Showing 117001 words to 120000 words out of 304903 words
da kuma lokacin da abun ya fara, after ta yi nata bincike ta kira likitan kunne y
a dubata ya rubuta mata magani, da kanta ta karbi takarda maganin taje ta siyo mata a pharmacy dake asibitin sannan ta dawo office din waya a kunnenta.
“To ka biyo ka sauke min bakuwa a Masarautar su Sirleem”
Tana fadar hakan ta sauke wayar ta mikaw
a Falmata maganin, kamin ta shiga mata bayanin yadda za ta yi amfani da shi. After like thirty minutes Ameer ya shigo Office din, hannunsa rike da makullin mota.
“Tashi kuje shi zai sauke ki gida”
“Tau na gode Allah ya saka da alheri”
“Ameen, dri
ve carefully”
“Okay Mom”
Ya amsata sannan ya juya suka fita tare da Falmata, a tare suka jera har gurin da ya aje motarsa, sai ya shiga sannan yai unlock din motar ta bude ta shiga.
“Ina wuni”
Ta gaishe shi ba dan ta san zai amsa mata yadda zat
a ji, bata a damu da sai ya amsa mata din ba, ta maida hankalinta gurin titi tana kallon motocin dake shigowa cikin asibitin a yayinda su suke kokarin fita. Lokaci zuwa lokaci yake kallonta haka nan yake jin takwanta masa a rai natsuwarta ya masa. Sau daya
ta juyo ta kalleshi sai ya sskar mata murmushi ba ta sake kallonsa ba har suka isa bakin gate din Masarautar, sai da ta masa godiya sannan ta bude motar ta fita, be bar gurin ba sai da ta shige cikin Masarautar sannan yaja motarsa ya gaba. Cikin masarauta
r ta shigo rike da ledar maganinta dake cikin hijab, kai tsaye ta nufi bangaren Ammy, tana isa ta danna door bell din wata hadimar ta bude mata, babu kowa a katon falon sai ac da katuwar plasma, dakinsu yaran ta nufa, a hankali ta tura kofar ta shiga, sai
ta samu Luma ta yi tana ta bachi, Labib kuma baya dakin, fita tai daga dakin ta sauka saka gaba daya ta nufi Garden daman da yamma haka a gurin take zama ko da yaran, balle yanzu da babu ko daya a hannunta.
SHATTIMA POV.
Ya farka da tunanin mag
anar da sukai jiya da Baba Waziri, babu abun da yafi tsaya masa a rai kamar maganar aure da kuma transfer, ba wai baya son zama kusa da iyayensa ba ne, irin halin da Mai Martaba yake ciki yana daga masa hankali gashi kuma idan yana gari dole ne sai an saka
shi cikin harkokin sarautar. Sakon DSP Nura ne ya shigo wayarsa cewar police din daya bukata suna waje suna jiran Zainab, call list dinsa ya shiga ya kira Zainab ya sanar mata, sannan ya mike tsaye ya fito harabar gidansa, a zahiri motocin dake jera a har
abar gidan yake kallo, abadini kuma zuciyarsa na can ta lula wani gurin da tunani. Juyawa yai koma ciki yana shiga ya tube tufafin jikinsa ya shiga bathroom yai wanka ya fito ya shirya cikin kananan kaya sai kamshin turare yake kamar wani sabon ango. Keys
dinsa ya dauka da wallet dinsa ya nufi motarsa Baba Adamu na ganin haka ya taso da sauri.
“Ran ya dade masarauta zamu je?”
