Showing 33001 words to 36000 words out of 304903 words
ko'ina da kallo har ya shigo bangaren mahaifiyarsa.
A falo ya tararda yaransa
, Iya na zaune kusa da su tana musu wasa sai dai gaba dayansu wani laye suke kamar basu jin bachi.
“Babban Mutum an shigo?”
Iya ta fada baki har kunne.
“Eh Iya ya gidan?”
Ya amsa mata yana leka yaransa.
“Gashi nan fa sun sha ado, yanzu na g
ama gyara dakinsu”
Da mamaki ya kalleta.
“Mai gyaran bata zo ba ne?”
Iya ta tabe baki tana mikewa tsaye.
“Wannan yarinyar, bata zo ba, wata kila sai gobe ko jibi”
Shattima be ce komai ba, but maybe dan ta kamata tana yi ma yaransa addu'a n
e yasa ta ji tsoro ta ki dawowa.
“Karka damu ba dole sai an kawo wata ba, ni kaina zan iya kula da su da dakinsu”
Dan murmushi yai.
“Haba Iya ai ba girmanki ba ne, idan bata dawo ba dai za mu samu wata”
Iya ta yi murmushi tana kallonsa.
“
Haka ne Allah ya taimaka, bari na maida su dakinsu”
“Amman a samo wacce zata tsaya da su bana son a na barinsu su kadai”
“An gama Babban Mutum”
Ta amsa masa har da dan risinawa, shi kuma ya wuce dakin mahaifiyarsa. Kwance ya same ta waya a hannun
ta tana latsawa, sai da ya zauna sannan ya mika mata gaisuwa. Sai ta dago ta kalleshi.
“Lafiya Kalau Shattima”
“Ammy ina tunanin gobe zan koma”
Bata ce masa komai a har na tsawon minti uku. Hakan yasa ya sake cewa.
“Amman ba zan yi dadewar wa
can lokacin ba zan dawo”
“Ya dai kamata ka nemi transfer gaskiya, ka fi kowa sanin halin da mahaifinka yake ciki”
Kwankwaso kofar dakin da akai ne ya hana shi cewa komai, be kuma dago ta kalli kofar ba, sanin wanda ya shigo dakin ba bayan Ammy ta ba
shi umarni, kamshin turaren kadai ya isa ya sanar nasa cewer Sirleem ne domin ya san kalar turarensa kamar yadda Sirleem din ma ya san na Shattima. A kasa ya zauna yana mikawa Ammy gaisuwa sai ta amsa masa da murmushi tana kokarin tashi daga kwancen da tak
e.
“Ya gida ya aiki?”
“Alhamdulillah, dazu Hajiya ke Fada min Nana ta samu accident”
“Eh amman da sauki sosai”
“Allah ya tsare gaba”
“Amin”
After some minutes ya mike tsaye yana mata sallama.
“Shattima ba ku gaisa ba”
Daga shi har
Shattiman ba su dadin maganar Hajiya ba. Domin kowa jin kansa yake ba ma kamar Shattima, ko da wasa Shattima be dago ya kalli Hajiya ba gudun kar ta masa umarni da ido cewar ya gaisa da Sirleem domin shi ya cancanci Sirleem ya gaushe shi ko dan neman auren
kanwarsa da yake. Sirleem ya kasara inda Shattima yake zaune ya mika masa hannu sanin cewar idan za a shekara dari a haka Shattima ba zai ce masa uffan ba.
“Shattiman ai ban kura da kai ba sai yanzu”
Sirleem ya fada yana mika masa hannu. Hannun kaw
ai Shattima ya mika masa suka gaisa ba tare da ya kalli Sirleem ba balle har wata kalma ta fito daga bakin Shattima. Sai da Sirleem ya nufi kofa sannan Shattima ya daga kai ya kalleshi, sai kuma ya dauke kai ya kalli mahaifiyarsa wace ke kallonsa tun lokac
in da Sirleem ya mika masa hannun.
