Showing 300001 words to 303000 words out of 407268 words
wayar”.
“Okay” munaya tafad'a tana yanke wayar.
Shima wata Number yashiga nema yana fad'in “Lall
ai akwai matsala, tunda kukaji Harun da Alhaji Shehu sun fad'a to sunsan misuka shiryama Abba, gashi nabaza su Ameer sumin wani aikin...” ya k'are maganar da saka wayar a kunne saboda daddy ya kira.
Bayan sun gaisa ya tambayesa ko sunyi waya da
Abba a yau?.
Daddy yace, “eh da asuba yakirashi akan zai dawo yau”.
Galadima yace, “Alhmdllh Dady wace number ce?”.
Dady yace bara Na turo maka.
Koda Galadima ya yanke wayar saiya kira baba k'arami shima, shima ya tabbatar masa
sunyi waya da Abba bayan fitowa salla, Dan wannan al'adarsu Ce ko a ina wani cikinsu yake saisunyi gaisuwar safe da bankwanan kwanciya barci, sannan idan wani cikinsu yayi tafiya zai kira y'an uwansa yayin dazai kamo hanya.
Hankalin su Nuren ma
duk a tashe yake, balle uban gayya Galadima.............
✍
🏻
🙆🏽
Turk'ashi, ana wata ga wata kuma
🤦🏻
♀
.
Lallai yaukam tura na shirin kaiwa bango
🤦🏻
♀
.
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu
😭👏🏻
_*
*_Typing
📲
_*
*_
💡
HASKE WRITE
RS ASSO...._*
*_
♦
RAINA KAMA...!!
♦
_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
__________________________
*_Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya Ubangijin Al'arshi kama mahaifin takwara (Bily s Fari) rahama,
ka yalwata kabarinsa da Ni'ima, ALLAH ka yafe masa, harda iyayenmu
😭👏🏻
_*.
_Takwara ALLAH ya k'ara mana hak'urin rashinsu, muma ALLAH yasa randa zaka d'auki ranmu muna cikin masu imani da tsoronka, da soyayyay Manzonmu ANNABI MUHAMMADU S.A.W._
😭
😭
👏🏻
____________________________
*_BOOK 3_*
👉🏻
1
⃣
5
⃣
.................Duk da Munaya a rikice take haka tayi jarumtar danne zuciyarta, cikin hikima ta dinga bin jama'ar gidan d'ai-d'ai tana tambayar wad'anda tasan Abba zai iya kira kai tsaye, a
mma kowa yakance tun daren jiya basuyi wayaba, hankalinta a tashe ta sulale gidan innaro ba'a saniba, itama dai tace tun bayan sallar asuba bai sake kiranta ba. Munaya tafito jikinta sai rawa yake, kiran Galadima tayi, lokacin yana waya, tamkar zata fasa k
uka ta cire wayar daga kunnen ta, tana niyyar sake kiranshi saigashi ya kirata.
Da sauri ta d'aga.
Yace, “yauwa Yayi waya da wani?”.
Muryarta na zuga alamar tahowar kuka tace, “A'a, innaro kawai ya kira bayan sallar asubahi, amma yau k
oda su innarmu baiyi wayaba”. ta k'are maganar hawaye na gangarowa a kumatunta.
Galadima ya furzar da huci daga can, a hankali yace, “Munaya”.
Muryarta na zuga ta amsa tana share hawayen da bakin hijjab.
Had'iye abinda ya tsaya masa a
mak'oshi yayi da k'yar, muryarsa takuma komawa can k'asan mak'oshi, cikin sigar lallashin da Munaya bata ta6a sanin galadima ya iyaba yace, “insha ALLAH babu abinda zai faru da Abba, kiyi mana addu'a, sanan karki sanarma kowa wani Abu har inna, wayarki ta
zama kusa dake, Dan zan dunga kiranki idan buk'atar hakan ta taso”.
