Showing 81001 words to 84000 words out of 407268 words
hararata, cikeda k'asaitarsa yace “cup d'in kawai nake buk'atar gani, kina 6atamin lokaci zanje na kwantane”.
Tamkar na makeshi haka naji, na harareshi nima a k'asan ido, muryata na rawa nace “wlhy na k'oshi, zanyi amaine”.
Bai tanka minba kuma bai k'ar6i mug d'inba, hakan ya nunamin dole dai saina shaye kenan, haka na rumtse idanu na shanye na mik'a masa mug d'in.
Kar6a yayi ya ajiye saman table glass d'in dake gabansa, sannan yad'auki magungunan ya 6alla min, bana t
soron Magani sai allura, dan haka babu musu na kar6a nasha tareda ruwan daya bani a cup.
Ina gamawa na zame na kwanta, mik'ewa yayi yaja bargon ya lullu6a min sannan ya fice batareda ya tanka minba.
Babu dad'ewa barci ya kwasheni, bamma San s
u Ayusher sun shigo sun kwantaba suma. da yake gadon babbane duk sai ya d'aukemu.
Washe gari natashi dad'an sauk'i, sai dai kewar munubiya data innarmu, harma data gayyar tsiyar 'yan gidanmu, sauk'i nama d'aya ina ganin su Feena.
Break fa
st mai rai da lafiya aka kawo mana, su Ameera sai zuba santi sukeyi, nidai uffan bance da suba, nad'an tsakura kad'an na turo, maganin jiya na d'auka nasha na safe, dan har lokacin kaina na ciwo kad'an-kad'an, babu dad'ewa barci yay awon gaba dani.
Ban farkaba sai 12, shima tadani akayi, wai za'ayi ko hawan mi, nidai wannan bidi'a ta isheni hakanan wlhy.
Shiri akamin yanzuma cikin farin less, sanan aka samin alk'yabba, yanzun ma fuskar tawa a rufe take.
Gaskiya gidan sarauta akwai girm
a, dan shimafa dole akirasa da suna wani gari guda kam.
A mota aka sakamu zuwa inda za'a gudanar da hawan, dukda kuwa acikin gidanne fa, nida Samha ne kawai a mortar, tana ta zubamin surutu har muka isa.
Wata daban santa bace ta fitar dani d
aga motar, tana rik'e da hannuna har gurin da aka tanada domin zamana, yanzun fuskata a bud'e take, ba'a sakamin hular alk'yabba d'inba, dan muna zama awajen matar data fidoni ta ciremin, sai dai kunya tasani kasa kallon kowa, duk tsiwata inada tsananin ku
nya da rashin son zama wajen da mutane suka cika yawa.
Aunty Mimi ce a gefena na haggu.
Ban iya kallonba saida ta min magana tana kamo hannuna, dole babu yanda na iya na kallesu, su Galadima ne a saman dokuna shida samari kusan biyar duk da i
rin shigarsa ta sarauta, dokunan suna a tsaitsaye, da alama umarni suke jiran abasu, dan kamar gasace zasuyi.
Caraf muka had'a ido dashi, murmushin gefen baki ya sakarmin, cikeda mamaki na janye idona daga kallonsa.
Ana busa wani k'aho kowa
yabama dokinsa k'aimi suka rera da gudu, nanfa hankalin kowa yakoma kansu ana zufa tafi, babu wata hayaniya dan bawani yawane damuba, kusan ma wajen duk 'yan matane sai abokan Galadima dasuke son ganin al'adar dabasu saniba. Saikuma yayunsa mata irinsu aun
ty Mimi, amma babu manya kamar su mom awajen.
Ni ban saniba Ashe wannan tafiya saisun zagaye masarautar su dawo, Wanda yafara zuwa shine na d'aya.
Muna nan kusan mintuna 30 saigasu aguje suna tada k'ura, ko ganin fuskarsu ma ba'ayi sosai bare k
agane wanene a gaba.
Jinai kawai ansaki tafi kowa na ambatar Galadima! Galadima!!, wai Ashe shine yafara isowa. ya diro akan dokin yana murmushi da goge hannunasa da handkerchief d'insa daya zaro aljihu, sannan yagoge fuskarsa.
Ruwa wani do
gari ya mik'a masa, ya d'auka daga saman tired'in da aka d'oro yabud'e Goran, batareda ya saka kofiba ya hau shan kayansa, tas ya shanye ya jefar da robar, suma sauran duk ruwan suke sha.
Daga nan hotuna akayi, sannan yazo har inda muke ya kama hann
una, wai Ashe nima yanzu dole saina hau dokin, ahakane zamuje sashe-sashe, dan kowa yanacan yafito waje yana jiran zuwanmu.
