Showing 234001 words to 237000 words out of 407268 words
“ki shirya, shirinsu na farko d'aukewar wutar hotel d'in nan gaba d'aya, na gaba kuma shine banida tabbas. Yara dai ALLAH yana tare dasu, gakuma su Aryaan suma”..
Cikeda mamaki Munaya ta kallesa, sannan
ta kalli yaran dake gabansu a wani d'an gado mai k'yau.
Jikinta har rawa yake tace, “yalla6ai mi su Aryaan zasu iya? Please k.....”.
Hannu ya d'aga mata alamar karfa ta ishesa yace, “wani ilimin aduhuwar daji kawai ake laluboshi, kinsan k
uwa dolene a gamu da had'arurruka Aciki”.
batada za6i sainyin shiru, ta kalli su Khaleel daketa wasa da abinci a teble da suke zaune hankalinsu kwance. Hawayene ya cika mata idanu, yama za'ayi wad'an can sakarkarun yaran ace suna masu bama yarant
a kariya? Yaushe suka gama sanin ciwon Kansu ma balle na waninsu? gaskiya wannan gangancine kawai, tasa handkerchief ta share hawayen da ke k'ok'arin zubo mata.
Duk abinda take Galadima yana kallonta. duk tausayinta saiya kamashi, ya tuna da wahalar
datasha, amma bashida za6in daya wuce hakan, kuma itace tabashi k'arfin gwiwa ai, yasaka aransa ko salwanta yaransa sukayi zaiyi tawakkali insha ALLAH.
Duk Wanda yake cikin shirinsu Galadima ya gama shirinsa, haka suma mak'iya masu buri a shiry
e suke.
Gaba d'aya saura mintuna 25 atashi, saboda gabatowar sallar magrib, a kuma time d'inne Sarki Abdul-fatah da Sarki jalalludden dadai duk wani babba Wanda sukazo tare suka mik'e domin tafiya, ganin haka Galadima yama Yaa marwan sigina da ido a
kan ya fita da Ameen and Ameena suma, yabi tawagar su papi, dan baya buk'atar a cuta musu..
Jikin Yaa marwan a sanyaye ya d'auki yaran ya fita cikin dabara, yana kallon y'an uku, shidai dan kawai Galadima ya dagene, amma bai kamata a saka yarannan
a matsayin tarko ba.
Munaya ma dai ta danne zuciyarta tayi shiru, tanason bama Galadima kwarin gwiwa.
Su papi na fita y'an rawar k'oroso suka fara wasa, mintuna goma da aka basu ya k'are, sai wani mawak'i ya fara nashi, nanfa y'an mata da sam
ari aka samu nayi, dama ganin su mai martaba ne ya sakasu nok'ewa, ana tsaka da cashewa hall d'in yay d'iff, wuta ta d'auke agaba d'aya hotel d'in, mutane aka fara hayaniya kowa na k'ok'arin damk'e dukiyarsa a hannu da k'ok'arin kunna fitulun waya.
Gaba d'aya jikin Munaya yahau 6ari, ta fashe da kuka tana laluben gadon da yaran suke, ruk'ota Galadima yay yasaka a jikinsa, muryarsa na rawa yace, “please ki nutsu”.
“bazan iyaba yalla6ai, karsu......”.
Yay saurin rufe mata baki, da ta
ttausan tafin hannunsa..... A dai-dai wannan lokacinne kuma wutar hotel d'in tadawo.
Hall d'in ya kuma kaurewa da hayaniya, zaram Munaya da Munubiya suka nufi gadon da yaran suke ciki, wayam babu komai.
Munaya tayi luuu zata fad'i, saurin ruk'
ota Munubiya tayi, Galadima yataso daga inda yake shima zuwa garesu. hall d'in yagama rikicewa da tsantsar hayaniyar rashin ganin yaran, sai kallon kallo akeyi. Securitys d'in da aka baza sun rikice da wannan tashin hankali, dan sune mutane na farko da za'
a fara tuhuma.
Rufe hotel d'in akayi aka hana kowa shiga balle fita,
Galadima ya shafama Munaya ruwa ta kawo numfashi, fashewa tayi da sabon kuka ta fad'a jikinsa, hannu biyu ya saka ya rungume ta shima yana had'iye kwallar bak'in cikin dake
Neman zuboma idonsa.
Tausayinsu ya kama mutane da yawa, innaro harda kukanta, hakama inno, abinda yabani mamaki shine tsantsar damuwar da mama Fulani ta nuna, dan itacema tabama Galadima ruwa ya shafama Munaya ta farfad'o.
