Showing 210001 words to 213000 words out of 407268 words

Chapter 71 - Raina Kama COMPLETE

murmushi jakadiya tayi, tace, “gaskiya ta fad'a, juyine, amma nadad'e banga uwa mai kawaiciba irinta a wannan zamanin”.

Murmushin itama aunty Mimi tayi

, ta maida kalonta kansu, yafara lafawa sosai, dan haka munaya tafara tsagaitawa da kukan.

Galadima yakuma k'ank'ameni a jikinsa sosai yana shafa kaina, nikam sai ajiyar zuciya nake saukewa tareda shashshekar kuka, ya manna min kisses a kaina idons

a a lumshe, danshi yama manta dasu Aunty Mimi a d'akin.

Jakadiya ma dai lalla6awa tai ta gudu, dan taga magajin gari yau sai a hankali.

Aunty Mimi ta tako inda suke ta zauna a sofa tana fad'in “sannu Munaya”.

Bud'e ido Galadima yayi,

harsun kad'a zuwa launin jaa, yad'an furzar da iska yana lek'a fuskarta, barci ya d'auketa. ido ya d'ago yana kallon aunty Mimi dake kallonsu cike da sha'awa, tamasa murmushin kwantar da hankali, ajiyar zuciya ya sauke yana cije lips da jinjina mata kai.

Tace, “tayi barcine?”.

Nanma kansa ya jinjina mata, yana gyarama Munaya kwanciya a k'irjinsa yanda zataji dad'i, yace, “Aunty Mimi amma yakamata muje asibiti aga miye matsalar?”.

“karka damu my k'ani, juyine kawai, insha ALLAH babu w

ata damuwa. bara inje nima saida safe, idan kuma kaga dawata matsala saika kirani muje asibitin tunkan dare ya kumayi”.



Bayan fitar aunty Mimi kuma k'ank'ameta yayi yanamai jin tausayinta na ratsashi, ya sumbaci goshinta, kafin ya d'auk

eta dukda nauyin datayi ya maidata saman gadon, yanzunma a jikinsa ya sakata, yaja bargo ya lullu6esu tareda musu addu'ar kwanciya.

Cikin barci ta farka da wata matsananciyar yunwa, k'irjin Galadima na shiga girgizawa ina kuka.



Galadima ya farka a firgice yana rik'e hannunna, ya yunk'ura da k'yar ya tashi zaune, “miya faru?”. ‘yafad'a cikin muryar barci’.

“yunwa yalla6ai, abinci xanci, kafad'a masa magana yabar halbina”.

Dukda tabashi tausayi saida ya murmusa, s

auka yay yafita, k'asa ya sauka zuwa kitchen, yau saiga Galadima a kitchen

🤣

, rasa mizaimayi yayi, ganin yana 6ata lokacine kawai dan ba iya uwar komai yayiba saiya fice, dole yaje ya tado kukunsu.

Mai aiki da aikinsa dannan saigashi ya had'a mata A

bu mai sauk'i, Galadima ya kar6a da kansa Yakoma saman.

Isketa yayi zaune tsakkiyar gado tana kuma rurus, saita k'ara bashi tausayi, ya haye gadon da abincin, da kansa yabata yana lallashi. saida tayi nak sannan ya sauka da tiren yana sauke tagwaye

n ajiyar zuciya.

Nikam hankalinna kwance nazame na kwanta, barci ya sake kwasheni.

Mamaki yasakashi tasata gaba yana kallo, saikace wata mai aljanu, lallai duk namijin daya kasa tausayawa matarsa lokacin da ciki yake jikinta yacika mara tausayi

number d'aya, babu abinda miji zai iya biyan matarsa dashi akan rainon cikinsa datayi da tarbiyyar 'ya'yansa, amma a wannan time d'in wani namijinma rashin tausayinsa ke tashi akan matar, ALLAH ya ganar dasu to.

Amin galadima

🙁😔

.

*********

*************

Washe gari

A safiyar yau su Abba suka tashi da shirin komawa Nigeria, gaba d'aya saina tashi duk babu dad'i, jinake kamar karsu tafi, dana tuna yaune zasu barmu sai hawaye ya zubomin, inama zai amince nidai nabisu mu tafi

tare?.

Agogo da zoben jiya na d'auka nafita masaukin su Abba, dan Galadima ya fita tunda sasaafe, bansan ina yajeba.

Saida nayi sallama aka bani izinin Shiga sannan na shiga, Abba na zaune a bakin gado agogo rik'e a hannunsa suna magana da

innarmu dake tsaye ita kuma tana zuba sauran kayansu a k'aramin akwati.

