Showing 18001 words to 21000 words out of 407268 words

Chapter 7 - Raina Kama COMPLETE

sun fice gidajen kakanninsu,

tacan masu ra'ayin zuwan suma zasuje.

Mukuwa mudasu yaa marwan muka tafi.

Acikin gari duk inda ka kalla jama'a ne keta kai kawo, musamman yara da 'yanmata da samari, kowa yaci kwalliya ta kece raini da garari (yo dama ai ance

ba'a za6ar budurw

a ran salla, saboda duk k'azantar mutum ranar saika sameshi cikin tsafta da gayu

😂

).

Dukda akwai rana hakan bai hanamu jeruwaba domin kallon wucewar mai martaba sarkinmu da jama'arsa.

Masu busa algaita da kid'an taushine suka fara wucewa,

sai kuma ga tawagar sarki Na biye.

tawagar saiki Na wucewa sai ta Galadima, kamar yanda mukaji wasu gungun samari Na fad'ar cewa ga Galadima nan.

Kowa yasan dama tsarin haka yake, daga sarki sai shi.

'Daga idanuna nayin donson sake gani

nsa a karo na biyu. yanzu kam ya canja shigarsa zuwa milk coulor d'in janfa da wando Na lallausan yadi, Wanda aka k'awatashi da d'inkin surfani Na ainahin gidan masu sarauta, ya d'ora Brown Na alk'yabba mai kwalliyar Milk Color, hakama rawaninsa daya zagay

e fuskarsa ya kasance milk ne, takalmansa heir cover masu lankwasa daga gaba irinna sarauta, sukuma Brown. yanzun kam fuskarsa d'auke take da k'asaitaccen murmushi mai kama da anmasa dole, hannunsa d'aya dayake d'agama mutane yana d'aureda farin agogon azu

rfa, sai zabba biyu a yatsunsa Na tsakkiya Wanda nake k'yautata zaton azurfane suma.

Nanfa su Ayusher suka fara d'aukarsa hotonsa a wayoyinsu.

Tsaki naja ina hararsu, “mtsoww wahalallu kawai, dama kanku kuka d'auka yafi Ku k'are wajen d'ura ho

tunan Wanda baisanma da zamankuba a wayarku”.

Kafin cikin su Ayusher wata tabani amsa, wasu 'yan mata dake kusadamu d'aya ta kar6e da fad'in “k 'yan mata kama kanki, kodai kema son nasa ne yakaiki ga kishinsa?”.

Wata wawuyar harara Na buga ma

ta, “kekuma shasha waya sako bakinki?, kajimin ballagaza kawai, uwarmiye abin so a jikinsa dahar ya isa ayi kishinsa? Ke dai dabakisan inda ke miki k'aik'ayiba ita dakon wahala, dan nakula ke amatanma suffar mata maza ALLAH yayiki....”

Gaba d'aya

suka taso min da masifa tamkar zasu cinyeni d'anya itada k'awayenta..

Yaa marwan dake zaune saman mota a bayanmu duk yana saurarenmu yad'ago kai ya kalleni, yasan tabas Munaya ce, baya buk'atar k'arin bayani kuma ko tambayar wacece ita, tunda Na nuna

halin nawa, yace, “K munaya zoki shige mota”.

Nasan halinsa sarai baya wasa damu, cikin tunzura baki gaba nazo nashige motar Na zauna, amma saina bar k'ofar abud'e k'afafuna awaje, banida buk'atar cigaba da kallon kuma, dan haka nabud'e data nashiga

chart kawai ina cika ina batsewa masifa nacin raina, gashi kuma an hanani amayar da'ita,. sai antayama yaa Marwan harara nakeyi ta gefen ido baima San inayiba, gaba d'ayama sainaji dama banzo kallon hawanba.

Koda muka bar nan ba gida muka komaba, y

awo yaa Marwan yaytayi damu gidajen dangin babansu, bamune muka dawo gidaba sai magriba, kowa yayi ti6is da gajiya.