Sam Sirleem be jidadin abunda Shattima yai masa ba, ya sani ba tun yau Shattima ya saba nuna masa cewar shi ne dan masu gida shi kuma agola, ba shi kadai ba har Zainab wacce kusan matsayinsu daya da shi haka take nuna
masa isa tana takama.
Kamin ya karasa fita falon Nana ta kira shi.
“Ya Sirleem”
Juyowa yai ya kalleta be ce komai ba, sai da ta kalli kofar corridor dakin Ammy sannan ta karaso inda yake.
“Ya jikin na ki?”
“Na ji sauki, Ya Sirleem ban kar
ya ba”
“Why?”
Ya tambaya cike da mamaki ganin har 5pm ta kusa ace bata karya ba. Sai da ta sake kallon corridor sannan ta ce.
“Dan Allah zaka kai ni restaurant na ci abinci? Amman karka tambayi Ammy?”
Ya kalli inda take kallo sai kuma ya kalle
ta kamar ya musa mata sai kuma wata zuciyar ta hana shi.
“Alright muje”
“Kaje can bangarenku ka jira ni, bari na dauko mayafina”
Har ta juya sai ya kira ta ta juyo.
“Nana... An hana ki fita da ni ne ko me?”
“Zan fada maka a mota kaje can ka
jira ni”
Bata tsaya jiran abunda zai ce ba ta koma dakin ta dauko kudin da Hajiya ta bata 20k ta saka a cikin skirt dinta sannan ta saka wani karamin veil ta fito da gudu kamar ba ita ce ke ciwon kafa ba. Kamar wacce tai wani kaifi take tsoron a ji hak
a ta sauka stairs din ta nufi bangarensu Hajiya gabanta sai faduwa yake kar tai arba da Shattima ko Zainab ko wani wanda zai fadawa Ammy ta fita tare da Sirleem.
Can bangaren Hajiya ta nufa sai dai bata shiga ciki ba ta nufi gurin da motocin gidan suke
, tun kan ta karasa ya bude mata front seat tana shiga ta rufe motar da sauri.
“X&Y restaurant za mu je, kuma ba fita za ka yi ba, ni zanje nai mana takeaway Please”
Jinginar da kansa yai jikin motar yana kallonta. Can kuma ya tashi motar suka fara
tafiya.
“Waya hana ki fita da ni hala?”
“Babu”
Da bashi amsa tana taba kudin da ta boye jikinta dan ta tabbatar idan suna nan.
*
🐄🐄
FULANI
🐄🐄
*
By Khadeeja Candy
*9*
Har suka isa be ce mata komai ba ita ba ce masa ba. Haka yake a
duk lokacin da suka hadu sai ya rasa abunda zai ce mata, na daya dai yana ganinta yarinya kuma yana ganin kamar akwai kurciya a cikinta sosai wanda be dace ya fara firan soyayyah da ita ba, na biyu kuma baya jin yana mata son da ya wuce na gida daya wanda
kusan sun zama yan'uwan juna. Ya rasa yadda zai yi Hajiya ta fahimce shi ya rasa da wane baki zai mata magana ta fahimci yarensa, idan ma bata son Mansura zai iya hakura da ita ya auri wata amman why Nana? Why? Har yanzu ya rasa dalilin Hajiya na son ya a
uri Nana.
Yana fakin ya bude inda yake ajiyar kudi a mota ta dauko 5k ya mika mata, sai ta bude motar da sauri ta fita.
“Ka jira ni a nan”
Shi dai kallonta kawai yai, daman can ya dade da ayyanawa a ransa Nana bata da hankali kamar sauran mutane
wata kila kuma gata ne yai mata yawa. Jinginar da kansa yai jikin kujerar motar ya ciro wayarsa ya kamo hoton Mansura yana kallo.
