Showing 345001 words to 348000 words out of 407268 words
Ya shafa kanta yana fad'in “Sannu, yanzu ina ke miki ciwo?”.
Fuska ta d'an yatsine, ta nuna masa hannunta da kanta.
Cikin tausayawa Yakuma mata sorry, sannan yace, “mizaki ci?”.
Kanta ta girgiza masa alamar babu komai.
Ya d'an
6ata fuska yana fad'in “Ban yarda ba, kinga kuwa yanda kika rame?”.
Murmusawa tayi, itama ta masa alamar wai ya rame shima.
Baki yad'an ta6e, amma baice komaiba ya d'auka wayarsa dake kusa da ita yay kiran Muftahu akan abinda za'a kawoma Munay
ar kozata d'anci.
Itadai kallonsa kawai takeyi. Ya yanke wayar yana kallonta shima da d'age mata gira d'aya alamar kallonfa?.
Dukda taji kunya saita yamutse fuska irin miye abin kallon anan.
Galadima yay wani miskilin murmushi ciki
n murya k'asa-k'asa yace, “Really?”.
Ta lumshe idonta alamun tabbabatarwa.
“zaki maimaitamin idan kin warke yarinya”. Yay maganar da wata siga harda cije lips.
Munaya ta kauda idonta tamkarma bata fahimci ina ya dosa ba.
A ra
nardai haka kowa ya yini cikin farincikin farfad'owar Munaya, gashi anbarsun sunshi sun gagganta, saidai anata musu gargad'in banda hayaniya, tausayin ta duk ya kamasu. Innaro harda hawayenta, aka saka bakin Zane ana sharewa da jemasu Alhaji balala ALLAH y
a isa, harda cewa sai an koma kotu an sake sabuwar shari'a an kar6oma jikarta hak'inta.
Shi Galadima ma abin dariya ya bashi matuk'a, yadai had'iye yana duk'ar da kai baiyiba, wannan tsohuwa akwai abin dariya wlhy.
Munubiya kam rungumeta ta
yi taita hawaye, itama Munayar nayin nata.
★★★★★★
***
★★★★★★
Bayan kwana hud'u da farfad'owar Munaya jikinta yayi k'yau Alhmdllh, Dan tana samun kulawa ta kowanne 6angare, ciwukan jikinta ne kawai basu gama warkewaba.
Aunty Mimi
da Laraba na a d'akin, Dan kowa ya tafi, suna zaune d'auke da su Abdurraheem da ake kawowa su yini yanzu, sai dare a koma dasu.
Munaya tana zaune ne a gadon datake jiyya an saka mata filo ta jingina, abincin da aka zuba mata taketa faman jujjuya
cokali a cikinsa, tasaba kullum Galadima ke bata abincin, gashi yau tun safe da'aka kirashi ya fita bai sake dawowa asibitinba har yanzu, dukta damu, da taji motsin tahowa za'a shigo d'akin saita zata shine, sai anshigo taga bashi bane sai haushi ya kamata
, Munubiya data fahimceta tsaf taita gumtse dariya har suka tafi, su Aunty Mimi hankalinsu gaba d'aya yanaga yaran, basusan mitakeyiba.
Turo k'ofar da akayi ya sakasu kallon k'ofar gaba d'aya, dan k'amshin turarensa yafara musu sallama kafin
shigowarsa, wayace manne a kunnensa yana magana a hankali, hannunsa d'aya cikin wandon aljihun Ash color d'in shaddarsa daketa maik'o, Munaya daketa sauke k'ananun ajiyar zuciya tunda taji k'amshinsa tad'an saci kallonsa, shima idonsa a kanta, gira ya d'ag
a mata, tai saurin janye idonta tana tura baki kad'an.
Murmushi yayi ya zauna a bakin gadon kusada k'afafunta yana cigaba da wayarsa, yayinda yakema Amaturrahman da aka kwantar kusada ita wasa, yaran sund'an fara wayo, Dan idanuwa k'yar suyita kalle-k
alle, kwanakinnan da suka dawo shan nono sunyi y'an k'u6ul-ku6ul dasu abin sha'awa.
Munaya dai tafara tura abincin da k'yar, sai wani faman had'e rai takeyi, shidai Galadima dariya na cinsa a rai amma baiyiba, saidai ya saci kallonta ya maida idon
sa ga Amaturrahman data rik'e d'an yatsansa gam daya saka a d'an hannunta, kaikace tasan minene.
Sudai Su aunty Mimi da laraba suna cigaba da hirarsu, Dan laraba na bata labarin halinda su Abdurrahman suka shiga a kwanakin da Munaya bata farfad'ob
a ne.