Mun tarar innarmu da mama Rabi'a sunata shan hirarsu ta zuminci.

Sai kusan 10 suka bar gidan.

★★★★

Washe gari muma a

gidansu mama Rabu'a muka yini har innarmu, koda yakema fitarmu mukayi nida Munubiya, Feena, Ayusher, mukabar su mama agida dasu Aryaan.

Yauma mun zaga gari sosai, dan Ayusher takira mana wani saurayinta yazo ya kwashemu, yauma munje munga hawan sarki

da la'asar, saidai yau babu Galadima a tawagar, hakan bai dameniba, dan nama manta da lamarinsa ni.

Kwanaki kusan biyar zuwa 7 munashan shagalin salla, munsha yawo tamkar bamuda mafad'i mudasu Ayusher, sai Fauziyya dakan bimu wani lokacin idan bas

u fitaba da mamarsu suma.

'Yan matan gidanmu kowa sabgar gabansa yayi, rana d'ayane muka fita gaba d'aya domin gaida danginsu Abbanmu da Innaro takafa ta tsare akan sai munje wai su Anty Ramla sunyo musu sallamar aure.

Kwanaki 10 cif dagama

bikin salla muka koma makaranta.

Haka rayuwa tacigaba da shud'ayawa, yayinda 'yan gidanmu keta shirin bikin 'ya'yansu, shiri akeyi babu kama hannun yaro, kowa burinsa ace 'ya'yan d'akinsa sune Star's, kuma sunfi kowa komai.

Sati uku kacal biki

n yarage, an kawo lefe daga gidan senator halliru, akwatina 24, siyama 12 Zarah 12.

Humm ai ranar munsha kallo Na al'ajabi wajen mamansu yaa Hameed da momy Hadiza, habaici da gugar zana da burga, kowa yashashi, har dai abin yak'ure mamansu haleematu d

a maman Safara'u suka tanka musu, kafin kice mi gida yagama kacamewa da hayaniya, kowa yana ya6ama kowa magana, saida suka gama cin zarafin junansu sannan sukayi shiru bisa tsawatarwar baba k'arami, dayake yana gida a lokacin.

An bar maganarne kawai a

mma badan ta k'areba, mudai a 6angarenmu ma innarmu hana kowa fitowa tayi, dayake weekend ne.

Suma sauran duk an kawo nasu lefan, Aunty Rahaima, Ramlah, Hauwa'u sai aunty khaleesa, suma dai Alhmdllh, komai sai dai mak'iyi, duk da basukai nasu siyama

ba gaskiya. a wannan karonma dai saida akayi 'yan gulmace-gulmace a gidanmu, amma basu bari tafito sarariba.

Suma su yaa Hameed aka kai nasu lefan gidajen matan dazasu aura shida Ya shafi'u da yaa Nasser. suma iyayenmu sunyi k'ok'ari wajen had'a musu

lefen girma, ankai kuma kowa Na sambarka.

Tun bayan gama kai lefe gidanmu yakuma d'inkewa da k'us-k'us na gutsiri tsomar gidan yawa, kowa yana gulmar kowa akan aga wace rawa zaka taka, su 5 masu aurar da 'ya'yan.

Mamansu yaa hameed zata aurar

da 3, yaa hameed, aunty khaleesa da Zarah.

Sai maman Haleematu zata aurar da aunty Hauwa'u.

Sai Momy Hadiza zata aurar da Siyama da aunty Raihan.

Mama Ruk'ayya kuma zata aurar da yaa Shafi'u da yaa Naseer.

Maman Safara'u kuma Aunty

Ramlah.

Innarmu da maman Fauziyya ne kawai bazasu aurar da kowa ba, dan haka suka zama 'yan kallo, sai idan mazajensu sun saka su acikin shawarane.............



🏼

*_Ya Rabbi ka gafarta iyayenmu

😭👏🏻

_*

[4/16, 9:53 AM] +234 811 277

0720: *_Typing

📲

_*

*_HASKE WRITERS ASSO...