Murmushi yai yana yinta sosai musamman idan ya tuna irin yadda suke mu'alama da kuma yadda take son shige masa jiki, yadda t
ake yabon daukakarsa da kyausa, gashi ta iya drees tana son duk wani abu da yake so, tana gudun bacin ransa, idan wani abun ya same shi hankalinta zai tashi sosai, duk inda yake tana nan manne da shi, wannan dalilin yasa mutane da yawa suka san alakarsu, k
asancewar fitattacen mawaki kuma mai tashe duk wani motsi nasa yan media da yan jaridu sun saka masa ido.
Cikin jindadi Nana ta shiga cikin restaurant din, kai tsaye ta wuce reception sai rabon ido take ko zata ga AA. Tsaye tai tana a gurin ta rasa abu
n da zata ce.
“Hajiya me kike so?”
“Wannan yaron nake nema, wani yaro fari dogo ba sosai ba be da jiki ana mishi lakani da Sardauna”
“Okay kwana biyu be zo ba, ya samu hadari ne ”
Ta dan yi shiru kamin ta sake kallon mai bata amsar ta ce.
“Dan Allah kana da number shi ka kira shi?”
“Okay”
“Yauwa Thank You”
A take ya ciro wayarsa yai dialing number AA ba da wani dade tana ringing ba yai picking.
“Hello Jafar”
“Sardauna wata yarinya ce ta zo nemanka yanzu”
Saurdauna ya tsay
a daga tafiyar da yake yana mamaki gabansa kuma na mugun faduwa.
“Wata yarinya? Wacece?”
Jafar ya mika mata wayar.
“Hello”
Yana jin muryarta ya gane ta.
“Nana”
“Na'am na zo baka nan, kana ina ne?”
“Miyasa kika tambaya? Kama ni za ay
i?”
“A a ba abunda za a maka, kawai na zo na ji ya jikinka ne, kuma na kawo maka kudi”
“Kudi....”
Dan murmushi yai sai yaji wani karfi da kuzari suna ratsarsa, sai dai tunawa da wani abu yasa tsoro ya kama shi, what if plan ne?
“Nana bana kusa
na je Kano, amman idan da gaske kike ki bawa Jafar kudin ya saka min a account”
“To amman yaushe zaka dawo?”
“Sai next week”
“To zan karbi number ka na kira ka da wayar Hajiya Karama ko wata”
“A a ban yarda ba”
Ji yake kamar zata yi amfanin
da number na sa ne a gano shi.
“To ka dawo da wuri ka ji”
“To”
“Zan aje wayar kuma zan bashi kudi ya saka maka a account 20k ne”
“Na gode”
Ya mikawa Jafar wayar.
“Jafar zata baka 20 ka saka min account 18k sai ka dauki 2k din”
“Ok ba
matsala na gode”
Ta ciro kudin a cikin skirt dinta ta mika masa, sannan ta ba shi 5k din hannunta.
“Ka saka mishi wannan, wannan ka hada min takeaway ka dauki canjin”
Da mamaki ya karbi kudin ta dayan bangaren kuma yana jindadin canjin da tace y
a dauka. Cikin sauri ya hada mata komai jalof da naman kaza da lemu da ruwa ya saka mata a leda ya mika mata.
“Please ka ce ya dawo soon ka ji?”
“To zan fada masa na gode Allah ya tsare”
Kai ta gyada masa ta fice cikin rashin jindadin ganin AA da
ba tai ba. Sirleem na zaune cikin motar yana jiranta har ta iso ta bude motar ta shiga. Gaba jin tai kamar ta fasa kuka, yana ganinta ya san yanayinta ya canja gashi ta dade a ciki, sai dai be damu ya tambaye ta yai reverse suka dauki hanyar gida.
Da
farko AA yai nufi zuwa restaurant din daga can ya tambayi ko ta zo nemansa, sai dai ganin kiranta da wayar abokinsa yasa ya fasa zuwa kuma ya ji duk be da natsuwa, hakan yasa na koma gida jikinsa na ta fada masa plan aka shirya masa wata kila ma za a fara
bibiyar line.
