Showing 285001 words to 288000 words out of 304903 words
musu komai, haka Fadime taje tai musu bankwana da sunan zata tafi Yola bikin Shattima, a kasan ranta sai fadar take wai sai dai kawai su ji ta auri dan sarki. Inna Uwani da
Inna Dije a gidan suka kwana domin Ra'ees ya fadawa Bappa cewar da sassafe zai zo ya dauke su.
Cikin daren Inna ta ja Fadime gafe tana mata nasihar da ta saba mata tun a lokacin da aka saka mata rana, cewar ta natsu ta daina abubuwan da take, kuma ta rik
e addu'a ban da raina mutane surutun nan da take kamar an bude redio.
“Kina gani dai Allah ne ya kai ki wannan matsayin ba dan kin isa ba, kuma duk wanda yake cikin gidan sarauta zaki ganshia natse, ba kamar ke ba, kina musu hauka za su koroki ki dawo r
uga”
“Aa duk watsar da komai zan yi, ba zan yi komai ba na natsu zan yi biyayya”
Fada sosai Inna tai mata irin na ya da uwa, sannan ta motsa mata fura ta bata ta sha, Fadime ta je ta kwanta babu komai a ranta zai zumudi kamar wanda aka cewa ana zuwa
za a daura mata auren, mafarki babu kalar wanda ba tai ba. Washe gari sun da asubar fari Inna ta shirya musu abun karyawa tana ta tunanin Fadime a ranta irin kewar da zata yi amman Fadime hankalin baya kan Inna, Bappa ma sai da yai mata nasa fadan ya ja ma
ta kunne sosai sannan yai mata albishir da gafararsa na abubuwan da tai ta masa na bacin rai. Misalin 8am Ra'ees ya iso ya daukesu zuwa Katsina sannan su wuce airport, Inna da Bappa suka tsaya suna ta kallon motar har sai da suka daina hangota sannan Inna
ta share hawayen idonta ta koma cikin gida tana jin kamar ta fashe da kuka, zuciyarta ta cika.
SHATTIMA POV.
“Amaryarka ta iso”
Ammy ta fada da murmushi a fuskarta, Shattima ya aje cup din hannunsa yana murmushin jin kunya
“Ammy har da ke?”
“Ramawa na yi, ni ma dazun Mai Martaba yake zolaya ta wai ana masa kuri za'ayi sabuwar in-law, na ce masa lallai kam wannan Amaryar ta fi saura domin ina son yarinyar sosai da sosai Wallahi ta kwanta min rai kuma ta mana komaia rayuwa”
Shattima ya fada
da murmushi yana shafa kansa.
“Mai Martaba dai lafiya ta samu”
“Wallahi yanzu kam Alhamdulillah sai dan abu ba a rasa ba, gashi har yana fita abu kamar wasa”
“Daman ai komai yai farko yana da karshe, sai a cigaba da addu'a”
“Haka ne kam, addu'
a kuma ai ta zama dole, daman can Mai Martaba baya wasa da addu'a ni ma kuma ina masa, ai da baya addu'a da abun be zo a haka ba, kasan wani lokacin ko da addu'a abubuwan su kan samu bawa saboda an rubuto masa hakan sun kafi na haife shi”
“Haka ne Allah
yasa mu dace, amman ita ba nan zata sauka ba?”
Ammy ta yi murmushi domin ko fito kai tsaye ya mata magana ba ta san wa yake nufi.
“Kai da ganinta yanzu ai sai an kai maka ita”
“Tooo”
Ya mike tsaye yana cigaba da murmushi.
“Nana ta min maga
nar graduation dinsu, wai a Abuja za su yi”
“Eh ta fada min ni ma nace ban yarda ba, yayi nisa duk abun da za a ce sai an bar Yola anje wani guri ayi sa ban zan bari ba”
“Ni ma ban bata shawara ba gaskiya, mace kiwonta ake, na ce mata dai zan yi maga
na da ke, zan fada mata kin ce ba ki aminta ba”
“Haka ya kamata Allah ya muku albarka”
Ya amsa da Ameen sannan ya fice daga dakin sai zuba kamshin turare yake.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wada
nda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Da
n hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman n
e, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar
nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
65
*Khadeeja Candy*
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith ba
nk, then send the evidence via 08036126660*
A harabar makaranta yake tsaye, yana sanye da bakin wando sai rd T-shirt da black shoes, a saman T-shirt din ya dora rigarsa sanyi irin mai kaurin an hannunsa sanye da safa kansa ma sanye hula, waya ce makalle
a kunnensa sai faman murmushi yake kana ganinsa ka san yana cikin farinciki.
