Showing 162001 words to 165000 words out of 407268 words
innaro an fito ana warware gya
le za'a yafa, “yauwa jafaru muje Na shirya”.
Habiba dake kitchen tana girki duk diramar da ake tana saurare ta tuntsure da dariya, lallai tsohuwarnan akwai daru, mama Na hanya ai, itace maganinki (gwaggo Safiyya mamarsu).
Kallonta Dady yay yana
murmushi, yace “to inna mu jira jafar d'in yaje shiryawa”.
“ato shikenan bara kafin ya dawo nad'anci abinci, k! Habiba zubomin idan abincin nan ya tsotse, gara Na fita cikina da d'an nauyi”.
Habiba ta had'iye dariyarta sannan tace “innaro bai
tsotseba, amma nanda kamar dai minti 5”.
“babu damuwa ai, nasan jafaru ma bai dawoba harnaci, kinsan shi da dak'undar shiri, ya tsufa amma kullum kallon kansa yake sa'ar Abdul-hameedu”.
Dariya Dady ya had'iye da k'yar, yasa handkerchief yana
toshe baki dan karta fito.
★★★★★★★★
Tsaf na kammala shiryawa sannan Na kimtsa d'akin, ni dukfa a nufina nayi shirin asibitine.
Fitowa nayi dan naga ko yana falone, wayam babu kowa, sai sallama da nakeji a bakin k'ofar, amasawa nayi na
bada izinin shigowa saboda naji muryar matane.
Su 10 ciff suka shigo, k'asa suka zube suna gaisheni, Na amsa musu da 'yar sakewa, “lafiya dai?”.
“lafiya lau ranki ya dad'e, mune zamu kasance hadimanki, masu miki dukkan hidima.
Nifa wlhy b
anason wasu bayi, amma dolene Na barsu tunda wad'ancanma Galadima ne yace su tafi, yanzu kuma baya wajen, ni kuma banida ikon korarsu tinda bansan kan abinba.
Amsa musu nayi da “to” sannan nawuce Na zauna a kujera.
Tasowa sukai suka biyoni, a
tsanake suka dinga fad'amin sunansu da aiyukan da zasuyi.
Wad'anda naga bazan iya yarda suyiba Na canja musu aiki. Sallamarsu nayi, Ina k'ok'arin tashi Na shige ciki saiga Sauban ya shigo, duk zubewa sukayi suna kwasar gaisuwa a gareshi, ya amsa mus
u yana wani yatsine face, sai kuma ya basu izinin tafiya, fita sukayi harabar sashenmu.
Na kalleshi ina murmushi, “ashe kaima dai sarautar Na jininka yaa Sauban? Wanda bai saniba saiya d'auka duk bazaka iya wani Abu daya shafi sarautaba”.
Dari
ya yayi yana zama, “aunty gimbiyar mu kenan, wannan ai sai mijinki”.
Nima murmushi nayi kawai.
Ya mik'omin kayan hannunsa yana fad'in “ga break fast d'inki”..
“wayyo yaa Sauban, nikam dai nagaji da ciye-ciyennan ma, zuwa zanyi Na far
a abinci da kaina”.
“wlhy dakin taimakemu Aunty gimbiya, mijinki shiya saba da cin abincin waje shiyyasa bai damu ba, ya kamata kafin Na wuce gobe naci girkinki”.
“kamarya gobe? Kana nufin zaka koma kenan?”.
“tab da gudu kuwa, aini ba
zan iya zaman k'asarnanba Na tsawon lokaci, tarema zamu wuce da Abba ai, harma da innarmu, yaa Sam bai sanar dakeba kenan?”.
Baki bud'e Na girgiza masa kai alamar a'a.
Sauban yay murmushi, “kinsan halin Galadiman namu ai, soyake yamiki surprise
maybe, yanzu hakane yaje cuku-cukun visa d'insu ne. waito miyasa bazamu koma tare da kubane?”.
Murmushin yak'e nayi, nace, “maybe akwai ayyukan dabai gamaba shiyyasa”.
“inaga hakanne kam, ni bara naje, yace Na iskeshi birnin gayu, ga mahfuz c
an Na jirana”.
“ok sai kun dawo” Na iya cewa, danni daga 'yan matan masarautar har samari ba kowa Na saniba, tunda time d'in daya kamata nad'an San mutane sai muka tafi India. ni bama nason Na saba da kowa, ni da ba zama ya kawoni ba.
Maganar
fita da Abba da Galadima yakeyi sai yayta cin zuciyata, kimar Galadima da darajarsa saita cika zuciyata, inason mahaifana, kuma dukkan Wanda zai nuna musu kulawa bazan manta da shiba, harda 'Yar kwallata Na share, Na tashi Na koma bedroom ba tare da nayi
break fast d'inba ma.