Sai da Jafar ya tashi daga aikin sannan ya bawa mai POS din daje kusa da restaurant din ya saka ma AA 18k a account dinsa, AA na zaune yana wanki trouser dinsa wayarsa tai kara ta sauri ya dauka ya duba dan tun dazun yake jiran yaji kudin id
an har da gaske ne zai ga kudin, idan kuma plan ne zai gane. Ganin kudin yasa shi murmushi a dubiya be da abun so kamar kudi, ko da Plan ne ake hada masa tun da kudin sun shigo shi be da matsala. Wani irin farinciki ne ya baibaiye shi kamar an masa albishi
r da gafara. Yana son ya kira Jafar din yai masa tambayoyi kuma tana jin tsoron kar ya kira a bibiyi line sa.
Kamar yadda suka zo dazu, haka ma gurin komawa babu wanda yace da wani uffan, Nana gaba daya mood dinta ya canja titi kawai take kallo, Sirlee
m kuma driving yake yana ta tunanin yadda zai kwashe da Mansura idan Hajiya ta hana shi aurenta, bayan irin alkawarin da yai mata. Yana ji a jikinsa Hajiya ba zata yarda ya aureta ba ko da bayan ya auri Nana saboda ta tsani Mansura sosai.
After yayi park
ing Nana ta bude motar ta fita, Bangaren Hajiya ta nufa ta shiga har cikin falon ta bata yi magana da kowa ba ta bude takeaway ta fara ci. Su ma yayyenta kuma kanen Sirleem babu wanda yace da ita komai tun da suka kalleta suka dauke kai ba su sake kallon i
nda take ba sai da Sirleem ya shigo. Yana kallon Nana ya dauke kai ya nufi corridor da zai sada shi da bangaren Hajiya.
“Bana son duk wani abu da za ace sai an ci, kin san yanzu wani babban aiki ne na ce zan shirya wani abu kuma na basu shi ya ci, ade s
amu samu wata hanyar, ki mayar masa da abunsa, ke fada masa yai masa wani abun da zai iya samunsa a can inda yake ba wai sai ya ci ba”
“To za ayi haka ranki ya dade, to shi na Mai Martaba fa?”
“Shi be da matsala zan iya dafa wani abun ya saka masa”
“To Hajiya, amman Hajiya zai na ke ganin kamar Talba be da farin jini a masautar nan kamar yadda Shattima yake da shi, anya ba sai an tashi tsaye ba?”
Hajiya ta yi murmushi tana kallon Talatu har na tsawon mintuna biyar sannan ta ce.
“Shattima ne
ya hana shi tashe, ssboda Shattima ne babba shiyasa komai shi ake wakiltawa, kuma kin san mahaifiyarsa ba zata bar shi haka nan ba, da shi da duk son da Mai Martaba yake musu ai bana banza bane har ita uwar ta su, ba jin maganar kowa sai tasa komai sai ita
, shiyasa na ke son nuna mata wannan karon bokanta sai ta yi kuka da hawayenta, mulkin mallakar da tai min a baya ba zai yiyu ba a yanzu, tana ji tana gani Sirleem zai auri danta Talba kuma ya hau sarautar na bayan na ta yaran sun lalace komai ya koma kark
ashin iko na”
Hajiya Talatu ta daga kai.
“Lallai kam, na san Jarma da Ammy sun fi kowa farinciki da ciwon Mai Martaba, saboda ita tana ganin danta za a dora Jarma kuma yana ganin shi zai gaji kujerar babansu kuma kujerar dan'uwansa”
Hajiya ta y
i murmushi.
“Sun wuni da shiri mu kuma mun kwana da shi.... ”
Kwankwaso kofar dakin da Sirleem yai ne yasa gaba daya hankalinsu ya koma can, Hajiya ta jefawa Hajiya Talatu kullin hannunta ta gyara zamanta. Talatu kuma ta saka komai a jakarta sannan
Hajiya ta ce.
“Waye?”
