Showing 330001 words to 333000 words out of 407268 words

Chapter 111 - Raina Kama COMPLETE

su

Alhaji balala matuk'a, amma babu yanda zasuyi.

Zaman Galadima babu jimawa saiga alk'ali ya fito, kowa ya mik'e domin girmamawa, saida ya zauna sannan duk aka zauna.

Kotun tayi shiru kowa ya zubama alk'ali idanu, yagama dube-duben ta ka

rdun gabansa sannan ya d'ago ido yana kallon jama'a, yace, “Yau shari'ar zata tafine kai tsaye batare da shigar lauyoyi Na kowanne 6angare a tsakiyaba, Dan haka muna buk'atar Wanda yay k'ara, da wad'anda ake k'ara a gaban kotu”.

A hargitse su alhaj

i Sageer suke kallon kallo, hakama lauyansu dukya shiga rud'ani, saboda mugun shirin dayayo yau akumace ba haka za'ayiba.

Shikam Galadima wani mugun murmushi yayi yana kallonsu Alhaji mansur d'in damusu wata inkiya da yatsu biyu alamar a kafta, sannan

ya mik'e.

Dole suma duk suka mik'e inda aka buk'aci ganinsu, dukda wajen yamusu kad'anma.



Alk'ali ya kalli galadima. Yace, “kaine Wanda kai k'ara, Dan haka munason jin shin minene mafarin wannan takun sak'a kai tsaye?”.

Murmushi ga

ladima yayi, ya cire eyeglasses d'in idonsa ya saka cikin aljihu, tareda zaro handkerchief ya goge fuskarsa, yasa hannayensa biyu ya dafe katakon gabansa yana jifan waziri mahaifin Harun dawani mugun kallon daya hargitsa y'an cikinsa da tunaninsa, hakanne

yasaka mutane kallon waziri suma, duk sai yaji ya muzanta.

Galadima ya ta6e baki yana janye idonsa dad'an cije lips, cikin k'asaitacciyar muryarsa yace, “ya mai shari'a labarina mai tsawone kwarai da gaske, sannan cike yake da abubuwan ban mamaki da

takaici masu tarin hargitsi, duk da nasan kowa yasan sunana amma zan sake maimaitawa, sunana Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar, gidan sarauta Na fito, mahaifina shine tsohon Sarki da k'addarar ciwo ta kwantar tsawon wasu shekaru, amma lallai da sanadi, wa

nnan kuma sanadin shine Na d'auki tsawon shekaru tundaga tasowata har zuwa yau ina nema. tun daga lokacin dana mallaki hankalin kaina nasan minene matsalar mahaifina natashi da burin d'aukar fansa, sai dai kuma tayaya? Wannan shine yayta wahalar da Muhamma

d Sameer a tsawon shekaru”. Galadima ya k'are maganar idonsa Na ciko da hawaye, yay murmushin takaici yana jinjina kansa da had'iye hawayen.

Hakanne yasaka jikin wasu fara yin sanyi, musamman wad'anda suka k'ullaceshi da farko.

Galadima ya cigab

a da fad'in, “Ban taso maraya ba, amma nayi rayuwa irinta marayun, ALLAH shine gatana saikuma mahaifiyata da kakana da suka tsaya tsayin daka wajen tsayamin nazama jarumi wajen sanin wahalhalun rayuwa Na yau da kullum, duk Sana'a mai wahala kad'ance banyit

aba a k'asar daba tawaba, gakuma gefe ana gwagwarmayar Neman ilimi, ga burin son sanin suwaye suka durk'usarmin da mahaifi?, ban cutar da kaina wajen nutsuwa Na fahimci rayuwa ba, hakama nabama karatuna muhimmanci saboda k'aunarsa da nakeyi, duk da banida

burin yin aiki a k'ark'ashin kowa, Alhamdllh yanzu haka inada Company Na had'aka da duk shekarar duniya yake fidda wayoyin Hannu da computers dakan zagaya cikin duniya, ina alfahar da samun cikar burina sosai, Na dad'e ina bulayin Neman hanyar bincike akan

abinda yafaru da Abie na, alokacin mutum d'ayane zuwa biyu ke bani gudun mawa, wato lauyan mahaifina, baffina Barrister Usman Audu, sai kakana Sarki Abdul-fatah. Ganin inata wahala sanan babu wani haske a cikin lamarin sai suka bani shawarar mizai hana a

