Showing 231001 words to 234000 words out of 304903 words

Chapter 78 - FULANI COMPLETE

ya tabbatar ta taune sannan yake saka mata wani a baki. Bayan sun gama ya shiga yai wanka ya saka kananan kaya ya zo kusa da ita ya zauna yana janta a jikinsa kamar z

ai shigar da ita.

“Zan fita yanzu, na san kawayenki za su zo ganin daki, ban da fadawa kowa wanene ni pls”

Ta daga masa kai tana jin kamar tai kuka.

“Ki kula da jikinki idan zan dawo zan biyo miki da wani magani okay”

Nan ma kan ta daga masa sa

nnan ya sumbance ta ya fita. Hakan ya bata damar karewa katon dakin kallo tana mamakin ace wai ita ce a ciki.

ZAINAB POV.

Tana zaune falon har akai sallah magariba sannan ta tashi ta shiga cikin domin yin sallah. Iya na ganin haka ta tashi da saur

i ta shige dakinta ta maida kofar dakin ta rufe har da makulli, sannan ta nufi wardrobe ta ta bude ta dauko tukunyar kasar nan mai jan kyalle ta kara bakinta tai magana da muryar da ita kadai zata iya jinta, sannan ta kara kunnenta ta saurari abun da ake f

ada kamin ta maida tukunyar a mazauninta. Ta duka karkashin gadonta ta dauko wayarta ta bude ta dauko kurwar daya daga cikin kurwa biyu da suka rage ta warware zaren da yake kai sai ga wata yar abu ma kamar tsokar danyen nama karami yana numfashi, rufe han

nunta tai ta janyo wani bakin mayafi ta rufe hannun dake dauke da kurwa, sai kurciya ta bayyana ta cikin bakin mayafin yana ta fisge fisge alamar lafiyayya ce mai jini a jika, dukawa ta sake yi wata robar ta janyo ta bude ta dauko wata tsohuwar kaya ta sai

ta bayan kurciyar ta bangaren hannunta na dama ta caka mata ƙayar, take kurciyar ta zabura ta sai ta lafe, wanda hakan yai daidai da zaburar Maijidda dake zaune a dakinta tana duba wasu kayan na order da kawarta ta turo mata. Iya ta maida kurwar ta nade so

sai sannan ta dauko wani karamin gwangwani ta kunna aci balbal din jiki ta kifa wani kwano ta dora kurwar a kai ta tura gwangwanin karkashin gado ta tura kwanon saitin wutar ta yadda kurwar zata azabtu, ta kara kurwar a kam wuta, sannan ta sake saka kayar

ta soka ta gefen tsokar dake nade ta bangaren damanta daga kasa, can kuma ta tashi ta nufi inda tukunyar nan take ta dauko ta kar bakinta, sai da tai kirarin data saba sannan ta fadi kalar ciwon da take son turawa Maijidda.

Gaba daya sai Maijidda ta ras

a natsuwarta ga wani uban zafi da ya sako ta gaba, duk ac dake dakin sai ta ji wani irin zafi ya taso mata, haka dai ta daure tana duba kayan kamin idonta ya fara cika da hawaye saboda azabar ciwon kai, aje wayar tai tana tana jikinta da yai mugun zafi kam

ar kyankyason wuta, ga bayan ta ta bangaren hannunta na dama sai ciwo yake kamar an soka mata abu a ciki, da zafin ya fara mata yawa sai ta gane ba daga dakin ba ne daga jikinta ne, kamar mahaukaciya haka ta fita daga dakin ta nufi kitchen ta bude firiza t

a dauko kankaran ta fasa a roba ta dawo ta dakinta ta shiga bathroom ta surka kankarar ta cire tufafin jikinta ta watsa ruwan kankarar tana jin kanta kamar zai bare, daker ta daura zane ta fito da gudu zuwa dakin mahaifiyarta tana kuka.

“Momy zafi na ke

ji sosai, kaina ma ciwo yake kamar zai bare, kuma nan ma ciwo yake min sosai”

Ta nuna bayan kafadarta, ba karamin tashi hankalin Hajiya Talatu yai ba, daman can mace ce mai shegen son yaya balle kuma Maijidda da ta fi kwanta mata a rai fiye da sauran.

“Subhanallahi, me kika sha?”

“Ban sha komai ba, ban ci komai ba”

Ta fada tana lumshe ido tsabar ciwon kan da take ji. Hajiya Talatu ta kai hannu ta taba jikin yarta sai ta ji shi ba zafi.

“Kuma jikinki babu zafi”

“Akwai zafi Momy kaina”

Ta dafe kan tana kuka sosai.

