Showing 198001 words to 201000 words out of 407268 words

Chapter 67 - Raina Kama COMPLETE

/>
imaninta, shima murmusawa yayi yana lasar lips, kafin ya d'auke kansa ya maida ga Wanda suke maganar.

Zuwa can gardama ta hark'ume tsakanin yaran akan wani game da iyayen ke dubawa maybe zasu saya musu ne. Kuma games d'

in suna kusada Munaya ne, d'aya a cikin yaran ya d'akko yazo wajen Munaya yana tambayarta wai “Aunty wannan yafi dad'i aidai ko?”.

Munaya bata fahimceshiba, dan yayi maganane da yaren dabata ji, dan haka saitayi murmushi ta tambayesa yanajin English?

.

Yaron ya d'aga mata kai alamar eh.

Ta kuma murmusawa, duk abinda ke faruwa a idon Galadima ne.

Da turanci munaya tace, “yarona kai kata6a irin wannan game d'inne?”.

Murmushi yamata shima, yace “aunty akwai dad'i ma sosai, ranar

saida na cinye kharan a gidansu ma”.

“da gaske?”. munaya tafad'a tana dafa kafad'arsa.

Kansa ya d'aga mata, cike da d'oki yace, “Aunty na koya miki?”.

Munaya ta d'aga masa kai.

Game d'in ya d'ora a cinyarta, ya danna wasu Number, sa

i kuma ya zubasu cikin d'aya, duk suka shige. Cikin mamaki munaya tace “mikenan to?”.

Shima dariyarsu ta yara yayi, yace “Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'ayane, amma sainayi ammafani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi n

a canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacal”.

Sosai abun ya birge munaya, tayi dariya har hak'oranta na bayyana, jawo yaron tayi a jikinta ta run

gume.

Iyayensa dake tsaye suna kallonsu tun d'azun duk sukayi dariya suma, sannan suka matsa kusada munaya suna bata hannu alamar gaisuwa. itama ta mik'a musu suka gaisa, d'aya tace sunanta Radha, d'ayar kuma tace Anjali, munaya ta fad'a musu nata su

na itama, sannan takamo hannun saran yaran tana tambayarsu suma, d'aya yace vanish, d'ayan kuma Anjun, duk kumatunsu ta sumbata tana sakama rayuwarsu albarka.

Wadda tace sunanta Radha tace “kiyi hak'uri da surutun Vishnu shi baya gajiyane ko kad'an”

.

Munaya tace babu komai.

Daganan sukai gaba, munaya tana binsu da kallo tana murmushi, yaran sai waigenta suke suna d'aga mata hannu.

Sunje wajen biyan kud'i akace subar kud'insu inji mai shagon, da mamaki suka tambayi wanene? Mikuma y

asa ya barmusu.

Mai kar6ar kud'i ya murmusawa yana fad'in mijin matarcan da kuka gaisane mai shagon ai.

Munaya batasan mike faruwaba taga sun dawo, godiya suka shiga yimata, ta tambayesu akan me?.

Suka bata amsa da cewar mijinta bai

kar6i kud'in kayansu ba. Murmushi tayi, k'asan ranta tana mamakin dama shagon na Galadima ne?.

Sun katse mata tunani da tambayar kozasu samu number ta, babu musu tabasu sukayi sallama suka tafi.

Maida kallonta tayi ga Galadima dake zaune yan

ata latse-latsen laptop tamkar baisan mike faruwaba, da alama yana duba kayane ko wani Abu, dan time to time Wanda yake gefensa yakan nuna masa wani yanki na kayan dake

shagon, shikuma ya waiga ya kalla, idan bai hango sosaiba saiya kalla ta cikin Computer

d'in dake tareda cctv cameras d'in shagon.

Munaya tace kai mutuminnan akwai son kud'in tsiya, kai komai kana saidawa, wata zuciya tace idan bai nemi kud'iba dame zai kula da mahaifinsa?. “hakane kuma”. ta fad'a a fili tana sauke ajiyar zuciya.

Kusan mintuna 15 saitaga ya taso ya nufota. Zama yay kujerar kusa da ita yana fad'in “sorry friend na barki ke kad'ai. kin gaji mu tafi ko?”.

Munaya tad'an yamutsa fuska tace “ba sosaiba”.

Ya d'an murmusa, “ok tunda baki gajiba koza

ki d'an mana taimako ni da abin cikin kwan?”.

