Showing 132001 words to 135000 words out of 304903 words

Chapter 45 - FULANI COMPLETE

sanyin jiki abubuwa suna faruwa da mu, ya kamata mu yi maganin komai tun a yanzu”

“Wai daman Nana ta fara dan hali Hajiya”

“Hmm Jarma kenan, ai har abunda ya fi sata sai Nana ta yi, ba ni da buri sai na ganin ku

kan Ammy kuma sai ta yi shi indai ina raye, yanzu dai ka nemo yaron kuma ka san wanda aka hannatawa case din, gobe ka zo ka karbi kudi ayi komai tun da wuri, abun ai ya zo mana da sauki tun da har haka ta faru”

“Shikenan Hajiya zan shigo gobe inshallah”

“Yayi kyau sai anjima”

Ta fada tana sauke wayar, tare da sauke wata doguwar ajiyar zuciya.

“Dole ne na shirya jibi nai tafiyar nan, idan ba haka ba ban san me zai sake faruwa ba, ya kamata na tari Fadimen ita kuma tun kamin ta tare ni”

Line H

ajiya Talatu ta nemo ta aika mata kira, ringing daya ta dauka kamar daman can jiran kiran take.

“Hello Talatu”

“Hajiya ina cikin tashin hankali, Waziri ya dage sai ya hada auren nan”

Ta amsa da muryar kuka wanda hakan ke nuna ta ci kukan har ta

gode Allah.

“Nima ina cikin nawa tashin hankali, amman dai ki shigo gobe sai mu yi magana, be kamata mu kyale yarinya akaita ga halaka ba”

“Shiyasa nake son tun wuri mu tafi garin nan tun da aikinsu kamar yankan wuka ne, su wargaza komai tun abu be

yi nisa ba”

“Hmm ke dai ki shigo gobe kawai”

“Tau Allah ya kai”

Hajiya ta sauke wayar tana jijjina lamarin bokayen nan sai yanzu ta kara tabbatar ba da wasa suke aiki ba, kuma dama ta dade tana son irinsu masu aiki kamar yankan wuka. A yanzu ne

take jin ya zame mata dole ta je garin ko dan maganin matsalolinta.

**

Shirun da Nana ta ji ne ya tabbatar mata da Hajiya ta gama wayar da take, sai ta daga daga jikin kofar wasu sabbin hawaye masu zafi na sauko mata. Why Hajiya zata juyar da case d

in to kisan kai bayan tace zata taimake ta? Mi Sardauna yai mata? Anya ya cancanci haka? Da sauri ta ta bar kofar ta dauki hanyar da zata sadata da part dinsu hawaye na sauko mata kamar ba gobe, daman ta bi bayan Hajiya ne da zimmar ta sake rokonta sai ta

tararda kofar dakin a rufe tana kokarin turawa ta ji sautin muryarta na tashi kadan-kadan hakan yasa ta kai kunnenta domin ta ji abun da Hajiya take fada, domin azatonta zata ji ko Jarma ya gano inda suke ne ko kuma wani abu sai gashi ta ji mummunan abu da

bata taba mafarkin ji ba, kuma ba tai zato daga Hajiya ba.

“Miyasa ma nai satar to? Why?”

Ta tambaya cikin kuka tana jin haushin kanta. Ganin bata da mai taimakonta a yanzu wanda zai fito da Sardauna, bata isa ta tunkari Ammy da wannan maganar ba,

daman daga Hajiya sai Zainab ne suke mata gata a gidan, sai kuma Shattima, sai dai ba zata iya fada masa ba, gudun kar Ammy taji ko Baba Waziri. Silently ta isa bangarensu ta shige dakinta ba tare da kowa ya sani ba. Maida kofar dakin tai ta rufe ta jingin

a da kofar ta fashe da sabon kuka tana kallon hoton AA dake gaban wayarsa. Haka ta shafe awa uku zaune a gurin tana aikin kuka abun da bata taba ba, idanuwanta da fuskarta suka kumbura, tun tana jin kuzarin kuka har ta nemi kuzarin ta rasa. Can ta mike tsa

ye ta cire tufafin jikinta ta dauki tufafin bachi ta saka ta shiga bandaki ta wanke fuskarta, sannan ta fito ta hau saman gadon ta kwanta ba dan tana jin zata iya bachin ba sai dan jin jikinta da take da rashin kwari. Misalin 10 da yan mintuna kiran Anti R

abi ya shigo wayar AA dake hannun Nana.

