Showing 189001 words to 192000 words out of 407268 words

Chapter 64 - Raina Kama COMPLETE

fara k'ok'arin cire kaya, na mik'e zan fice, dan yanzu na lura lamarinsa kullum k'ara girmama yakeyi, baya shakkar cir

e kaya a gabana ko sakawa, sai dai ni na fita na bashi waje.

Hannuna ya rik'o, na waro ido waje cikin mamaki.

“ina zaki?”. ya fad'a cikin tsare gida.

“ba wanka zakayi ba?, idan kagama zan dawo ai”.

“toni dodone?”.

“A'a

na fad'a ina ta6e baki”.

“to koma ki zauna ki kalli sadakinki”.

Idanu na waro masa waje da hangame baki.

Yiyai kamar bai ganniba ya basar. bai sakeniba yakuma cigaba da cire kayansa da hannu d'aya. Ni daifa k'in kallonsa nayi, dan wl

hy kunya nakeji sosai, dukda 'yar shak'uwa ta shiga tsakaninmu hakan bai sa mun saki jiki da junaba, garama shi idan rashin kunyarsa ta motsa yakanyi abinda ya gadama yana basarwa a dole kar'a kawo masa raini. Yakan bani dariya sometimes, amma nima saina B

asar saboda Jan aji.

Iska kawai naji a cikin kunnena, da sauri na waigoshi, ganin sa dagashi sai boxer sai na juya fuskata.

Bayana ya koma ya zagayo da hanayensa duka akan cikina, yayinda kansa ke a kafad'ata, muryarsa can k'asan mak'oshi y

ace, “miya sakaki kuka?”.

Salon da yay maganar ya sakani lumshe idanu saboda tsigar jikina data tashi.

Nace “kabari ka gama zan fad'a maka”.

“miyasa ba yanzu ba?”.

“ka saka riga to”.

Murmushi yayi yana shafa cikina, “my friend

sarkin tsiwa sarkin kuma Kunya, akwaiki da abubuwan bi........”

Saikuma yay shiru yak'i k'arasawa, hannuna na saka na rik'e hannunsa da ke yawo saman cikina, nace, “ka k'arasa mana, akwaini da mi?”.

“Humm” kawai ya fad'a yana sakina, yaja b

athrobe d'insa dake jikin hangar ya sanya, saida naga ya fara k'ok'arin d'aure igiyar sannan na d'ago na kalleshi.

“To mikuma kike kallo?”. Ya fad'a cikin tsare gida.

Baki na ta6e ina fad'in, “miye abin kallon to?”.

Ya d'an fiddo ido

sannan ya matsoni, “zona nuna miki”.

Nasan ko guduwa nayi saiya kamoni dan haka na duk'e ina fad'in “wash ALLAH cikina”.

Tsayawa yay cak, saikuma ya tako da hanzari yana tambayar lafiya?.

cikin marairaice face nace “Motsi yakeyi ALLA

H”.

rankwashina yayi aka yana cewa “ke d'inan ko”.

Dafe wajen nayi, bai kulani ba ya shige bathroom, na harari bayansa ina masa gwalo, nasan inda banyi hakaba bakina ne zaisha wahala.

Ina zaune ya fito, na d'auke kaina tamkar ban ga

nshiba, shima hakan yayi, ya wuce wajen frigate ya d'akko ruwa da Kofi, kujerar dake wajen karatunsa ya jawo ya zauna yana fuskantata, batareda yayi yunk'urin cire bathrobe d'in jikinsa ba, yanzun kam babu wasa a fuskarsa, ban damuba dan nasan halin kayana

yanzu, yanzu zakiga yasaki jiki yana magana kamar ba shiba, anjima kad'an saiya koma Asalin Galadimansa dana fara gani a Hospital, Mara dariya mara later r

😏

.