Banta6a hawa dokiba sai yau, dan haka jikina yakama rawa. Muryarsa can k'asan mak'oshi yace “k bak'auya ki nutsu”.
Mag
anarsa saida tabani haushi amma ya zanyi, da taimakonsa na hau dokin bayan dogarai sun baza rigunansu yanda baza'a ga hawa naba.
Saida na hau da k'yau sannan shima yaje ya hau nasa, kuyangine a gabanmu suna zuba flowers, a bayanmu kuma dogarai, gefe
da gefenmu ma dogaraine, wasu suna busa algaita wasu suna kid'an taushi, sai gayyar abokansa biye damu abaya dasu Ayusher da 'yammatan masarautar.
Ahaka muka dinga zuwa sashe -sashe inda duk sun firfito, duk muna akan dokin bamu saukaba, sai dai muka
n risina alamar gaisuwa. fuskata kuma tana abud'e yanzun kowa Na ganina, saida muka zagaye ko ina a masarautar sannan aka maidani wajensu mom. Lokacin la'asar tayi.
Dukna damu saboda kiran munubiya danaketa yi wayar akashe, tsakin danakeyine ya
saka Ayusher tambayata, na fad'a mata.
Dariya tayi, “yo banda abunki ina zakiji munubiya kuwa, yaa marwan nacan nashan amarci kema kin sani ai, kema zuwa gobe wazai kiraki ya samu, Galadima nacan yana kwa.....”.
Filo na d'auka Na jefa mata a fus
aka, suka sanyamin dariya kuwa.
★★★★
Nasha kuka yayin tafiyarsu Ayusher, inaji ina gani suka tafi suka barni nikad'ai cikin wad'anda ban saniba.
Tun magriba aka shiryani tsaf cikin wata tattausar atanfa, sannan aka d'oramin alk'yabba, w
lhy nagaji da saka alk'yabba r nan, saboda nauyi sukemin, har mamaki nakeyi yanda su basu damuba.
Zan iya cemuku nidai yau wanka akamin da turare dan kowane lungu da sak'o na jikina saida yasha ruwan turare, ruwan danayi wanka dashi kansa na musamm
an ne, nayi k'yau harna gaji.
An fiddoni aka sakani cikin mota, sannan aka nufi sashen Galadima dani. Dukda nasan auren Contract nayi, hakan bai hana zuciyata luguden dakaba, tunda bamuyi wata yarjejeniya dashiba ta zaman da zamuyi, addu'a natayi
a zuciyata ina tunano innarmu da munubiyata da kewarta ta gallabeni, jinake tamkar mun shekara 5 bamuga junaba, bamu ta6a yini ba'a tareba, saigashi yau munyi kwana da yinima, ko'a waya bamuji muryar junaba.
Duk da fuskata a rufe take hakan bai hana
ni shaida 6angaren Galadima ya had'uba, dan k'amshinsa ma da banne.
Muryar wata na tsinkayo a cikinsu tana fad'in wai falon Galadima za'a kaini, gabana yakuma fad'uwa.
Nidai naji mun iso inda turaren Galadima yafi ko ina yawa, inaga nanne f
alon nasa, gawani lallausan Abu danake takawa a k'afata, sun zaunar dani akan wani laushin dayafi Wanda nake takawar, sannan sukayi addu'a suka fice.
Tunda suka fita ban iya d'ago kainaba, dukda falon tsitt yake alamar babu kowa cikinsa, sai k'arar AC
kawai da ni'im taccen k'amshin dake tashi, a falon, sai TV dake magana can k'asa an rage k'arar sosai, hawayen danaketa rik'ewa tun d'azun suka shiga ziraro min a kumatu. a hankali nakejin takun takalmi na tunkaro falon.........
✍
🏼
Muhad'u tomorrow i
dan munkai da rai da lafiya, yau kaina namin ciyo kuyi manage da wannan please
🤦🏻
♀
.
Ko Galadima zai angwance oho mar
😜
🥳
.
⛹
🏻
♀⛹
🏻
♀
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
👏🏻😭
_*
*_Typing
📲
_*
*_HASKE WRITERS ASSO...
💡
_*
_(Hom
e of expert and perfect writer's)_
*_
♦
RAINA KAMA......!!
♦
_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
👉🏻
2
⃣
2
⃣
..........Takun takalminsa yana bada sautine dai-dai da kowacce dak'ik'a na bugaw
ar zuciyata, gaba d'aya saina nemi jarumtata na rasa, musamman da firarsu a Ayusher tashiga dawomin a zuciya.
Zuciyata tashiga tsitstsinkewa, saikace ba Munaya mai tsiwarnan ba da rashin barin kota kwana, kululu cikina yabada sauti lokacin da aka mur
d'a handle d'in k'ofar. kamshinsa ne ya buso min har cikin hancina.