Second Mother shine rubuce a wayar dauke ta emoji din heart. Kasa daukar kiran tai sai kawai tai rejecting call din ta kashe wayar gaba daya.

“Innalillahi”

Ta furta, she can't remember when last ta furta wan

nan kalmar ma. Bata taba jin ta a tashin hankali irin yau ba, abun da ta ji Hajiya Babba na fada ya fi daga mata hankali fiye da halin data jefa AA. Sauka tai saman gadon ta bude kofar dakinta ta fito falo, babu kowa a falon an kashe kayan kallo wanda haka

n ke nuna Ammy tana bangaren Mai Martaba ko kuma tana shirin tafiya ne. Dakinta Nana ta dosa tana taba kofar ta ji ta a bude sai ta tura ta shiga, duk wani tsoron kar Ammy ta ji da take da gudun fadanta ko dukan Baba Waziri sai ta ne meshi ta rasa, bata da

buri a yanzu da ya wuce AA ya zama free. Daga bakin kofar ta tsaya tana kallon Ammy dake tsaye jikin wardrobe dinta tana daukar wasu kaya, ta jikin madubin wardrobe Ammy ta hango Nana sai ta juyo tana wani kallo fuska ba yabo ba fallasa.

“Ya akai?”

Nana ta kalleta hawaye na sauko mata, sai kuma ta nufi inda take ta karasa har kusa da ita.

“Ammy... ”

Sai kuma tai shiru hawayen na sauko mata.

“Ammy na san ni da ke don't get along, amman dan Allah ki taimaka min”

“Minene?”

“A gurin bik

in da naje dazun na su Amal na saci sarkar gold ta kawar Amal, nasan be dace nai sata ba right? Na sani amman ban san miyasa nai ba, direbana sai ya karbi sarkar yaje ya maida shine suka ce shine ya dauka kuma Wallahi ba shi ba ne ni ce, shine suka kira ma

sa police aka tafi da shi, dan Allah ki taimaka Ammy a fito da shi pls”

Ammy ta saki kayan hannunta sun zube kasa, tana yi ma Nana wani irin kallo kamar na tsoro kamar na mamaki, a take idonta ya cika da kwalla. Tassss ta dauke Nana da wani irin mahauka

cin mari, cikin wani irin zafin nama da bata taba sanin tana da shi sai yau.

“Sa... Sa... Sa... Sata Nana?”

Ta furta daker hawaye na sauko mata, Nana kam tun da Ammy ta tsinka mata mari tai bata da sauri tana ma Ammy wani kallo tsoro domin ji take k

amar babu fuska a jikinta.

“Na san be dace nai ba Ammy na sani....”

Ta furta a rikice tana girgiza ma Ammy kai. Sai kuma ta juya da gudu da fice daga dakin, Ammy ta bita da kallo baki sake, wani abu ta ji yana mata yawo a zuciya yana neman numfashin

ta, da sauri ta rike murfin wardrobe din ta jingina ta zauna a kasa tana numfashi daker.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ta furta daker tana ta kokuwa da numfashinta.

FADIME POV.

Hannu biyu Wasim ya saka ya dauki Fadime ya ya nufi ko

far fita, zaratan mazajen da suke fadar tsaye suka nufishi sai Sarkin ya daga musu alamar su kyaleshi. Zainab na ganin hakan ta bi bayansu yadda yake tafiya da gudu sai ka dauka biyo shi akai Fadime kam sai tari take hankalinta ya dade da barin jikinta. Du

k inda ya nasa kafarsa Zainab sai ta nasa tata, har suka isa wani karamin gida mai dauke da dakuna uku, dakin farko ya shiga wanda shi ya fi ko wane daki girma. Yana shiga ya kwantar da Fadime gaban makahon bokan ya soma magana da shi da yarensu.

“Kaka

ka taimaka mata ta daina tarin nan kar ta samu matsala”

Bokan ya mika hannunsa ya taba fuskar Fadime.

“Wasim miyasa ka aikata haka?”

Wasim be tsaya bashi amsa ba ya nufi inda bokan yake aje magani ya bude ya dauko wani garin magani ya cika hannu

nsa da shi ya zo ya zuba a bakin Fadime sannan ya dagata ya jinginar da ita jikinsa. Tana yin tarin garin maganin ya bi ta cikin makoshinta sai kaikayin yai kasa, haka ya rika sauka kasa kasa har ya daina mata gaba daya. Wani irin sanyayyiyar ajiyar zuciya

ta sauke ta lumshe ido sai bachin wahala. Duk abun da ake Zainab na tsaye kusa da Fadime, yadda yake ta kula da Fadime sai abun ya burgeta duk kuwa da kasancewar rabin hankalinta yana gurin nama da ta ci be mata komai ba. Daukar Fadime yai ya kwantar da i

ta kan wata shimfida dake dakin, ana dakin bokan kuma kakansa kadai yake da tabbacin zai aje Fadime mahaifinsa ko wani be taba ta, domin be isa ya fitar da ita daga garin ba tare da izinin sarkin ba, gudun kar a cutar da ita daga baya. Hannun Zainab ya rik

o ya fito da ita daga cikin dakin ya zagaya da ita wani guri mai hudu.