“Yanzu kun yarda ku yi a Yola kenan?”
“Eh dolen mu ai, because most of us iyayenmu ba su yarda ayi a Abuja ba”
“Good hakan ya fi duk da na san kuna da family a can amma
n dai kara komai ayi a gaban iyaye”
“To yanzu ai karatu zanje India a gabansu zan yi?”
“Wannan yana da banbanci, kuma idan sun barki kin je hakan na nufin sun yarda da ke kenan kuma hakan ba zai baki dama ki yi rayuwar da kike so ba, kuma ita fatar b
a za ki ba mu kunya ba”
Ta yi murmushi yana juyawa saman gadon da take.
“Zan yi karatu sosai, kuma ba zan yi wani abu da zai tsaba tarbiyarta ba, ba zan ba ku kunya ba”
“Thank You”
“Ur Welcome”
“Bari na barki yi bachi saboda na san nan dare
ne ko? Nan kuma rana”
“Yeah 1am ma ta kusa”
“Oh Wow kai ki kwanta kar Ammy ta ji kina waya da ni”
“To sai miye ai ta san muna waya, ta san ina kiranka ai kuma kana kirana”
“Yeah zata san muna gaisawa ai”
“Gaisawa kawai?”
Yayi murmushi.
“Yeah gaisawa kawai, domin bana jin idan ta san akwai wani abu a tsakaninmu zata bar mu mu cigaba da mu'amala”
“Saboda me?”
“Saboda yanayin rayuwata da taki ba daya ba ne, mu'amalarmu ma ba daya ba matsayinki yana da nisa da ni, kuma kina sama da
ni sosai a komai n rayuwa idan aka cire shekaru”
“Shikenan?”
“Yeah”
“Hmmmmmm sai da safe”
“Goodnight...”
Sweetheart, ya karasa a zuciyarsa sannan a sauke wayar yana kallon hotonsa dake screen din wayarsa, babban yatsansa ya saka yana shafa s
creen din sannan ya daga kansa yana karewa makarantar kallo, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushin wai shi ne yau a uk yana karatu cikin turawa abun da be taba mafarki ba. Duk iya fatan samun kudin da yake da misalin arzikin da yake karatunsa da burinsa a
Nigeria ne, but look at him a kasar waje da sunan karatu karatun da zai inganta rayuwarsa. Tafiya ya fara yi yana tuna yadda rayuwa ta kasance musu before now, but komai ya canja cikin kankan ne lokaci.
“Arziki kashi...”
Ya furta yana kara yarda da
kalmar nan da hausawa kr cewa idan Allah ta so ka tsinuwa zai baka, kuma dare daya Allah kan yi bature, lokuta ta dama ta inda baka yi tsammanin abu ba yake zo maka, domin be taba tunanin sanadin Nana zai samu haka ba, a iya tunaninsa zai samu yan kudaden
a hannunta ne sai ya taimaki kansa da yar'uwarsa sai ga shi sanadinta an masa komai kuma an yi ma yar'uwarsa, farinciki na farko da ba zai manta da shi ba shine kudin da Shattima ya saka masa a account one million, a daren ranar kasa bachi yai yana ta gani
n kamar karya ne one million in his account! Shi da ko 100k be tana ajewa a ciki ba, dai gashi an masa kyautar 1m. Daman tun da Nana ta fada masa ya tura account din yakr rike da wayarsa ko kara yaji sai ya duba sai ya ga sakon mtn, kudin be shigo account
dinsa ba the following day, a ranar kasa yadda yai a farke yake, ya tisa Anty a gaba wai ta mare shi ko zai yarda.
“Wane irin mari kuma?”
“Dan girman Allah ki mare ni Anty”
Anty tai tsaye tana masa kallon mamaki.
“Sardauna ince dai ba wani ab
u ka sha ba?”
“Ni dai ki mare ni dan Allah”
Shiru Anty tai tana kallonsa kamin ta matsa baya.
“Gaskiya akwai abun da yake damunka Sardauna”
“Kai Anty dan Allah ki mare ni”
Ganin ba marinsa za tai ba yasa ya juya kamar zai fita sai kuma ya j
uyo.
