Showing 69001 words to 72000 words out of 304903 words

Chapter 24 - FULANI COMPLETE

dan jin take kamar Tumba zata biyota har nan ne ko Baba.

Matar ta zuba mata shimkafar da bata wuce loma biyar ba a leda ta saka mata miya.

“To samin ta duka”

Ta fada dan ta san ta darin ba isarta zata tai ba tun da ta wuni da yunwa kuma ta kwana da ita. Da sauri ta kai hannu ta karba ta sake ciro dari biyu ta mika mata.

“Ba ni ruwa mai sanyi na daya”

Matar ta karba ta cire kudinta ta mika mata ruwan da c

anjinta, Falmata ta juyo da sauri ta baro wajen, a lokacin data dawo cikin motar sai ta saka cin abincin saboda kunya, duk kuwa da ta lura da wasu matan da maza suna ci amman ita ta kasa ci saboda bata saba ba. Sake fita tai ta koma can bayan masallacin da

ke tashar inda babu mutane ta zauna ta bude ledar shimkafar ta fara ci hannu baka hannu kwarya kamar wacce ta shekara bata ga abinci ba. Ko rabin shimkafar ba tai ba sai ji ta koshi saboda tsoro da kuma daurewar da cikinta yai, sai kawai ta sha ruwa ta kul

le sauran a leda ta boye a hijab ta dawo cikin motar ta zauna.

Ba a jima ba aka samu wani passenger ya shigo. Basu bata lokaci ba driver ya shiga suka dauki hanyar gidan mai, sai ta ya sha mai sannan suka kama hanyar Kaduna.

Duk tafiyar da ake da fir

ar da wasu ke yi Falmata na cikin motar ta yi zugum tana tunani, idan ta je Kaduna ina zata sauka? Wa zai karbe ta? Ina zata kwana? A lokacin ne ta soma jin kamar tace wa Direban ya juya da motar su koma gida, idan kuma ta koma gidan wahalar ce zata sake s

ha, kuma ta riga da taba kudin Tumba idan ta koma ma me zata ce mata?

Wasu na bachi su farka su cigaba da fira ko kallon titi ko taba waya ban da Falmata dake ta aikin zubar da hawaye a cikin hijabin da ta boye kanta.

Bata gasgata ta bar garin yola ba

har sai da ta soma jin wani yanayi na dabam yana rabarta, duk tsayawar da direban yake yai sallah Falmata bata daga kai ta kalli kowa ba, dan bata son a gane kuka take.



Kamin su shiga cikin garin Kaduna direban ya fara kiran mutane yana sanar da su ga

sakonsu ya shigo da su su zo su zo su karba, a lokacin ne hawayen Falmata suka kara yawa ta soma jin kamar zazzabi na sauko mata. Bata kara tausayin kanta ba sai da diraban ya isa cikin tasha, mutane dake motar suka fara fita suna yi ma Allah godiya na sa

uka lafiya da su kai, sai da kowa ya fice sannan ta fito daga cikin motar yana jin wani yanayi na dabam. Inda ta ga mutane na fita ta nufa tana tafe tana sharar hawaye tana nishi kamar wata mai ciki sakamon nauyin da zuciyarta tai mata. Haka ta fito cikin

tashar dunkule da hannu a hijab kana kallonta ka ga marar galihu, ga fuskarta da kwancin bulala idonta daya kuma ya kankance ya bar dayan, Hijabinta a kode kamar dai tufafin da ke jikinta.

Tafiya ta fara yi tana kallon kasa hawaye na ta zubar mata kamar

dan kukan kawai aka yi ta, ina zata je? Ga yamma na yi sallam ma ina zata yi? Abinci fa wa zai bata? Kamar daga sama ta ji an dafata.

“Ke....”

A firgice ta juyo ta kalli matar wacce ke sanye da doguwar rigar atamfa, sai dan karamin gyalen da ya bay

yana gashin dokin da ke kanta.

“Ina magana ba ki ji ba lafiya kike kuka?”

A nan din ma bata ji komai ba sai dai ta san magana take mata tun d har ta taba gashi kuma bakinta na motsi kamar yadda idon matar ke sanar ita saboda irin kallon da take mata

.

“Bana ji sosai ai an daga murya ko an yi kusa da kunnena”

Falmata ta amsa mata tana kokarin fashewa da kuka. Kallon tausayi matar wacce tafi kama da budurwa take soma mata, kamin ta matsa kusa da ita ta rada mata a kunne.

“Me kike yi wa kuka?”

A nan Falmata tai shiru kamar ba zata amsa ta ba, hawayen kuma ya cigaba da sauko mata.

“Ban san kowa ba a nan, ban san inda zanje ba”

“Daga ina kike?”