Da farko Muna
ya ta d'auka ko Galadima wasa yake mata yasan inda yaran suke, amma ganin damuwar da yake ciki saita kuma rikicewa, dandanan numfashinta yafara gagarar k'irjinta, ta mik'e a kid'ime, dan taji a jikinta kuka sukeyi, nononta sai tsitstsirawa suke, wani jiri
ne yafara hajijiya da ita da zuciyarta ta k'iyasta mata zafa su iya kashe mata yara, luuuu tayi baya Galadima ya ruk'ota. sume musu ta kumayi.
Hankalin Galadima kuma tashi yayi, dole ya d'auki Munaya aka sakata a mota suka bar hotel d'in.
S
auran mutane kam kowacce mota zata fita sai an binciketa.
Yayinda Securitys d'in suka bazu ko ina na hotel d'in ana bincikawa.
Gida aka wuce da munaya, har suka isa tana jikin Galadima, yanata murza tafin hannunta kozata farfad'o, har d
'ora bakinsa yayi akan nata ya jawo iskar numfashinta amma a banza, hakanne yakuma tada hankalinsa.
Kai tsaye d'akinsa ya wuce da ita, ya shimfid'eta a kan gadon ya cire mata alk'yabbar jikinta, Akash suka k'araso da hanzari shima, taimakon gagga
wa yafara bata shida doctor jalal, cikin amincin ubangiji saigashi takawo numfashi, bama su bari tadawo dai-dai ba suka mata allurar barci.
Suna fita Galadima ya cire rawani da alk'yabbar jikinsa shima, ya sassauta bottom d'in wuyan rigarsa.
Safa da marwa ya shigayi a tsakar d'akin yana Mirza agogon hannunsa Wanda daka gani kasan ba normal agogo bane,.
Wayarsa datai k'ara yay saurin d'auka, d'agawa yayi yasaka a kunne, “Muftahu ya ake ciki?”.
Cikin hakki Muftahu yace, “komai yana
tafiya yanda ya kamata ranka ya dad'e, har yanzu gamu muna bin bayansu, amma munkai inda yakamata ka fara Controlling namu, yanzu mun.......”
Da sauri Galadima ya katseshi ta hanyar fad'in “karka damu ina kallon Ku, saidai kilometer's d'in dake tsak
aninku dasu fa yakai 1½, Saleem da Sauban sunfi kusa dasu, dan haka ku k'ara azama. daga lokacin da suka farga da abinda nasaka jikin Amaturrahman tabbas zasu cireshi, kuma zamu rasasune gaba d'aya”.
“Ok babu damuwa, ranka ya dad'e”.
Yanke wa
yar sukayi, Galadima ya bud'e wani k'aramin akwati ya fiddo kayan aiki wanda a ready dama yagama had'a komai, bajesu yayi akan gadon kusada Munaya, ya zauna yafara Control cikin matuk'ar kwarewa.
Saleem ya kira aunty Salamah wadda itama take tare
dasu Ameer yaran da suka sace Muftahu, d'agawa tayi jikinta na rawa, “Saleem kuna inane?”.
“Aunty Salamah gamunan bayansu kad'an, amma mund'an basu k'afa saboda na kula sunfara fuskantar muna bin su, yanzu dai haka mun ajiye motarmu mun samu mash
in”.
“Hakan yayi, insha ALLAH indai ta Anguwar da muke tsammanin zasu shigane kamar yanda kaji Harun d'in yay magana to tabbas mu dai mun iso, saidai suzo su iskemu, ka kira yalla6ai ka sanar masa yakamata ya fito yanzu”.
“no Aunty Salamah, ba
zai yuwu boss yabaro masarauta ba yanzu, saiya tabbatar mun Isa, saboda dukma inda suka shiga yana bibiyarsu, dan bazai saka yaransa a matsayin tarko ba babu tsaro k.......”
Tai saurin k'atseshi ta hanyar fad'in “yauwa ina zargin kamar gasunan a wa
ta bak'ar mota sun wicemu fa”.
“Alhmdllh, su Ameer Susan yanda zasuyi su bisu bara na kira boss”.
“ok”. Kawai Aunty Salamah ta fad'a ta yanke wayar.
Kiran Galadima Saleem yayi, bugu biyu ya d'auka, “Saleem mike faru yanzu?
”.
“Ranka ya dad'e gamu dai biye dasu, amma Aunty Salamah tacemin gasu tagansu”.
“wacece Salamah? ”.
Gaban Saleem ya fad'i, dan ya manta Galadima baisan Salamah ba, “Am sorry sir, idan komai ya dai-daita zan maka bayani”.
“Sa
leem!!!”. Galadima ya kirayeshi a tsawace.