nemamin aiki k'ark'ashin wata hukumar tsaro, da farko ban aminceba, Dan irin wad'annan ayyukan basa wani birgeni, hasalima haushin masu yinsa nakeyi, Dan sun gaza binciko Wanda ya cutarmin da Abie na. A tashin farko dana nuna banaso Papi da Baffi sun k'yal

eni, basu sake min magana ba, sai wata rana kwatsam wani Abu yafaru anan Nigeria, wasu y'an ta'adda sukayi mummunar 6arna a sirrin gwamnati, k'ark'ashin hukumar DSS. wannan 6arna ta rikita Nigeria sosai a lokacin, shekaru 10 kenan inhar ban mantaba, a loka

cin nagama bautar k'asata anan Nigeria ina shirin komawa india, bansan ya akayi sukasan nasan Computer ba, har masarauta akazo aka rok'i mai martaba akan Na taimakesu. Da farko kam naso bijirewa amma babu abinda iyayena zasuce nayishi banyiba inhar bai sa6

a shari'a ba, nasanma bazasu sakani wannanba, bisa umarnin mai martaba Na amince da gwadawa idan zan iya, haka akaje dani headquarters d'insu, tun hawan Computers d'in danai a tashin farko Na gane da had'in kan waaunsu aka kwashi bayanan, sannan masu kula

da Computers d'in sunada buk'atar k'arin ilimi ma gaba d'aya. Cikin sauk'i Na d'akko bayanan da aka d'auka Na dawo musu dashi, sannan nasaka musu securitys masu tsaurin gaske daba wani mahaluki dazai kuma musu irin wannan kutsen. Ni ban d'auki abinda nayi

matsayin komaiba, amma agaresu sun girmamashi, sunkuma biyoni har gida da rok'on kasancewa a cikinsu amma nak'i Sam, nama tattara Na koma India, Ashe sunata bibiyata ta wajen kakana, to shima dama yana burin nayi aikin, Dan haka yabasu goyon baya, sannan y

aje har India ya sameni da batun, ya nunamin ta wannan hanyarne kawai zan iya binciko abinda ya faru da mahaifina cikin sauk'i, hakama Baffi ya fad'amin a lokacin, Na zauna nayi nazari dakuma samun kwarin gwiwa daga Mahaifiyata. Rana d'aya sai nima naji ya

kamata Na amince, Dan haka Na amince, tundaga lokacin nashiga cikin hukumar CID nima, saidai ina musu aikine cikin sirri, a hukumarma ba kowa yasan daniba, tunda ni komai ta computer nake gudanar dashi. Sir Isa Maharazu shine ya taimaka min wajen binciko f

ile Na binciken case d'in mahaifina, Wanda tun kusan shekaru 8 mai kula da case d'in ya rasu, Wanda kuma suke ta fannin y'an sanda suma sukayi shiru, daganan aka ajiye case d'in gefe kawai. Tun a file d'in nafara cin karo da sunayen wasu daga cikinsu Alhaj

i Lawan tanderu. Nasha mamaki kwarai da gaske amma sai banyi wani yunk'uriba, ina wata shida da aiki wani yaso min kutse a cikin Computer, ta silarsa nagano uban gidansa, har zuwa Kansu Marigayi Alhaji Labaran kachia. Tundagafa wannan lokacin saina tsanant

a bincike da kwakwalwa dakuma tannin aiki, bisa taimakon sir Isa, mun baza yara cikinsu Tanderu batare da sunsaniba, kullum kuma cikin bin diddigin motsinsu suke. Kwatsam sai Tanderu ya rasu sanadin had'in mota, babu jimawa shima Alhaji Labaran khacia ALLA

H yamasa rasuwa sanadin rashin lafiya. daga nan saina d'an dakatama gaba d'aya da wani bincike Na koma gefa Na zuba musu ido kawai.

Saida Na d'auki kusan shekaru biyu ban sake wani yunk'uriba sai kwatsam muka wayi gari mijin Yayata Haneefa yayi

had'arin Mota, saidai kuma a ranar ne aka turomin massage daya nuna accident d'in nashi akwai saka hannu a ciki, dayake bai rasuba a lokacin sai a asibiti bayan awanni uku da kaisa, Alhaji shehu Darma abokinsa ne Na kut da k'ut sannan d'an uwansa, Dan haka

yana tare damu a wajen, saina matsanta akan tambayarsa kozai fad'amin akan miya faru dashi kafin had'arin? Bai iya cemin komaiba sai murmushin k'arfin hali da yayi yana kallon Alhaji shehu har numfashinsa ya k'are, wannan kallo ya tsayamin a rai sosai, Da

n nagaza mantawa dashi, abinda Yakuma k'arfafa min zargin Alhaji shehu shine Aunty Mimi Na fita daga takaba sai Yace yanason aurenta, nine Na hana, nama tattarata gaba d'aya itada y'ay'anta Na maidasu india, dukda dangin mahaifin yaran sunso d'aukarsu suma