*****************************
Innaro dai tun ana jiran dawowar baba k'arami harta fara gyangyad'i, habiba data kammala abincin ta d'ebo ta kawo mata, nuni Dady yay mata akan ta koma.
Habiba ta koma da baya ba tare da
ta k'araso falonba.
Tun tana gyangyad'i harta 6ingire a kujerar barci mai nauyi ya d'auketa (ho innaronmu ta mutunci
🤸🏻
♀
😜
).
Baba k'arami da innarsu munaya kam tuni sunyi ficewarsu, dayake Abu Na kud'i dandanan aka gama cuku-cukun komai, Nu
ren ne tsaye, saida komai ya daidaita suka samu visa d'insu a hannu sannan suka fito.
Har gida ya maidosu ya koma suna jera masa godiya da addu'a shi da Galadima.
Innaro daga gyangyad'in jiran abinci ya tsotse aka zarce da barci mai nauyi, sh
ima Dady lalla6awa yay ya fito dan asibiti zaije.
Tafiyarsa babu dad'ewa saiga gwaggo Safiyya ta iso da yaranta biyu.
Hayaniyar su Dahiru ita ta tada innaro, ta mik'e zumbur tana fad'in “yauwa Jafaru kadawo mu tafi ko? Habiba bar abincin kawai
idan muka dawo naci.
Mi Dahiru da Naja'atu zasu ba dariya ba, suka shiga shek'ama innaro dariyar shak'iyanci. Wai kota kwanta da yunwa ne.
Zaginsu ta hau yi ta d'auki filon kujera tana dukansu.
Sai da gwaggo Safiyya ta musu magana sannan
suka nutsu, “inna ina zakuje da Jafaru ne?”.
Gyara zama innaro tayi tashiga bama gwaggo Safiyya labari.
Murmushi kawai gwaggo Safiyya tayi, danta gane wayo suka mata suka gudu kawai, itama sai tace “to inna ki cigaba da jiransu, k'ila dan sun
ga kina barcine suka jira ki tashi sannan Ku tafi.
Da wannan gwaggo Safiyya ta rufe bakin innaro ta zauna jiran su dady.
Aiki
🤣🤣😝
.
**********
Galadima daya fita kai tsaye asibiti ya nufa, su yaa hameed kawai ya iske can
, dan dady ya hana matan gidan zuwa sai anjima, doctors Na complain akan suna cika wajen da yawa.
Cikin mutunta juna Galadima ya gaisa dasu yaa sabi'u sannan yashiga yaga daddy.
Yau kam Alhmdllh dan ba barci yakeba, kumbirin fuskarsa kuma yad'an
sa6e kad'an, saidai baya iya magana sai dai yayta bin mutane da idanu.
Dukda bazai iya amsawa ba haka Galadima ya risinna ya gaidashi, tare da masa fatan samun lafiya sannan ya fita office d'in doctor.
Bayan sun gaisa doctor ya bama Galadima fil
e d'in bayanan Abba dasuka tattara.
Kar6a Galadima yayi ya duba, dukda bawai ya fahimci bayanan bane, ( kusan dai rubutun doctors sai su). Suka d'an tattauna akan cigaban da aka samu sannan Galadima ya fito.
Ya iske daddy ya iso, suka gaisa sann
an yamasa dukkan bayanan da doctor yamasa shima. Dady ma yaji dad'in cigaban da aka samu.
Galadima yay musu sallama ya fito.
Guntun tsaki yaja saboda yanda jama'a suka wani zuba masa idanu tamkar sunga magiji, da sauri wani dogari ya bud'e masa
motar ya shiga, sannan suma suka shiga.
Daga asibiti Galadima yace su wuce birnin gayu plaza.
Cike da girmamawa sarkin mita ya amsa da to.
Maida kansa yayi jikin seat ya kwanta tareda lumshe idanu ya fad'a duniyar tunani................
✍
🏼
Barkanku da juma'a
💋💋💋🤝🏻
.
Musha weekend lafiya sisters
⛹
🏻
♀⛹
🏻
♀⛹
🏻
♀⛹
🏻
♀
😄
.
*_ALLAH ka gafartama iyayen mu_*
🙏🏻😭
*_Typing
📲
_*
*_Haske writer's asso...._*
💡
*_
♦
RAINA KAMA......
