Showing 156001 words to 159000 words out of 304903 words
saukinsa, abubuwa sai faruwa suke marar dadi, daman bata da lafiya ko da kika ce
wa Mai Martaba ita zaki je dubiya”
“Wallahi lafiyarta kalau, wai abun jiya ya fara zuwa yau”
Ta sauke ajiyar zuciya tana kara jin abubuwan sun mata nauyi fiye da da.
“Ina ganin ni Kaduna zan wuce kai tsaye in yaso sai ku ku wuce Yola, zama ai be
gan ni ba”
“Ki tafi Hajiya, ni kuma zan yi duk abin da ya dace da yardar Allah zan kara bincika mana wani wajen”
“To Hajiya Talatu dan Allah ayi kokari”
“Karki damu Hajiya kamar dai baki san wacece ni ba”
“Allah ya kyauta”
Shine kawai abun d
a Jurry ta fada ta mike tsaye ta fice daga dakin.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno,
gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka t
saya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkuba
ri abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Ni
geria.
37
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
FADIME POV.
Sai da ya zauna sannan ya aje mata akushi dake cike da kayan marmari.
“Ya
u ka ce zaka kai ni gida”
Ta fada tana kallonsa.
“Eh amman sai Baba na ya yarda”
“Ai kai kace yau ya yarda”
Ta fada da muryar dake nuna tana daf da fashe masa da kuka, domin har ga Allah zaman garin ya isheta.
Shiru yai yana kallon yadda idon
ta ya fara tara hawaye, ta rame sosai kamar wanda tai ciwo kana ganinta kasan akwai tashin hankali da kewa a tare da ita, be son ya sake fada mata wani wanda zai sakata kuka ko tashin hankali a yanzu, domin shi kanshi baya son wani bakincikin ya rabe ta.
“Baka ce komai ba”
Shiru be ce komai ba sai kallonta yake, kamar mai saka a abun da zai fada mata.
“Kai kace yau zaka kai ni gida, miyasa kake saba alkawari? Kuma miyasa ka ce idan ina tare da kai babu abun da zai same ni? Na san yanzu Inna da Bap
pa suna can suna nemana, ko ma su dauka na mutu”
“Zan kaiki gida amman sai Babana ya amince, bana son wani abu ya same ki ne”
“Ni babu abunda zai same ni kullum haka kake cewa, ni dai ka kai ni yanzu dan Allah”
Ta fashe masa da wani irin kuka mai
ban tausayi. Wasim ya kalli kakansa dake zaune yana cin abincin ya soma masa magana da yarensu.
“Yarinyar tana son ta tafi gida”
“Ta jira har sai shugaba ya amince”
“Zaka iya tirsasashi ya amince”
“Ba zan masa haka ba, saboda kai ka karya mana
doka, wannan horo ne wanda zai zame maka izina a nan gaba”
“Amman miyasa laifina zai shafeta?”
“Saboda ita ka aikata abun da ka aikata, karka sake tambayata”
Wasim ya sauke ajiyar zuciya tare da maida dubansa gurin Fadime.
“Ki karya sai na ka
i ki gida”
“Da gaske?”
“Na zan miki karya ba”
Ta kai hannu da sauri ta fara cin yayan itatuwan da kullum take karyawa da su, domin abincin garin baya mata dadi saboda basa saka sinadarin girki, (Magi) sai dai gishiri da wasu abubuwan na mutanen da
. Tana cikin ci Liya ta shigo dakin, Fadime ta zabura kamar wacce tai arba da mutuwa.
“Wayyo na ba ni”
Wasim ya juya a hankali ya kalleta, daga inda take tsaye ta risina tana yi ma kakansa gaisuwar ban girma sannan ta karaso inda Wasim yake.
“In
a son nai magana da kai”
Ta fada da yarensu, dauke kai yai daga barin kallonta ya cigaba da kallon Fadime da ke mata kallon tsoro.
“Ki ci zan tafi na kai ki gida yanzu”
“Na koshi, dan Allah ka ce ta tafi ta bar nan”
Cewar Fadime cike da tsoro,
uffan Wasim be ce ba ya kama wuyan hannun Fadime ya fito da ita daga dakin.
“Duk abun da na ce ki yi zaki yi?”
“Eh Wallahi ni ba zan sake saba umarnin kowa ba”
Yayi murmushi daman ya san za a rina indar Fadime ce, be sake ce mata komai b ya zagay
a da ita ta bayan dakin kakan ya rikata.