Abba yay murmushi yana fad'in “sannu munaya kinji”.

Murmushi nayi a kunyace, na dafa gadon zan durk'usa k'asa na gaidasu amma saiya dakatar dani ta hanyar rik'e hannuna, “k

inga zauna, inake ina durk'uso yanzu”. da taimakon Abba na zauna a kujerar dake kusada gadon, sai faman jeran sannu yakeyi, nikuma ina amsawa cikeda jin kunya. gaishesu nayi, suka tambayeni yaya jikin? na amsa da “Alhmdllh”.

Jakar hannuna na mik'ama

Abba, ya amsa yana fad'in “minene kuma?”.

“Abba ka bud'e to”. ‘nayi maganar a shagwa6e’.

Dariya yayi yana k'ok'arin bud'ewa, “yanzu dai fitinarki k'aruwa ma tayi Munaya”.

Innarmu dake ta6e baki tace, “ai bamaka san fitinarta ta zarce

tadaba sai jiya, juyi kawai ta zauna tana rusama mutane kuka a gidannan, yo ke aibama asan abin fad'in dazaki bariba ranar haihuwar?”..

“babu abin fad'in dazata bari insha ALLAHU”. cewar Abba yana juya agogon fuskarsa d'auke da murmushi.

N

ima sai ban kula zancen Innarmu ba nace, “Abba yayi k'yau?”.

“sosai kuwa Munaya”.

“Abba kawo na saka maka to”.

“to amma kekuwa ina kika samu kud'in sayen wannan agogon da zoben mai tsada haka?”.

Murmushin nayi, nace, “Abba awani

shago mukaje sayen kaya tun kwanaki dashi, daga nace agogon yamin k'yau shinefa yace na d'auka to”.

“Amma munaya yayi tsada da yawa, karna sakejin irin haka, dan takurawace ai, idan kuma bashida k'arfin siyen abunfa? Karki sake kinji ko?”.



inasha ALLAHU Abba bazan sakeba, amma dan ALLAH karkace bazaka kar6i wannanba, dan shima bazaiji dad'iba”.

Murmushin Abba yayi, yashiga sanya albarka a garemu da abinda ke cikina, hardama addu'ar d'orewar lafiya ga Abie shima. cikeda d'oki naita am

sawa da amin, da kaina na saka masa agogon da zoben.

Daga nan muka d'an ta6a hira. Dan akwai sauran time sosai na tafiyarsu. Mun dad'e muna hira, dan ko break fast yau tare dasu na sakeyi, dama tun asuba ni yanzu nakeyin nawa

🤭

, sanda kowa zai k'ara

sainayi na biyu.

😂

Galadima ma daya dawo ya kimtsa nan yazo ya samemu, yanda suke sakin jiki da juna shida Abba abin na bani mamaki, Galadima yakuma yima Abba bayani sosai akan yanda zaicigaba da tattalin lafiyarsa da kulawa da dukkan dokokin

da sukai masa, daga nan muka cigaba dad'an ta6a hira, itadai Innarmu duk adabaibaye take, danma taga yau zasu wuce da bazata zaunaba.

Wajen 12pm mukabar gidan zuwa asibiti, a asibitine akayi dogon zama, dan godiya ta musammance tashiga tsakanin s

urukan guda biyu, Abba kuma yay alk'awarin kuma tsayawa wajen dagewa da addu'oi na musaman ga jikin Abie da alk'awarin kawo wasu taimakon na tsarin jiki, dan sunga fa'idar addu'a sosai.

Kowa jiyake tamkar karsu tafi, saboda shak'uwace ta musamman

tashiga tsakanin wad'annan families guda biyu, zaman mutunta juna ya gudana sosai a tsakani.

Kuka na shiga rairawa lokacin danaga tafiyarfa da gaske yinta za'ayi, sai alokacin muka san ashe wai harda Sauban, zai rakasu saudiyya suyi umrah ta kwana

10, daga nan saisu wuce shikuma yadawo. na kama hannun Abba na rik'e gam nak'i saki zai hau jirgi, su Sauban suka tasani da dariya kuwa, oho ban

kulasu ba, Galadima ya girgiza kaiwai yana murmushi, yarinyarnan ta6ararta tayi yawa, yafad'a yana takowa inda

muke da Abba yana lallashina.

A Kallonsa Abba yayi sukayi murmushi, Abba ya zame hannunsa a hankali yajuya zuwa ga jirgi, yunk'urin binsa nayi Galadima yay azamar rik'o min hannu batareda yayi magana ba, juyowa nayi na fad'a k'irjinsa ina kuma sakin s

abon kuka.