K'afarsa d'aya ya d'ora kan d'aya yana shan ruwa, yasha kusan rabi sannan ya cire, bata

reda ya ajiye kofinba ya maido dukkan hankalinsa kaina, “A kwana biyunnan kokin lura Abba yana cikin damuwa?”.

d'ago idanuna nai na kallesa, a sanyaye nace, “abinda naji innarmu na masa Complain kenan yanzu, amma saiya nuna fusata”.

“shine

kika shigo kina kuka?”.

Na jinjina masa kai batareda nace komaiba.

Shima bai sake cewa komanba ya kauda idonsa daga kaina yana kur6ar ruwansa. kusan 2minutes sannan yakuma kallona, “Munaayaa mukawo k'arshen 6oye-6oye mana”.

Kallonsa

nima nayi, nace, “kamar ya?”.

“humm” yafad'a yana cije lips, mik'ewa yayi tsaye ya ajiye cup d'in hannunsa a gabana, sannan ya shiga zagaye d'akin hannunsa goye a baya, nikam dai binsa kawai nakeyi da kallo kamar na samu television, maganarsa ta k

atsemin tunanina.

“Munaaya! Mikuka ta6a gani a d'akin Abba ke da 'Yar uwarki?”.

Zumbur na mik'e dan mamaki, “yalla6ai a ina kasan wannan?”.

batareda ya kalleni ba yace “Munaya Sameer ya wuce dukkan tunaninki, dan haka fad'amin?”.

Ajiyar zuciya na sauke, wadda ta tilasta masa juyowa ya kalleni, nace, “yalla6ai ba fad'a maka bane matsalar, kuskuren muhallin fad'arne da kuma makomata”.

“bakida dukkan Matsala da wad'annan, idan bai danganceni ba zan d'auki matakin taim

akon sirikina, makoma kuwa inada yak'inin kare martabar matata uwar d'ana ta kowanne hali”.

Furicinsa yaban mamaki, dan haka nace, “matar Contract ko?”.

“Well Duk yanda kika fassara dai-daine, abinda na Sani kawai wannan maganar batada nas

aba da waccan, dan haka kibar kowanne a muhallinsa sai lokacin yinsa yayi”.

“humm” kawai na fad'a na koma na zauna inda na tashi.

Idonsa a kaina ko k'yaftawa bayayi.

Na nisa sannan nafara fad'in,

_“Na tabbata tunkan ka k

'ulla alak'a dani saida kasan koni wacece, dan babban mutum irinka bazaiyi Abu babu wani tanadiba, banida matsala wajen maimaita maka sunana ko tarihin ahalin dana fito, kamar yanda kasani mu 'yan biyune hakan yasaka ba'a banbancemu ni da 'yar uwata, sai d

ai hallaya takan banbantamu ga Wanda ya sanmu, Munubiya mutumce mai hak'uri da yawan kawaici, a wajen gadon hali tabbas ta biyo mahaifiyarmu ne, sa6anin ni Munaya mai zafi da yawan tsokana, a lamarina babu ragi ko d'aga k'afa, inhar kaga nayi dogon zama da

mutum babu sa6ani to ka tabbata ya tanaji matakan iya zama danine, basai amfad'a ba nima kaina nasan halayena na kamanceceniya dana Mahaifina da kuma kakata innaro, a wata litinin d'in da bazan ta6a mantawa ba sai mahaifinm

u yayi wani bak'o, matsalar da a

ka samu shine yazo bai iske Abba a gidaba, a wannan ranar innarmuce da aiki, dan haka hak'in tarbar wannan bak'o saiya rataya a wuyanta, maimakon tayi da kanta saita saka cikinmu ni da Munubiya wani yayi”._.......................



🏼

Mu had'u a p

age na gaba

🤫

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu

🙏🏻😭

_*

*_typing

📲

_*



💡

*_HASKE WRITERS ASSO....._*

*_



RAINA KAMA.....!!