“Ni ne”
Sirleem ya amsa cike da mamakin rufe kofar da Hajiya tai, abunda be taba gani ba indai tana cikin dakin bata rufewa sai idan fita za tai. Hajiya Talatu ta mike tsaye ta murda makulli ta bude masa kofar.
Why dan ma
haifiyarsa za tai magana da Matar kanen mijinta, sai ta rufe kofar? Dan tsayawa yai kallon Talatu kamin ya shigo cikin dakin, ya nufi inda mahaifiyarsa take ya zauna kasa.
“Ya akai?”
Ta tambaya kamar ba ta jidadin shigowarsa ba, shi ma dai ba zai iy
a fadar abunda ya kawo shi ba kawai ya shigo ne.
“Na je na gaishe da Nana”
“That's good, Allah yai maka albarka, ina jindadin yadda kake bin umarnina Sirleem, zan fi kowa farinciki idan ka auri Nana kuma ka gama cika min burina”
Be ce komai ba ya
mike tsaye yana satar kallon Hajiya Talatu ya fice daga dakinta Hajiya Talatu tana shi masa albarka.
“Ai Sirleem akwai biyayya Allah dai yai albarka”
Sai ya fice ya rufo dakin sannan Hajiya Talatu ta dawo kusa da Hajiya Babba tana fadin.
“Wai y
anzu ya daina maganar Mansurar ne?”
Da sauri Hajiya ta daga mata hannu alamar tai shiru tana kallon kofar, sannan tai mata alama da ta dauki jakarta ta fice. Kai Hajiya Talatu ta gyada ta dauki jakarta tana mata sallama.
“To Ranki ya dade zan wuce s
ai kuma wani lokacin”
“To Talatu na gode na ziyara”
Hajiya ta amsa mata tana murmushi sannan Talatu ta fice daga dakin.
SHATTIMA POV.
After Sirleem ya fice Ammy ta ce.
“Tun daga lokacin da Sirleem ya nuna yana son Nana sai ka yanke
alaka da shi, duk wani shiri da kuke sai ka maida shi gefe ka aje”
“Ammy ai yanzu ni surikinsa ne ko? Ya kamata na yi respecting kaina shine kawai”
Kallonsa kawai Ammy take, sai yai murmushi kadan ya shafa kansa.
“Tsakani da Allah Mama bana son Na
na ta auri mutunen nan, not because yana mawaki, har da mahaifiyarsa kin fi kowa sanin yadda ta tsane mu a can baya then why yanzu zata bar danta ya auri Nana? A yadda na lura kamar shi kansa Sirleem din baya son auren”
“Bana tunanin Hajiya Balki zata c
ilasta Sirleem ya zo Nana? To akan wane dalili? Miyasa za tai haka? Kamin yanzu Sirleem da Nana suna shiri sosai wata kila hakan ne yasa soyayya ta shiga tsakaninsu, yanzu kuma ka kore mata kunne ta fara cewa bata son shi bayan a gaban kowa ta ce shi take
so”
“Nana bata da wayon sanin irin mijin da ya kamata ta aura”
“Ya kake so na yi Shattima? Na ce ba za ayi auren ba? So kake a fara cewa ina jindadin ciwon Mai Martaba ne? Daman can ana fadar ni nake mulkin masauratar nan so kake hakan ya tabbata?”
Wani dogon numfashi yaja ya sauke a hankali. Ya kasa cewa komai.
“Kai ma ya kamata ka fara tunanin aure yanzu”
“Akwai wacce zata so ne Ammy?”
“Akwai da yawa, kuma zaka samu In-Sha-Allah, mun yi magana da Waziri, yace kamata yai aje can wata uwa
duniyar a dauko samo wata matar ko yar ruga ce”
“Karka a cuci yar mutane kamin a aura mata ni a barta ta san ko kaddarata dan Allah”
Ammy bata ce masa komai ba, shi ma din be shirya yin wata maganar ba hakan yasa ya mike tsaye ya fice daga