“No zauna abun ka ni kadai zanje”
Ya furta yana bude motar ya shiga, kamin yai warming din motar har mai gadi ya bude masa
gate. Kai tsaye ya dauki hanyar da zata sada shi da masarautar daman can a ka'ida ba a masarauta yake kwana ba sai idan ta dauro, duk wani abun daya shafi masarautar yana nisanta kansa da shi domin ko kadan sarautar bata burgeshi. Tun daga babban gate din
har cikin gida ake ta mika masa gaisuwa amman be amsa ko ka daya ba, daman can kasaita bata barinsa amsa gaisuwa balle kuma yanzu da tunani ya saka shi gaba. Yadda ya fito cikin motar yana takawa sai ka rantse da Allah ba zai mutu a saka a cikin kasa ba, k
allo daya zaka masa kasan cewa jinin sarauta ne, domin sarautar ta nuna a tafiyarsa da maganarsa da isarsa da fuskarsa da kamalarsa ga wani irin kasaita a tafiyarsa kamar shi ne sarkin ma. Kai tsaye ya nufi bangaren Mai Martaba sai ya kararda shi yana bach
i, hakan yasa ya dawo bangaren Ammy, sai da ya fara duban yaransa dake hannun Jekadiya sannan ya nufi dakin Ammy ba tare da ya tambayi mai rainonsu ba. Ammy bata dakin Sai Nana dake aikin mata abincike a wardrobe ganin Shattima yasa jikinta ya fara rawa.
“Ya Shattima sannu da zuwa”
“Yauwa Sis Morning baki je school ba”
“Eh sai gobe?”
“Why”
“Bana jin dadi ne, kuma na fadawa Driver yaje makarantar ya fada”
“Me ke damunki?”
“Fever amman an sha magani”
Tana amsa masa ta nufi kofa da saur
i, shi kuma ya bita da kallo cike da kulawa. Tana fita Ammy ta shigo rike da plate din wainar kwai a hannunta.
“Morning Ammy”
“How are you?”
Ya dan tabe baki alamar ba Kalau ba.
“Tunani ko rashin lafiya?”
Ammy ta tambaya yana mika masa far
antin.
“Tunani dai”
Sai tai murmushi.
“Waziri ba zai yi abun da zai cutar da kai ba, ni kaina na dade ina son ka dawo garin nan da aiki ka ki, yanzu kuma baka isa ka sabawa Umarninsa ba”
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana kallon Ammy.
“Maganar Auren ma bana fatar ka saba masa, tun da har ya zabi rufe ido ya aura maka yarsa be kamata kace aa ba”
“I accept it”
Daga haka be sake cewa komai ba. Be koma bangaren Mai Martaba ba sai da suka fito daga sallah la'asar. Ko da ya shiga falons
a sai ya same shi a ciki zaune, ko'ina na falon duhu ne kamar dare, bayan kuma yamma ne akwai haske a ko'ina. Ganinsa a falo ma abun ma farinciki gurinsa domin a da kullum yana kan gado kwance, amman yau gashi akan kujera zaune. Kamin ya karasa kusa da shi
yai masa sallama, Mai Martaba ya dago kansa a hankali ya kalli Shattima, wanda siffarsa da ke shimkide a siffar Shattima kallo daya zaka masa ka san jini daya ne. Gaban Mai Martaba Shattima ya zauna yana murmushi.
“Barka da Yamma Mai Martaba ya kufan
jiki?”
“Alhamdulillah”
Mai Martaba ya amsa yana ta kallon Shattima.
“N ga jiki ya fara kyau Alhamdulillah”
Shattima ya fada cikin jindadi, sai Mai Martaba yai murmushi ya ce.
“An samu shigowa?”
“Eh Baba Waziri ne ya kira ni jiya, akan m
aganar fitar da kai waje da kuma aurena da neman transfer”
A hankali Mai Martaba ya sauke ajiyar zuciya.
“Hakan yana da kyau, ni kaina aurenka yana cikin rai na, neman transfer ma yana kyau, domin kai ne babba a yanzu, sai dai magana fita da ni waje
a bar wannan maganar”
Shattima ya dago ya kalleshi.