Munaya takuma goge hawayen dasuka gaza tsayawa, cikin had'iye kukan tace, “ALLAH yabaku nasara, ya tsareku da tsarewarsa”.
“Amin ngd”. Galadima ya fad'a yana yanke wayar.
A bakin fanfo Munaya ta tsaya ta wanke fuskarta, akuma lokacinne Zarah da Siyama suka shigo kusan lokaci d'aya.
d'agowa nayi Na kallesu ina k'ak'aro murmushin da musu sannu da zuwa. Saidai ayanda suka amsamin cikin sanyin jiki saina tsora
ta, nabaro bakin fanfon da hanzari zuwa garesu ina fad'in “Kai lafiyarku kuwa?”.
Duk d'insu murmushi suka k'ak'alo, Siyama tace, “babu komai fa sis...”.
Dukda ban yardaba haka nayi murmushi, sannan Na kar6i yaransu duk biyu Na rik'e ina yaba
Girman da sukayi, saikace tagwaye.
Daga Siyama har Zarah basuce dani Uffanba duk suka shige, kowa tanufi d'akin Uwarta. Duk binsu nayi da kallo, saida suka shige Na sauke ajiyar ziciya nima Na nufi sashenmu Ina tunanin mike faruwa? Dan alamu sun nun
a akwai dai wani Abu a k'asa.
Saidai bankai ga Shiga d'akinmu ba mamansu Yaa hameed ta tareni ta kar6i yarinyar Zarah. Ban musaba Na bata tundai ALLAH yasa Nima Na Haifa balle ace, na shige falonmu da d'an Siyama nima.
Bayan Galadima sun gama
waya da Munaya, number da daddy ya turo masa ya duba, ganin wadda yake da itace saiya gwada kira, switch up, ya ciza lips yana kallonsu Nuren da suma duk suka zuba masa idanu.
Muftahu yace, “Ranka ya dad'e mu sanarda y'an sanda mana?”.
Murmuahi t
akaici Galadima tayi, ya girgiza kansa yana fad'in “Hakan zai 6ata aikinmu, duk indama yake a safiyar yaune suka sameshi, akwai zoben dake hannunsa zamu iya bibiyarsa tanan, saidai matsalar d'aya dole sai wayarsa Na aiki, gashi number sa kuma switch up”.
Nuren yace, “to mizai hana mu bincika kozamu samu daga inda Number tabar aiki”.
Da sauri Galadima yace, “yes, yes Nuren, shawara mai k'yau.....”
Shiru yay yakasa k'arasawa, saboda tuno da matsalar da Computers nasu suke ciki kuma, ya dafe
kansa.
Daga Muftahu har Nuren duksun fahimceshi, zuwacan kuma miya tuna saiya mik'e da hanzari zuwa cikin d'akin, babu dad'ewa yafito dawani k'aramin abu a hannunsa, lap-top yajawo ya manna a jiki, ya had'a da waya ya Shiga sarrafata cike da kwarewa.
Zuwa can yad'ago yana kallon su Muftahu da tura musu lap-top d'in gabansu, yana sanar dasu titin da wayarsa ta daina aiki.
Cikin takaici yace, “Sunriga da sun tsara komai, mubarma tunanin plan A, muje zuwa plan B kawai”.
Cikin mamaki duk
suka kallesa alamar miye plan B d'i?.
Lips d'insa yad'an ciza yana d'age gira d'aya da buga yatsan saman bakinsa, Yace “maida hankalinmu a nemansa shine target d'insu Na farko wajen janye ra'ayinmu, plan d'inmu mukuma anan shine bazasu ta6a kashes
hi ba inhar bai basu Camera d'inba, a yanda Na lura kuma yanada taurin kai shima, bazai ta6a basuba ko fad'a musu inda take. Sunada damar yin amfani da surukan senator halluru wajen turasu gida su nema musu camera d'in, kodai ta hanyar musu barazana da mut
uwa, kokuma akan aurensu, ko kashe mahaifinsu, kodai wani Abu daban, shiyyasa dolene mumaida matsalarsa cikin plan B d'in”.