“Zan kai ki gida yanzu”

“Okay”

Ta amsa da sauri daman abun da take nema kenan.

“Amman camera tana can mun baro”

“Ki tsaya a nan karki je ko'ina”

Ya fada yana yin bay

a baya, kamin ya fice daga gidan, ko minti uku be yi ba ta hango shi ya dawo rike da jakar tata. Yana isowa ya mika mata jakar.

“Rike ta da kyau ki rufe idonki karki yarda ki bude”

“Tau”

Ta rufe idon da sauri, sai ya rika saitin kunkurunta ya kai

bakinsa saitin goshinta, yayi hakan ne ssboda kar ta bude idon, domin matukar bakinsa na kan goshinta ba zata iya bude idon ba. Wani irin tsam taji a hikinta, duk yadda ta so ta bude idonta Jin kamar tana kan wani abu sai ta kasa, har sai da ta ji kafafuw

anta a kasa, sannan ta bude idon a hankali ta sauke su a fuskar Wasim da hasken fari wata ke haska fuskarsa. Nesa kadan da gidansu Fadime ya sauke ta, ya kai hannunsa jikin walkinsa ya tsinki wani ziri daya ya kama hannunta ya daura mata.

“Shaidar kin

zo garin mu”

Ta kalli zaren sannan ta kalleshi.

“Yarinyar fa?”

“Zan kula da ita, ba zai yiyu ta dawo yanzu ba, ki yi tafiyar ki kawai karki bari iyayenta su ganki”

Ta daga masa kai tana binsa da kallo har sai da ta daina hangoshi sannan ta aje

jakar ta dauko wayarta ta kunna, number police din ta kira, bata wani dade tana ringing ba ya dauka.

“Hello Hajiya”

“Karka bari mutanen dake tare da kai su san na kiraka, kai musu sallama ka Fada musu tun da ban dawo ba ku za ku wuce, sai ka same n

i a gurin karfen sabis”

Ta fada tana daga kanta ta kalli karfen, sannan ta kashe wayar ta fara tafiya da kafa zuwa inda karfen yake, bata karasa ba sakon kar ta kwana wato sms ya shigo wayarta da line Auwal, jiki na rawa ta bude, sai tai arba da mummuna

n abu.

“Allah yayi ma Auwal Sa'ad rasuwa, idan akwai bashi a tsakaninku ki fada, ko ka fada a sauke nauyi”

Sai da ta karanta sakon sau ba adadi sannan ta yarda hausa take karantawa, bata san lokacin data saki jakar hannunta ba.

“Ya Allah........



Ta furta da karfi tana jin wani irin kuka na taso mata.

“Allah kasa ba gaske ba ne”

Ya shiga neman line Auwal din sai ta ji shi a rufe, ta sake bugawa ta ji shi a rufe, hannu ta dora saman kai hawaye a sauko mata.

“How...”

Sai kuma ta sh

iga neman line matarsa kai tsaye. Bata dade tana ringing ba matar ta dauka.

“Assalamu Alaikum”

Ba karamin jihadi Zainab tai ba na danne kukanta ta amsawa kawarta.

“Wa'alaikissalam, ya gida?”

“Lafiya Kalau Zainab, sai kewa da bakinciki”

“Da

gaske ne?”

“Ai ba a karyar mutuwa, Auwal ya tafi ya bar ni, na shiga liyin zaurawa yayansa kuma sun zama marayu”

Ta karasa cikin kuka. A sanyaye Zainab ta sauke wayar hawaye na bin fuskarka.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

Ta kashe wayar

ta durkushe a gurin fuskar Auwal nata yi mata gizo, kamar daga sama ta ji wani irin kuka ya sauko mata.