_*

_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

~Book 2~

👉

1



7



_..................“Da haushi na d'auki ruwan da innarmu ta bani na fita, saboda muna tsaka da kallon wani film daneke masifar sone, Munubiya dan kartaje kaiwa saita hau barcin k'arya. Tunda na shigo shegen mutumin nan ya tsura min idanu yana las

ar baki, kai kace tsohon mayene yaga nama, a zafafe na dire tiren agabansa ko k'ararsa zatasa ya dawo hayyacinsa, amma wawannan yayi nisa, na buga tsaki a zuciyata zan fice, caraf ya kamo hannuna, ban dubi girmansa ba na dage na watsa masa mari, hakan kuma

yayi dai-dai da shigowar Abbanmu falon. Amma d'an iskan ganin Abbanmu da marin danai masa baisashi sakin hannunaba, saida Abba ya daka masa tsawa da fad'in “SD! wane irin iskancine wannan? a cikin gidana ka kama hannun 'yata?!”. Abba na rufe baki ina kuma

bashi mari na biyu, tunda naga alamar shi bunsurune. a wannan karon ya saki hannun nawa, saboda janyeni da Abba yazo yayi, Abba ya nunamin k'ofar fita, koda na fita saina la6e a corridor d'in shiga falon bak'in._

_A zafafe Abbanmu naji yana fad'in “

SD ubanwa yabaka damar shigomin gida ne?”. sautin tafin bak'on na jiyo dan haka nai saurin lek'awa ta kafar labule, gani nai yana zagaye Abba yana dariya da tafi, cikin shak'iyanci yake cewa “Alhaji Auwal, Alhaji Auwal! dama kanada k'yawawan 'yammata haka?

Woow nice babie, idan na samu wannan ai ko rana bazata sake ganina ba, wlhy nasan zan kwashi rom........., mari Abba ya zuba masa a kumatu, yana nunashi da yatsa, a matuk'ar fusace yace, “wlhy idan ka kuma furtawa saina datse kazamin harshenka a falonnan,

wawa kawai”. SD ya shafa kumatunsa sannan ya sumbaci hannun yana hurama Abba, “Kafa birgeni Alhaji Auwal, kai jarumi, 'yarkama jaruma, kai inason irin haka mutumina uhhhhhhm mutccch”. ya k'are maganar da kuma kissing hannunsa. Banza Abba yamasa ya d'auke

kai daga kallonsa yana fad'in “miya kawoka gidana?”._

_Alhaji Auwal kenan, kaima kasan dakaga SD kasan zancen, a wannan karon da albishir d'in k'arin farashi akan tayin baya nazo maka, sannan kuma damace a gareka ta k'arshe hakan, mun yanke shawara

r baka naira milyan 500”. Abba yaja tsaki yana hararsa, “ka koma ka sanar ma iyayen gidan naka ina kan bakana, sannan Ku farka daga barcin da kukeyi, dan bazan ta6a badawa ba, kamar yanda ban ba da jiya ba, bazan bayar yauba, sannan gobe ma bazaku samuba,

wannan kuma yazama first and last dazaka shigomin gida, inba haka ba ina mai tabbatar maka zaka aikata kuskuren da bayan bayanka ma saisunyi takaicin jin yanda zaka k'are”. “kwantar da hankalinka sarkin jarumai, tabbas zan tafi, bakuma zan sake dawowa ba b

alle nayi nadama Oga, ammafa bazan 6oye makaba, kana bani mamaki, kak'i bama Wanda akace ka bamawa, sannan kak'i saida mana mu masu buk'ata, shikuma wannan Abu ba tuwoba balle muyi tunanin zakacine, waikai mike damun kankane haka? ka zauna kanata rik'ema W

anda yarigada ya mutum amana, shikuma Wanda kakema tanadin bashida maraba da gawa, koda

yake ashefa ga Galadiman Ku nan, koshi kakema tanadi?”. “wannan ba matsalarka bace”. Abba yafad'a cikin karsashi. “kumafa gaskiyarka wannan ba matsalata baceba, amma ta

bbas inada yak'inin kai zata zama taka matsalar maybe ma harda santaleliyar budurwar 'yarka, lallai labarin k'yak'yk'yawa da ahalinta zai Shiga duniya kwanannan, nabarka lafiya, ka huta”._