“Saboda me? Ba san inda za a dace ba Mai Martaba duk fata muke yi”
“Hakan yasa nake son maka wata wasiya, na san matsalar auren nan yana damunka, ina son nai maka wasiya cewar kai ta aure ko da
kuwa yau zaka aura gobe ta mutu, to jibi ma ka sake auren wata, a koda yaushe ina maka kallon babba a cikin iyalina, ina jin dadi da alfaharin da Allah ya bani kai a matsayin da, Omar ina maka wasiya da ka ji tsoron Allah, kuma ka rike yan'uwanka tsakani d
a Allah babu banbanci ko nunawa wani ya fi wani...”
A take jikin Shattima yai sanyi, sai ya ji kamar Mai Martaba na masa wasiyar bankwana ne. Shiru mai Mai Martaba yai na dan lokaci sannan ya cigaba.
“Rayuwa a gida da Family irin wannan akwai wahal
a, amman idan ka jure Allah zai taimakeka, bana son ko bayan raina a samu rabuwar kai a tsakaninku, bana son tsabani ko kiyayya ta shiga tsakaninku, ka yi kowa biyayya ka bawa kowa hakkinsa...”
Mai Martaba bai karasa ba Shattima ya katse shi jin kamar k
unnuwansa da zuciyarsa ba za su iya daukar abubuwan da Mai Martaba yake fada masa ba.
“Inshallahu zaka samu sauki Mai Martaba”
Mai Martaba ya gyada kai.
“Sauki yana tafe da yarda Allah, amman sauki na har abada, sauki wanda daga shi babu wani ci
won Inshallahu, ni kadai na san me nake ji akan ciwon nan Omar, bayan ciwon jiki a nake kwana da shi kullum na tashi da shi, ga ciwon tsoron rabar mutane da tunani, na yarda wannan jarabawa ce, babban Sarki kamar ni ace bana iya shiga cikin mutane, bana iy
a sauraren al'ummata, ina jin tsoron abun da zan fadawa Ubangijina, ina jin kamar sauka ta cancance ni wata zuciyar kuma na raya min idan nai hakuri nan ba da jimawa ba zan tafi na bar Sarautar, ba barin sarautar ce tashin hankalina ba, yadda zan tafi n ba
r ku, rashin hadin kanku da irin matsalolin da kuke samu tun a yanzu da nake raye, babu uban da zai so ya tafi ya bar iyalansa a watse kansu a rarrabe, kai ne babba Omar dan Allah ka kula da yan'uwanka, na san na dora maka abu mai nauyi, amman Allah zai ta
ya ka, ka bi Hajiya Bilki kamar Ammy, kuma kai ta hakuri da yan'uwanka, musamman Mama Aisha (Nana) ita ce karama a cikinku ita ce kadai ta tashi bata san gata da dadin uba, bata san ta rabe ni ba saboda lalurata, ka kyautata mata ka zame mata uba, kuma kai
hakuri da halayenta akwai kurciya a tare da ita, sannan ka saka ido akan tarbiyar Karima, ka bi kanen mahaifinka kamar ni.... Kuma kai ta hakuri da rayuwa”
Shattima ya rufe idonsa da suka gama cika da hawaye.
“Inshallah zaka same ni mai cika umarni
nka Mai Martaba”
“Allah ya maka albarka”
“Amin”
Ya amsa yana jin kamar ya fashe da kuka.
“Anjima idan Ammy ta shigo, zan sa ta duba maka takardun wasu filaye da gidajen da baka san da su ba, akwai kuma takardar da nai rubutu na wadanda nake bi
bashi da kuma wadanda kasuwanci ya hada mu, zan hannata maka su ka aje inshallah”
Uffan Shattima be ce zai iya kara cewa ba ya mike tsaye.