Shikam cak yatsaya yana kallona da mamaki, yasan wannan aikin aunty Mimi ne ko mom, yakuma tamke face saboda tsaro ba tsoroba
😎
.
Oho ni bamma san yanayiba, nima tawa ta isheni a
zuciya, dan wani tsoronsa ALLAH ya dasamin lokaci d'aya. kusan mintuna 2 yana a tsaye tamkar bak'on falon, yayinda k'amshin turarena ke dukan hancinsa, yau da ace auren soyayya yayi da wadda yakeso, babu abinda zai hanasa sauke nauyin daya damesa tsawon sh
ekaru. a hankali yacigaba da takowa har cikin falon, ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu cikeda izza, k'afarsa d'aya a kan d'aya yana wani kallona a k'asan idanu, shiru kakeji tamkar bama a cikin falon.......
Muryata a sanyaye nace “ina yini”.
tamkar bazai amsaba, saikuma yace “lafiya”.
Daga nan kowa yay shiru.
Knocking d'in k'ofar da akayine yasakashi sauke 6oyayyar ajiyar zuciya, cikin muryarsa mai kama da anmasa dole ya tambayi wanene?.
Cikeda girmamawa sarkin k'ofar y
ace, “nime ranka ya dad'e, dama an kawo sak'one”.
Kansa ya jingina da kujera, sannan yace “su shigo”.
Kuyangi kusan biyarne suka shiga falon da sallama, duk muka amsa akan la66a, suka dire kayan hannunsu sannan suka zube suna kwasar gaisuw
a agaremu, hannu kawai ya d'aga musu, nidai koma motsi banyiba, dan nima kunyama nakeji idan naga sun durk'usa suna gaidani, danfa wasuma sun girmeni sosai wlhy, wasuma sun haifeni, kai sarauta dabance gaskiya, al'amuransu sunada wahalar gaske, nidai harma
yanzu ban fahim ci komaiba wlhy.
Bayan fitarsu da kusan mintuna 4 naji alamar mik'ewarsa, yanzu ma baice dani uffan ba yashige wani d'aki danake k'yautata zaton bedroom d'in sane a wajen.
Guntun tsaki naja, a raina nace ALLAH ka rabamu da gir
man kai dai wlhy.
Ban damu da cire hular alk'yabba d'inba, dan sanyin Ac yasa ban takura ba, sai zamana dana gyara sosai yanda zanji dad'i da k'yau a saman lallausar kujerar, duk da har yanzun a tsoracen nake kuwa. dan wannan d'an jinkan yafi k'arfin
a, zai iya amfani da k'arfinsa ya cutamin batareda yayi la'akari da matsayin auren namuba.
Shikam yana shiga d'akin nasa yafara k'ok'arin cire bottom d'in rigarsa, idon sane ya sauka akan gadonsa dake lailaye da zanin gado blue, dan komai nasa na
nan white and blue ne, sa6anin na India dasuke White and Golden, kuma matsawa yayi sosai saboda ganin farin k'yalle dake saman bedsheets d'in.
Tsaki yaja yana fad'in “waisu wad'annan mi suke nufi da shinfid'amin wannan farin abun a saman gado? samazo
su d'auki kayansu yanda suka ajiye, motsww”. Yakuma jan tsaki sannan ya shige bathroom.
Acanma yana wankan yana jera tagwayen tsoki, bai wani dad'eba yafito sanye da bathrobe milk, hannunsa rik'eda k'aramin towel yana goge fuskarsa zuwa kansa.
Bai shafa maiba, wando yasaka da t-shirt duk milk color marasa nauyi, da alama yayi shirin barci kenan, ya d'auki turarensa na barci mai sanyin k'amshin ya faffeshe jikinsa, sannan ya saka silifas bak'ak'e a k'afarsa yakuma fitowa..
Kallona
yayi da mamaki ganin ko fuskarta na kasa bud'ewa, ya ta6e baki da cije lips nashi saman ya zauna bisa tattausan carpet d'in tsakkiyar falon inda kuyangin suka ajiye kayan d'azun.
Tankwashe kafafunsa yayi yashiga bud'e kwanikan domin duba abinda ke
ciki. “halan kekam bak'ya jin zafi?”.
Yayi maganar yana zuba fruits salad a k'aramin bowl na tangaran mai k'yau.
Shiru nayi tamkar ban jishiba, shima saiya shareni yaja bowl d'in gabansa yafara sha a hankali tamkar bayaso.
Duk abinda ya
keyi ina kallonsa ta k'asan ido, saboda kaina Dana jingina da kujera.
Kusan mintuna 5 yana shan fruits salad d'in tamkar wani k'aramin yaro, dan ko Rabin Wanda yazuba baiyiba, araina nace abincinma sai an masa sarauta kenan.