Saida Saleem ya janye wayar akunnensa, muryarsa na rawa yace “ka yarda dani sir, wlhy itama ta kwarai ce”.
Ajiyar zuciya Galadima yayi, muryarshi cikin tsantsar damuwar yace, “wannan anguwar da
kuke tanada hanyoyi da yawa, dan haka Ku fara amfani da live GPS navigation maps naku, yanzu zanyi settings komai yanda zaku ringa ganinsu duk layin da zasu shiga insha ALLAH, waye yake driving d'in a cikinku?”.
“nine sir”.
“ok bama Sauban wayar
”.
Saleem ya mik'ama Sauban wayar, Galadima na fad'a masa yanda zaiyi, shikuma yana Controlling maps App d'in dake cikin System d'in cikin kwarewa, (dan shima Galadima bai barsa hakaba, dukda bashida ra'ayin karantar wannan fannin saida ya tsaya
tsayin daka ya koyan saboda irin wannan ranar).
Saida Galadima ya tabbatar komai ya dai-daita, sannan ya kira su Nuren ma, suma suka dai-daita komai nasu, cikin sauk'i duk suka koma ganin inda yaran suke, saboda Galadima ya saka Abu jikin Amaturr
ahman, dukda bawai hotonsu ko video suke kalloba kai tsaye.
Duk da haka Galadima ke fad'a musu su shiga layin haggu, ko dama, kosu canja hanya dadai sauransu.
Duk Wanda yake a wannan masarauta yau hankalinsa a matuk'ar tashe yake, saifa k
allon kallo da hasashen juna ake a zuciya, kowa yana zargin Wanda ya raina.
Hankalin Abie a matuk'ar tashe ya nemi ganin Galadima, koda sarkin k'ofa yazo yana knocking Galadima bai amsaba, kuma yana kallonsa ta CCTV.
d'an aike ya koma ya s
anar Galadima ya kulle kansa a d'aki yak'i bud'e k'ofa.
Papi inno ya kira, yace maza taje sashen Galadima taga mike faruwa.
Ko kuyangi inno batajira sun mata rakkiyaba, hasalima babu Wanda yaga fitowarta a sashen mama Fulani, dan kowa a r
ikice yake da wannam bak'on lamari na satar yara.
Galadima daya ga sarkin k'ofa yabar wajen ya mik'e shima daga gaban kayayyakin da yake aikin, shaddar jikinsa ya cire yasaka bak'in wando da t-shirt, ya kawo bak'ar jacket mai k'yalli kamar rigar
sanyi ya ajiye gefe, a bakin gadon ya zauna yana d'aura takalminsa yana cigaba damasu Sauban da Nuren bayanin hanya, a dai-dai lokacinne Inno ta iso sashen nasa, da hanzari Sarkin k'ofa ya bud'e mata k'ofar, bata jira wani isoba ko masa sallama ta turo k
'ofar falonsa ta shigo, babu kowa a falon, komai ma a kashe yake. Bedroom d'insa ta nufa, nandai saida tayi knocking kam, saidai kafin yay yunk'urin tasowa ya bud'e mata ta turo k'ofar ta shigo, mik'ewa yay yana kallonta da d'aukar jacket d'insa zai saka.
Ajiyar zuciya inno ta sauke, saboda ganinsa normal.
“Ranki ya dad'e da kanki? lafiya dai ko?”.
“Inafa lafiya Muhammad? takawa ya aiko a kiraka ance ka kulle kanka, gashi baka sanar mana halinda yarinyar nan take cikiba”.
Galadima yace, ba kulle kaina nayiba, bansan kuma d'an aiken daga papi yakeba” ya juya yana kallon Munaya da cigaba da fad'in, “itama ta farfad'o, amma sun mata allurar barci”. ‘ya k'are maganar da daidaita zaman kwalar rigar jacket d'insa’.
Ajiyar
zuciya inno ta kuma saukewa, tace, “to Alhmdllh. ina kuma zaka naga kana shiri?”.
Wani murmushin takaici yayi zuciyarsa dake gudun daya wuce kima da suya ya dafe, Inno dai ta zuba masa ido, takowa yay inda take ya kama hannunta ya rankwafo (dan yaf
ita tsaho) ya d'ora bisa kansa, cikin murya mai nuna tsananin karsashi da alwashi yace, “kisamin albarka inno, zanje farautane”.
Da sauri ta janye hannunta daga kansa tana matsawa baya, “Muhammad mikake nufine? kana ganin tashin hankalin da muke ciki
shine zaka k'irk'iro mana wani kuma? kana tunanin wad'annan mutanen zasu barkane? dama kai suke fako, shiyyasa sukayi tarko da bayin ALLAHn dabasu ji ba basu gani ba, su takawa cikin k'ok'arin d'aukar mataki suke, yanzu haka naga IG da kansa gashican ya i
so bisa umarnin kiransu”.