. Dama can lokaci-lokaci Alhaji shehu yakanbi mijin Aunty Mimi suje duba Abie, dan haka ko bayan rasuwarsa bai daina zuwaba, abinda na fara fahimta shine Samha d'iyar marigayi tana tsoron Alhaji shehu, amma shi yana tsananin nuna mata kulawa dayin kaffa-ka

ffa da ita a gaban mutane. Wannan ma yasa na kuma saka ido a kansa, abinda Na fara karo dashi shine Alhaji shehu yana tursasa Samha ta hanyar mata barazana akan ta d'akko masa wasu sirrikana”. Galadima ya murmusa cikin takaici yana gyara tsayuwa da goge fu

skarsa da handkerchief. Yaciga da fad'in,

“Tunda Na fahimci hakan saina jata a jikina, nakuma dinga ajiye mata dukkan abinda yasaka ta d'akko, itako data gani saita tura masa saboda tsoron barazanar da yake mata. Suma sauran Na cigaba da bibiyarsu

suda ayyukansu, so banida matsala da sauran mugayen halayyarsu, nidai kawai wadda ta had'amu nakeson Sani, Dan Na gano sun gana da mahaifina ana gobe abinda ya sameshi zai sameshi, kuma yafito daga d'akin tattaunawar ransa a 6ace. Batanci da akaimin a she

kara d'aya data wuce cikin jaridar manuniya shine mafarin yalwatur haske a matsalolina, dukda Na fahimci ankai tsawon shekaru ana bibiyar dukkan al'amurana, kuma inhar Nazo k'asarnan kullum cikin bibiyata ake, domin rufe bakin mak'iyana Na auri wadda sukas

o sakawa a matsalar dabatajiba bata ganiba, wadda a yanzu Alhmdllh itace uwar y'ay'ana, nasan hakan ya girgizasu a lokacin kwarai da gaske, adalilin zama da ita nama fahimci abinda ban fahimtaba da farko, Dan da Duk zargina ko da itane aka had'a kai wajen

Neman 6atamin suna, amma sainaga dukba haka baneba, ya mai shari'a Alhaji Auwal Fharuk sai shine surikina mahaifin matata, kuma anyi yink'urin kasheshi watanni kusan 7 da suka shige, saidai ALLAH ya k'addara yanada sauran kwanaki a gaba, bisa dalilin yun k

'urin kisansa ne kuma Na fara karo da alak'ar case d'in mahaifina dashi, hakan kuma tafaru bisa sanadin matata, data dinga zak'ulomin wasu masu alak'a da mahaifinta kuma Na jikinsu tanderu, irinsu Mamman k'afur, Alhaji Halluru, saikuma daga baya ga SD, wat

o Alhaji shehu Darma, Wanda shine aka saka yake bibiyar Alhaji Auwal Fharuk yana masa barazana, satar yarana da akayi a ranar sunansu ta kawo bayyanar aminina d'an uwana cikin case d'in mahaifina daban ta6a tunanin kasantuwarsa a cikiba, wato Harun d'an gi

dan waziri, shine wazirin mahaifina shine kuma wazirin Sarki Na yanzu, ina cikin rud'anin Hakan saikuma ga Alhaji Rabilu ya bayyana a gareni shida Badi d'a ga mai dokuna a masarautarmu, Wanda tun ina k'arami Na sanshi, amma daga baya ya 6ata 6at. Bayanan w

ad'annan bayin ALLAH da bincikena Na had'a suka tabbatar min da zargina akan wad'annan mutanen, nasan abune mai wahalar gaske samunsu cikin sauk'i da fahimtata da duniya zatayi akan zargin danake musu, shiyyasa naza6i yin Garkuwa da yaransu bisa tursasasu

tilas sufad'i abinda ke ransu da Wanda suka aikata. Dukkan Wanda ya shigo cikin labarin nan nawa akwaishi a wajennan, mijin yayatane kawai bayada rai sai mahaifan Badi, dakuma wasu daga cikinsu da sukabar duniya, Dan haka ina rok'on wannan kotu data nemo d

ukkan Wanda Na ambata domin jin ta bakinsa”.