Hannu biyu ya saka ya rungumoni yana guntun murmushi.

Innarmu dake hangenmu ta cikin jirgi ta share hawayenta itama tana murmushi, banda aure waya isa ya rabaka da 'ya'yanka. Abba daya zauna kusada ita ya saka hannunta cikin nasa ya

na murzawa, juyowa tayi ta kallesa, yamata murmushi yana share mata hawayen da har yanzu sun kasa tsayawa, jikin kafad'arsa ta d'ora kanta kawai.

Sauban dake kallonsu yay murmushi, lallai Aunty gimbiya 'yar gatace a gidansu.

Saida naji al

amun jirgi zai tashi sannan na d'ago kaina, inaji ina gani jirgin yafara shawagi a samaniya harya shilla da iyayena.

A motama haka naita sharar hawaye, dayake dagani sai shi da Samha a motar, cankuma Aunty Mimi da Khaleel da jakadiya.

Samha ta

na ta bani hak'uri, amma tamkar tana zuganine, saida Galadima ya harareta yana mata alamar tamasa shiru sannan tayi shiru, shikam ko sau d'aya baicemin uffanba..

Asibiti muka koma, tunda muka shigo Momma ta taso ta rungumeni a jikinta tana lallash

i.

Galadima ya jingina da bango ya hard'e hannayensa yana kallonmu, a haka sauran suka shigo suka iskemu, Abie ma kallonmu yakeyi cike da tausayina.

Saida nasamu na tsagaita da kukan sannan nacema Momma zanci abinci.

Galadima yaje kus

ada Abie ya zauna yana k'aramar dariya, “dama kice yunwa kikeji kika zauna kinama mutane ta6ara?”.

Hararsa Momma tayi tana masa dak'uwa, hakama Abie, aunty Mimi kam saida ta rankwasheshi akai.

Gurin ya dafe yana fad'in “a'a yazaku tararmin

ne kuma?, gaskiyafa na fad'a ko Samha?”.

Samha tace, “Uncle nima dai ina bayan aunty gimbiya”.

Idanu ya kwalalo alamar tak'aremin.

Muka had'a ido na hararaesa.

Lips d'insa ya ciza yanamin alamar zan kamakine da ido.

Na ta6

e bakina nikuma. Dolenesa yatashi yanemomin abinda zanci.

★★★★★★★★★★

Tunda su Abba suka tafi lafiya tamin k'aranci, bana iya tsinanama kaina komai sai kwanciya, dukna fita hayyacina na canja kamanni, ga cikifa sai kuma bud'ewa yake yana k'

ara girma. Kai kace ba halitta d'aya bane a cikinsa.

Galadima dole ya d'auki hutu a office, idan abinda yazama dolene saiyaje Office kam yakanyi shine ta yanar gizo.

Gakuma nasarar jikin Abie daketa k'ara k'yau, dan wasu sassan jikinsa suna n

una alamun fara aiki kamar yanda doctors d'insa suka sanar mana.

A kwana na 8 da tafiyarsu Innarmu ranar a asibiti na kwana, saboda jiki dai yak'i dad'i, ga masifaffen cin abinci abin babu arzik'i.

★★★★★★★

Su Abba sun gudanar da ibad

ar Umrah cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, ga Sauban dake nuna musu komai yanda bazasu wahala ba.

Suna cika kwanaki goma yasakasu a jirgi suka nufi k'asar haihuwa Nigeria kenan, sun rabu cikeda kewar juna suna saka masa albarka.

Sun i

sa Nigeria batareda sanin kowa namuba sai Yaa marwan da Galadima yakira ya sanarma yaje ya d'aukesu a airport.

Isowarsu gidanmu tazama a bazata, hakan yasaka gidan rikicewa da murna, dukda kishin daya cika matan gidan ganin innarsu munaya takoma wa

ta d'anya shakaf saboda Hutu da canji wajen zama data samu, dandanan 'yan anguwa suka shiga shigowa taya murna dama Abba jajen ALLAH ya kiyaye gaba.

Innaro babu kunya taketa haba-haba da d'anta, kota innarsu munaya batayi, dan haushinta takeji taje t

a zauna a India itako an maidota gida. (Babu mai iyama Innaro dai sai ALLAH

🤦🏻

‍♀

🤣

).

Su Ayusher da sukazo suka zage suka gyarama inna d'akinta, komai ya koma need, tamkar ba shineba ya had'a uban datti na tashin hankali.

Tafiyarsu Abb

a Nigeria da kwana 5 Sauban ma ya dawo India, ya iske ina asibiti, dan gado suka bani dole, babu ranar sallama ma, k'ila saina haihu.