Hararsa tad'anyi, itafa haushin wannan abin cikin kwan dayake fad'a takeji.

Hannu yasa ya dafe bakinsa yana fad'in “maida wuk'ar”.

A tare suka dinga zagayawa cikin shagon, dayake

babbane sosai, kayan yarane kuma zalla a wajen, komai bibbiyu take d'auka, baice komaiba, dan yasan dai bai wuce tana had'awa da cikin 'Yar uwarta Munubiya bane. Sund'an d'iba kaya babu laifi, yabada ATM d'insa aka d'auka harda na wad'ancan matan, yaran sh

agonne suka kai musu har cikin mota.

Yanzuma haka suka taho tamkar kurame.

Kowa da abinda yake sak'awa....

Danja data tsayar damune yasakashi juyowa yad'an kalleni, ganin hankalina nakan wasu yara 'yan makaranta dake mota yace, “dama

haka kike da son yara?”.

Juyowa nayi Na kalleshi, amma saiya d'auke kai tamkar bashine yay maganarba ma.

Nima maida kaina nayi ga yaran, a kuma time d'inne muka sami damar barin wajen.

Saida muka fara tafiya nabashi amsa da “yalla6ai k

enan, waye zaice baison yaro, a duniya babu abinda yafi k'uruciya dad'i”.

Kad'an ya juyo yad'an kalleni yana fad'in “really?”.

Nima kallon nasa nayi ina fad'in “na tabbata amsarnan kowama zai baka idan ka tambayesa”.

Bai kalleniba y

anzun kam, hankalinsa naga tuk'insa, yace, “ALLAH ya kawoka duniya lafiya abin cikin kwan”.

“shiru namasa bance uffanba”.

Har muka isa gida kuma babu Wanda ya sake magana a cikinmu. Saida yay parking motar a harabar gidan sannan ya juyo garen

i, ina niyyar bud'ewa Na fita ya ruk'o hannuna. kallonsa nayi da mamaki, yawani ci magani irin babu raininnan, kamar zanyi magana saikuma nayi shiru muka zubama juna ido, kowannenmu zuciyarsa Na bugawa da sauri-sauri. Cikin k'asaitarnan tasa yace, “Addu'a

nayi amma jan aji yahanaki amsamin da amin”.

Ni dariyama ya bani wai jan aji, hakanne yasakani murmusawa kad'an ina k'ok'arin janye idona daga cikin nasa, amma saiya hanani hakan, nace, “na amsa ai, bakaji bane kawai”.

“aiba kurma kika aura

ba”.

Uhm wannan aure ana tak'ama dashi, Na fad'a a raina, a fili kuma nace, “a zuciya Na amsa”.

“k'arya haramun, banji wannan sak'onba a tawa zuciyar”.

Da mamaki Na waro idanu waje ina fad'in “ban fahimceka ba”.

Lips d'insa yad'

an ciza da hak'ora yana matsoda fuskarsa dab da tawa, gashi ya sark'eni da idanu nakasa matsawa, d'an yatsansa ya d'ora saitin zuciyata, muryarsa k'asa-k'asa tamkar mai rad'a yace, “zuciyoyi aminan juna sukan kar6i sak'on juna alokacinda d'aya ya aikashi g

a d'aya, karki jahilci kanki har yanzu akwai sauran dama”.....

Yana gama fad'a ya saki hannuna, tareda bud'e motar ya fice.

Galala nabisa da kallo tamkar wata sokuwa, nakasa motsi nakasa fassara zantukansa da ma'anarsu.

Tsawon mintunan dah

ar bayin gidan sungama kwashe kayan da mukazo dasu ban fitoba, bud'ewa naji anyi, hannunsa kawai ya mik'omin alamar nakama Na fito. tamkar sokuwa haka Na d'ora hannun cikin nasa, ya kamoni ahankali Na fito, maimakon ya sakeni saiya jawoni Na shige jikinsa,

ya d'ora kansa a dokin wuyana, cikin kunnena yace “wasu bayanan basa buk'atar fassara, ayanda sukazo ahaka ake barinsu, karki zurfafa tunani, dan yana kawo ciwon kai da hana Hutu”.

Ya d'ago kaina tareda janye jikinsa yana d'agamin gira da salute d'i

na, ya juya zuwa cikin gida.

Binsa kawai nakeyi a baya tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki.

A falo muka iske duka ahalin gidan, har Momma dazata kwana yau a gida, Abba ne kawai babu, muduka sun birgemu, Dan hira suke ta nishad'i da girmam

a juna.

