Showing 114001 words to 117000 words out of 407268 words
hanata shiga tashin hankaliba, sa
ita shiga tsangwamar gimbiya bagobura da aibanta d'anta *Saifudden*, wani lokacin har shegantashi tayi, saida Sarki Abdul'fatah yazo har masarautar ya taka mata birki sannan.
Mama Fulani tasaka sauran matan Sarki Abubakar sun juyama gimbiya bagobu
ra baya gaba d'aya, batada sakewa ko kad'an acikin gidan. Sarki Abubakar yasan komai dake faruwa a gidansa, amma saiyayi tamkar bai ganiba, bakuma Dan mama Fulani tafi k'arfinsa baneba, yadai zuba mata idanu kawai yaga iya gudun ruwanta.
Ahaka yaran
suka taso, gimbiya bagobura ma bata sake haihuwa ba, sai mama Fulani ce takuma biyu, mace 1 da autanta namiji Hayatudden.
Saifudden da jalaludden sun tashine tamkar tagwaye, dukda Saifudden ya girmi jalaludden d'in dakusan 1½ kuwa. danma mama Fulani
na hana jalaludden sakewa da Saifudden ne. Kokuma Kamaludden da Shamsudeen suyita dukan Saifudden idan sun gansa tareda jalaludden d'in.
Ahaka Saifudden yatashi cikinsu a tsangwame har suka girma suka zama manya.
Saikuma wani Abu tashin han
kali ya samu, a time d'in da mama Fulani ke ganin sarauta zata dawo wajen 'ya'yanta sai ubangiji ya nuna mata ikonsa.
Dan kuwa Shamsudeen da kamaludden sai sukayi had'arin jirgi zasuje umara duk suka rasu.
A time d'in a marine kawai ba a saka m
ama Fulani ba, amma hauka tuburan tafara a masarautar gagara badau. Saida aka had'a da addu'a sannan talafa, saita kullaci gimbiya bagobura, wai ita tama 'ya'yanta asiri suka mutu domin d'anta Saifudden yagaji sarauta.
Gimbiya bagobura zata tada han
kalinta Sarki Abubakar yace tama kwantar da hankalinta.
Bayan mutuwar su Kamaludden babu dad'ewa aka had'a auren gimbiya Zakiyya d'iyar Sarki Abdul'fatah da Saifudden aure, shikuma lokacin Jalaludden da Rafi'atu d'iyar wani Sarki.
Aikam sai m
ama Fulani ta hau bala'i wai munafunci aka shirya. Babu Wanda yabi takanta akasha biki.
Gimbiya Zakiyya da gimbiya Rafi'atu kusan atare suka haihu a time d'in, gimbiya Zakkiya ta Haifa d'iyarta mace, saidai tana haihuwarta ko ganinta batayiba takom
a ga ALLAH
😭
.
Wannan shine silar aurena dana Saifudden.
Dan bayan rasuwar yayata gimbiya Zakiyya da kwana 7 aka d'aura min aure da yarima Saifudden, domin nacigaba da rainon abinda tabari.
Banason Yarima Saifudden, domin ina masa kallon
*Mijin yayata* amma banida yanda zanyi, dole na aminta da auren domin yima iyayena biyyaya.
Nasha wahalar zama dashi, saboda shi hankalinsa yana kan yayata ne marigayiya, silar soyayyar danake nunama Habeefa (aunty Mimi) d'iyar da gimbiya Zakiyya tab
arine ya siyamin soyayyar yarima Saifudden, a hankali har shak'uwa tafara shiga tsakanina dashi. Soyayar dayakema 'Yar uwata saita dawo kaina.
Sai daifa inashan wahalar mama Fulani, duk da kuwa itad'in (Gwaggona ce) tana amsa sunan k'anwar mahaifina
, amma k'iyayyar datakema mahaifiyarmu gimbiya Khadija (inno) saita shafemu, duk da abaya tana ik'irarin son mahaifinmu Sarki Abdul'fatah kuwa. Kamar yanda yayata gimbiya Zakiyya tasha wahalarta a gidan nima hakane, saima tawa taso fin ta 'Yar uwata, bansa
n dalilintaba, wai Ashe dan ina tsananin kama da inno ne
😆
.