💡

_*

_(Home of expert and perfect writer's)_

*_



RAINA KAMA......!!



_*

_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

_________________________

_Happ

y marriage life *SANNA S MATAZU* ALLAH ya sanya alkairi da albarka a wannan aure, yabaku zaman lafiya na har Abadan da zuria d'ayyiba, bad'i muzo cin rangam

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻😄👌🏻

._

__________________________

👉🏻

8



.......Hidimar biki ta

kankama gadan-gadan, dan har bak'in nesa sun fara isowa, a ranar alhamis aka gudanar da sister's and brother's day Wanda mune k'annensu muka shirya musu da yayinmu maza. da farko a tsakar gidan innaro aka shirya, saboda su Abba bazasu barmu mu saka kid'aba

a gidanmu, gashi mun gayyato k'awayenmu ne, sai abokan su yaa Nasser danasu Anas. daga baya kuma sai muka canja shawara saboda samun wani fili damukayi can k'asan layinmu, filin a zagaye yake da katanga an saka gate. Tunda safe suka fara shirye-shiryen gy

ara wajen, kasancewar sai 4pm za'a fara, mudai makaranta muka tafi nida fauziyya da Munubiya, dan munada lectures, amma sauran duk k'in zuwa sukayi, barema su Siyama amare.

Around 3pm muka dawo gida, yauma kam da alama wasu bak'in sun iso, dan gida

n Yakuma cika da yara da 'Yar hayaniya.

Mun tarrar innarmu tana d'akin abbanmu, dan haka mukayi wanka muka fara shirin tafiya wajen taron, ko abinci bamu nemaba, dagani har munubiya mun iya makeup, kasancewar mama Rabi'a tasakamu wajen koya muda Ayus

her lokacin damuka gama secondary, a d'an tsakanin kafin fitowar results d'inmu, taga damuyi zaman banza gamma muje mukoya wata 'Yar sana'ar, tunda bamusan inda rayuwa zata kaimuba. Ko gama shiryawa bamuyiba Rahma tashigo kiranmu inji su Aunty Rahaima, dan

mune zamu musu kwalliya.

Mun tarar dasu duk sunyi wanka dama mu suke jira, zaman musu kwalliyar mukayi, ni nafarama Aunty Hauwa'u, yayinda Munubiya takema aunty Ramlah.

Kiran Ayusher yashigo wayar munu...., ta d'aga tana fad'in “kin isone?”.

Bansan mitace mataba daga can, naji tace, “kizo muna 6angaren su Aunty Ramlah”.

Babu dad'ewa saiga Ayusher itama, ta gaggada su Aunty's d'in, sannan muma tabamu hannu muka gaggaisa cikina musabaha.

“lah dear nifa harna fidda ran zakizo ALLA

H”.

Ayusher tace “kibari kawai, wancan jarabbaben ne yasakani aiki, tuwo mama tayi da rana, kinsan kuma bayaci shi, shinefa ya tsareni wai saina masa sakwara, harfa nayi shirin tahowa”.

“uhm ai lamarin yaa marwan saishi, matarsa dai taga banu

wlhy, shi anya ma yata6a budurwa kuwa?”.

Dariya duk muka sanya a d'akin, aunty Hauwa'u tace, “ai marwan akwai miskilanci wlhy shima, nifa zan iya cewa mun ta6a magana dashi kuwa?”.

Ayusher tace, “yo aunty ai wannan kowama haka yake masa, kom

u muka gaidashi sai yaso yake amsawa, kullum mama cikin masa fad'a take amma abanza wlhy?”.

Nann dai hira Yakoma kan yaa Marwan da mutane masu muskilanci irinsa, Munubiya ce mai kareshi, (dama ita suna d'an d'asawa, nice dai kamar muna ganin hanjin j

una dashi danma ina tsoronsa ).

Kasan cewar mu uku ne sai kwalliyar tai sauri, dan danan muka kammala, nida munubiya mukayi tamu muma, simple makeup mukayi, amma komai iri d'aya, dama haka mukeyi, komai namu kullmun iri d'ayane.