Duksun gamsu, dukda sufa har yanzu yak'i sanar musu miyake shiryawa a plan B d'in.
Cikin damuwa Nuren yace, “Amma nasan
zasu wahalar dashi”.
Galadima baice komaiba dan shikad'ai yasan azabar da zuciyarsa kemasa, bayason ya nuna karayarsane saboda karsuma su Muftahu su karaya, sannan koda sanyin jiki yanemi tasiri gareshi sai kalaman Munaya su masa allura, inhar yarin
ya k'arama kamarta zata iya tasirantuwa da abinda ta fad'a, mizai hana shima ya samu jarumta cikin tagomashin fik'irarta.
Mik'ewa yay tsaye yana tattara kayansa da fad'in “Bara Na wuce, sai kunji yadda zata kaya kawai”.
Basu barshi yatafi shi
kad'aiba, saida sukai masa rakkiya har masarauta, koda ya shige sashensa saiya kulle kansa, domin yin shiri.
Hummm,
🤸🏻
♀
shirya da k'yau Galadiman mu.
★★★★★★★★★★★
Abinda ya faru da Abba shine, bayan yagama kammala shirinsa domin b
aro inda sukaje shida S... halluru daya jashi domin masa rakkiyar tafiyar kwanaki biyu kacal.
Lafiya lau suka shiga mota zasu taho, amma sai shi S... Halluru ya dakata da cewar Abba yayo gaba, shi anmasa kiran gaggawa, bai kuma kamata ace ya tsaidashi
ba shi, tunda ya sanarma iyalansa yau zai dawo.
Da farko Abba kamar zaice suzauna kawai harya gama, saikuma tunanin yariga da ya sanarma su innaro zai dawo ya fad'o masa, shiyyasa kawai yataho, basuyi wani nisa da tafiya ba driver ya tsaya wai motar N
a d'aukar zafi, ALLAH Sarki Abba, sai shima ya fita domin taimaka masa, suna tsaka da duba motarne garadan samari hud'u suka fito daga ma6oyarsu sukai ma Abba d'aukar amarya. Duk yanda yaso kare kansa ya gaza.
Driver da dama duk cikin shiri yayi haka
saiya hau tsallen k'arya cikin pretending yana ihun azo a taimakesu, (
🤦🏻
♀
bayan yasan baza'a samu kowaba a wajen tunda jejine
☹
).
Abba mutumne mai dagiya akan ra'ayinsa, hakan yasa duk yanda sukaso yabasu had'inkai akan zancen Camera yak'i, ya
ma dage shi baisan Cameran da ake magana a kaiba, kuma dayaso basun tun lokacin da ake bibiyarsa da dukiya mai tsoka daya bada, amma basuda kud'in dayakai darajar camera d'in, sannan inda zai bada kodan barazana da rayuwarsa da sukasa aikaitayi tunba yanzu
ba daya bada, amma yasan ruhinsa Na hannun Wanda ya halicceshi, shine kuma mai kar6a aduk lokacin da yaso, inma sun kasheshi dama kwanansa ya k'arene, Dan haka subar wahalar da Kansu kawaima.
Wannan maganar Ce ta fusatasu, wani ya daki Abba a baki ha
rya fashe, dukda yaji zafi saiyayi murmuahi kawai yana kauda kai gefe.
Wanda sukasa yamusu aikin lalata documents d'in Galadima Na cikin Computers ne ya ankarar dasu zoben hannun Abba akwai wata kimiya a cikinsa, wannan ne ya sakasu cire zoben daga
yatsansa, shi Abba saima yanzune yasan manufar zoben, yay murmushi, Dan hakan ya tabbatar masa cewar Galadima yasan wani Abu game dashi.