“Ina fata dai kina fahimtata Munaya” ‘Momma tayi maganar tana kallona dana rabga tagumi inajin cakwakiyar masarauta.
Kaina na jinjina mata cikin damuwa.
Saitayi murmushi taci
gaba da fad'in.
Mama Fulani taso d'iayarta ta farko gimbiya Mansura ta auri yayanmu yarima Abubakar, Wanda babanmu Sarki Abdul'fatah yayma amininsa takwara.
To saikuma hakan bata faruba, dan ita tata dabarar itada iyayenta, idan Yayana Yar
ima Abubakar ya auri gimbiya Mansura sarauta takoma hannunsu kenan, tunda yarima Abubakar shine magajin masarautar mu, kinga ai d'ansa ne zai gajesa kenan, idan tahad'a auren kuwa yazama jikanatane da masarautar nan gaba.
To saikuma tsarin nata
bai yuwuba, saima nida yayata mukazo masarautar gagara badau tushen mahaifiyarmu mukayi kane-kane, gashi kowa yana Saran Saifudden shine zai gaji masarautar gagara badau alokacin, tunda manyan 'ya'yan Sarki Abubakar sun rasu, Saifudden kuma shine babba nam
iji a lokacin.
Shiyyasa takuma d'aukar karantsana ta d'aura mana muda gimbiya bagobura.
Bayan haihuwar Haneefa babu dad'ewa gimbiya bagobura ta rasu, rasuwar data gigita yarima Saifudden kenan da Sarki Abubakar har ma da jama'ar masarautar ga
gara badau, amma banda mama Fulani da sauran matan Sarki, dansu hakanma dad'i yamusu.
Sanadin rasuwar gimbiya bagobura Sarki Abubakar ya kwanta ciwo, sai yayi murabus yace a d'aura d'ansa Saifudden a madadinsa.
Wannan Abu yama kowa dad'i a
masarautar, amma banda mama Fulani dakejin tamkar tamutu dan bak'in ciki.
Saidai batada yanda ta iya, tanaji tana gani yarima Saifudden yazama Sarkin masarautar gagara badau.
Alokacinne kuma akace dole ya k'ara aure, dan Sarki baya zama da m
ace d'aya, gashi kuma ni ban haihuba har lokacin.
A rana d'aya aka d'aurama Sarki Saifudden aure da mata biyu. Nanfa mama Fulani tashiga jansu ajiki wai dan a kuntatamin, tana kuma koya musu yanda zasu kuntatama shi Kansa Saifudden d'in.
Sa
rki Saifudden nada shekara 9 a karagar mulki ALLAH yayma Sarki Abubakar rasuwa, mutuwarnan ta girgiza mahaifinmu Sarki Abdul'fatah sosai, dan saida aka had'a masa a addu'a.
Tun daga wannan lokacin masarautar gagara badau takoma hannun mama Fulani, da
n sai yanda tace tanaso Sarki Saifudden zaiyi, dayake shi mutumne mai sanyin hali, baya ta6a sa6a mata.
Duk da haka wannan bai ishetaba, hattada yanda za'a gudanar da mulki saita tsara.
Har lokacin amaren Sarki Saifudden babu wacce ta ha
ihu.
Cikin ikon ALLAH sai gani da ciki, babu kitumurmurar daba aima cikinnan nawaba d'anya zube amma ALLAH ya k'addara mijinki *Muhammad Sameer* saiyazo duniya.
Lokacin Dana haihu shekarar haneef 10 cif a duniya.
Muhammad shine jika nami
ji na farko da aka fara haihuwa a masarautar gagara badau, dan kuwa matar Jalaludden ma mata taketa haihuwa.
Daga nan nima ban sakeba saida Muhammad yacika shekara hud'u, yanda Saifudden yasha tsangwamar mama Fulani haka Muhammad ma yashata tun ya
na yaro.