Munyi k'yau, 6a

ngarenmu muka koma mukayi shiri cikin blue d'in skirt da pink d'in Riga kamar yanda aka tsara sai veil shima blue.

Na jujjuya ina kallon kaina a mirror, “kai jama'a nikam bazan iya fita hakaba gaskiya”.

Ayusher dake kwance tana danna wata tad'ag

o ta kalleni, “kai amma kuma wlhy kayan sun miki k'yau, kinganki kuwa? dan ALLAH ki barsu, kiyi rolling veil naki kawai”.

“kai ba munaya kad'aibafa, nima bazan iyaba, after dress zan d'ora wlhy”.

Dariya Ayusher tayi, ta tashi zaune tana ajiy

e wayar, “waiku miyasa k'auyawane sister's, naga a ke6antaccen waje za'ayi?”.

“amma kuma dai ai akwai maza kema kin sani”.

“to alaranmiya, Ku saka, amma kafin Ku saka d'in nidai kuzo miyi hotuna”.

Gaskiya koni nasan munyi k'yau, kasa

ncewar mud'in fararene, kalolin duk sai suka kar6i jikinmu blue & pink. Wanda bai saniba saiya ce mu 'yan uku ne har Ayusher, dan muna matuk'ar kama da juna, sai dai Ayusher tafimu haske da d'an jiki.

Sai da mukad'anyi hotuna sannan muka fito. Inna

rmu tace kunyi k'yau, amma dan ALLAH kar inji wani yayi abinda za'ace gashi-gashi, Ku kama kanku da mutuncinku kunga dai acikin anguwane, idon kowa akanku yake”.

Mukace to innarmu insha ALLAH. mun fita tana binmu da addu'a.

A k'afa muka taka

har wajen taron, tunkan mu k'arasa muke jiyo tashin kid'a. wajen dank'am yake da 'yanmata da samari, k'awayen amare da namu muma, sai 'yan uwa kuma da abokan su yaa Nasser, dama shi ya Hameed bai gayyaci kowaba, yace ya bar mana mu k'anne (shidama ba aure

n farko bane).

Tunda muka shigo akai mana caa da idanu, wasu tsantsar kamarmu ce tajawo hankalinsu kanmu, wasukuma burgesu mukayi, wasu kuma gulmarmu sukeyi da zaginmu, to dama shi taro ya gaji hakan, ballemu da ake ganinmu k'ask'antattu agidanmu, kam

ar kowama yafimu komai.

Amare suma duk sunyi k'yau cikin tasu shigar ta Riga da wando pink gaba d'aya, sai suka d'aure k'ugunsu da blue d'in belt, suka d'aura jacket blue.

Snacks ne kawai akad'anci a wajen da drinks, sai pictures da'aka d'auka

da video, 'yan mata sunata casar rawarsu da samari, mudai muna daga gefe zaune muna shan kallo. mun rarraba gifts d'in damuka tanada, bawani Abu bane masu tsada. silifas d'in wankane sai brush, MacLean, soson wanka da sabulu d'ad'd'aya aciki, gifts d'in na

n mun shiryashine kawai dan tsokana dama. gabda magriba taro yatashi lfy, kowa ya kama gabansa. muma gida muka koma.

★★★★★

Washe garima saida mukaje makaranta, sai dai 11:30 muka fito lecture, ALLAH ya taimakemu muka samu taxi da wuri.



Sanda muka dawo har 'yan jere sun dawo, kowa dangin mamarsa sukaje jerensa, shiyyasa mukaji tsitt babu gutsiri tsoma.

Muna dawowa ko wanka bamu tsaya yiba mukaci abinci muka tafi shagon auntynmu data koyar damu makeup domin yin k'unshi da saloons.

Cikin farin ciki ta tarbemu, dan mun rabu da ita cikin mutunci bayan mun iya aiki, Aunty salamah batada damuwa, inkaga tana maka fad'a to baka fahimtar abinda take koyar dakai ne, kwazon damuka nuna alokacin yasa takeji damu over. Tana kiranmu 'yan uk

un ta.