“A tashi lafiya Mai Martaba”
Ya fice daga falon da sauri kamar zai tashi sama, be taba daukar haka wasiya t
ake da nauyi ba sai a yau. Gaba daya jin yake duniyar na juya masa, ta ina zai fara ina zai sauke why mai martaba yai masa wannan wasiyar a yanzu.? Why him? Har ya iso bangaren Ammy kirjinsa be daina nauyi ba, ga zuciyarsa sai bugawa take kamar zata fito,
nauyin ba kirjinsa kadai yake ba har a kansa ji yake kamar Mai Martaba ya dauki wani katon dutse ya dora masa a kai. Sai ya samu kansa a falon Ammy sannan ya soma tambayar kansa abun da ya kawo shi a falon, but he need to see his mother maybe ko zai samu s
aukin abun da yake ji. Hakan yasa ya nufi dakin yana kokarin tura kofar dakin ya shiga ya ji muryar Nana.
“Ni sai na tafi”
“Nana kina ganin rashin kunyar da kika min zai barki ki rayu in peace, kina min tsawa your own biological mother”
Tsaye yai
jikin kofar yana kallon Ammy dake zaune kasa ta jingina da gadonta tana kallon Nana kamar Nana ce uwar ita ce yar.
“What is happening?”
Nana kamar mai jira ta juyo gurinsa da sauri ta soma masa bayani kamar zata yi kuka.
“Ya wai bikin yar Farin
gida da ake wai Ammy ba zan je ba, kuma Amal kawata ce ita ce ta gayyace ni ita kanwar Amarya ce class din mu daya”
“Yaushe ake bikin?”
“Yau ake budar kan Amarya, kuma ba cikin manyan zan tsaya ba, ni gurin su Amal zan tsaya”
“Shikenan je ki fara
shiri tun yanzu, zaki je anjima”
Da sauri ta rumgume shi tana murna.
“Thank Youu Ya I love you”
Ta sake shi sannan ta fice daga dakin cikin murna ranta fes tun da Shattima yace zata je. Sai da ta fice sannan ya nufi inda Ammy take ya zauna gefen
ta sai shi akan gadonta ya zauna tsabanin ita data ke kasa zaune.
“Ammy why kika hana ta zuwa?”
“Bata son makaranta, duk abun da aka ce tai ba zata yi ba, sai kuma a rika bin ra'ayinta ana mata yadda take so?”
Shiru yai yana kallon yadda idon Amm
y ya cika da hawaye, sai ya ji tausayinta ya rufe masa zuciya.
“Amman idan kina irin kalaman nan marar dadi a gareta wani abu zai iya samunta, kuma still mu ne zamu shiga matsala, she's still young”
“Like a baby?”
Ta tambaya hawaye na sauko mata.
“Ina jin kamar ace Nana tana da wata uwar ba ni ba, da yanzu na maida ta hannun mahaifiyarta na gaji da wanne zan ji”
Ta fashe da kuka. Hakan yasa Shattima yaji damuwarsa ta karu, ya mike tsaye jiki ba kwari ya fice daga dakin domin ko kadan baya so
n jin kukan mahaifiyarsa. Dakin yaransa ya nufa or maybe zai samu peace of mind a can, Luma kadai ya samu a dakin tana ta bachi, kusa da ita ya zauna ya shafa fuskarta a hankali yadda ba zata tashi ba, sannan ya mike tsaye yana sauke ajiyar zuciya ya nufi
gurin windows dakin wanda ke saiti da Garden din bangaren Ammy, tsaye yai jikin window yana kallon itacen dake garden din wani iska mai dadi yana bugunsa, hannayensa ya dora jikin window wanda hakan ya bashi damar hango Falmata dake zaune a garden din tana
ta kallon wani gurin na dabam kamar mai tunani. A inda take tsaye na kasa baya iya hango na sama sai dai na sama ya hango na kasa.
Hango Sirleem da tai tafe yasa ta mike tsaye tana jiran ya karaso kusa da ita, tun daga nesa yake sakar mata murmushi ha
r ya karaso.
“Naje daukarki Momy tace tasa Ameer ya kawo ki, na shiga bangarenku n karbi takardar maganin wata hadima tace min kina Garden”
“Eh ta bani maganin ma”
“Oh Momy akwai karamci sai da ta siya maganin ma”
Ya fada yana murmushi domin k
adan daga halin Momy ne taimako da karamci ga tausayi da son mutane.