Da sauri nabar wajen gudun karya fito ya ganni, nakoma ciki

n gida ina juya wad'annan zantuka na abbamu da bak'onsa, masu tsananin wahalar fassara, mi bak'on yake nema a wajen Abba dahar yake ik'irarin sun basa zunzurutun kud'i naira na gugar naira, d'ai-d'ai har miliyan d'ari biyar? Amma dukda yawansu Abba bai fir

gitaba balle mik'a wuya?, sannan wanene Galadima kuma? Miyake nufi da labarina zai shiga duniya? Na shiga uku ALLAH karka bama bawannan damar cutar da rayuwata ko ahalina gaba d'aya.

Munubiya data lura da halin danake cikin ta sakani gaba da tambay

ar, tun ina k'ok'arin 6oye mata Dan kar hankalinta itama ya tashi, harna fito fili na sanar da ita gaskiyar abinda naji da kuma gani, harma Wanda na aikata.

Hankalin Munubiya ya tashi sosai itama, nanfa muka Shiga kullawa da kwancewa Munason gani ga

skiyar lamarin, amma mun kasa kama bak'in zaren, fita kuwa mun koma yintane a d'arare saboda tsoron furucin mutuminnan.

a wata ranar talata da Abba zai dawo daga tafiya sai innarmu ta sakamu gyaran d'akinsa saboda kanta namata ciwo. muna tsaka da

aikin sai muka tsinci wani file da yasha k'yak'yk'yawar adana a awani akwati dake cikin wardrobe d'in Abba, to dama da biyu muke aikin, harda bincike akan Neman hasken maganganun da mukaji ranar, jikinmu har rawa yake muka bud'e wannan file, a shafin farko

mukaci karo da wani Abun daya kuma rikita tunaninmu”.



👇🏻

*_Tabbataciyar wasiyya ga ahalina, koda ace na kwanta dama kafin cimma burina ko mik'a wannan sak'on amana ga Wanda ya cancanta, to na shaida muku da cika umarnina na i

da nufina a garesu 'ya'yana ko 'yan uwana, inason Ku isar da wannan amana da aka bani ga ahalin wannan masarauta............”._*

“iya nan rubutun ya tsaya, muka bud'e shafin na biyu kozamuga sunan masaurar da Abba ke magana da k'arashen zancensa, am

ma sai sunayen mutane muka gani a k'alla sunkai goma. Wucewa mukayi shafi na uku, a dai-dai wannan lokacin Abbanmu ya shigo d'akin batare da mun Ankara ba, wata hargitsatstsiyar tsawa mai tsinka hanji ciki da zukata ya daka mana yana fad'in “ku harkunkai g

irman da zakumin bincike a d'aki a matsayina na mahaifinku? mi kuka sani akan wannan takardar dahar kuke binciken abinda ke cikinta? Yaushe kuka koma la6e?”. haka Abba ya rikice gaba d'aya muma ya rikita mu, ya dinga zabga masifar dahar tajawo hankalin jam

a'ar gidanmu, indai tak'aice maka bayani har innarmu saida fushin Abba ya shafa ranar, hakanne yasani fahimtar Abba ya gane naji komai a ranar. munshiga damuwa a time d'in matuk'a, dukda hak'urin da muka bashi yak'i saurarenmu, ya d'au tsawon lokaci yana f

ushi damu kafin ya daina. bayan komai ya daidaitane kuma wani yammaci mun fito daga school saiga motocika a jere suna tsula uban gudu a titi, wucewarsu tamkar iska yasakani fad'ar bak'ar magana ga manyan k'asarnan har 'yan uwana na tayani. Sai kuma mukaji

sunanka a bakin wani saurayi da 'yammata biyu. Wannan ganinaka ne yasakani dawoma Munubiya da abinda ya wuce, saboda sunan Galadima da mukaji saurayinnan ya ambata, sai muka dinga tunanin kokaine

