Showing 12001 words to 15000 words out of 407268 words

Chapter 5 - Raina Kama COMPLETE

inamaijin haushin wannan mutumin, to wayema shine? dayakema mutane wannan jinkan., motsooww aikin banza kawai.

Tabbas yaji tsakin da akayi, hakanne yasakashi d'ago k'yawawan idanunsa yakai duba

saitin Inda yajiyo tsakin, akan *munaya* dake zaune bisa kujerun dake Jere awajen ya sauke su, sai dai baya ganin fuskanta sosai, saboda ta duk'ar da kai tana danna waya, kuma gyalen jallabiyarta yarufe mata Rabin fuska, ita kad'aice zatayi wani motsi aw

ajen suji, dan tafi kusanci da Inda suke tsaye.

Janye idanunsa yayi kawai daga gareta, yay saurin d'agama bayin dake k'ok'arin tafowa gareni hannu. Cikin Wata tattausar murya mai aji dake cike da k'asaitar masu isa najiyo yana fad'in “Bayta kawai”.

Cikeda girmamawa bawan yace, “ya shugaba tsaki tayi fa”.

Shiru yay kamar bazai tankaba, saikuma najiyo yace, “kasan dawa take?”.

Bawan girgiza kai yayi alamar a'a.

Bai sake cewa komaiba yay gaba suka bishi a baya.

'Dago ido n

ai nabi bayansu da kallo, sainaga sun nufi 6angaren mata masu haihuwa.

janye idona nayi ina fad'in “kadaiji dashi Malam, kana fama da Girman kai kamar wani Sarki? Abinma dariya ko (R) bai iyaba, wai bayta”.

Dai dai nan su Ayusher suka iso ciked

a farinci, hannunsu d'auke da ledar jinin

Cikeda jin haushi nace, “wai uwarmi kuka tsaya yi acikin lab d'inne?”.

“Uwarmu ta gode”. ‘ cewar Ayusher’.

Munubiya kuma tace, “zaman namu aiko yayi amfani, tunda gashi mun samo sauran jinin ko”.

Na kallesu da mamaki, “ina kuka samo jinin kuma to?”.

“Galadima ya bayar”.

Cikin ta6e baki nace, “miye kuma Galadima? A inama kukaga wani Galadima kome ma kukace?”.

“wanda yashigo muna cikifa, ai Galadima ne (Yareema Sameer d'an

sarki)”.

Ido na waro waje, “wai kuna nufin wannan mai shegen girman kai d'in dama shine Galadiman? kenan munu.... shine yawucemu d'azu munfito makaranta?”.

“kwarai kuwa sweetheart shine, kuma wlhy bashida Girman kai kamar yanda kike zato ko Si

s.. Ayusher? ”.

“Wlhy kuwa hakane Munu..., ashe duk k'arshen ko wane wata saiyazo asibitinan yabada jininsa gamasu buk'ata, gashi jinin nasa mai irin wahalar samu d'inanne irinna feena, kai mutuminnan yayi wlhy, Sarauta ba karya baceba, danyau naga

tsantsar sarauta da mulki da k'asaita ajikin Galadima, yanzu haka zai zagayane yaduba marasa lafiya”.

Harara na ballama Ayusher daketa zabga surutu uwa aku, na warce jinin daga hannun munubiya ina fad'in “idan kun gama shirmen kwa taho”.

Kal

lo suka bini dashi, Ayusher tace, “Anya yarinyarnan batada aljanu?, ke kowama bai mikiba?, yanzu nan duk had'uwar Galadima Munaya tana nufin bai burgeta ba kenan?”.

Dariya Munubiya tayi, sis... Ayusher har yanzu baki gama fahimtar Munaya ba na lura,

kyagama abinda yafi haka indai daga wajentane. Yanzu hakama tunda kikaji tace haka ko sau d'aya bata kalleshiba wlhy bare tasanma kalarsa. kinga muje kinji.