Shima Sameer hak'urin mahaifinsa Saifudden ya gado sosai, dan ko abu aka masa saidai yayi kukansa ya goge hawaye, koni bazai sanarmawa ba, saidai in wata baiwa tagani ko Haneefa (aunty Mimi) su sanarnin.
Da *Ciwon zuciya* na haifi Same
er, dan haka kullum cikin kaffa-kaffa muke dashi saboda gudun samun matsala ga lafiyarsa, da yawa jama'ar gidan sukan masa abune wai dan zuciyarsa ta buga
💔
ya mutu. sun manta rayuwa da mutuwa duk Na ALLAH ne.
Da sauri na kallo momma.
Ta d'aga min
kai tana murmushin takaici, “hakane d'iyata, kullum burinsu kenan akan Muhammad tun yana yaro..
Ranar wata litinin da asuba Sarki Saifudden yafita sallar asubahi sai kawo manashi akayi cikin gida, wai yafad'i ana tsaka da sallah.
A lokacin
kafafunsa ne kawai basa aiki, amma sauran jikinsa yana motsawa.
Nice naita wahalar jinyarsa, ga cikina yafara tsufa, sai jakadiya ke taimakona, amma sauran matan Sarki ko'a jikinsu.
A hankali ciwo yacigaba da girmama a jikin takawa, tun ana
kafa har yadawo duka jiki, idonsane kurum ke aiki a lokacin.
A asibitin garinan muke jiyyarsa a time d'in, a asirce batareda jama'ar gari sun saniba.
Acikin wannan tashin hankalin na haihu Namiji, shine Abubakar (Sauban).
Nidai lokacin
kawai ina rainon Sauban ne, amma rabi duk Haneefa ce (aunty Mimi) yayinda kulawar Sameer takoma hannun k'anwata Zaituna (mom), autarmu kenan, dan dole aka dawo da ita wajena tana taimakamin.
Na haifi Sauban babu dad'ewa aka maida sarautar Saifudd
en akan Jalaludden d'an gidan mama Fulani, saikuma lokacin jama'ar gari suka San Sarki Saifudden bashida lafiya ma.
Ko kad'an ban damuba, danni ta lafiyar mijina nakeyi ma.
A lokacin anta kananun magana akan zargin mama Fulani dawasu kuma manya
n attajirai, dan akwai wani zaman sirri da sarki Saifudden yayi dawasu attajiran k'asar ana jibi abin zai sameshi, kuma anga yafito ransa a 6ace daga tattaunawar, alamar sun buk'aci wani Abu ya hanasu kenan. suma angansu ran nasu A 6acen. Nikam bamma maida
hankali akan wannanba, mahaifina Sarki Abdul'fatah shine kawai tsaye akan ciwon Saifudden, saini kuma da jakadiya.
Masarautar kuwa ai duniya sabuwa. Matan Sarki Saifudden ma duk sun kama gabansu, sunce bazasu iyaba.
Shekararmu d'aya a asibiti
babu wani canji, saima jikinsa dake neman fara ru6ewa saboda komai sai an masa. Baya iya d'aga koda d'an yatsane. (Tun farko likitocinmu na nan sun Sanar damu an masa allurar gubane, kuma guba mai had'ari, dan babu makarinta, itakuma tana sakar da jijiyoyi
n jikine su daina aiki gaba d'aya, wannan yasaka jikin Sarki Saifudden ya sandare
😭
.
Wani amintaccen likitanmune yabada shawarar mu maidashi India dansu sunada kwararrun likitoci, kuma zaifi samun kulawa da tsaro a can.
Wannan shine silar
dawowarmu wannan k'asa, da cuku-cukun mahaifina Sarki Abdul'fatah, dan komai namu mukam ya k'are, duk abinda Sarki Saifudden kedashi yagama k'arewa a neman Magani.
Tunda muka dawo India kuwa Sarki Saifudden yafara samun kulawa ta musamman, saidaifa
maganar ta kud'ine. Wasu sarakuna da yawa sun bamu gudunmawa, wasuma suna akan bamu.