Galadima ya ajiye wayar yana d'aukar Amaturrahman da fad'in, “O my lil princess I miss you”. Ya k'are maganar da sumbatar kumatunta, sannan ya juyo suka gaisa dasu aunty Mimi dake kallonsa shida babyn tashi abin sha'awa.
Cikin tsokan
a aunty Mimi tace, “Ai dama shirin kiranka nake danna kula my k'anwa bazataci abincin nanba sai kana kusa”.
Galadima ya juya yana kallon Munaya data waro ido tanajan mayafi ta rude fuska Dan kunya, dama aunty Mimi suna kula da ita kenan, itakam taga
idi.
Galadima yace, “A lallai Aunty Mimi da gaskiyarki fa, kamarma kuka tayi?”.
“kad'an dai ya rage tayishi my k'ani, tun d'azun ina lura da ita, rabin hankalinta naga k'ofa”.
Laraba da Galadima sukayi dariya, ya kuma kallon Munaya
data kasa d'ago kai ta kallesu.
Galadima ya had'iye dariyar dake Neman kufce masa, ya ajiye Amaturrahman d'in yana matsowa kusa da ita, Murya k'asa-k'asa yanda su Aunty Mimi bazasujiba yace, “Any problems my Princess?”.
Munaya ta saci kallon
su Aunty mimi, ganin basa ganinta saita tura masa baki kad'an tana matso k'ananun hawaye.
“O my God”. ‘ya fad'a a hankali yana d'ora tattausan hannunsa saman nata, cikin wani salon daya saka tsigar jikinta tashi ya kar6ar spoon d'in. Babu shiri ta s
akar masa.
Yakuma k'asa da murya yana d'ebo abincin da fad'in, “nifa kibarmin shagwa6arnan kokuma humm”. ‘ya k'are maganar da ciza lips yana jifanta da wani kallon mai cike da sirrika’.
Waro idanu Munaya tayi tana kallonsa baki bud'e. Abincin
ya zuba mata yana kashe mata ido d'aya.
Kunya ta kamata, Dan wlhy Galadima bashida kunya ko kad'an, kad'an daga aikinsa ya aikata duk abinda yazo masa a rai d'in, danta San halin kayanta sarai.
bata k'ara yarda sun had'a idoba har yagama bata
abincin, ya d'akko d'an Basket d'in da drugs d'inta ke ciki yana dubawa.
Aunty Mimi data kasa hak'uri ta mik'e tana tawa, “Oh ni Haneefa, dama abinda ya hanaki cin abincin kenan da gaske dai tun d'azu kiketa cuna baki my k'anwa”.
Munaya t
ai saurin jan d'an gyalen dake yane bisa kanta ta rufe fuska saboda kunya dataji, Aunty Mimi ma akwai iya 6aro zance, kuma ta Fiske abinta.
Laraba tayi y'ar dariya itama tana bin bayan Aunty Mimi suka fice, itakam dai birgeta sukeyi sosai, komai nas
u a nutse.
Galadima dake binsu da murmushi ya juyo da kallonsa ga Munaya yana fad'in, “Saiki bud'e fuskar, dama haka kikeso su fita a barki daga ke sai mijinki ko?”.
Babu shiri Munaya ta janye mayafin tana d'an hararsa da kwa6e fuska tam
kar zati kuka.
Ya ta6e baki da d'aukar ruwa ya zuba a cup yana mik'a mata, kauda kanta tayi gefe kamar bata ganshiba.
Mik'ewa yay ya koma kusada ita sosai yana sakata jikinsa, “Haba dai yalla6iyan yalla6ai miye na fushin to?”.
Muna
ya ta ture fuskarsa tana fad'in “Ni babu ruwana dakai, ka koma inda ka fito”.
Yace, “Oh God Babie na sorry kinji, wani babban uzirine ya rik'eni, yanzu dai ga maganin kisha, sai amin hukuncin laifina”.
Munaya ta matso hawaye sannan ta bud'
e bakin ya zuba mata maganin ya bata ruwan tashanye, yakuma zuba wani, ahakadai tagama sha.
Dawowa yay tagabanta ya zauna yana murmushi, “Dad'ina dake shagwa6a, amin murmushin mana”.
Kauda kai Munaya tayi gefe murmushi na kufce mata.
Gal
adima ya dawo da fuskarta suna kallon juna, cikin k'ank'ance idanu yace, “ko kefa sweedy na, kindai hak'ura ko?”.
Kaita jinjina masa tana wani far da ido.
Hannunta mai lafiyar ya sumbata, yace, “Thanks My Queen, Saura wanka ko?”.
Mu
naya tai k'asa dakai saboda kunya, danta zata ya manta da maganar wankan da Doctor yace tafarayi yau indai zata iya. Murmushi Galadima yayi, dan kunyar tata na sakashi a shauk'i.