“humm aiko wlhy inabata kalleshiba anyi babu ita kuwa, ruwa ta shata kuma, yo kobabu komai

aina bada koda labarine nace nata6a ganinsa ido da ido ko”. ‘cewar Ayusher’.

Dariya kawai Munubiya tayi, taja hannunta suka tafi.



Sanda suka iso harma an fara k'ok'arin sakama feena jinin, dama wancan yak'are.

Duk muna zaune a k'o

far d'akin bisa kujerun wajen, Aryaan da Aiyaan duk suna jikin mama Rabi'a barci ya d'aukesu, fadeel na kusada innarmu yanacin abincin dasu Munubiya suka kawo, zama nayi kusada fadeel d'in na saka hannu nad'au cokalin dayake cin abincin ina fad'in bro... n

imafa yunwarnan nakeji, rabona da abinci tun kusan 1 danaci a kafteriya na makaranta”.

Kallona yayi yana cewa “sannu da k'ok'ari sis...., shiyyasa gakinan tsula guda bak'ya gaba bakya baya keda munu....”.

Cokalin nakai zan kwala masa a ka

i ya kauce yana dariya, nima dariyar nayi na d'auki kular abincin na k'ara mana.

Muna cikin ci Ayusher ma tamatso tace zataci, munci mun k'oshi sannan muka gyara wajen, mama da innarmu ma sukaci, dan zuwa yanzu duk mun sami 'Yar nutsuwa.



Kusan 10pm saiga Abbanmu shida baba k'arami, duk muka gaidasu suka tambayi mai jiki, innarmu da mama Rabi'a suka amasa musu da sauk'i.

Har d'akin suka shiga, suka duba feena daketa barcinta, sannan sukace muzo mu tafi gida, za'a bar innarmu da mama Ra

bi'a su kwana.

Saida safe mukai musu muka fito, Fadeel ya d'akko Aryaan, baba k'arami ya d'akko Aiyaan.

Saida muka fara sauke Ayusher da Fadeel gida sannan mukuma muka wuce.

Mun tarar gidan tsitt alamun duk anyi barci, saidai masu wayar

dare da samari irinsu aunty Ramla, saikuma masu charts.

Abbanmu da baba k'arami suka d'auki su Aiyaan, har d'akinsu suka kaisu sannan suka fita.

Muma shirin barci mukayi muka kwanta cikeda kewar Innarmu, muna kwanciya muka kirasu da k'arajin mai j

ikin sannan muka tafi duniyar barci muma, dagani har Munubiya babu mai wani saurayin da zamu 6ata lokaci wajen yin hirar dare...............



🏼

Kumuje zuwa my guys

🤩👎🏻

Gobe idan ALLAH ya kaimu baza kujiniba, inada wani d'an uziri, sai Mon

day idan ALLAH ya kaimu kuma.

https://chat.whatsapp.com/K1qwmMusX7ILDLATGSvfHJ

*_RAINA KAMA........ FANS CLUB_*

_Duk Wanda yasan yana karanta wannan buk d'in ya garzaya yanemi link Na RAINA KAMA FANS CLUB, a wannan gidan kawai zan dinga post

ing a halin yanzun, awannan karon bazan turama kowa buk ta PC ba, narigada nayi rantsuwa. Amma annan zaka iya samu da faro, sannan inhar ba'a tattaunawa akan novel d'in zanyi waje da mutum babu ruwana, kuma kar a turomin kowanne novels acikinsa Dan ALLAH,

inba hakaba zan fidda mutum ko Yaya nake dashi

🙅🏻

, nabud'e gidanne saboda anan kawai zan dinga posting yanzu, sai wasu groups dabasu wuce 3 ba._

Ina fata zaku bani had'in kai please, inba hakaba ALLAH zai koma Na kud'ine saboda tsaro ba tsoroba

😎🤣

One luv

🥰🥰

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu

👏🏻😭

_*

[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing

📲

_*

*_HASKE WRITERS ASSO...