Sanin Zara bata barin dami, gashi kullum cikin buk'atar kud'i muke sai mahaifina yakafa wasu sana'oi da sauran kud'enmu, tanan muke samun kud'in shiga. Karatun Mu
h'd da Haneefa kuma Mahaifiana ke d'aukar nauyi..
Tundaga primary har jami'a anan Sameer yayi karatunsa.
Kiyayyar Saifudden kuma ga mama Fulani saita dawo jlkan Muh'd gaba d'aya, kokad'an bata k'aunar ganinsa, kullum tsakaninta dashi sai a
ibantawa da jifansa da kalamai masu had'ari ga yaro.
Tunda Muh'd yafara sanin Kansa, yaga halin da mahaifinsa yake saiya fara canjawa daga mai hakuri zuwa mai zafi.
Ga ciwonsa kuma, duk yabi yayta kuntata zuciyarsa akan ciwon mahaifinsa da
burin d'aukar fansa.
Muh'd mai fara'a da barkwanci yakoma mutum marason magana da azabar rashin d'aukar raini, duk da hakurinsa nanan bai dainaba, dan zakata masa Abu
ya shareka kamar bai ganiba, sai randa yazo k'arshene zaka gane kurenka a wajensa
.
Mahaifina Sarki Abdul'fatah shine yamatsa tun Muh'd na secondary school dole idan akayi Hutu yazo najeria, dan acewarsa tahakane kawai zai fahimci sarautar gidansu.
Muh'd ya karanci Engineering ne, dama tun yana yaro kingansa kullum cik
in son had'a Abu yake, shine tsinka wayar fitila tsinka ta redio ya had'a wani abun, tunma ina masa fad'a harna bari kawai. Ashe abincinsa awajen yake. Yanzu haka sunada Company na had'a wayoyi
📱
da Computers
💻🖥
, da sauran kayayyaki dai. Sannan yana wasu
business domin dai muke samun kud'ad'en kulawa da mahaifisa da sauran matsalolinmu, dan babu mai kulawa damu a masarautar gagara badau sai Sarki Jalaludden.
Wani zuwa da Muh'd yayi Nigeria shine aka bashi sarautar *Galadima*, galadima Sarautace mai
k'arfin gaske, dan sai d'a mafi soyuwa ga Sarki ko k'ani ake bamawa. Kuma akance batada banbanci da sarautar waziri, dan duk abinda waziri zaiyi Galadima ma zai iyayinsa. Akwai ma wasu abubuwan da daga Sarki sai Galadima kan yisu a fada.
Da da farko
nace ya mayar musu amma sai mahaifina yace a'a, ai hakan da sukayi dai-daine.
Sharrin kuwa dakika sun masa, har tsautsayi ya jefaki a ciki, sunyine dan hankalinsa ya tashi, har takai zuciyarsa ta buga ya mutu sun huta.
Dan ayanzu ne suke gani
n sunfa *kashe macijine basu sare kansaba* Galadima yazamar musu *RAINA KAMA.....*, basuyi tunanin zaikai tsawon rai hakaba, saboda Ciwo mai had'ari dake a tare dashi.
Shikuma Muh'd yafi karkata hankalinsa ga jama'ar wajene sukama mahaifisa haka,
koda akwai jama'ar masarautar gagara badau to kalilanne, kuma mama Fulani kawai yake zargi.
Nikuma ba ita kad'ai nake zargiba, amma yakasa fahimtata gaba d'aya har kawo yanzun kuwa. Dagashi har Haneefa sunfi zargin jama'ar waje, don mutananen masara
utar suna 6oye musu ainahin fuskarsu ta zalunci, mama Fulani ce kawai tata take a bayyane.
Wannan yasaka tun sharrin da akai muku nasaka amin bincike a kanki, Alhmdllh ban samu wata matsalaba a tarihinki,, daga nan na dukufa addu'a da neman za6in ALL
AH.
bamma kai ga furtama kowa matsalata ba sai mahaifina Sarki Abdul'fatah (papi) yace Muh'd saiya aureki.