Galadima dake tattara abinda zai amfani dashi yana zubawa a aljihu, yace, “inno Muhammad Sameer d'inku ba ragon namiji bane da zai zauna jiran Police d'in da suka gaza gano wad'anda suka durk'usar masa da mahaifi tsawon shek
aru a yanzu kuma nayi tunanin zasu iya dawomin da gudan jinina har uku, ba sune sukamin tarko ba nine namusu tarko, idan tsoron na mutu kuke, Ku cire inno, ko babusu mutuwa tabbataccen abune rubutacce a kundina, kimin addu'a saina saina dawo”..
B
iyosa inno tayi har babban falo tana Kiransa amma yak'i dakatawa, saima d'aga mata hannu da yakeyi, yana gab da zai fita ya juyo yana fad'in “karki d'aga murya da yawa ranki ya dad'e, dan kunnen magauta a bud'e yake”.
Yana fitowa Sarkin mota y
a taso, dan suna zaune jigum-jigum a rumfar bunun dake sashen na Galadima, duk gaisuwar da suke masa babu ta wacce ya amsa, yau kam ko d'aga hannun basu samuba ma.
Basu damuba dan dolene kowa yamasa uziri.
Da kansa ya bud'e mota ya shiga mazaunin
driver, Sarkin mota daya k'araso yace, “ranka ya dad'e ka gafarceni gani”.
Da hannu yamasa nuni da gefen mai zaman banza batareda yace uffan ba.
Sarkin mota bashida za6in daya wuce zagayowa ya shiga.
A 360 Galadima ya ja motar, kamar
ma ya manta yana cikin masarautane, saida suka fito gaba d'aya sannan ya bud'e baki da k'yar yace, “ka dinga kallon bayanmu, dan nasan dole za'a samu masu binmu”.
Da “to” sarkin mota ya amsa cike da girmamawa.
Sarkin mota yace, “tabbas rank
a ya dad'e ana binmu”.
Cije lips Galadima yayi, ya canja hanya, cikin salon iya taku suka 6acema su Harun dake bin su tundaga masarauta.
Hankalin Harun ya tashi kwarai da gaske, dan bai shirya fito na fito da Galadima ba yanzu, saiya cimma bu
rinsa, daga nan komai ta fanjama fanjam, iya zagaye-zagayensu baiga ko motar datai kama data Galadima ba.
Shima yana 6ace musu ya dawo kan titi sosai, Maps d'in GPS ne yazama jagoran Nuna masa hanya, da taimakon Sarkin mota kuma dayasan gari. Dansh
i Galadima ba tuk'i yakeba idan yazo 9ja, saidai idan ta kama tilas babu yanda zaiyi kamar irin haka.
Sunyi tafiya mai tsawo, yayinda yake Communication dasu Nuren dasu Saleem. A haka ya iso inda suke, duk fitowa sukayi daga motocin, shima Galadima
ya fito, idonsa akan agogon hannunsa, yad'an kallesu sannan ya koma kan waya yana fad'in, “maps d'in ya nuna suna a wajennan, kunga kenan tsakanin gidajennan guda hud'une dake kallon juna?”.
“kwarai da gaske suna nan”. cewar Muftahu yana furza
r da iska.
Galadima yace, “Sauban da Saleem zaku cigaba da Control namu”. ‘yay maganar yana ciro agogon hannunsa ya mik'a musu, “ga wannan kuci gaba da using dashi”.
Suka amsa da “to” suna kar6a. ya mak'ala abinda zai taimaka masa yaji m
agana, suma su Nuren duk yabasu suka saka.
Har zasu bar wajen ya dakatar dasu ta hanyar d'aga musu hannu, takawa yay gaban k'ofar gidan farko ya haska gaban gate d'in da fitilar wayarsa, babu abinda yake nema, ya matsa na biyu ma haka, komawa y
ay d'ayan 6angaren, yana haskawa saiga sawun tayar mota data shiga gidan, duk'awa yay ya d'iba k'asar wajen ya shinshina, ya d'ago ido ya kalli gidan yana jizar lips, saiya zubar da k'asar daya d'iba ya mik'e, da hannu yayma Nuren da Muftahu nuni nan ne.
Tahowa sukai garesa, Aunty Salamah datun d'azun suna daga cikin mota suna kallonsu suma suka fito ita da su Ameer.
A tare suka rissina suna gaida Galadima ya amsa yana bin su da kallon mamaki.