“Anty yau yau ce? Ba mafarki na ke ba? Shiyasa na ke son ki mareni na tantance”
Anty na jin haka ta san kudin ne suka iso domin ta san da labarin izuwarsu, sai ta matsa kusa da shi ya ware hannunta iyakar karfinta ta zabgamar mari mai dan karen
zafi, har sai da yaji wani shockin kamar na wutar lantarki, a nan kam ya yarda ba mafarki yake ba gaskiya domin da mafarki ne da yanzu ya farka.
“Na rantse da Allah da abokina ne yai min wannan marin yau sai mun yi dambe da shi”
Anty ta saka dariya
domin ita kanta da tai marin ta ji zafi balle shi da aka mara.
“Ai dan ka tabbatar ba mafarki bane gaske ne miliyan sun shigo”
Sai gashi yana murmushin ya duka yai ma Allah sujudar godiya, tun a ranar ya rabawa abokansa da yan uwa 100k ya bawa Anty
500k ya rike 400k. A week later Ammy ta saka Nana ta kira shi ya zo ta hada shi tare da mutanen da Mai Martaba ya wakilta suka kai shi million quarters aka nuna masa gidan da Mai Martaba ya bashi, sai ya rasa bakin godiya, ba tabbatar da gaske ba ne sai d
a aka ba shi keys din gidan da takardu, ba shi kadai ba Anty ma kuka ta rika shi ganin katon gida mai gate da manyan dakuna da falo, ko'ina an gyara furniture ne kawai ba a saka ba, daman duk wanda ya san unguwar ya san yadda gidanjen unguwar suke da kyau
da tsaruwa, ba su da wani girma sosai sai dai an musu tsari mai kyau ta yadda kowa zai iya zama ciki, 500k din da Sardauna ya bata ta siya gado da duk wasu abubuwa na bukata, abun ka da mai nema ko sati ba a kara ba ta tare a gidan tare da Sardauna da daki
nsa ke daga waje kamar na saukar baki, mutanen unguwa da yan'uwa sai murna ake musu. After komai na karatu ya kammala Mai Martaba ya kira Sardauna da kansa suka ga juna ya sake yi masa kyautar kudi mai yawa kuma ya karbi account dinsa ya bawa Waziri, sabod
a a rika tura masa kudi time to time na karatun da yake, duk wani abu na biza da komai Mai Martaba ne ya biya kudi akai masa har komai ya zama ready.
Ana saura Two weeks ya bar kasar ya samu Anty Rabi da wata shawarar.
“Anty akwai maganar da nake son
mu yi wata magana, ban san yadda zaki kalli abun ba, amman ina ganin ya dace na tunatar da ke idan kin manta, domin zai amfane mu ne gaba daya”
Anty Rabi ta dauke hankalinta daga gurin karamin plasma ta kalleshi.
“To ina jinka”
“Anty daman akan
maganar aure ne, ni sai na ga kamar aure baya gabanki, kuma ya kamata ace kin yi aure domin kina da kurciyar da maza za su so ki, ko dan saboda ki kara tsare mutuncinki da kuma na yayanki, misali ni yanzu zan tafi karatu wata kasar, zan yi nesa dake ya kam
ata ace akwai Namiji a gidan wanda zai rika kula da gidan da kuma ke kanki,ko ba komai hakan zai kara miki kima a idon mutane kuma za ki samu wanda zai rika tsawatawa yaranki”
Anty ta yi murmushi.
“Sardauna kenan, ba auren ne bana so ba, zaman ne su
n zama sai hamdala, an mutu an barka da yara kana neman mai tallafa maka wasu kuma abun da suke dubi ya za ayi su ci daga gareka, kuma ba ko wane namiji ne yake son yayan wani ba, ba auren ne bana son ba, rayuwarce nake duba yadda tai tsanani kowa ta kansa
yake, yayana kuma a yanzu ba su da kamar ni a rayuwarsu, idan ba su jidadi a hannun mahaifiyaba a hannun wa za su ji?”
“Kina da gaskiya amman ai kin ga ke kina da gidanki kuma kina sana'arki, duk wanda zai aureki zai same ki a gidanki ne, idan yaji ba
zai iya ba kuma sai ya kama gabansa, ina jin tsoron yadda zan tafi na barku ku kadai ne a gidan nan”
“Allah shi zai kare mu, kai dai kai mana fatan tsarin Allah kawai”
“Allah ya tsare”
Ta amsa da Amin tana kallonsa, tun a lokacin ta fara kewar dan
'uwanta, ba dan neman ilmin zai je ba ta ba zata yarda yai nisa da ita ba. Ya fara shirye shiryensa da bankwana da mutane a cikin satin, ranar da ya sauka a uk sai ya ga komai sabo a gunsa turawan da yake gani a film yau gasu yana gani a fili, duk da kasan
cewar cikin dare suka isa kasar.