“Yusra, duba driver waje idan baya nan ki kira Haroon yanzu muje asibiti”

Daker Maijidda ta iya saka tufafinta har suka shiga motar Haroon din ya ja su zuwa wata private hospital Annuri, kamin su isa asibitin Iya ta jany

e kurwar Maijidda jikin wutar wanda hakan ya bawa jikinta damar karbar zafin da kurwar ta dauka, sai zafin ya maye ilahirin jikinta, Hajiya Talatu na tabawa ta ji yayi zafi sosai. Ta samu kula ta musamman kasancewar asibitin wanda ta saba zuwa ce kuma asib

iti ce ta masu nera, duk wanda ka gani asibitin babban mutum ne ko kuma dan babban mutum dole a kula da kowa yadda ya dace. Gado suka bata bayan sun tabbatarwa Hajiya cewar taifot ce, allurar suka mata sannan suka saka mata drip, hakan yasa ta dan samu sau

ki har bachi yai gaba da ita. Sai a lokacin hankalin Hajiya Talatu ya kwanta domin da farko har ta fara jin tsoro tana tunanin ko abun da suka saka ayi ma Fadime ne ya dawo yarta, ko kuma saboda zancen aurenta da Baba Waziri yai ne da Shattima yasa it ma z

ata leka kiyama.

Zaunawa tai a kujerar dake dakin ta majinyata tana kiran mijinta ta shaida masa abun da ke faruwa, bayan a sauke wayar ta kalli Haroon dake tsaye ta ce.

“Ka tafi gida, ka farawa Yusra da Nazma su shirya komai na kwana sai ka kawo wa

ta a cikinsu ta kawo min”

“A nan zaki kwana?”

“Dole ai, maybe gobe su sallame ta idan ta samu sauki, ka tafi kawai ka fada musu an ba mu gado”

“Okay”

Ya fada sannan ya juya ya fita, fitarsa tai daidai da shigowar kiran Hajiya Babba a wayar Haji

ya Talatu, da muryar da za ta karantar da Hajiya Babba damuwarta tai picking call din.

“Hajiya Talatu? Haka aljannun nan suke aiki kamar yankan wuka? Yanzu nan Shattima ya turo a duba masa yarinyar wai ta bata a ganta ba”

Hajiya Talatu ta zaro cikin

wani irin jindadi take ta manta da wani damuwar ciwon yarta.

“Alhamdulillahi abun nema ya samu, dauke ta su kai kenan? To ai haka ya fi ba ganta ba balle wata maganar ta fito”

“Wallahi ni ma haka na ce, amman fa tsorona daya kar ta dawo ko kuma ta fa

di masarautar nan a dawo da ita”

“Aa haba Hajiya, ai ke ma kin san maganin biri karen maguzawa, ai ba za su kaita inda zata iya dawowa ba, tun da har mun fada musu asiri ne ba ma son ta tonu dole su san yadda za su yi da ita, ni ai murna ta zo min a wan

i yanayi ga ni a asibiti Maijidda ba lafiya wai tafot ne”

“Subhanallahi Allah ya bata lafiya, agaishe ta da gobe zan shigo na dubata”

“Amin Amin Hajiya na gode sosai”

Ta sauke wayar cikin wani irin farinciki marar misaltuwa.

***

Hajiya B

abba na aje wayar ta kalli Jurry da ita ma murmushin jindadi take za ta yi magana sai ga Sirleem yayi knocking kofar sannan ya turo ya shigo. Hakan yasa Jurry saurin mikewa tsaye ta fice ba tare da ta gaishe shi ba, domin ita har yanzu fushi take da shi sa

boda marin da yai mata kwanakin baya akan Falmata.

Shi dai be kula ta ba ya zauna gaban Hajiya Babba dake ta yakar hakora kamar wanda akai wa gafara.

“Sirleem sai yanzu”

Ta fada tana kallon yadda fuskarsa ke ta annuri kamar ba shi ba, har wani kya

lli yake.

“Barka da dare Hajiya”

“Yauwa, ya jikin?”

“Alhamdulillah”

“Ka je asibiti?”

“Eh sun ba ni magani”

Ta yi shiru har na wani lokaci shi kuma sai sake saken yadda zai shera mata wata karyar yake so that ya samu ya sake kwana a gidan

amaryarsa.

“Alhaji Kabir ya kira ni, ya ce ka same shi da maganar ka na son a mika maka ragamar mahaifinka a hannunka”

Ya dan shafa kansa.