Dagani harshi gaishesu mukayi, Sauban da Samha dasuka k'arasa da kayanda da bayi suka shigo dasu suka sakko daga samanmu suna mana sannu da zuwa.

Ni kad'ai Na amsa, Galadima hannu kawai ya d'aga musu.

Momma tace, “kuje ku huta ma

na”.

mik'ewa mukayi duk a kunyace, ina gaba a yanzu yana baya, suduka da kallon sha'awa suka bimu, dad'i da farinciki Na ratsa zukatansu, innarmu harda kwalla suka cika idonta, Wanda ita kad'ai tasan fasaarar kayanta.

★★★★★★★

Da dad

dare Galadima Na zaune akan sofa ya d'aura k'afafunsa saman teble yana latsa laptop, yayinda Munaya ke zaune a tsakkiyar gado tana karatun wani English novel na Galadima, buk d'in love story ne dan haka taketa faman zabga murmushi, lokaci-lokaci yakan d'ag

o ido ya kalleta, saboda idan tayi murmushi yakan jiyo sautinsa.

Maida kansa yayi, yacigaba da aikinsa dayakeyi akan numbers d'in layin Abba na sirri, kwatsam sai maganar yaron d'azu na shago mai suna Vishnu ta fad'o masa a rai.

*_Aunty ai

wayo na miki, Abu guda d'aya ne, amma sainayi amfani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'ay

a kacal._*

Saida yakuma maimaita maganar kusan sau uku a ransa, kafin ya kalli Munaya da dukkan hankalinta ke kan Novel,

“Friend!”.

Ya kirata a nutse.

Da “na'am” Na amsa ina kallonsa, saikuma Na janye saboda wandon jikinsa bai

ko rufe masa cinyaba, sai k'aramar riga mara hannu.

Yace, “mikika fahimta ga zancen abokinki na shago?”.

“abokina? waye abokina?”.

Tasowa yayi dagashi har laptop d'in da coffee d'insa ya hawo gadon, nima saina tashi zaune sosai.



Ya zauna ta gefe tareda ajiye mug d'in hannunsa a drowa d'in gefen gadon, laptop d'in kuma a saman gadon d'ayan gefensa. hannu ya mik'amin alamar nazo.

Ban musa masaba Na matso, ya kamoni ya sakani a jikinsa, dan tsakkiyar k'afafunsa ya sakani, sain

a zame Na kwanta na d'ora kaina a cinyarsa, (dama wajen lak'ewa nake nema

🤪

).

Ya kar6i buk d'in hannuna ya ajiye gefe, ya d'ora hannunsa a saman cikina.

Kuma maimaita masa tambayar nayi.

Ya shafa sajensa yana cije lips, “miyasa wataran ki

ke da basarwa”..

“ni d'in?”. ‘nafad'a ina nuna kaina da kallonsa’.

Bai bani amsaba yace “ina nufin yaron d'azun”.

“Oh sorry”. nafad'a ina gyara kwanciyat.

Nace, “wai Vishnu? ”.

Kansa ya d'aga min

“to amma wace magan

ace tasa? tazama abin nazari yalla6ai?”.

“game”.

“game! game!” nashiga fad'a ina k'ok'arin tunanowa.

“okay, wai yanda yafad'i yaci game d'in?”.

“Uhhm”. ya fad'a a tak'aice..

Nikuma saina murmusa, “to dukda dai bansan ma'an

ar d'aukar maganar da muhimmanciba amma anawa tunanin yana nufin _abinnan mabanbantane, amma saiyayi amfani dasu cikin Abu d'aya, kuma sukai masa aiki iri d'aya, sannan duk shi kad'ai ya sarrafasu akan Abu d'aya bawai yayi tarayyar da wasu mutane da yawa b

ane ko aikinsa had'aka,_ wannan itace fahimta ta ga zancen nasa”.

Lumshe ido Galadima yayi, ya duk'o a hankali ya mannamin Sumba mai k'au a goshi. Sannan ya d'akko novel d'in ya damk'amin a hannu, yajawo laptop d'insa yacigaba da aikinsa.

Kal

lon mamaki kawai na zuba masa, kokad'an ban fahimci muhallin maganar tasaba da son fashin bak'i.

Batareda ya kalleni ba, idonsa akan system d'insa yace, “kallonfa?”.

Janye idona nayi ina ta6e baki.