Alk'ali ai yama kasa magana, sai kad'a kai kawai yake mamaki da al'ajabi Na cinsa, yayinda kotu tayi tsit kowa yana k'ullawa da kwancewa da tausayin Galadima, irinsu Alhaji Halluru kam ai cikine ya d'

uri ruwa, sunsan dai tasu tagama k'arewa kam, Dan yau ranar bankad'a Ce da walle-walle.

Alk'ali yad'anyi rubuce-rubucensa sannan ya buk'aci ganin Badi da Alhaji Rabilu, Galadima kuma yaje ya zauna.

Alhaji Rabilu da Badi sun bayyana a gaban k

otu, hakan ya kuma hargitsa hanjin cikin Waziri, yana mamakin dama Badi bai mutuba? Amma su hak'ilu sukazo sukace ya mutu a wancan lokacin, dan agabansu mai besfa ya kad'eshi, innalillahi ya shiga ambata a zuciyarsa, sai zufa ke jik'eshi, sauk'insa ma akwa

i malun-malun da rawani a jikinsa, Abba Hayatudden kallonsa kawai yake da tsantsar tsana da mamakinsa.

Duk yanda Badi da Alhaji Rabilu sukaima Galadima bayani haka suka maimaita a gaban kotu, wasu harda hawayen tausayinsu suke matsewa, Alk'ali yace, a

kawo Alhaji Auwal Fharuk Dan Badi yaga idan shine yabama camera.

An kawo Abba, Wanda Alhmdllh jikinsa yayi sauk'i sosai, saidai abinda ba'a rasaba Na k'arfi, kallo d'aya Badi yayma Abba ya ganeshi Dan bai canja masaba sai canjin girma irinnan sheka

ru, hakama Abba ya gane Badi sarai Dan shima d'in bai canja masanba, aiko suka rungume juna kowa yana hawaye, Abba yana fad'in “Bawan ALLAH Dama baka mutuba a waccan ranar?”.

Shima Badi cikin kuka yace, “ban mutuba, sai daga baya ne Na farfad'o a waj

en”.

Alk'ali ya ankarar dasu cewa a kotu suke, kotu kuma Na buk'ar jin bayani daga bakin Abba, ta Yaya Camera ta dawo hannunsa?.

Abba ya dai-daita tsayuwarsa sannan ya gabatar da kansa ga kotu, ya d'ora da fad'in “shekaru 22 kenan da suka s

hud'e wannan camera take a hannuna ranka ya dad'e, nakuma sametane ta hanyar kad'e wannan bawan ALLAH danayi da abin hawana a wancan lokacin, saboda ya shigo hanya yana matsanancin gudun dabansan mafariba sai yanzu danaji a ya fad'a a gaban kotu. bayan na

bigeshi numfashinsa Na Nuna alamar bankwana da gangar jikinsa ya d'auki wannan camera yabani acikin akwati da sunan amana, yakuma ambatamin sunan wad'anda zanba kamar yanda yafad'a, daganan numfashinsa ya tsaya cak da aiki, ina cikin k'ok'arin taimakonsa s

aiga wasu mutane da gudu da makamai sun dosoni, tsoro naji, Dan inada tabbacin shima sune suka biyoshi, saboda son isar da amanar daya bani inaji ina gani badan nasoba Na tsallakesa Na gudu, Dan nasandai zasu iya kwatar abinda yabani d'in. tunda camera d'i

n nan ta dawo hannuna ban sake barci mai dad'iba, kullum burina da tunanina tayaya zan Isar da amanarta Na huta, tsawon shekaru ban ta6a fuskantar wani k'alubale akanta ba, Dan ko iyalina babu Wanda yasan da zamanta a hannuna, matata tasha tambayata idan t

aganni cikin damuwa amma banta6a fad'a mataba, kwatsam cikin laluben Wanda zan bamawa sai Marigayi Alhaji Abdul-hakeem Uba tsohon Governor d'inmu ya fad'omin, Dan ganin yana auren d'iyar tsohon Sarki wadda tana d'aya daga cikin wad'anda akace nabamawa, to

lallai anan Alhaji shehu SD yasan Camera Na hannuna, Dan tabbas yaji zancen da mukayi da Alhaji Abdul-hakeem d'in ta hanyar la6ewa, aranar da mukayi zan bama Alhaji Abdul-hakeem camera ya damk'ata ga matarsa sai aka samu akasi wani aiki ya tasomin Na manta