💡

_*

_(Home of expert and perfect writer's)_

*_



RAINA KAMA......!!



_*



_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

_____________

*_ASSALAMU ALAIKUM_*

_Jiya da daddare akaita kirana mutane Na tanbayata Yaya jiki, tun ban fahimci maganarba hardai nafara tsarguwa nayi tambaya. Dan sai kira kan kira

ake jeramin, wata take sanar dani taga wani posting ne yana yawo wai za'amin CS. babu shiri nabud'e data naga mike faruwa, group d'in farko dana bud'e sainaci karo da wannan posting d'in mutane nata comments, nabud'e nabiyu ma hakan dai._

*_Assalamua

laikum Alaikum,Dan Allah kuyiwa billyn Abdul(ma rubuciyan RAINA KAMA. Adua'baby ya mutu a cikin ta zaa cire Mata Shi yanzu_*

_sai daga baya nakejin Bily galadanci ce batada lfyar, amma wata ta maida zancen haka saboda sunan namu yazo d'aya, to ALLAH yab

ata lfy itama._

_sannan ina shawartar jama'a Dan ALLAH kuringa nutsuwa wajen tantance Abu kafin Ku yad'ashi, domin wadda tayi wancan write up d'in ta zaunane ta tsara nata son zuciyar, wadda tayi posting d'in farko akan ciwon Bily galadanci sunan Bily

tasaka ba nawaba, itakuma ta canja nata tsarin tashiga ya d'awa, ALLAH ya shiryar damu, yakuma bama marasa lfyarmu lafiya._

*banyi niyar posting ba yau, amma ganin wancan write up d'in yana cigaba da yad'uwa yasani dole yi Dan na warware muku zance

n.*

______________________________

👉🏻

6



.......Bamusan abinda yafaruba, mukaji 'yan gidanmu suna k'ananun magana da safe, wai girkin jiya na dare da mamansu yaa hameed tayi sai asararsa akayi, girkin yay d'anye yak'i dahuwa, kuma a

gas tayi girkin bare ace iccen yabata matsala, gashi kuma normal gas d'in yake aiki.

Muna cikin yima su Aiyaan shirin school muka fara jiyo hayaniya, sai da muka gama musu shirin sannan muka fito, cirko-cirko muka iske 'yan gidanmu, yayinda mamansu y

aa hameed keta zabga masifa. tana fad'ama abbanmu wai mune muka mata kwari shiyyasa jiya abinci yay mata d'anye danta hanamu abinci, kuma gashi yanzuma tasaka doya amai tak'i soyuwa.

Ni dariyama taso bani wlhy, wai mune muka mata kwari, to miye kwa

rinne ma datake magana a kai? danni bamma sanshiba.....

Maganar Abbanmu ta katsemin tunanina.

“ 'Yan biyuna kuzo nan naji kunji”.

K'arasowa mukayi kusada abbanmu harsu Aiyaan, ya kallemu cikeda kulawa, “haba 'yan albarka mike faruwa haka?”

.

Cikeda rashin fahimta nace, “Abba a ina?”.

“haba twins d'in Abba, bakuji mi mamanku take fad'aba? abinci yamata d'anye jiya da yau”.

“amma Abba Dan abinci yayi d'anye kuma sai ace mune? Kagafa jiya munama asibiti bamuci abincin dareb

a agida, darana ma mama hanamu tayi tace innarmu tatafi da kasonmu asibiti, haka muka dawo muka iske su Aryaan sunajin yunwa, sai Munubiya Ce tamana girki, kuma tayi takai mana wani asibitin, ni wlhy Abba bammasan wani kwari dasuke maganaba akai, wannan ai

canfine, tunkuma zamanin da aka barsa”.

“canfin uwarki, kujimin munafukar yarinya, inbakune kukayi muguntarba uwarwaye yayi, to wlhy ahir d'inku, ba 'yan biyu ba ko 'yan gomane ni ubanku zanci a gidannan.......”