“Rufe idonki, komai kika ji karki bude”
“To”
Ta rufe idon da sauri, sai ya rikata kamar yadda ya rika Zainab ya saka bakinsa a goshinta ta yadda b zata iya bude idon ba ko da ta so yin haka. A hankali ta j
i kamar suna daga samawa daga kan faifai sai kuma ta ji sun sura a guje kamar iska ya dauke su.
“Wasim”
Ta kira sunansa dan tabbatarwa idan yana nan, sai ta ji shiru be amsa ta ba, kuma ba su daina bin iskan ba, hakan yasa ta fara kokarin bude idon,
sai ta ji idanuwan a like gam kamar an saka mata super glue.
“Na bani Wasim...”
Nan ma dai shiru, sai ta fara lalabe har kan fuskarsa ta ji alamar yana nan tukuna hankalinta ya dan kwanta, kamin tai wani yunkuri ta soma jin abun da suke kai yana yin
kasa kamar suna sauka. Sai jin kafafuwanta tai cikin ciyayi, a karo na biyu ta sake yunkurin bude idon ta kasa har sai da ya dauke bakinsa daga goshinta, da sauri ta bude idon sai ta sauke su akan Wasim dake ta faman sakar mata murmushi.
“Na san baban
ki ba zai bari ki sake fitowa ba, ni kuma saboda gudun wani abu ya same ki dole nai nisa da ke, zan yi marmarkin kuma zan rika ziyartar ta hanyar da be zama lallai ki gan ni ba”
Juyawa tai a hankali tana karewa guri kallo, sai a lokacin ta gane inda tak
e, bayan gidansu na zana ne ya aje ta da inda gonaki suke, gashi safiya ce babu wanda zai ganta. Hannunsa ya kai ya kama fuskarta yana kallon cikin idanuwanta.
“Kina na raka ki gurin babanki nai masa bayani?”
“Kam Wallahi ubana zai ci, ka tafiyar ka
dai”
“Bana son babanki ya doke ki”
Ta yi shiru tana tunanin irin hukuncin da Bappa zai mata. Can kuma ta kalli Wasim tana tuna abun da ya fada mata.
“Da gaske ba zan sake ganinka ba?”
“Zaki sake amman kamar da ba, kuma be zama lallai Bappa ya
barki ki sake fitowa ba”
Sai ta ji wani iri, tausayinsa ya kamata.
“Zan iya satar kafa na fito ba?”
Ya daga kansa sama yana murmushi kamin ya sake kallonta.
“Ba kin ce ba zaki sake kin jin magana ba?”
Sai tai shiru tana kallonsa kamar mara
r gaskiya.
“Fateme ina son na fada miki wani abu, ki saka a ranki ina kaunarki tun a ranar da na bara ganinki ba tare da kin sani ba, rayuwarki da mu'amalarki tana burge, wannan rawar kan da mutane suke ganin rashin natsuwarki da shi, ni burge ni kike
kina saka ni nishadi, ko da baki kusa da ni idan na tuna da ke sai na samu kaina cikin nishadi da marmarin ganinki ina kaunarki sosai Fateme, duk da na san addininmu da al'adarmu ba daya ba ne...”
Tun da ya fara maganar ta ji kanta na juyawa yana wani h
ayaki, zuciyarta ta buga da mugun karfi for the first time in history wani ya furta yana sonta yana kaunarta tana burgeshi.
“Wayyo zuciyata...”
Ta dafa zuciyar ta fadi kasa zaune dafe da zuciyar dake buga mata da mugun karfi. Risina Wasim yai yana k
allonta, suna hada ido sai duk taji ya cika mata idon kunya da nauyinsa sun yi rufeta, sai ta saka hannayenta ta rufe fuskarta tana wani irin murmushi da bata san ta ina yake zuwa mata ba. Ta dade a haka kamin ta bude idon, a zatonta zata ga Wasim ne tsugu
ne a gaban ta kamar dazun sai ta ga babu kowa sai ita kadai. Da sauri ta mike tsaye tana kabe jiki tana waige waige.
“Yau ko na shiga uku ga dadi ga wuya Wallahi sai Bappa ya doke ni”
Ta fashe da kuka, nan da nan ta nemi farincikin furta mata kalmar
so da Wasim yai ta rasa, hannanyenta ta saka cikin gashin kanta ta yamutsa gashin kamar wata mahaukaciya, sai ta bi hanyar gida tana wani langadi kamar wacce ta sha giya ta birkice ido kamar ba nata ba. Sai da ta isa bakin kofar sannan ta kwange hannayent
a ta fara jan kafa kamar wata musaka haka ta shiga cikin gidan, tana dalalar da yawu kamar gaske. Inna dake zaune gaban murhu tana damu kunu ta shure bokitin kunun da sauri ta nufi gurin shanu tana kiran sunan Allah, Nappa kuma ya fito daga bukkar Inna da
sauri yana kallon ikon Allah domin shi ma kansa ya tsorata da yanayinta. Daga bakin kofar Fadime ta fadi kasa tana da nishin karya, can kuma ta fara ashisshawa har uku alamar aljanun sun tafi kenan. Zumut ta tashi zaune tana waige waige.