ban fito da camera ba, amma mun had'u da shi marigayi Alhaji Abdul-hakeem Na bashi hak'uri da sanar masa uzirina, shikuma SD a tunaninsu nabama Alhaji Abdul-Hakeem wannan camera, shine suka hari rayuwarsa da nufin kar6a kafin ya kaima matarsa, inaga daga

baya da suka fahimci babu Camera d'in a hannunsa shine suka juyo kaina. Sunta matsama rayuwata da barazana iri-iri, kiran waya da sauransu, duk number da suka kirani da ita gobe bada ita zasu kirani ba, hakkane ya sakani ware sim card guda kawai dansu, bab

u Wanda ya sanni dashi, sai matata Dana saka number cikin wayarta batare da itama tasan hakanba, nayi hakanne saboda watarana koda ALLAH yabasu nasarar kasheni d'in. A lokacin da akaima yarana 6atanci da Galadima lallai hankalina ya tashi matuk'a, amma dag

a baya danayi nazari saina gano maybe su SD ne suka aikata hakan domin 6atamin suna, hukuncin ALLAH kuma saigashi mai martaba Sarki jalaludden da mai martaba Sarki Abdul-fatah sunzo nemawa d'ansu Galadima auren yarinyata da abin yafaru akanta, dukda a 6add

a kama sukazomin ni sarai Na ganesu, amma ko y'an uwana ban sanarmawaba, abinda yabani k'arfin gwiwar aurar musu da yarinyata shine Isar da amanar hannuna cikin sauk'i, saikuma aminin mahaifina Baba mai kanwa yace nabasu, Dan shine kawai yasan da zaman Cam

era a hannuna, shima bani Na sanar masaba, bankuma San a ina yajiba. A randa za'akai y'ata gidan mijinta a ranar Na saka wannan camera da takarda cikin wani kwali Na sakashi a kayanta batare da tasaniba, bansaniba kota gani? Dan cikin gifts d'inta data sam

u a hannun abokan mijinta ranar dinner d'in auranta Na sakashi, nabama d'an uwantane Abdul-Hameed babban d'ana yabata batare da shima ya san minene a ciki ba. Hikimata anan idan tagani tabama mijinta batare da kace Na ceba. SD bashikad'ai ke bibiyar rayuwa

ta ba, Dan akwai masu sakashi yazomin da farashin kud'i masu tsoka akan camera d'in amma nayi kunnen uwar shegu dasu, hakanne yasakasu k'ok'arin salwantar da rayuwata wai tunda Na hanasu camera, nasan sunajin tsorone saboda Na kusantu da Galadima a lokacin

, zan kuma iya bashi camera d'in, saidai abinda basu ma saniba tuni Camera d'in tabar hannuna. Alhaji Halluru abokinane Dan school mate d'inane, ada babu wata alak'a mai k'arfin tsakanina dashi, amma daga baya sai yayta Jana a jikinsa, ban fahimci manufars

aba dagashi har Alhaji Mamman, Dan da zuciya d'aya ni nake zaune dasu. Sai wannan karon da suka tabbatarmin da zulwa jahainin fuskarsu, sannan suka tursasa y'ay'ana biyu Dana d'auka nabama y'ay'ana Alhaji Halluru aure saboda yarda wai su d'akko musu camer

a a d'akina kosu kashesu dani dakuma iyayensu mata, sun razanasu da cewar sun dasa bomb a gidana, agabana duk suka sanar musu a waya. Abinda yasa ban damuba nasan k'arya suke, sannan Camera d'inma bata gidan, duk k'ok'arin lalatama Galadima sirrika da suka

yi agabana sukayishi, amma ALLAH baibasu nasaraba, jin asirinsu zai Toni ta hanyar Garkuwa da y'ay'ansu da Galadima yayi shine suka shak'amin abinda ban saniba, daganan ban kuma Sanin ina kaina yakeba sai a asibiti yamai shari'a”.

Wannan bayanima Na

Abba ya girgiza zukata sosai. Dan har alk'ali kasa motsawa yayi, saidai yaja kusan mintuna biyu sannan ya sauke ajiyar zuciya mai k'arfi. Ya buk'aci a kawo masa camera nanda awa 2 kacal. Anbar lokacin a matsayin hutun kotu.

Babu Wanda yaso matsawa

konan da can, kowa burinsa dai camera ta iso aga mita k'unsa.



Galadima ya kira Munaya,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login