Ya kai hannu ya karbi maganin yana dubawa.
“Ta fada miki yadda za ki yi amfani da shi?”
“Eh ina son sai na je gida sai na fara idan zan kwanta”
“Amman dai yau ba zaki kai da
re kamar jiya ba ko?”
“Sai yaran sun yi bachi tukuna”
Ya mika mata ledar maganin yana fadin.
“To ya kamata ki samu Mai Napep din da zai rika kai ki ya dawo dake, zan biya shi”
Kallonsa kawai take baki sake tana mamakin yadda yake da karamcin d
a son taimako har haka. Kamin tace komai yace.
“Ba ki ba ni labarinki ba fa”
Ta yi kasa da kanta, ba dan bata ji domin duk maganar da yake mata yan mata ne cikin daga muryar ta yadda zata ji, ba ita kadai ba har wanda ke kusa da su ma zai iya ji.
“Hey....”
Ya fada yana leken fuskarta. Sai ta dago ta kalleshi, ta sake maida kanta kasa.
HAJIYA BILKI POV.
Hajiya Bilki ta sauke ajiyar zuciya jin abun da Aminiyarta kuma matar Waziri wato Hajiya Talatu take fada.
“Wallahi kuwa”
“Ki ce kina cikin tashin hankali, to wai Waziri lafiya yake kuwa?”
“Ni ina na sani, sai wani fadar yake duk na sake yi ma dan da'uwansa kazafi a bakin aurena, ina zaman zamana zai dauko min wata masifar, wannan duk na Ammy na na sani, shi kuma baya iy
a musa mata tun da ta shanye shi, daga ni har Maijidda jiya ba mu runtsa ba, kuka kawai take”
“Ai dole tai kuka za akai ta ga halaka, yarinya tana zamanta za a aura mata mutuwa, Wallahi ki tashi tsaye karki yarda sam a kai ki a baro”
“Ai ba zan yarda
ba, sai dai ayi wacce za ayi, amman ba zan Waziri ya aurawa Shattima yata ba, ko ana zaune kalar ai ba zan yarda ba balle kuma mutum ya zama maye, idan dama ta ki hagu zan koma, idan ta gwada be yarda ba be janye maganar ba, garin su mutanen nan zanje ayi
masa asiri ya janye”
“Ai haka ya dace gaskiya, sai muje tare, kaji min tashin hankali”
“Wai sai fdar yake indai ba Shattima ya fasa ba Wallahi ba za a fasa auren ba, so yake yana aura masa ita ta mutu, waya sani ma ko Ammy ce take cinye masa mata, k
o kuma can garin tsafe tsafensu suka kwaso wani mugun abu”
Hajiya ta dade tana magana da Hajiya Talatu kamin ta katse wayar shi M saboda shigowar Nana.
NANA POV.
Tana Fita daga dakin Ammy ta nufi bangaren Hajiya. Tana tura kofar dakin ta shiga
sai Hajiya tai wa Hajiya Talatu sallama ta kalli Nana tana murmushi.
“Daughter”
“Na'am Hajiya dan Allah wayarki zaki ara min na kira driver na”
“To gashi”
Ta mika mata wayar, Nana ta kai hannu ta karba ta fice daga dakin tana nemo line AA call
list din Hajiya domin bata yi saving number ba. Bugu daya ya dauka.
“Hello”
“Sardauna”
“Na'am”
“Ka shirya anjima da 8 ka zo ka kai ni gurin budar kan Amarya”
“Okay”
“Karka wuce 8pm”
“Okay”
**
Ya amsa mata tare da sauke wayar ta
re da saka ta aljihu sannan, ya marasa cikin gidan yana nade wandonsa.
“Anti wanki da yamman nan”
“To kayan sun yi datti, kai kuma ba zama kake ba”
Hannayensa ya jefa cikin ruwan ya soma taya ta wankin, daman can idan tana wanki ya kan taya ta