Wanda muka ta6aji a furucin bak'on Abba?. ga kuma sunan masa

rauta da muka gani a rubutunsa, dukda bamuji sunan ainahin masarautarba kuma, balle mu tabbatar da kaid'inne.. Ganinmu dakai na biyu kuma saika bani haushi, dan ganinka mutum mai yawan izza, sainaga bebekin Abba daya saka kansa had'ari akan Wanda shi baima

damu da damuwar kowaba sai tasa gakuma tarin girman kai Dana hango tartare dakai”. (Kafayi hak'uri, gaskiyata nake fad'a, guntun murmushi kawai Galadima yamata baice uffanba) taci gaba da fad'in “Wannan ne dalilin yimaka tsak'i a asibiti, idan har baka ma

ntaba, har dogarinka d'aya yataho da zummar d'aukar mataki amma ka dakatar dashi da fad'in ya barni”.

Galadima ya murmusa alamar bai mantaba.

Nace, “ka tuna kenan?”.

“Na tuna kwarai da gaske, dan bancika manta abuba saidai idan na d'a

ukeshi mara muhimmanci, amma a time d'in ai banga face nakiba, shiyyasa banida tabbacin kece, saidai na muku kallo d'aya a lab da muka iskeku keda sisters d'inki, ni nama zata Ku 'yan uku ne ai”.

“Umyim, amma a time d'in babuma Wanda zai d'auka Kasa

n da zamanmu a lab d'in, dan gaisuwar da ake maka ma, kamak'i amsawa sai d'aga hannu, hakanne ya tunzurani na fito daga lab d'in, dasu munu sukace kainema kabada jinin da za'a sakama feena ban yardaba”.

Baki Galadima ya d'an ta6e yana shafa kwantac

cen sajensa, ya d'agamin gira d'aya yana fad'in “bazaki fahimta bane yalla6iya. yanzu labarin da kika bani ya farune duk a wace shekara?”.

Na d'an ya mutsa fuska ina fad'in bamai nisa bace, dan ko 2years cikakku baza'a k'ulla ba, Muna Exam d'in NECO

nema, dan har results d'inmu suka fito aka fara biyan JAM Abbanmu ya biyama sauran 'yan uwanmu amma banda ni da Munubiya, sai baba k'aramine ya biya namu, so munfara karatu dai babu dad'ewa muka shirya da Abbanmu saboda magana da dad d'insu Ayusher yamasa

Yakuma sake bashi hak'uri. tundaga nan komai yazama Normal. Amma kaikanka yakamata kayi mamakin yanda a kwanaki kad'an na amince da tayin auren Contract d'in da kukaimin, dukda ba waccan binciken namu kawaine keda alak'a da amintar tawaba, akwai wani dalil

i daya shafi ahalina”.

Mik'ewa Galadima yayi yana salute d'ina, yace, “kin cancanci yabo my friend, dukda tabbas a farkon aurenmu kema kina cikin zargina akan turoki akai gareni tun farko, amma yanda kike halayyarki da d'abi'unki sai kika kauda han

kalina, a tunani na dukkan mutum dazai kwantarmin dakai yaringa nuna tsorona to tabbas wannan mutumin sunamsa *MAGE MAI KWANCIYAR 'DAUKAR RAI* a wajena, amma kece mutum ta farko kuma mace data iya mayarmin murtanin magana kai tsaye, batare da shakka ba, sa

i dai inason Sanin minene alak'arku da Muftahu to?”.

“muftahu kuma? babu wata alak'a bayan wadda kasani, dan tare Na fara ganinku ai”.

Takowa yay zuwa inda yake zaune a da, ya koma saman kujerar ya zauna, “kin tabbatar babu alak'a ta k

owane fanni?”.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login