“Eh tun kwana bayan nai masa magana, yace min na jira ayi a gaban kowa kuma yace zai hada wasu takardun ya h

annata min, ya ma ba ni wasu and i think yanzu ya kamata na rika natsuwa ina duba komai yadda ya kamata, jiya a gidan na wuni duba su sai gashi dare ya zo da fever”

“Ayyah, dole ai saboda baka saba ba, amma da sannu komai zai zama kamar an saba din, ya

fada min zai tara kowa saboda a zama shaida, kuma yace na saka ranar da nake ganin ya dace a yi launch din new manager a babban kamfanin mahaifinka, na saka karshen watan nan”

Sirleem ya kalleta da sauri.

“Hajiya karshen watan nan be yi wuri ba? Sai

kace abun da za a gudu?”

“Me ye abun sauri a dukiyarka? Shekarana nawa suna juyawa? Sai yanzu da lokacin karba yai za a ce an yi sauri? No karshen watan nan ya wadatar ayi biki a mika maka ragamar kamfaninka a hannunka da ma sauran kamfanonan da gidanje

n da komai ma”

“To Allah yasa hakan shi ne mafi alheri, kuma ya bani iko kula da ita yadda ya dace”

“Ameen haka na ke son ji, Allah yai maka albarka”

“Ameen”

Ya fada yana mikewa tsaye.

“Ni zan koma can, Hajiya na fi jin zakewa a gidana gaski

ya, ko ba komai zan samu na maida hankali kan abubuwan da suke gabana”

“Rantse min ba Mansura ta zo garin nan ba”

Kamar abun wasa sai ya fara dariya.

“Wallahi Hajiya bata zo ba, Mansura tana Kaduna Wallahi”

“Shikenan Allah ya tsare ka kula da k

anka”

“Ameen sai da safe”

Ya fice cikin jindadi, Hajiya ta bar shi ya tafi ne kawai saboda ita ma tana cikin wani farincikin, kuma tana son ya maida hankalin kan abubuwa da ke gabansa kamar yadda ya fada, ba dan haka ba babu abun da zai saka ta kyale

shi ya kwana a gidansa shi kadai.

TUMBA POV.

Ko da aka isa da ita asibiti bata cikin hayyacinta, gaba daya hankalinta ya bace, duk wanda zai ga halin da aka shigo da ita sai yayi tasbihi ya kawar da ido, domin kafar da babur ya buga gaba daya ta c

ire a hannu a ka iso da ita, ga naman fuskarta ya kwaye gaba daya baka ganin komai sai fatar can ciki mai jini wanda bata da kyau gani, hannunta na dama ma ya karye sai dai shi be cire ba sakamakon motar dake bayansu da bugu babur dinsu ita da Mai babur di

n sukai sama ita ta fada jikin wata motar, wanda hakan ya sa wani mai babur din ya bugeta babur din kuma ya fada kanta, shi kuma mai babur din da ta hau ya fada gefe, sai yai hanzarin tashi da jimuwar da yai, ganin yadda ta Tumba take sai ya saka ya manta

da na shi ciwon, da taimakon wasu mutane da kuma jama'in dake kula da titi aka kawo su asibiti, ba dan suna da tabbacin ita Tumba din tana da rai ba, Likitocin ne suke tabbatar da tana da rai sai dai tana cikin mawuyacin hali.

A take aka hau neman yan'u

wanta cikin mutane da suka kawo ta, kowa yace be santa ba, yar jakar kudinta ma an dauke tun a can gurin da hatsarin ya faru balle a binciki wayarta ko wani abu da zai bada shaidar inda take, a dole aka koma gurin mai achaban ana tambayar inda ya daukota.

_________

Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi

na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutu

ra turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua

nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.

Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.

53

*Littafin nan na kudi ne biya ki k

aranta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Ta yi shirin bachi cikin kayan bachinta ba dan tana da tabbacin bachin zai dauke ta ba, sai dan ya zame mata al'ada saka kayan bachi a

kowa ne dare. Kwance take a dakinta hannunta rike da waya tana ta kallon sakwannin dake shigowa ta kasa amsa ko daya kuma ta kasa kashe datar gaba daya duniyar wani irin take mata, tun daga lokacin da abubuwan da suka faru suka faru ta saka komawa daidai k

amar da. Har kusan 10:30pm bachi be dauke ta ba, sai da ta gaji da rikon wayar ta kashe data ta aje tana kokarin sauka ta leka bandakinta ta ji karar bude gate, hakan yasa ta nufar windows dakinta ta bude lalulen ta leka waje, sai ta hango mota ta shigo ci

kin gidan, kamin tai tunanin komai Jekadiya ta bude ta fito tare da dogarai. Barin jikin window tai ta bude kofar dakin ta fito falo kamin ta karasa gurin kofar ta bude har gabanta ya soma faduwa, domin ta san ba lafiya ba, ganin Jekadiya a irin wannan lok

acin cikin gidanta. Jekafiya na kai hannu ta kwankwasa Zainab ta bude kofar.