FADIME POV.
Suna sauka airport matoci har biyu suka zo daukarsu, a iya tunaninta masarautar za a sauke su sai ta ga an nufi wata unguwar da bata sani ba da su, ba dan hoton Baba Waziri da ta gani a falon Hajiya Ma
ryam ba wato uwargidan da tace ba a yola take ba, domin bata san kowa ba a cikin iyalan gidan, daga Hajiya Maryam har yaransa da kuma yaran Hajiya Talatu da kulawarsu ta dawo karkashin Hajiya Maryam, sakamakon haukacewar da mahaifiyarsu tai wato Hajiya Tal
atu.
Sun samu tarba ta musamman daga gurin Hajiya Mairo, sannan ta kaisu masaukinsu, a nan su ka yi karo ta kalolin abinci da aka jera musu, ga lafiyayyen gurin bachi da bandaki mai kyau, plasma da ac suna kunne suna aikinsu, ba laifi Fadime ta natsu sa
boda kunyar da take ji, sai dai ta taji muryar Namiji sai tai ta saurare tana son taji ko yana tare da Shattima ne. Washe garin ranar da suka iso da safe Baba Waziri ya shigo ya gaisa da su, kuma ya isar musu da sakon gaisuwar Ammy da Mai Martaba. Two days
after aka canjawa Fadime daki, aka kaita wani dakin na dabam, baka jin komai sai kamshi, gadonta da take bachi kamar an yi ambaliyar turare, kullum da safe mai aikin Hajiya Mairo zata shigo mata ta turare tai n jiki da na tsuguno da kuma na wanka, order H
ajiya Mairo tai mata tun daga Zamfara har yola, Yar gidan Mai Fata tai mata gadin kayanyaki kala kala tun daga na gyara jiki har na turaruka da kuma kayan mata, hadi tai mata na musamman na Amaren, kullum mai dilka zata zo tana gyara mata jiki, Fadime bata
fara kuka ba sai da aka fara mata shafa mata halawa, ta soma jin zafi tana ganin yadda ake fitar mata da gashin jiki kamar ba a sonta. Ba dan tana jin kunyar Hajiya Mairo ba da babu yadda za ayi ta kyale ana zaluntarta da sunan gyara, yanayin turaren da a
ke saka mata ana ana turara mata a jki da tufafi da kuma dakinta sai kamshi ya soma bin jikinta ta zarar ta wuce zaka ji kamshi yana tashi, farinta ya kara fitowa ga dogon hancinta gwanin sha'awa sai dai ta yi rama saboda fargabar gyaran jikin da ake mata
kullum da shi take kwana take tashi a ranta, domin har ga Allah abun ya isheta sai dai babu yadda ta iya.
A zatonta haka gyara jikin ne kawai a iya jikinta abun zai tsaya, sai gashi ta ga ta Hajiya Mairo da kanta take saka ta gaba tana bata hade haden da
aka karbo mata daga Zamfara, duk wanda Fadime ta sha ta ji a shi da dadi sai ta aje mai zakin sai ta shanye duka.
“Wannan naman duka za ki cinye”
“To”
Ta karba ta dan ci kadan sai ta ji shi kamar ba naman kaza ba, saboda hadin maganin da ya sha.
“Inna tace na daina shan abu mai daci yana da illa ga lafiya”
Hajiya Mairo ta yi murmushi.
“Wannan ba wata illa da zai miki sai dai ya kara miki lafiya, ki yi kokari ki cinye”
“To”
Ta saka bowl din a gabanta kamar ci zatai da gaske, ganin
hakan yasa Hajiya Mairo ta fice daga dakin, Fadime na ganin ta fita ta tashi ta shiga bandakin ta kunna fanfon ta wanke kazar ta dawo da ita ta ci ta a haka ba tare da magani ba.
“Haka kawai sai a rika bawa mutum abubuwa cikin mutum ma sai ya lalace”
Ta fada tana turo baki, duk yadda ta zo ta cinye kazar sai ta kasa saboda babbar kaza ce kuma Hajiya Mairo ta riga ta cika mata ciki da garin magani masu kyau.
Kwantawa tai saman gadon tana ta nishi kamar mai nakuda saboda cikar da cikinta yai.
“Ni g
askiya na gaji, kullum sai an bani wannan