“A ina nake a i
na nake? Bappa ina Inna?”
Bappa dai na tsaye yana kallon ikon Allah tsoro duk ya kama shi, domin be taba ganin Fadime a irin wannan yanayin ba, kuma baya saka ran zata iya irin wannan abun. Inna na jin an kira sunanta ta susuda ta fito cikin tsoro tana
leken Fadime.
“Fulani...”
“Na'am Inna”
Ta fashe da kuka, sa sauri Inna ta nufo inda take ita tana kukan murnar ganin yarta ta rumgumeta. Tun batan Fadime bata iya cin abincin kirki ga fadan Bappa ga tashin hankalin da take cikin ga kuma maganganun
mutanen kauye dake fadar Fadime ta kai kanta ga halaka, wasu kuma na fadin wai wata ta zo daga birni yar yankan kai ta tafi da Fadime, kowa da da abun da yake fada.
“Ina kika je Fulani?”
Shine abun da ya fito daga bakin Bappa, cikin kuka Fadime ta
kankame Inna tana bayanin karya.
“Ban je ko'ina ba Bappa bakin rijiyar can mai gaba dubu kawai na raka wannan matar, sai tace min ita zata kara cikin dajin ta dauki hoto, ni kuma na tsaya ina leken rijiyar sai na hango wani tsoho cikin rijiyar yana kal
lo sai cewa yai ke ce Fadime ko? To zan dauki fansa abun da Bappa ki yai min a bakin kasuwa, lallai sai Sama'ila ya dandana kudarsa, da ke zan fara amman zan zo kansa shi ma, sai na juyo da gudu daga nan ban sake sanin inda nake ba sai yanzu a ganni a nan.
...”
Ta kara fashewa da kuka, gaba daya sai jikin Bappa yai sanyi, karyar data tsara sai ta shiga cikin kwakwalwar Bappa tai zaune ras, jin an ambaci bakin kasuwa gurin da yake neman halalinsa, duk da dai ya san shi ba mafadaci ba ne, sai dai dan adam t
ara ne be cika goma ba, zai iya yiyuwa ya tsabawa wani cikin rashin sani kuma ya kasance ba mutum ba ne.
Sai dai abun mamaki miyasa wacan matar bata dawo ba, kuma police din da suka ce zasu je gobe su dawo su ma ba su dawo ba? Ga tufafin jikinta ba kala
r na su ne na fulani ba, to kodai ita ma matar da police din duka aljannu ne.? Gaba daya sai Bappa ya rasa wanne zai yi tunani, wata zuciyar tana kin bashi hadin kan yardar da maganar Fadime, sai dai kuma ya san bata san kowa a wacan garin ba balle yace a
can suka tafi tare da matar, amman idan ita matar ce ta tafi da ita fa? Kamin yai wani yunkura har mutane sun cika gidan suna ta yi ma Inna barka da dawowa Fadime, irin karyar da tai ma Bappa ta dora Inna tana ta fadawa mutane haka, kowa sai fadar albarkac
in bakinsa yake, wasu sun yarda wasu kuma su karyarta abun a zuciyarsu. Har mazan da basu yi sammakon fita ba suka rika sallamawa Bappa suna masa barka da arziki. Inna da kanta ta hadawa Fadime ruwan wanka Fadime ta shiga tai wanka ta fito ta shiga bukkart
a ta saka wasu tufafin tana ta tunanin Wasim, ta kasa daina murmushi kuma gabanta ya ki ya daina faduwa kan abunda ya fada mata a yau, da zarar ta tuna sai ta ji kunya duk ta rufe ta kamar yana gabanta yana kallonta.
Inna ce ta shigo cikin dakin ta aje m
ata sabuwar fura da ta ji nono ta fice tana amsa kiran da Bappa ke mata.
Fadime ta dauki furar ta sha cike da marmari sai kace wanda ta shekara goma bata gida sai a yanzu take jin sakewa nishadi. Sai da ta sha furar sosai sannan ta dauko jakar littafanta
ta bude ta dauko littafin da take rubuta ta fara sana'arta wato rubuta abubuwan da suka faru tun farkon zuwanta garinsu Wasim.