Idanunsa ya d'ago
yana kallona, “k wai bakijin ana Miki maganane? bazaki bud'e face nakiba?”.
Saida naja kusan seconds 20 sannan na janye hular alk'yabba d'in.
Janye idonsa yayi yacigaba da shan kayansa, nikuwa saima na zame na kwanta a kujera, dama 3setter c
e, idanuna na maida na lumshe saboda ciwon da kaina yakeyi kad'an-kad'an, ga kewar innarmu da munubiya dasu Aryaan na damuna, ga wannan auren na fargaba na addabar zuciyata.
Dukda yaga kwanciyar danayi bai tankaba, ya kammala shan fruits salad d'in
yamik'e, saman kujera yakoma ya zauna, ya d'auki wayarsa yana latsawa, saikuma ya ajiye ya d'auki remote ya canja tasha zuwa labarai.
Haka muka zauna tamkar kurame, shi yana kallon labarai yayinda nikuma barci 6arawo ya saceni batareda na shirya ba
, to gajiya na nuk'urk'usata.
Shi duk bai farga barci nakeba harya kammala kallon labaransa ya kashe tvn, kallona yayi da nufin min magana saiyaga kamarma nayi barci a haka.
Yay d'an jim yana tunanin tayaya zai tasheni, danshi soyake ya sh
ige yayi shafa'i da wutiri ya kwanta, a ganinsa kuma bai kamata ya barni a wajenba.
Matsowa yayi kusada kujerar, ya d'an bubbuga hannun kujerar, dama barcin nawa baiyi nisaba, na bud'e idanuna dasukayi d'an jaa a hankali, saboda barcin dana fara.
“tashi muje ki kwanta”.
Gabana ya fad'i, amma saina yunk'ura da k'yar natashi zaune.
Ganin ya nufi k'ofar futa sainaji d'an sanyi, tashi nayi nabi bayansa muka fita, bakowa falon alamun duk suntafi makwanci. Wani falon muka shiga daban kuma
, gaskiya shima ya had'u, komai na cikinsa lemon green ne da milk, sai tashin k'amshin turaren wuta da air fresheners masu dad'i yake. bai tsaya ananba yay gaba, nidai ina binsa abaya kawai, munshiga k'aton bedroom tamkar nasa, saidaifa aganina nasan yafi
had'uwa duk da ban ganiba, nanma komai lemon green ne acikinsa, sai labuloli milk kamar falon, shima yanata tashin k'amshin.
Juyowa yayi ya kalleni “nan shine d'akinki”. ‘yayi maganar tamkar an masa tilas’.
Uffan bance masaba, sai d'aga masa
kai nayi alamar naji, shima bai sake cewa komaiba ya fice abinsa.
d'akin na shiga bi da kallo, yamin k'yau sosai, na cire alk'yabba jikina ina sauke numfashi, sanan na cire sark'a da 'yankunne da bangles d'in duk na zube saman madubi. Suma kayan na
hau cirewa dan bazan iya barci da suba, sai kuma na shiga tunanin inda zan samu kayan barci? tunda lefena suna gidanmu ba'a kawoba, akwatin da'a kawoni dashi kuma jiya ban Ganshi a d'akinba, zuciyatace tabani shawarar duba wardrobe d'in dake d'akin, banyi
musuba naje na bud'e, a
mamakina saina ganta da kaya, sai dai duk k'ananune, kayan barcinma babu na mutunci, tamkar zan fasa kuka haka naji, da k'yar nasamu wasu Riga da wando masu sauk'in fidda tsiraici, duk da suma d'in dai sai a slow.
Gadon na hau
amma saina kasa barci, kewar 'Yar uwata yadawomin sabuwa, na tashi zaune na fashe da kuka.
Ina zaune ina kukana sai kawai naga mutum yashigo min da sallama ciki-ciki.
Da Sauri na jawo gyalen dana ajiye gefe na yafama jikina, plate d'in hannu
nsa ya ajiye a table d'in dake jikin gadon, dan harya kwanta yatuna banci komaiba, gani yayi bai dace ya barni da yunwa ba, danni bak'uwace yanzu a gidan, dole sai an bani zanci.
Tamkar bazai tankaba saikuma ya kalleni, “mike faruwa kike kuka?”.
Wasu kwallanne masu zafi suka sake kwararomin, na sharesu da gefen gyalena nace, “wlhy ni tsoro nakeji, ban ta6a kwana ni kad'aiba, dan ALLAH ka kiramin Samha ta tayani”.
Shiru yay ya tsaya kawai yana kallona, azuciyarsa yace kajifa wannan yariny
ar dawani batu, kawai saina tafi kiran Samha ta tayata kwana?. guntun tsoki yaja, Wanda yasakani d'agowa na kallesa. Ya cije lips d'insa sannan ya juyo yakuma kallona “mikike nufi