Nasan ba sonsa kikeba, amma ina rok'on ubangiji da yasa wataran kuso junanku, kinada tarbiyya da wayon da zaki iya canjamin Muh'd, da
n banason hallayarsa ta yanzu, nafi son nake ganin walwala atare dashi a ko yaushe, ki taimakeni ki shiga rayuwarsa sosai, dan ke macece, sai kin fishi zama cikin jama'ar masarautarsu, zakuma ki fishi fahimtar halayyarsu, sannan kidinga bashi shawara akan
abinda yadace dashi. Inaji a jikina zaki iya canjamin Muh'd, saboda kinada hankali. gudun kar wani yasakama zuciyarki tunani daban yasaka nace yakawoki da wuri, domin kisan yanda zaki rayu a masarautar, kafin kutafi insha ALLAH komai Na zamantakewar masara
uta za'a koyar dake kinji”.
Kaina Na gyad'a mata, sannan a sanyaye nace “Momma namiki alk'awarin zai taimakesa akan matsalarnan, kuma zan bama rayuwarsa gudun mawa insha ALLAH, Sai dai Abu d'aya ne ban ganeba”.
“miye baki ganeba d'iyata?”
.
“Abokinsa Muftahu, shima a masarautar yake?”.
Murmushi Momma tayi, tace “daga Muftahu har Harun duk 'yan masarautar ne, Muftahu kakanni suka had'a dasu Muhammad, da kakan Muftahu da Sarki Abubakar kakansu Muh'd uwarsu d'aya ubansu d'aya, sh
ikuma Harun d'an waziri ne na yanzu, kuma shima wazirin haifaffen gidanne, saidai inason sanin ko wani Abu kika gani tareda wani acikinsu?”.
Kaina Na girgiza alamar A'a.
Momma ta sauke ajiyar zuciya, “Munaya saikin dage kinji, domin Na had'a
ki da aiki mai wahalar gaske, mai kuma sark'akiya, musanman akan halayyar Muh'd, dan bai yarda da kowaba dakike ganinsa nan, koyaya Abu ya had'aku sai yayi zargin turoka akayi garesa, kuma zaka Shiga jerin wad'an da yake tuhuma. amma kekad'aice mafi kusanc
i da Muh'd yanzu, zakifi kowa sanin matsalarsa da wuri, saikuma kin fimu fuskantar tunaninsa, danni kinga jinyar mahaifinsa tasa banwani zauna dasu irin sosai d'innanba, yanzu haka kafin nasan matsalarsa 'Yar uwata Zaitun (mom) tasani ko Haneefa (aunty Mim
i), garama Sauban.
Nace “shikenan Momma ki tayamu da addu'a kawai”.
“insha ALLAH muna kan yimuku kullum, ALLAH yayimuku albarka, ya albarkaci aurenku da dukkan rayuwarku da abinda zaku haifa”.
Ban iya amsawa ba, kaina Na k'asa nikam, ko
azuciya ma ban amsaba, dan nayi alk'awarin zai taimakesa kamar yanda ta buk'ata. Amma ina gamawa zan nemi sakina, koda nanda shekaru 2 ne kuwa, amma gaskiya Na tausayama Galadima, dan nakula yana cikin tsakkiyar mak'iyane masu fuska biyu. abinda kuma nalu
ra da Momma bata ganeba shine Galadima bawai bai yarda 'yan gidansu nada saka hannu akan ciwon babansa bane, baya dai nunawane kawai, sai dai bansan dalilinsaba.
CCTV camera d'in dana gani a d'akinsace tadawomin a rai, maybe ya sakatane domin sanin m
asu shiga da fita koda bayanan.
Haka Na kusan yini cikin damuwa da tausayinsa, dan duk saiya bani tausayi wlhy. shiyyasa zaka gansa kullum shiru-shiru, gaskiya 6angaren hak'uri Na yarda yanada hak'uri kam.
***********
Yau saida yamma muka
je muka duba Abie, mun iske Galadima baya asibitin, dama tun da rana yazo gida yay wanka yakuma fita.
Har dare muna a asibitin, saida Galadima yazo muka taho tare, ina gaba ni da shi da khaleel dake barci a cinyata, yayinda sauban da aunty Mimi da Sam
ha ke baya.
Maganar da