suma, innarmu saita saka karatun alkur'ani ma a waya tashige d'aki tarufe kanta.

Har sukaci suka tsire dan kansu sukayi shiru.

Kusan k'arfe hud'u n

a gamma saiga Zarah wujiga-wujiga tashigo gidan, ga ciki yafito masha ALLAH, Innarmu dake tsakar gida tana wankin kwanuka tayi saurin cewa “zarah lafiya?”.

Jikin innamu tafad'a ta fashe da kuka, “innarsu 2 ki taimakeni zai kasheni, wlhy bani na d'a

uka masa kud'iba, narantse da ALLAH........”

Tuni 'yan gidanmu duk sun fito, danjin kururuwar Zarah, mamansu yaa hameed tazo ta janyeta daga jikin innarmu, “k mahaukaciyar inace dabazaki nutsu kisan wazaki fad'ama matsalarki bane?”..



Oho ita Zarah ba wannan bane matsalarta a yanzun, takuma fad'awa jikin mamansun tana kuka da rantsuwar ba ita ta d'auki kud'iba.

Ganin tana neman yage musu zani a kasuwa sai mamansu tajata suka shige d'aki.

Wata dariyar gatsatsa maman Safara'u t

ayi, tareda ta6e baki tana kallon Gwaggon Haleematu dake k'usa da ita “to anfara da bismillah kenan? Wata 6 an koro yarinya da duka?......

Caraf Momy Hadiza ta k'ar6e “yo mai kashi a gindi ai baya toshe hanci yace makwafcinsa na wari, kidai iya bak

inki tunda kema kinkai gidan wani”.

“can a bakinki, nakai kuwa, kuma tawa zama daram babu yaji balle nik'a gari, tunda ba auren hange-hange da tauye hak'in wasu namata ba, ai bama saikin zak'eba, munsan mai kaza a aljihu dama baya jimirin Asss!, in

dai nice kinga tafiyata, kiyi da wani ba niba”.

Tamkar Momy Hadiza zata daki maman Safara'u haka ta hayayyak'o mata, wannan hayaniya ce tafara jawo kunnen makwafta gidanmu, saiga innaro tamkar an jehota, ta shiga tambayar ba'asin hayaniyar, dansu Abb

anmu duk suna wajen aiki.

Duk shiru sukai mata, sai innarmu Ce da maman Fauziyya suke fad'a mata abinda yafaru.

d'akin mamansu yaa hameed tashige domin jiyo ba'asin dawowar Zarah n.

Itadai innarmu jikinta duk yayi sanyi, wannan zamani

n ko aurar da yaranka mata kayi tsugunne bata k'are makaba, dan sai ALLAH yabasu mazaje na garin

dazasu iya hak'urin zama da juna, aurene tunkan ayisa zakaga angama kwashe masa albarka wajen buruka da bidi'oin biki, ga iyaye yanzu gaba d'aya hankalinsu Yak

oma ga d'irkama 'ya'yansu kayan mata kawai ba koya musu dabarun zaman aurenba, sun manta kayan mata basu kad'ai bane ma'aurata ke buk'ata a zaman aure, sudai sukan kawo wata nutsuwane da kuma dank'o cikin rayuwar auren, gaba d'aya yanzu zakiga gidajen aure

n Malam bahaushe sun canja, wuyarta dai akai yarinya miji ya kauda mata budurcine, wata biyu yayi yawa kwarnafinsa ya kwanta saiya fara Neman makusarta, gakuma yaran basuda wata dabara dazatasa su taka tsantsan ga zamantakewar, har yakai an sami sassaucin

cin zarafi daga mazajen nasu, to an nuna musu kayan mata sune kawai jigon aure da hangar mallakar mijin kansa, to ALLAH ka zaunar mana dasu lafiya dai agidajensu.

Nace amin innarmu

😘👌🏻

★★★★



Kusan minti 10 da shigarsa saina tashi na

bi bayansa, waya nakeson ya aramin nayi kiran su innarmu Susan mun sauka lafiya.

Saida nai sallama yabani izinin shiga sannan, saman sofa na iskeshi zaune yana latsa waya, da alama waya yagama ko zaiyi.

Zama nayi a kujerar da yake karatu ta

kusa da kanta, na kwantar da murya cikin sigar ladab nace “yalla6ai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login