Afusace Abba yace, “to ai g

ani, saikizo kici ko, ai gaskiyama yarinyarnan tafad'a, wannan canfine kawai, dan abinci yayi d'anye saikuma a fassarashi dawani Abu daban, haba Dan ALLAH, saikace wata mara ilimin addini? Karna sake jin wannan maganar, inba hakaba rankowa zai 6acine a gid

annan”.

Yana gama fad'a yabar wajen. muma ganin haka muka tasa su Aiyaan gaba muka koma 6angarenmu. duk da nakasa fassara mi mama ke fad'i hakan yamun dad'i, koba komai dai ai ALLAH yamana sakayya da hanamu abinci datayi muda wad'anan k'ananun yaran

da basu da alhakin kowa.

Yanzuma munubiya Ce ta dafo mana indomi mukaci, sanan ta zubama su Aiyaan a kulolinsu Na makaranta, suna tafiya muma mukayi shirin tafiya School.

Bamu tsaya jiran sauranba mukayi gaba saboda zamu biya ta asibiti, ku

ma munsan acikinsu babu mai binmu, harmun fita saiga Fauziyya tabiyomu, itama zataje taduba feena d'in.

Alhmdllh munma tarar an sallamesu sunata shirin tafiya gida, mukaima feena sannu, ta amsa tana fara'a da tambayarmu ya makaranta?. mukace gatanan

zamu tafi.

Bamufi mintuna 30 ba muka fito, Fadeel ya d'aukesu, mukuma muka wuce school.

A mota Munubiya take bama Fauziyya labarin ganin Galadima damukayi jiya a asibiti, ko sau d'aya ban saka musu bakiba har muka sauka.

★★★★★

A

wannan karon har mamansu yaa hameed tagama girkinta Na kwana biyu asarar abinci akaitayi, Dan kullum d'anye yake mata. hakan yasa taita sakin habaici agidan itada muk'arrabanta irinsu momy hadiza,.

Maman Fauziyya ta sanar ma innarmu komai tun rand

a taje duba feena agidan mama Rabi'a, Dan haka Innarmu tayi kunnen uwar shegu dasu, tamkarma batasan da ita sukeba balle ta nuna tama fahimci zancen nasu.

Innaro ma tazo tayi tata tsiyar San rai, tabi duk ta zagemu dacin mutuncin innarmu, koma fitowa

innarmu hanamu yi tayi, har Innaro tagama tafice. Matan gida najin dad'i.





★★★★★★

Haka rayuwar tacigaba da tafiya, yau da gobe kayan ALLAH har gashi azumi ya rage saura kwanaki uku kacal a fara, Dan haka musulmai NATA shirin tarba

r wannan wata mai tarin albarka da falala.

Kasuwanni sun cushe saboda yawan hada-hada, duk da 'yan kasuwa sunyi taiyar tasu ta k'arama abinci kud'i, maimakon su sassauto bayin ALLAH su sami sauk'i (ALLAH ka shirya 'yan kasuwarmu subar wannan hali dai)

.

A 6angaren gidanmu ma iyayenmu maza duk sunyi shirin, Dan dukkan wani abun buk'ata an tanadeshi, sai abinda ba'a rasaba dazai iya lalacewa idan an ajiye, wannan anbarsa yayunmu maza su ringayo cefanensa kullum kamar yanda aka saba.

Itama Inn

aro an ajiye mata dukkan abinda zata buk'ata, dukda kullum daga gidanmu ake kaimata abinci, safe yamma da dare, kuma dolene kowane 6angare sai sunkai nasu.

Muma a 6angarnmu munyi dukkan namu shirin, dukda abin zai had'e mana da zuwa makaranta, hak

an yasa nake tausaya mana, gashi ana tsula rana mai zafi kuma.

Alhmdllh yau ta kasance Alhamis, kuma yaune ake saka ran ganin wata atashi da azumi washe garin juma'a.