“Yola”

Murmushin budurwar tai.

“Allah sarki garin masoyina”

Ta fada da sigar da i

ta kadai zata iya jin kanta sannan ta sake kai bakinta a kunnen Falmata.

“Me kika zo yi nan?”

“Komai, kawai gudowa nai daga gida”

A lokacin ne ta fara mata kallon mamaki.

“Au.... Okay...”

Sai kuma ta sake kai bakinta kunnen Falmata.

“Miya

sa?”

Falmata tai shiru tana murzar ledar da ke hannunta wacce ta boye a cikin hijabinta.

“Za ki iya bina muje gidana zan sauke ki a can sai na baki abinci da gurin bachi”

Da sauri Falmata ta daga kai, daman abun da take nema kenan kayanta ya tsin

ke a gindin kaba, ko da yar yankan kai ce ita zata iya binta. Hannu budurwar ta dagawa wata jar mota dake nesa da su kadan alamar mai jan motar ya karaso, kamar daman can umarni yake jira sai gashi a kusa da su in few seconds.

Da kanta ta budewa Falmat

a gidan baya, ita kuma ta bude gidan gaba ta shiga ta saurayin yaja motar mai cike da sanyin ac da hannu daya dayan hannunaa kuma rike da wayarsa.

“Tun a tasha kike bin yarinyar nan”

Ya fada ba tare da ya kalleta ba, sai ta dan kalleshi kadan tana d

aukar lemun gwangwanin dake gefenta ta sha.

“No ai ina ganinta na gane tana ciki damuwa, kuma tana tafe tana kuka, you know idan na ga mutum a irin yanayin na ina son taimakonsa saboda ni na san wahalar da na sha”

Ta fada tana sauke ajiyar zuciya ka

min ta cikawa bakinta iska ta busar, sai ta dan juya ta kalli Falmata da kanta ke sunkuye sannan ta kalli wayarta da ke ringing.

“Kina picking call din nan zamu samu matsala da ke, idan ya jira ki jiki na rawa ki dauka”

Saurayin ya fada yana kallon

wayar cike da fusata. Murmushi kawai tai ta cigaba da kallon wayar tana jin kamar tai picking din.

HAJIYA BABBA POV.

“Talba wai baka sha'awar yadda mahaifinka yake milkin garin nan ne? Baka lura da yadda mutane suke ba shi girma ba, a duk lok

acin da ya so ganin governor zai ganshi a take, idan ya so ganin shugaban kasa ma zai kira waya a fada masa ya same shi su gana, baka lura da irin arzikin da mahaifinka ya tara ba, baka lura da yadda yake juya duk wanda yake so ba? A sanadinsa kuka zama ab

un da ku ka zama a yau, da isarsa da kudinsa kuke yadda kuke so duk wannan abun be taba burge ka ba”

Talba yayi shiru yana nazarin kalamanta.

“Shin baka taba son ka saka mahaifiyarka a cikin farinciki ba? Baka taba jin cewar ya kamata ka gaji mahaif

inka ba?”

“Hajiya ba zan iya gadon Mai Martaba ba, tun da Shattima da Baba Waziri da Baba Jarma da mutane da yawa suna raye”

Hajiya ta yi murmushi tana dauke kai daga barin kallon dan nata.

“Ai Shattima da duk wani da kake gani ba komai ba ne, ma

tukar zaka saka son abun a ranka kuma ya cusa kanka komai na gidan nan, kai baka lura da yadda Shattima yake ba, Ammy ta nuna masa cewar Mai Martaba na mutuwa shi za a dora, shiyasa yake ta shiga yana fita ana komai da kai, kai kuma sun maida ka can gefe b

abu wanda ya sanka, shi Shattima ba kula da kanen mahaifinsa ba ne? Talba na dade da sanin cewar ciwon Mai Martaba har da sa hannun Ammy saboda Shattima ga samu sarautar”

A firgice Talba ta mike tsaye yana yi ma Hajiya Balki wani irin razanenen kallo.

“Ammy fa kika ce Hajiya”

Hajiya ta kalleshi.

“Baka lura da yadda take mulkar gidan nan ba ita da danta? Tun kamin yau ai kasan yadda ni da ku ta maida mu bayi, Mai Martaba baya jin maganar kowa sai nata, yanzu kuma da ya kwanta ciwo a gidan nan b

ata jin maganar kowa sai nata da na danta, Shattima ya taba kiranka a matsayinsa na yayan uba daya yace kuje wani guri ko ka yi wani abun a matsayinka na jinin Mai Martaba?”

Talba yayi shiru yana nazarin kalaman Hajiya, tabbas biri yayi kama da mutum.