Duk yanda suka ringa k'ok'arin yima Galadima mugunta a sirrinsa Na Computer Abba Na kallonsu, hankalinsa kuma a
tashe yake, amma jarumin namijineshi mai iya sarrafa kai aduk yanayin daya kasance, ko'a fuska bai nuna musu yana tare da damuwar abinda sukeyinba, saida Galadima ya kashe komai nasune Abba ya sauke 6oyayyar ajiyar zuciya, dukda yasan hakan ba shine nasara
ba.
Wanda suka saka aiki mai suna William yashiga rud'anin abinda Galadima yayi, Dan da farko yanata cika baki babu wani d'an African daya isa ja dashi a fannin ilimin Computer, bak'ak'en fatar ai a wajen su suke koyan komai, ta Yaya kuma zasu fisu
Sani?.
wad'annan kalamai nasa sun Sosa zuciyar Abba da sakashi cikin takaici, shiyyasa yayta jerama Galadima addu'ar samun nasara a zuciya.
Yayinda sukuma wad'anda akema aiki suke kuma hurama William kai da kwanzartashi (ko kishin Kansu basayi
😏
, a zageku da kuma k'ask'antar daku kuna yabon mai ganinku marasa daraja
🤦🏻
♀
, wata dai bahaguwar rayuwa sai bak'in fata
😏🙄
.
Dak'ilesu da Galadima yayi ta hanyar kashe komai ya fusatasu suda William d'in, suna kuma kunna Computers d'in komai
naciki ya goge, wannan Abu ya rikita William matuk'a, gashidai yagama proud d'in shi kwarone kuma bak'in fata d'an Africa ya masa kwaf d'aya, dukkan fushinsu saiya dawo kan Abba.
Ana cikin haka saiga Alhaji halluru da sauran tawagar y'an group d
'in, wad'anda sai yanzune suka samu k'arasowa, da farko Abba ya zata Alhaji Halluru taimakonsa yazoyi, saida yaji suna masa izgilanci sannan ya fahimci komai, cikin tsantsar mamaki yace, “Alhaji Halliru da kanka?”.
Ta6e baki Alhaji Halluru yayi, y
ace, “zaka bani takarar Governor ne?”.
Abba yay murmushin takaici yana fad'in “Tir da kai Halluru, wannan ai jahilcine, ALLAH shikad'aine ke bada mulki ga Wanda yaso, akuma lokacin dayaso,, yanzu kana nufin duk shekarun daka d'auka a jikina kai da
ma da manufa kake tare dani?”.
Alhaji Halluru ya kuma ta6e baki yana murmushin mugunta, yace, “Alhaji Auwal kenan, ai bama zaka tabbatar da hakanba sai y'ay'anka da kansu sun d'akko min camera sun kawo, sannan mukuma kasheka a gabansu babu yanda z
asuyi, yanzu haka suna gida, zuwa anjima kad'an kuma camera zatazo garemu”.
Zufa ta fara karyoma Abba a dukkan sassan jikinsa, danjin za'ayi amfani da gudan jininsa wajen tarwatsa abinda yad'au shekaru yana rik'ewa amana, k'ala baice da Alhaji Hal
luru ba, su kuma sai kiraye-kirayen waya suke Na had'ama Galadima tarko.
🤦🏻
♀
Abba ba tausayin kansa yakejiba, tausayin Galadima yakeji matuk'ar tik'ewa, Dan ganin rai kusan 15 kowa k'iyayyarsa akansa take da muguntarsa...
★★★★★★★★★★
Tunda Galadima ya shigo bai zaunaba, saida yagama had'a komai dazai buk'ata, yabama sarkin mota yakai cikin motar dazaiyi amfani da ita, alwala yay yafita salla massalacin masarautar, bai yarda sun had'u da Sarki ba, yay fitowarsa, koda ya dawo sai
yasha magani ya kwanta, kaikace bashida wata matsalane, babu dad'ewa kuwa barci yay gaba dashi.