Shima saiya ta6e nasa alamar yaganni kena

n. karatuna nacigaba shima yacigaba da aikinsa yana shan coffee time to time.

Yayi aiki mai tsawo kafin yasaki wani murmushi da ajiyar zuciya, ya kalli munaya da barci ya kwashe, fuskarta ya shafa yana kuma sakin wani murmushin, “tabbas gaskiya Vi

shnu ya fad'a, mutum d'ayane ke amfani da Numbers daban-daban wajen kiran Abba munaya, duk wadda yagama da ita bazai sakeba, tagama aikinta, a wannan karon lallai kunyi aiki da basira, wadda harta birkita tunanin Sameer, kuna kiran Abba da mabanbanta Numbe

rs wad'anda kunrigada kun gama shirya matakan da kowacce number bazata sake aikiba, shima kansa ya d'auka mutane daban-dabanne ke kiransa. O ALLAH wannan shine bada k'afa, to ai inkunsan wata bakusan wataba kuma, Muhammad Sameer ruwane, idan

bakasha yanzub

a zakasha anjima, idan kak'i kuma k'ishirwa ta kasheka. Inhar tarkon dazan d'ana zai d'annu dai-dai, tabbas zan cafke kurayen daji mai duhuwa a wannan karon”. ‘Ya k'are maganar da jan hancin munaya yana kuma sumbatar goshinta’.

Kwanciya ya gyara mata

sosai, ya ja bargo ya lullu6a mata sannan yaje bayi ya d'auro alwala, kamar yanda ya saba ya raya wannan dare da nafilfili da godiyar ALLAH, kafin yazo ya kwanta gefen munaya zuciyarsa na cike da annashuwa da farinciki, kaikace komai yayi done ne.



Addu'a ya musu sannan yasakata jikinsa barci ya Lula dashi shima.

Nima mai d'aukar rahoto bara nad'an rintsa my sweet sisters

😉🤩

......................



🏻

Duk Wanda yaga ban amsa massage nashiba yamin afuwa, nayi up date WhatsApp d

'inane

🥰🥰🥰

🤝🏻

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu

👏🏻😭

_**_typing

📲

_*



💡

*_HASKE WRITERS ASSO....._*

*_



RAINA KAMA.....!!



_*

_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

~Book 2~

👉

🏻

1



8





1



9



.................Na dad'e ina barci kafin Na tashi, nayi mamakin ganina ni kad'ai, bansan time d'in da Galadima ya ficeba, sakkowa nayi daga gadon Na nufi Na watsa ruwa.

Ina tsaka da shafa mai Samha ta shigo, saida tayi sallama

nabata izinin shigowa sannan, ledar hannunta Na kalla ina fad'in “mikika samo mana 'Yar Uncle?”.

Cikin dariya ta zauna kan sofa tana cewa “kayan dad'i ne Aunty gimbiyarmu, alfarma nazo nema wajenki keda Uncle”.

Hankalina gaba d'aya Na m

aido kanta, “Alfarmar mi kuma?”.

“Aunty gimbiya please ki lalla6a Uncle ya barki muje birthday d'in k'awata Dhibya, ALLAH yarinyarnan tana sonki sosai, kullum hirarki”.

Nad'an zaro ido “kai Samha yaza ai naje wani birthday da wannan cik

in? kuma kema kinsan bazai bariba tunda Na 'yammatane”.

“kai aunty, cikin saikace Wanda yayi wani k'ato, kumafa a cikin gida za'ayi wlhy, iyamu goma ne kawai”.

“to naji, ALLAH yasa ya bari, mikika kawo mana a ledar?”.

“yes my swee

t aunty, wannan wani sari ne yamin k'yau a wani shagon da muke zuwa siyan kaya, shine nayi alk'awarin siya miki, Uncle Sauban ya cikamin na siya, yanzu Na kar6o please ki gwada muga”.

Dariya nayi, nace, “inye kaga 'Yar Uncle Anfara jink'an iyaye, t

o amma ni ina na iya saka sari?”.

“kowama koya yayi nidai ki saka muga dan ALLAH”.

“to shike nan bara na gwada, ALLAH ya saka da alkairi, ina alfahari da d'iyata”.

Samha ta fita tana dariya, nikuma na warware kayan, masha ALLAH sa

rin ya had'u gaskiya, farine anmasa kwalliya da pink and silver kad'an-kad'an. Na saka rigar, sai dariya ta kamani, saikace wata bafulatana

🤭🤣

.

Warware zanin nayi, tofa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login