Tana tsaka da rubutun sai ga duhu ya maye ko'ina na dakin, kamar an dauke wutar nepa da dare haka idanuwanta suka cika da duh
u ta ko'ina kai kace ba 11am ba ce.
“Inna ranar ta dauke ne?”
Ta tambaya tana murza ido, kamin ta mike tsaye rike da littafin tana lalaben hanya.
“Wayyo na boni... Wayyo.... Wayyo... ”
FALMATA POV.
Gaba daya jin tai duniyar na
juya mata idan za ta yi tunani sai ta rasa ta inda zata fara, miyasa za a aura mata tsoho? Hakan na nufin an kashe mata rayuwa kenan gaba daya.
A yanzu kam ta yarda bata da wani buri da zai cika, bata da wata dama na yin komai ciki har da na zabin wanda
take so, ta ya zata rayu da tsohon mutumen da ya tsofi mahaifinta? Mutumen da bata taba ganinsa ba sai jiya? Idan bata amince ba tana da wani zabin ne? Ta isa ta musawa mahaifinta ne balle kuma Tumba da take tsoro?
Bayan gargadin da Tumba tai mata jiya
cewar idan ta ki amincewa zai iya korarta, idan ya koreta ina zata tafi? Wa zai karbeta? Ya rayuwarta zata kasance? Idan ta tuna wani bangaren na rayuwar Mansura da Sirleem ya bata labari sai ta ji bata son kasancewa a irin yanayin! Amman haka zata zuba id
o rayuwarta na tafi kullum bata da gata bata da iko akan komai? Tabbas wanda ke da uwa raye kuma ubansa yake kula da shi yayi babban dace, bata tana jin kewar mahaifiyarta ba irin wannan lokacin da ta gama yarda cewar bata da gata. Domin ta tabbatar da ace
mamanta tana raye da haka be faru no matter how bad Tumba zata so ta auri mutumen, tana son ta aure shi ne saboda taje ta wahala, da mutumen arziki ne da Naja za a bashi ko kuma a koreshi gaba daya.
Jin kamar yawun bakinta zai shaketa yasa ta tashi za
une hawaye na mata zuba.
“Mama ashe kin hango irin wahalar da zan sha shiyasa kika ce nai hakuri, shiyasa kika ce zaki tai ki bar ni a cikin kunci, kin ce min nasara tana nan tafe, amman har yanzu ban ganta, sai karin wahala”
Ta fada murya kasa kasa
tana fashewa da kuka. Can kuma ta yunkura ta tashi tsaye ta nufi kofar dakinsu ta bude ta fita tsakar gidan, gurin da suke ake botocinsu ta nufa ya dauki butar da ta fi alwala da ita zuba mata ruwa ta shiga bandakinsu haka nan cikin duhu tai fitsari sanna
n ta fito tai alwala a tsakar gidan. Bayan ta gama ta koma dakin ta dauko tabarmar da suke sallah da ita ta shimfida a waje ta saka hijabinta.
Sallah tai raka'a biyu raka'ar farko ta karanta ayatul kursiyu da kulhuwallahu, raka'a ta biyu ta karanta fatih
a da kulhuwallahu kafa uku sannan ta zauna tai zaman tahiya, bayan ta sallame ta daga hannunta sama tai fara salati ga annabi salatin ibrahimiya, sannan tai istigari sai kuma ta fara yabo da jinjina ga Allah, ya rabbana ya rabbana ya rabbana sannan ta fara
karanta huwallahul lazi la'ilaha.... Har zuwa karshe kalmomin da wasu malamai suka ce sune ismillahul azeem, bayan ta gama ta fara kankantarda kanta tana kuka.
“Ya Allah ya baiwar makaskanciya a cikin bayinka, Ya Allah ga mai yawan aikata sabo mai yaw
an zunubi, Ya Allah ga mai kaunar Rahamarka mai tsoron azabarka, ba ni da kowa Allah sai kai, gatan da nake da shi naka ne ya mahallicina, ya gata na, ya ubangijina, ya mai jinkaina, Allah ina godiya akan ni'imominka, rahamar a gareni ba zata kirguba, na g
ode maka Allah, kuma ina kara kawo kuka na a gareka babu mai ba ni sai kai, idan ka hanani wani be isa ya bani ba, Allah yau ma gani da kokon bara, Ya Allah ga Fateema a kasa na daga hannuna a sama ina rokonka, Allah ina cikin damuwa da bakinciki kuma na s
an ka sani, ba dan ka manta da ni ba, kuma ba ka so na