“Lafiya?”

“Ba lafiya ba, Shattima ne ya turo mu bincika wata yarinyar Fateema makauniya”

“A nan?

Ta tambaya da mamaki, Jekadiya bata sake ce mata komai ba ta kunno kai

cikin falon, mutanen da take tare da su ma suka shigo kowa ya hau aikinsa, har karkashin kujerun falon sai da Jekadiya ta leka duk da tana da tabbacin ba za ta iya boya a gurin ba. Zainan dai na tsaye tana kallonta da mamaki da kuma tunanin inda Fadime ta

tafi, wata kila ta sake bin wani ko kuma ta fito gurin karanbaninta wani yayi gaba da ita. Iya ma fitowa tai bakin kofar dakinta ta tsaya tana kallon ikon Allah ba dan ta ji Fadime ake nema ba da tace bincike aka zo mata, ita kanta mamakin yadda akai Fadi

me ta bata take. Sai da suka bincike dan madaidacin gidan kaf har da harabar ba su ga wani alama na an boye mutum ba. Sai da za su tafi sannan Zainab ta biyo bayan Jekadiya tana fadin.

“Jekadiya ki fadawa Shattima idan an ga yarinyar, Wasim ya ce kar a

kuskura a taba idonta, kuma yace akwai masu kokarin cutar da ita, komai zai same ta kar a taba ta ko a ce za a mata magani”

Jekadiya ta juyo tana kallonta kamin ta gyada kai ta dan saci kallon Iya dake tsaye bakin kofa sannan ta juya ta cigaba da tafiya

rta har ta isa gurin motar ta bude ta shiga, hankali be kwanta ba sai da ta ga sun bar gidan, har ga Allah da ba umarnin Shattima ba ne babu abun da zai saka ta zuwa gidan mayya har tai mata bincike bayan kuma ita Ammy ta saka tai mata turaren nan ko dan s

hi kadai ya isa ya saka ta kame mata kurwa, hakan yasa tun da suka kamo hanya take ta addu'a.

Bayan sun wuce Zainab ta dawo cikin falon tana ta mamakin batan Fadime? Daman abun da Wasim yake nufi kenan da cewar za a cutar da ita? Ko kuma dai wannan bata

n nata ne na kanta daga baya cutarwa zata zo? Ko kuma wani abun ne dabam? Tana ta kokarin kawar da abun da zuciyarta take son raya mata akan mahaifiyarta na ganin kamar tana da hannun a batan Fadime idan ma ta bata din da gaske. Dakinta ta nufa tana kara n

itsawa cikin tunanin, ko dai Wasim ne ya dauke ta? Ko kuma Iya ce tai wani abu?

“Ko dai minene ita ta sani can, ai ita ta jawa kanta”

Ta furta tana zaunawa saman gadonta, mamaki da tunanin da ya bijiro mata ya saka ta manta da zancen fitsarin da take

ji, babu abun da ta hango a abun da akai musu sai cin zarafi da zubar da mutunci wanda take ganin Iya ce ta haifar da komai, domin da ada ne ko wani ne ya ce zai yi musu haka hanawa zai yi saboda yana ganin kimarta da kuma ta Iya sosai, amman a yanzu Iya

ta barar musu da komai.

Ba ta yi waya daya da kwantawa ba ta sake jin an bude gate din, saurin tashi tai ta leka window sai ta sake hango motar dazun, daman ta san indai ba daga Masarauta ba ne babu yadda za ayi mai gadinta ya bude gate a irin wannan lok

acin. Kamar dazun haka ta sake fitowa ta bude kofar falon da kanta sai dai wannan karon tsoro ya cika mata zuciya, sama da dazun da mamaki ne kawai da tunanin dalilin zuwan.

“Shattima yace mu ta ho da ke?”

“Ni..?”

Ta nuna kanta.

“Akwai wanda t

ake tsaye a gaba ne bayan ke?”

Jekadiya ta amsa mata ta sigar da ba ta yi zato ba, daman can basa jutuwa ita da jekafiya saboda tana da dagawa da ji da kai wanda 80% din mutanen gidan suka tsaneta da shi musamman wadanda suka san asalinta. Bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login