♦
_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull Ce_*
🤙🏻
_________________________
_Duk marubucin daya kafa alk'alaminsa bisa takarda tabbas yagama tanadar yanda labarinsa zai kasance ne, amma sai wasu wabubuwan mamaki kaga sun ga
za k'arewa a social Media, ban saniba ko samunmu available ne yakesa a kullum kuke mana kallon marasa aikinyi?, ni dai nasan time d'in dana shirya labarin RAINA KAMA ban zauna tebirin shawara da kowaba a online, inkuwa hakane tayaya wasu har suke tunanin n
afara sauka akan layin labarin?, to magana d'aya zanyi a wannan ga6ar, ban gina labarin Raina kama akan kwanciyar aure bane, dan haka masu maganar munaya bata da aiki saima Galadima rashin kunya saisu jira saina kai k'arshen labarin kafin su k'alubalancen
i, abin dariya, (wai aikina kenan daga nasa munaya ta murgud'a baki sai ta harari Galadima da mas
a k'unk'uni) tunda aikina kenan babu lallai wajen 6ata lokaci karantawa, haka Na tsara labarina tun farko kuma haka zanyi, duk wanda yaga bai masaba zai fara i
ya rubuta nashi shima kawai. wannan abun da kukema writer's yana 6ata mana rai, bai kamata ku dinga k'alubalantar writer's ba, bayan su suke da masaniyar yanda suka shirya labaransu, idanma zakuyi saiku ringa tanadar lokaci har zuwa bayan mun kammala, haka
n zaifi tasiri fiyeda katsalandan a tsakkiyar labaran mu, akoda yaushe kuzama masu kula kafin Ku k'alubalanci mutum
🤷🏻
♀
._
*Ba akan kaina kawai nayi wannan bayaninba, harda sauran writers da yawa da akema makamancin hakan koma fiye da nawa.
🙅🏻
*
_____________________________
~Book 2~
👉🏻
1
⃣
0
⃣
➖
1
⃣
1
⃣
...................Koda motocin suka tsaya sarkin mota ya bud'e masa k'ofa yakai tsawon lokaci baiko motsaba, saboda tsantsar tunani da zuciyarsa ta lula, aduk sanda zuciya take
cikin matsanancin matsi gangar jiki ma gazawar karfin ikon jini dana 6argo sukan mata k'aranci, shi kansa yasan yanada buk'atar mataimaki a kan wannan lamarin, amma k'arancin rik'on amana Na d'an Adam ne yake yawan gargad'arsa da taka masa birki, ba kowan
e zai fahimci ma'anar nok'ewar tasaba, sai mutum daya tsinci kansa a makamancin halin da yake ciki.........
“Ranka ya dad'e mun iso”. Sarkin mota yasake fad'a cikin taraddadi da taka tsantsan.
A hankali Galadima ya bud'e idanunsa da suka ko
ma launin jaa saboda damuwa a kan sarkin mota, batareda yace uffanba ya ziro k'afarsa k'asa yana cije lips da had'iye wani kududun damuwa a mak'oshi.
Tunda ya fito ma'aikatan wajen suketa masa sannu da zuwa, dan tunda ya shigo k'asar sai yanzu ne za
i shiga cikin plaza d'in.
Hannu kawai yake iya d'aga musu, amma bakinsa yay masa nauyi, kallo d'aya kuma zaka masa ka nazarci damuwa da buk'atar hutun dake tartare da kuzarinsa.
A cikin plaza d'in ma bata sauyaba, d'aga hannu agaresu shine yaza
ma linzamin amsa gaisuwar dasuke masa.
Da hannu yayma d'aya daga dogaransa nuni da amso masa key.
Da sauri dogarin ya amsa yana mai nufar sashen da zai kaishi office d'in Saleem mai kula da CCTV camera's.
Sai dai kafinma yakai ga k'arasawar
suka had'u da saleem, Wanda tun shigowar motocin Galadima ya gansa.
Keys d'in ya damk'ama dogarin, sannan ya k'araso domin mik'a gaisuwa ga ogansa na wajen aiki kuma magajin garinsa.
Shima d'in dai hannu Galadima ya d'aga masa, hakan kuma ya sa
ka Saleem fahimtar akwai damuwa kenan.
Koda aka bud'e ya shiga saiyayma dogaransa nuni da suje kawai, sannan ya maida idanunsa ya lumshe tareda kwanciya jikin kujerar yana lilawa a hankali.
Shi kansa baisan tsawon lokacin daya d'auka a h
akanba, amma tabbas yasan yashiga kudin nazari mai zurfin gaske. Knocking d'in k'ofar da akayi yasakashi bud'ar baki da k'yar ya bada izin a shigo.
Nuren daya shigo ya maida k'ofar ya kulle, kafin ya ida takowa cikin office d'in, idonsa nakan d'an uwa
nnasa.
Zama yay a d'aya daga kujerun dake fuskantar Galadima, “brother what happen?”.
“Northing”. Galadima ya fad'a batare da ya bud'e idonsa ba.