Kanta a duk'e tace, “Nidai kabarni zan iyayifa da kaina wlhy”.
Bai
ce uffanba ya mik'e zuwa k'ofar ya saka key, yazo yawuce cikin bayin dake a d'akin. A sace ta bishi da kallo harya shige, ta lumshe idonta wani farinciki nabin sassan jikinta.
tsaf bayin yake, dan kullum cikin gyaranshi ake, hakama kayan ammafani
irinsu boket, buta da sauransu komai need yake, ruwa ya saka danya d'anyi zafi dayake akwai wuta, ya fito yabarshi.
Har yanzu idon munaya a rufe suke.
Saukar Numfashin Galadima da k'amshin turarensa kawai taji a kan fuskarta, ta bud'e ido da sau
ri, Ashe yana gab da ita, motsawar datayi saiyazama kawai fuskarsu ta manne da juna, hakan yabashi damar aikata yanda yaso cikin sauk'i.
Batada za6in daya wuce mik'a masa ragama gaba d'aya, danya cancanci abindama yafi haka a gareta.
Tsawon min
tuna biyu ya d'ago suna kallon juna, kasa daurewa Munaya tayi ta rufe idonta, yay murmushi gefen baki yana hura mata iska a saman idon.
Dole na bud'e idona nakuma sakasu cikin nasa, a hankali ya furta “I love you so much my Munaah”.
Murmushi na
masa mai kashe ga66an jiki, na matsa kad'an ina bashi Sumba a kumatu, lumshe idonsa yayi yana sauke wani nannauyan numfashi, ya d'ora kaina a k'irjinsa, daddad'an k'amshin turarensa ya shige hancina, nima na lumshe idanu ina shak'a da godema ALLAH. muduka
nutsuwa ta musamman ta sauka a zuciyoyinmu. Wayata datai ring ce ya sani d'agowa daga jikinsa na zauna sosai ina kauda fuska saboda kunyarsa.
Ganin Samha Ce na d'aga wayar cikeda farin ciki.
Galadima mik'ewa yay shima ya lek'a ruwan daya sak
a, ganin yayi zafi saiya kashe ya juye, surkawa yay, saida yaji yayi dai-dai sannan ya fito yana cire bottoms d'in rigar shaddarsa, hankalin Munaya baya garesa, shiyyasa batasan miyakeyiba, sai ji kawai tayi an amshe wayar tareda yin sama da ita. Da farko
ma tsorata tayi, zata saka masa ihu yay saurin cemata “Shiiiii!!”.
Ajiyar zuciya na sauke na kallesa, ya kashemin ido d'aya. Murmusawa nayi ina janye idona daga kallonsa, dan naga lamarin nasa na Neman fin k'arfina, koya manta a ina muke oho? ha
rda su cire rigafa.
Nidai wannan wanka anyisane kawai dan banida yanda zanyi, dan dana nema yin gardama saiya had'e fuska yana hararata, dole nabarsa yayi yanda yakeso, ya d'auramin towel ya kamo hannuna muka fito, Muduka Kallon Amaturra
hman mukai daketa wutsil-wutsil da k'afafu.
Na zauna a bakin gadon shikuma ya jawo kujera ya zauna yana rik'o hannuna mai ciwo, fara'ar dake a fuskarsa dukta d'auke, alamar ransa yana 6aci inhar ya tuna tushen ciwon.
Cikin son kauda mas
a damuwarsa nayi murmushi ina d'ora hannuna mai lafiya saman nashi dake rik'e da mai ciwon, d'ago ido yay muka kalli juna, nad'an juya idanuna ina fad'in “yafi k'yau a haka ko?”.
Hararata yayi kawai baice komaiba.
Nayi k'aramar dariya.
Yi
yay tamkar zai matsa hannun nai azamar janyewa ina d'ane gadon gaba d'aya dayin y'ar k'arar tsorata, kad'an yarage na haye Amaturrahman.
Murmushi yayi har hak'oransa na bayyana. yace, “ga tsoro ga tsiwa”.
Nace, “naji dai ba komai”.
Bai
kuma cewa komaiba, sai murmusawa da yay, da kansa ya shafamin mai ya canjamin riga, dukda kakkauda fuskan kunya danaitayi, shikam ko a jikinsa, kai tsaye yake lamarinsa kuma hankali kwance.
A gurguje please
😏😜
.
*******************
**
Satina Uku a Asibitin aka sallameni, jikina kam sai godiyar ALLAH, dan na warke sarai, saidai y'ar ramar danayi, dakuma ciwon kai dake yawan addabata inhar waje yacika hayaniya.