“Zauna mana”

Ya zauna kamar yadda ta bukata.

“A karatu ma Shattima American yai nasa, kai fa ta bari a an kai ka ne? Ga Karima nan babu yadda bata so barin kasar nan taje Karatu ba, amman Ammy ta hana Mai Martaba, sai Jurry aka kai da Salima”

Talba yaja wani dogon numfashi ya sauke, ya dade da kiyayyar Ammy a ransa amman ba irin na yau ba, domin be taba lura da wannan ba sai a yanzu da Hajiya ta fada masa abun da ya kasa fahimta shekaru da dama.

Hajiya ta kai dubanta a gurin wayarta da kira

n Jarma ke shigowa.

“Dauko min wayata”

Talba ya tashi yaje ya dauko mata ya mika mata, sai da ta dan kalleshi sannan taj picking call din.

“Hajiya ke kadai kike? Gani nan zuwa yanzu”

“Sai ka shigo”

Ta amsa masa tana murmushi, sannan ta aje

wayar.

“Shiyasa nake son kai da Sirleem ku hada kai ku taya ni wannan yakin, ba ni da burin da ya wuce na ga ka hau Sarautar nan Talba”

“Ni”

Ya nuna kansa yana jin wani irin abu na ratsa shi na isa da kwadayin Sarautar.

“Kai mana, Uwa kawai k

uka hada da Sirleem da ace mahaifinka ne ya haife shi, da shi ya kamata mu marawa baya ya samu sarautar nan, amman kai ne jinin Mai Martaba kai ya kamata ka hau Sarautar nan Talba, ka samu Sirleem ku tattauna akan maganar nan ka nuna masa illar abun da Amm

y take mana, amman karka nuna masa ni na fada maka, domin ba zai fahimta ba”

“Sirleem ina jin baya nan yace min zai je Kaduna”

Da sauri Hajiya ta kalleshi.

“Yaushe?”

“Be fada min ba ban san ko ya tafi ba, maybe kuma yana nan tun da be fada mik

i ba”

“Ai ba zai fada min ba tun da zai je gurin wacan yar'iskar karuwar, amman zai dawo ya same ni”

Ba kalamanta kadai suke bayyana bacin ranta ba har da fuskarta da numfashinta.

“Tashi kaje Jarma zai shigo yanzu ”

Ta fada ba tare da kalleshi

ba. Shi kuma ya mike tsaye cike da tunani kala kala a ransa ya fice.

*FULANI -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence to 08036126660 ƴan nijar za ku tura 500cf to +22790165991*

18

*Littafin nan na kudi n

e biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

Tana cikin bukkarta Hajjo ta leko tai mata ya jiki, daker ta amsa mata da sauki kamar ita taja mata akai mata dukan, Amo ma dake ta ma

maki ta leko.

“Fulani ya jiki?”

“Na ji sauki”

Sai da ta kare mata kallo sannan ta juya ta fita, cikin jin haushi Fadime ta fito daga dakin ta zauna a waje, Inna ta dauko koko ta kawo mata ta saka mata ludayi.

“Ki sha yana da zafi”

Kallon ko

kon kawai tai ta dauke kai tana ta jin haushin dukan da akai mata, gaba daya yanzu laifin Wasim take gani domin shi yaja mata koma minene.

‘Ai ban ce yai min a lokacin ba, amman wai yai min mugunta’

Ta fada a ranta, a fili kuma sai tai kwafa har sai

da Inna ta juyo da tsoro ta kalleta, domin yanzu tsoronta take ji ganin abunda ya faru jiya. Mikewa tai tsaye ta karasa gurin Inna tana dan murmushi kamar ba ita ba.

“Inna yaushe shi mutumen zai zo?”

“Wane mutume?”

“Shi mana”

Ta rufe ido tana

dariya wai ita kunya. Inna ta tabe baki, ta wani bangaren bata ganin laifin Fadime, tun da ba a taba cewa ana son ta ba ba a taba sallama mata ba da sunan fira ba dole kuwa idan ta ji ana sonta ta jidadi.

“Ban sani ba”

“Inna in be zo ba ni a kai ni

to, kin san su mutane birni basa zuwa kauye ko saboda irin hanyar nan, kin ga tun da na iya boko shikenan sai mu yi ta magana da turanci zai ji na burge shi”

Ta fada tana ji wani irin dadi a ranta, jiya har mafarkinsa tai, ta ganshi wani mummuna amman b

ata ji komai ba saboda neman mijin kawai take ita dai burinta ta ga miji. Jin Inna ta mata shiru yasa ta tashi ta koma inda take ta zauna tana kallon yadda Inna ke raba kokon da ta dama.