Shiru kawai Nuren yayi shima, ya d'akko laptop a briefcase d'in daya shigo da ita, kunnawa y
ay, kusan mintuna biyu ya d'ago ya kalli Galadima, sai kuma ya maida kansa ga laptop d'in. “Sameer nasan kaga cigiyar da akeyi takowacce kafar yad'a labarai ta k'asarnan akan d'iyar minister, sannan jami'an tsaro tsaye suke akan binciken inda take. yakamat
a musan abinyi kafin lokaci ya k'ure mana”.
Guntun murmushi Galadima yayi, batareda ya bud'e idanunsa ba yace “Nuren indai har babu wata waya datake aiki inda kakai yarinyarnan, kuma ka cire sim card d'in phone nata a lokacin daka d'auketa, to babu w
ata hanya dawani jami'in tsaro zai ganota, dama hanya d'ayace da kuskure zai basu damar bibiyarta, na d'aya lokacin daka d'auketa yazam wayarta na aiki, tabbas zasubi ta wannan hanyar su gano har iya inda ka kashe wayar, hanya ta biyu itace ka kashe wayart
a baka cire sim card d'in ta ba daga phone nata, koda wayar a kashe take zasu bibiyeta ta hanyar
📡
su ganota” ya tashi zaune sosai yana bud'e idanunsa akan Nuren, “wannan hanyoyin biyu kawai ke garesu saikuma idan da camera tare da ita, idan duk babu wann
an basuda wata hanya, ka kwantar da hankalinka my brother, komaina da tsarinsa right?”.
Murmushi Nuren yayi, kafin ya salute d'in Galadima yana fad'in “I thrust to you my dear broth”.
Shima galadima salute d'in Nuren d'in yayi yana murmushi
.
Komawa yay ya sake kwanciya jikin kujerar, “yanzu inaga time d'in turama minister Massage yayi?”.
Cikin zaro idanu Nuren yace “baka kallon hakan a matsayin ganganci kuwa?”.
Baki Galadima yad'an ta6e yana crossing k'afarsa, cikeda izzarsa
yace “sai idan nabama wani damar hakan ai”.
Nuren baice komaiba, dan yagama sanin hatsabibancin Galadima wajen iya sarrafa Computer, dan haka ya bar wannan zancen ya d'akko wani. “yauwa to maganar Malam Saminu fa? Kasan yana hannunmu fa har yanzu?”
.
“wannan barsa saiya kuma magantuwa, dan da alama yasan wani Abu, saidai akwai abinda ya sakashi za6ar 6oyewa. ni yanzu damuwar 6atan Muftahu yafi damuna, nasaka camera's jikin mutane 10 danake iya zargi a masarauta amma banga alamun da hannun koda
mutum d'aya ba, hakan ya tabbatar min da gaske
Muftahu na bibiyar lamarina, sai dai bansan dalilinsa ba, ko kuma waye sakashi?”.
Nuren ya jinjina kansa, “brother aini da Harun dama mun dad'e da zargin Muftahu, Kaine kawai kake masa kallon mutumi
n kirki daman”.
Lips kawai Galadima ya cije, amma baice uffanba, Nuren yaci gaba da 'yan danne dannensa a laptop d'in, zuwa wasu mintuna batareda ya d'agoba yace, “maganar Sirikinka fa?”.
Shiru Galadima ya masa, saida ya mula dan kansa sannan y
a murmusa tareda maida idonsa ya lumshe, “a daren jiya nagama da wannan matsalar, sim card d'insa 3, akwai Contact 300 da 38, mtn yanada mutum 172, ya fara saka credit a layin shekaru 15 kenan, ranar 3/6/2005, glo 107, ya fara amfani dashi shekaru 8 kenan,
wad'annan sune Sim card d'insa da yake mu'amulla da kowa a ciki, kuma anfi saninsa da su, akwai 6oyayyen layinsa Na mtn shima, yafara aiki dashi shekaru 13 kenan, kuma mutane 59 ne kawai acikinsa, sannan ba kowane yasan layinba, dan dukkan family nashi ba
su San da zamansa ba, ita kanta mahaifiyar su Munaya batasan anyi saving number a phone nata ba, suma da suka kirata basusan da number a wayarta ba, dan baita6a kiranta da shiba, akwai matakan tsaro dake tattare da Layin, hakanne ya tabbatar min da akwai
abinda yake 6oyewa a Sim card d'in, dan sai time to time yake amfani da shi, kiran matarsa da sukayi da layin wannan shine kuskuren farko da suka tafka da Sameer ya samu hanyar musu takun sauro. zan fara aiki akan layin na shigesu ta hanyar da basu zataba”
.
Jinjina kai kawai Nuren yakeyi dan mamaki, Galadima da banne, kamar yanda basirarsa take daban, ya sauke ajiyar zuciya yana kama hannun Galadima da idonsa ke a lumshe har yanzun, cikin karsashi yace “lallai kai RAINA KAMA ne