Tunda na dawo sai kuma kewar Galadima ta tasoni gaba, su Fa
uziyya nata shirin komawa gidajensu, sainaji inama harda mu
🤭
.
Tunda na fito asibiti Aunty Salamah takuma k'aumi wajen bamu kulawa, musamman ma ni, dan ita Munubiya ina asibiti akaita mata nata.
Tunda aka sallami Munaya daga asibiti
ta koma gida sai yaji zaman k'asarma dukya gunduresa, ganin zai saka kansa a damuwa saiya had'a inasa-inasa yabar k'asar, itama Munaya rana tsaka yazo mata da zancen komawar.
Addu'ar fatan alkairi kawai tamasa, da kuma sak'on magungunan Abie, a rana
r yaso shiga su gaisa da baba mai kanwa, amma sai akaje wai bayanan, d'ansa yaje kaisa wani k'auye nan kusa gaisuwar Mutuwa da akayi.
............................
★
Su momma sunyi farin cikin dawowarsa garesu cikin k'oshin lafiya, sai dai y'
ar ramar da yayi.
Shima wani matsanancin farin cikine ya kamashi ganin jikin Abie ya k'ara k'yau, yanzu har mitsa hanunsa yakeyi sosai, ga doguwar hira da akanyi dashi batareda ya k'osa ba, ranar sunsha hira sosai, har saida doctor d'in Abie yace s
ubarshi ya huta sannan Galadima ya tafi gida shi da Momma, ranar Aunty Mimi aka bari wajen Abie tunda ita tasan komai.
Sabuwar hira Momma da Galadima suka kuma dasawa a gida, dukkan abinda yafaru yabata labari dallah-dallah, dukda Aunty Mimi tabata d
ama, Momma harda hawayen jin dad'i, ta rungume Galadima tana saka masa albarka shida matarsa da yaransu.
Babu kunya ya ringa amsawa cikin tsantsar farin ciki.
Yanzu kam koba komai hankalinsa ya kwanta, ya maida hankalinsa ga dukkan aikinsa
da sana'oinsa da suke samun kud'in shiga akan jiyyar mahaifinsa.
Shiri yake a gaggauce saboda kiran da Doctor d'in Abie yamasa tun a daren jiya akan yanason ganinsa yau da sassafe.
Yayi k'yau cikin Orange d'in Suit, sai k'amshinsa
yake mai dad'i, cikeda salon birgewa yake sakkowa daga steps d'in benen yana waya, bayin daketa aikace-aikacen k'imtsa falon duk suka zube suna gaisheshi.
Hannu kawai ya d'aga musu ya nufi hanyar fita a hanzarce yana cigaba da wayarsa, ya d'ora brief
case d'insa saman motar yasa key ya bud'e, bag d'in yafara ajiyewa gefen mai zaman banza sannan ya dawo ya bud'e ya shiga mazaunin driver ya tada motar ya fice.
“Muftahu kabari zamuyi magana daga baya dai kawai”.
Daga can Muftahu ya amsa da to
babu damuwa.
Ajiye wayar Galadima yay ya maida hankalinsa ga tuk'insa, yayinda sashen zuciyarsa ke tunano masa hirarsa da Munaya ta daren jiya, kwana biyunnan idan yamata maganar dawowarta saitai ta masa yawo da hankali, yarasa dad'inmi zaman can d
'in yake mata? Ai wankan jegon ya isa haka, shima yana buk'atar zama da iyalansa koya samu nutsuwa tamkar kowanne magidanci, k'aramar tsaki yaja yana furzo isaka daga bakinsa, mata kenan, wataran su baka zuma, wataran su caja maka kai.
Da wannan tuna
nin ya k'arasa asibitin, wayarsa kawai ya d'auka ya fita a motar, kai tsaye Office d'in Doctor Ajay ya nufa, yay Knocking aka bashi izinin shiga, (Abu Na CCTV suna kallon shige da ficin kowa) Doctor Ajay ya fad'ad'a murmushi sa yana mik'ewa, hannu suka bam
a juna cikin Musabaha suna gaisawa, Doctor ya nunama Galadima wajen zama.
Bayan sun zauna Doctor daketa faman murmushi yace, “Sameer wani abun farin ciki ne nasamo a daren jiya, shiyyasa nakasa sukune saida Na kiraka a daren domin buk'atar ganinka”.
Galadima dai kallonsa yake baice komaiba.
Dr Ajay yaci gaba da fad'in, “Wato wani Doctor ne mai suna Dr Erfan Fahad Sajaad, d'an k'abilar Kashmir ne, Likita ne babban masani ta fannin irin matsalolin su Abie, yanzu haka yana k'asar England akan