Bai tashiba saida aka kira sallar la'asar, nanma massalacin yaje, bayan ya dawo yay kiran Momma ta video call, duk suna asibitin hardasu Samha, d'aya b
ayan d'aya ya gaisa da kowa, Samha harda kukanta tanason zuwa Nigeria, ita missing nasu takeyi sosai. Galadima yace a'a ba yanzu ba, tashi tai tabar gaban lap-top d'in tana kuka, Galadima ya girgiza kai kawai.
Yasha hirarsa da Abie sosai, saboda Alham
dullah jikinsa saidai godiyar ALLAH, dama ciwo keshiga farat d'aya, sauk'i kam sai a hankaki. Addu'a kuma takobin muminice ako yaushe.
Bayan ya gama waya dasu Momma Sir Isa ya kirashi, ya tabbatar masa da komaifa is done, Dan ansami kowanne acikinsu,
yanzu haka wasu sunma iso.
Galadima yay murmushi yana shafa fuskarsa. Yace, “Nama canja shawara, zamu canja gidan da zamu ajiyesu da, yanzu akwai wani gida annan kusada plaza d'ina, nagama magana da Saleem komai yayi ready, Ameer duk yakaisu can, ins
ha ALLAH ana idar da sallar Isha'i zan fito”.
Sir Isa yace, hakan yayi, dan acikin yaran nasuma za'a iya samun munafukai, tunda duk sunsan gidan daza'a ajiyesun, yanzu kuwa shi Ameer kad'ai zaisan da wannan.
Galadima ya kira Munaya, d
ama tun d'azun kiran nashi take jira, ta d'aga tana shigewa cikin bayin d'akinsu Dan kar wani yaji.
Galadima yace, “haryanzu kukan?”.
“a'a” ta fad'a cikin share hawaye.
Yad'an murmusa kawai yana fad'in, “Akwai bak'in da sukazo gidanku?”
.
“A'a babu Wanda yazo, sai Siyama da Zarah”.
Galadima yay murmushin gefen baki yana cigaba da danna lap-top, hasashensa yazama gaskiya kenan, gyaran murya yad'anyi kad'an yana fad'in, “kina jina?”.
Munaya tace, “eh”.
“Ki saka ido
akan d'akin Abba, motsin kowa yazama akan idonki koda cikin matansane, ko yayyenki maza, Dan za'a iya yin amfani da kowa, inda da dama ma key d'in d'akin yazama a hannunki”.
Munaya tayi d'an jimm alamar tunani, zuwa can tace, “babu damuwa, zan gwada
hakan insha ALLAH, amma kunji labarin Abban?”.
“Karki damu, insha ALLAH Abba zai dawo gida, addu'a muke buk'ata”.
Munaya ta jinjina masa kai tamkar tana ganinsa, ta share hawayenta dake zubowa.
Yana yanke wayar nafito, cikin dabara n
ashiga d'akin innarmu, key d'in d'akin Abba Na d'akko, dukda nasan kowama yana dashi cikin matansa, fitowa nayi naje cikin dabara da sauri-sauri Na saka key d'in cikin k'ofa d'in, cikin addu'ar Neman nasarar kozai karye a ciki, amma ko gezo baiyiba, hannun
a sai azabar zogi yake, danma nayi amfani da wani abin sarrafa k'arfene, cirewa nayi nakoma ciki kozan samo wani k'aramin k'arfe dazai iya Shiga, saida nasha wahala nanma sosai kafin Na samo, gashi duk a tsorace nake kar wani ya fahimci abinda nakeyi, ciki
n kafar makullin Na turashi, Alhmdllh nasamu ya shige, nagwada saka key amma yak'i Shiga, nasan babu yanda za'ayi wani key ya sake shiga wajen harsai mai gyara yazo, tunda kuma Abba bayanan ai babu buk'atar hakan, Dan duk wanda zai buk'aci shiga yanzu lall
ai akwai manufa. Dukda haka saida nasamo kwad'o nakuma sakawa sannan hankalina yad'an kwanta.
**************************
*_9:00pm_*
Fitowarsa kenan daga wanka baiko tsaya shafa mai ba ya hau shiri cikin wandon da