Har zuwa 9pm kunnen kowa naga redio da talabijin, jira kawai Muke muji san

arwa daga sarkin musulmai. sai wajen 9:30pm sanan aka Sanar da ganin wata, duk wani Muslim yana cikeda d'okin fara azumin watan Ramadan da zamu Shiga goma ta marmari (inji hausawa

😂

).

Tun alokacin duk muka d'auki niyya, kasancewar girkin innarmu ne t

ayi shirin tafiya d'akin Abbanmu, muma tace mu kashe TV muje mu kwanta kar atadamu da asuba kuma muzo muna k'unk'uni.

Badan mun soba muka kashe mukaje mukai shirin barci muka kwanta da addu'ar abakunanmu.

Aiko da asuba dak'yar innarmu ta iya t

ashinmu mukai sahur, tea kawai muka shama, dama mu bama sahur da abinci nida munubiya, garama ita wani lokacin takan had'a da kunu ko fura.

Bamu kwantaba saida akayi sallar asubahi, still kwanciya muka kumayi, sai 8 innarmu ta tadamu, kasancewar yau

saima 10 mukeda lecture, kuma zamu fito 12 ne.

Tunkan aje da nisa azumin yafara garani, dak'yar Na daure aka kammala lecture muka fito, amma badan Na fahimci komaiba nidai yau.

Su Munubiya sai dariya suke mini wai Raguwa, nidai ban kulasuba,

Burina kawai naga mun Isa gida Na kwanta.

Tunda muka dawo school nazube a falo k'asan carpet, ban sake Sanin duniyar danake cikiba saida munubiya ta tadani nayi salla, Ashe harsu Aryaan sun sako masallacima inata barci, sallarma dak'yar nayita atsay

e, INA kammalawa nakuma kwanciya.

“oh ni Aisha, wai Munaya mikikeson maida kankine? yanzu azumin kikema langa6e haka? saikace yau kika fara azumi a rayuwarki?”.

“ALLAH innarmu bazaki ganeba, nidai ALLAH yasa akira salla da wuri”.

Mun

ubiya dasu Aiyaan suka sakamin dariya. “Aunty yanzufa k'arfe 2 ma, sauran kusan awa 5 dawani Abu asha ruwa”. ‘Aryaan yafad'a yana dariya’.

Harara Na Dalla masa INA fad'in “ALLAH inbaka rife wannan bakin naka mai gajerarrun hak'oraba zaka dakune, Da

n k'aniyarka kaiba yanzu kagama lodama cikinka abinciba?”.

Aunty nimafa Dan innarmu bata tadamu baneba kawai, amma insha ALLAHU gobe zamuyi ko Aiyaan?”.

cikin zumud'i Aiyaan yace, “eh mana, muma zamuyi bro”.

“kuma wlhy yaro bai I

sa karyashiba, garama karku d'auka”.

Munubiya tamik'e tana dariya, “imm innarmu bara kiga naje nafara rage aikin, miza'ayi?”.

“ki fere doya kafin Na fito, Munaya tashi maza kuje, kekuma ki gyara kayan miya”.

“wayyo innarmu ki tausaya

min mana”.

“mukuma mu kashe kanmu tunda bama azumin ko?”. ‘cikeda gatse tayi maganar’.

“a'a innarmu, bara naje kodaga zaune sainayi”.

“kimayi daga kwance, raguwar banza kawai, ai mijinki yashiga uku, wataran sai yadawo aiki baki

gama abinciba”.

Baki Na tura gaba sannan nafita.

Mun rage aiki sosai kafin la'asar, sai bayan sallar la'asar d'in 'yan Matan gidanmu suka shishshigo kitchen d'in kamar yanda aka saba, dama duk shekara gaba d'aya muke had'uwa a kitchen d'in

6angarenmu ayi abincin bud'a Baki, saidai saboda munada yawa akanyi time table saboda a rarrabu kowa da ranar da Zai taya mai aikin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login