K'unshi aka mana mai k'yau da gyaran kai, (dan d'aurema k'arya gindi irinnan aunty salamah harda mana gyaran jiki

😊

, wai tanaso muma musamo mazajen aure

🙈

).

Kowa ya gammu yasan munyi k'yau sosai.

Amakare mukaje gida, dan mun ta

rar amare nata jiranmu mu musu kwalliya, 'yan gidanmu harsun fara k'ananun magana, wai wulak'ancine yasa muka fita ai, kuma muna kallon lokaci yana k'urewa mukak'i dawowa. hakan da innarmu taji yasata kiranmu tana mana fad'a, hak'uri muka bata dacewa gamun

an a hanya.

Masifa mukaitayi nida Ayusher, munubiya na bamu hak'uri, wlhy badan innarmu ba da bazanyi kwalliyar nanba yau.

Babu zancen mu huta muka hau musu kwalliyar. aikam ranar k'in fita wajen kamun nayi da akayi a tsakar gidanmu, kwanci

yata nayi, innarmu taitamin fad'a kuwa.

😕

Washe garin asabar d'aurin aure, dakam gidanmu yacika tab, 6angarenmu dai da sauk'in mutane, sai mama Rabi'a kawai da matan abokan Abbanmu.

K'arfe goma aka d'auro auren yaa Hameed da amaryarsa, sai y

aa Nasser shima da yaa Shafi'u.

Na 'yan matan kuwa sai k'arfe 1:30pm. K'ofar gidanmu yacika dank'am da jama'a ta ko'ina, 'yan siyasa tawagar senator halliru da abokan su Sa'eed, hakama mijin aunty Rahaima d'an siyasane, dan haka harda governor a mah

alarta taron d'aurin auren.

Har aka gama d'aura aurarrakin ina d'akinmu kwance, ko wanka banyiba, garama munubiya da Feena da Ayusher su duk sunyi, amma suna d'akin basu fitaba, sai balkisu k'awarmu da itama tazo mana.

Hira suketayi, nikam dai

ina kwance kaina namin ciwo.

Gidanmu babu masaka tsinke, tako ina jama'ane, amare ansha k'yau, su siyama baki har k'anne an auri 'ya'yan sanata, hakama iyayensu sai burga sukeyi, ranar munga gasar dressing wajen iyayenmu mata kam, kowacce so take ace

itace uwar amarya datafi kowa fita.

Innarmu kam babu ruwanta, shiga d'aya tayi ta atanfar da Abbanmu yamusu Na fitar biki, sai da yamma ta canja da less.

Aranar kowaccensu tayi yini. Baza'a kai amareba sai washe gari, saboda anason agudan

ar da dinner waje d'aya, amma an kawo nasu yaa Shafi'u sudai.

Yau d'inma dai mune muka musu kwalliyar su dukansu, kafin k'arfe 8pm afara kwasar mutane zuwa wajen daza'a gudanar da dinner d'in.

Gurin yayi k'yau sosai, yayinda aka shirya ma am

are da anguna hi table.

Sai dai kuma wata sabuwa, ba duk angunan bane suka halarci wajen dinner d'in, nan fa aka fara 'yan gulmace-gulmace tsakanin dangin iyayenmu mata, tuni labari harya kai kunnuwan iyayenmu mata dasuke zaune a gida.

Amare

n da babu angunansu sunsha kuka, wad'anda kuma dama sukasan angunan nasu ustazaine bazasu zoba basu damuba.

Haka dai aka gudanar da dinner d'in zukatan wasu babu dad'i, tunkan agama ma wasu sukaita tafiya gida abinsu. K'arfe 11 aka tashi.

A waj

en dinner kam nayo saurayi mai suna Fu'aad, hakama munubiya da Ayusher dun sunyi, Fu'aad k'yak'yk'yawa dashi masha ALLAH, duk

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login