Saidai randa mukayi waya da Munubiya nake fad'a mata tace ai gidama yakamata na dawo na haihu, itama batada lafiy

ar sosai.

Da to na amsa mata kawai, amma ina tunanin yanda Galadima da ahalinsa zasu amince da zuwana haihuwa Nigeria, kuma tunda 'Yar uwata ta ambata dolene hakan za'ayi, kona so koban soba kuwa.

___________________________

*_T

wo months ogo_*

😬🤭



Watanni biyu kenan da tafiyarsu Abba, tunda sukatafi kuma babu wani Abu mara k'yau kona Sosa zuciya dayay gamo dashi, harma ya koma wajen aikinsa hankali kwance.

Jama'ar gidansu Munaya kuwa sunyi haushin da nuna ha

ssadar ga inna harsun gaji sun bari, dan sudai san ba kulasu zatayiba, ita yanzu babbar damuwarta ma 'ya'yanta su sauka lafiya, dansu Safara'u duksun haihu sukam, kuma dab da dab sukaita kancamo 'ya'yan, ayanzu haka sunan d'an Fauziyyane kawai yarage gobe

idan ALLAH ya kaimu, dan itace k'arshen haihuwa..

Su fiddausi duk suna gida sunzo wanka, iyayensu kowa ta zuba k'arya a hidimar sunan 'yarta, yanzu maman Fauziyya da innarsu munaya kawai aka zubama ido aga yanda zasuyi nasu.

Inna dai bata d'

ad'ara kanta da k'asaba, iya abinda ALLAH ya hore mata iya shine tai k'udiri yi a hidamar sunansu Munubiya idan sun haihu. Fatantama su sauka lafiyar, dan gasu suna neman share watanni na goma haihuwa babu amo babu labari.

Mama Rabi'a cema kawai keta

k'ok'arin ta na ganin sun tanadi dukkan abin fita kunya, sai Aunty Salamah dake taimaka musu, wadda a yanzu tazama 'Yar uwa agaresu makusanciya, dan komai nasu tana tsaye a akai tsakaninta ga ALLAH.

WASHE GARI akasha sunan d'an Fauziyya. Wanda mi

jinta da mamarta suka bada mamaki, masu shirin asha kunya sai aka barsu su dajin kunyar da shak'ar bak'inciki irinna masu hassada.

Itama tamkar su Haleematu gida ta taho wankan jego.



**************************

A wata ranar tala

ta datai dai-dai da cikar cikunanmu wata goma da sati biyu natashi da matsanancin ciwo, Wanda ya rikita Galadima da ahalinsa, nan take doctors sukace haihuwace, aka fara shirin kar6arta amma ina, gadai haihuwar gadan-gadan da gaske amma kuma nagagara haihu

war har washe garin laraba.

Nayi masifar galabaita, Galadima yace sumin cs idan bazan iya haihuwa da kaina ba.

Amma sukace zan iya haihuwa.

Ranar laraba da daddare Galadima da Momma na kusadani suna ta tofamin addu'a saboda zufar danake

yi, nace su kiramin munubiya, babu musu Galadima ya kira Yaa marwan.

Shima dakaji muryarsa zakasan a rikice yake, hakan yasaka Galadima tambayarsa ko lafiya?.

Yaa Marwan yace, “dadai sauki ranka ya dad'e, tun daren jiya Munubiya ke nak'uda am

ma haihuwa shiru, sai sunan Munaya kawai taketa kira”.

Mik'ewa Galadima yayi tsaye, yace, “muma ai halin da ake ciki kenan, yanzuma itace tace akira mata ita, please kakai mata wayar”.

“ok”. Yaa marwan ya amsa yana nufar d'akinda Munubiya t

ake...............



🏻

Barkanmu da dawowa.

🤩



🏻



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*

😭👏🏻

*_typing

📲

_*



💡

*_HASKE WRITERS ASSO....._*

*_



RAINA KAMA.....!!



_*

_(Kaga gayya)_



*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

_________________________

*_HASKE WRITERS...._*

_gaisuwarku ta musammance, alkairin ALLAH ya baibayeku aminan kwarai abokan tafiya

👍🏻😽

._

I love you manya-manya fa

🥰🥰🥰🥰

🤩🤸🏻

‍♀

___________________

_____

~book 2~

👉🏻

2



2



................Cikin kuka Munubiya tace, “y'ar uwata ki taho gida please”.

Munaya dake saurarenta ta share nata hawayen itama, “insha ALLAH zan taho, ki kwantar da hankalinki, daga yau zuwa gobe ko yaushe zaki iya

ganina sweetheart”.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login