‘Ni ma idan na yi aure haka zan yi, sai na yi girki nai komai irin

na mata, kuma na haihu ni ma’

Ta saka a ranta tana shafa cikinta murmushi ya wanke fuskarta. Mikewa tai tsaye ta nufi gurin ruwa ta dauko wani tulun.

“Ina zaki je?”

“Ruwa zan debo”

“Aa ba yanzu ba, jiya jiya kika je kika kwashe aiki yanzu kum

a kice zaki je, a a ban yarda ba, waya sani ko gulbin ne ke da aljanunn”

Amo dake cikin daki ta fito tana amsawa Inna.

“Lallai kam indan ruwa bari Hajjo ta debo sai ta cika mana gidan”

Ba dan ranta ya so ba ta aje tulu ta koma ta zauna ta fara mo

tsa kokon tana ta tunanin abun da zata yi ta fita. Bata sha rabin kokon ba sai ga Ma'u ta shigo gidan bakinta har rawa yake sai dai gani Inna yasa tai shiru bata ce komai ba bayan gaishe da ita da tai sai kuma ya jikin da tai mata. Can dai Ma'u ta tashi ta

na kyafta ma Fadime ido.

“Na tafi Fulani Allah kara sauke”

Sai Fadime ta mike tsaye tana satar kallon Inna.

“To bari na rakaki”

Har sauri saurin take ta riga Ma'u fita daga gidan. Suna fitowa Ma'u taja ta gafe

“Fulani Wallahi naje na fada

wa Inna Bubakar kin ce mijinta zai kara aure nan da kwana biyu”

Fadime ta zaro ido.

“Miyasa kika fada ba nace miki sirri ba ne”

“Dan dan ta tabbatar idan da gaske ne kuma ni na tabbatar, yanzu ta aiko tace a kira ki”

“Wallahi ba zan je ba, dan

ta karyata ta ni ko? Ko taja Bappa yai min duka”

“Ba duka zata ja miki ba, kika san ko kudin zata baki tace ki fada mata wani abun”

Duk yadda Ma'u ta so taje kiran da Matar take mata sai Fadime ta ki saboda ta san bata da gaskiya, idan aka ce waya f

ada mata dole tace aljannun ne kuma tasan Bappa zai iya dukanta ko ya sake mata wani karatun.

“Ki ce mata anjima zan zo”

Ta juya ta koma ba tare da jira abunda Ma'u zata fada ba. Dawowa tai ta zauna, da an yi sallah sai ta ji gabanta ya fadi dan gani

take kamar matarce zata so ta fadi maganar a gaban Inna. Can dai ta tashi ta shiga daki ta rubuta abunda ya faru jiya tun daga kan yadda su kai da Wasim har zuwa karatun da akai mata da aljanun karya da tai. Ana gama sallah la'asar Fadime ta kwance shanu

wai zata je gurin kiwo.

“Fulani kin san yadda kika yi jiya, ki bar zuwa kiwon nan sai gaba idan kin samu lafiya”

“Ni lafiya ta kalau, idan ina zaune ma sai na ji kamar nai ihu ai kara naje dajin dai”

Duk yadda Inna ta so Han Fadime zuwa kiwo a ya

u abu ya ci tura, dan Fadime tsayawa tai kai da fata akan sai taje ganin Bappa ya tafi gari, ta sani idan shi ne bata isa ta musa masa ba duk kuwa da irin son da yake mata.

Haka ta kora shanun suna gaba taba biye har suka isa cikin daji, a iya alkawarin

da tai a yau ba zata yi magana da Wasim ba, kuma ba zata sake kusantar inda yake ba, duk kuwa da irin burin da take da shi na wani taimako da take son yai mata, kin magana da shi na nuna fushinta ne, ta dayan bangaren kuma tana jin tsoronshi, dan ta san du

k mutunen da zai iya dabon maciji a take ba karamin matsafi ba ne.

A inda ta saba zama ta zauna, tana ayyana cewar ko ta ji busarsa ba zata leka ba, zuciyarta na raya mata dole zai zo inda take. Kamar yadda ta saka haka ta faru tana jin takun mutum a gef

enta ta ki ta daga kai ta kalli gefen dan ita ala dole tana fushi. Murmushi ne mai kama da dariya a fuskarsa, ya zauna kusa da ita yana kallonta, sai ta ki ta juyo balle ta san da mutum a gurin, dauke kai yai yana cigaba da murmushin mai kama da dariya yan

a cin guava dake hannunsa, can kuma ya leko fuskarsa wacce ita ce tafi komai daukar masa hankali a cikin hallitarta, bayan kyau da fari da gashi Fadime bata da wani abu da za a kalleta da shi a ce ana sonta, domin kirjinta da shi da babu duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login