***

Cikin hikima police din suka yi ma Bappa Sallama suka kamo hanya, ya bar su sun tafi ne kawai Saboda ganin su police ne, ba dan haka ba, d

a ba za su tafi ba yarsa ba ta dawo ba, duk kuwa da kasancewar sun fada masa cewar ita Zainab din tana can wai dare yayi ba za su iya jira ba, idan ta dawo ta kwana a nan da safe za su zo su dauke ta. Suna tafiya Bappa ya koma cikin gida ya rufe Inna da f

ada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, Inna kam sai kuka take ga fadan Bappa gashi kuma tashin hankalin rashin ssnin halin da yar gudaliyar yarta take ciki ba, abun sai ya zame mata biyu ta rasa inda zata saka kanta.

_________

Ina ma

ta matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma

garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turar

en wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 

09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.

Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.

32

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 30

0 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

FALMATA POV.

Washe gari misalin bakwai na safe, Baba Adamu ya faka motarsa a inda ya sauke ta jiya sannan ya samu wani almajiri yai masa kwatancin da gidan ya aikas

hi kiranta, bayan yaron ya dawo ya fada masa cewar tace gata nan zuwa sai ya bashi 50 naira.

Ba a wani dade ba sai ga Falmata ta bullo sanye da hijabinta sai zuba sauri take kamar zata tashi sama.

“Ina kwana?”

“Lafiya Kalau”

Ta bude gidan baya

ta shiga, daidaikun mutanen dake gurin sai kallonta suke cike da burgewa, domin ganin Baba Adamu tsoho ya isa ya sanar musu cewar direba ne, and most of them sun san tana aiki a gidan Sarki, dan a mata haka ba komai bane tun jikokin sarki take kula da su.

Tun da ta shiga motarta hankalinta yana gurin titi har suka isa cikin masarautar, bakin gate din Ammy ya sauke ta ta fita motar tana masa godiya, sannan ta dauki hanyar shiga ciki.

“Ke....”

Wata Hadimar ta tabota da sauri tana nuna mata Jurry, sai

Jurry tai mata alama da ta zo da hannu. Jiki na rawa Falmata ta tunkare gate din su Jurry ta karasa kusa da ita ta risina har kasa tana gaisheta.

“Fada mata idan ta gama gyaran can ta zo ta gyara dakin Hajiya”

Wata matashiyar yarinya dake tsaye kus

a da jurry ta fadawa Falmata cikin daga murya.

“Tau”

Falmata ta amsa sannan ta mike tsaye ta koma bangaren Ammy, da kallo Jurry ta bita har ta shiga sannan ta juya ta koma ciki. Kamar kullum sai da tai knocking kofar aka bude mata sannan ta shiga ta

na gaishe da Inna wuro data bude mata kofar a maimakon Jekadiya data saba bude mata kofar a kullum. Har cikin falon ta karasa ta gaishe da Shattima dake hakimce saman kujera rike da mug yana kallon plasma, kallonta kawai yai ya dauke kai uffan be ce mata b

a har ta gaishe shi ta tashi ta nufi dakin yara. Sai da ta gyara komai tsab sannan Jekadiya ta shigo tai musu wanka ta shirya su, sannan Falmata ta soma tofesu da addu'a, tana cikin karantawa tana tofa musu Shattima ya shigo dakin. Kamshin turaren da taji

ne yasa ta waigo sai ta ganshi tsaye jikin kofar, domin ko kadan bata ji karar bude kofar ba saboda karancin jinta. Mikewa tai tsaye ta isa gabansa ta mika masa gaisuwa irin ta talaka da dan sarki sannan ta fice daga dakin. Sai da ta fice sannan ta ya saka

rwa yaransa murmushi, sai wasa suke cikin walwala da kuzarinsu, cikin wata irin tafiyar kasaita ya taka ya isa gaban yayansa ya shafa kansu, da za a bude zuciyarsa a yanzu da babu abun da za a gani sai farincikin addu'ar da Falmata tai wa yayansa, da kuma

irin walwalar daya tarar suna yi. Wayarsa ya ciro ya dauke su hoto sannan ya sake shafa kansu ya fice daga dakin, dakin Ammy ya shiga sai ya samu bata ciki, hakan yasa ya nufo dakin Nana domin yi mata sallama, sai ya same ta kwance saman gadonta ta dunkule

kamar marar lafiya.

“Nana lafiya kike kuwa?”

“Lafiya Kalau, kaina ke ciwo”

Ta amsa masa ba tare da ta bude blanket din ba.

“Kin sha magani?”

“Eh”

“Wane iri?”

Ta yi shiru, sai ya kai hannunsa ya yaye zanen data rufa da shi, hakan yas

a ta tashi zaune idonta a kumbure kana ganinta kasan ba tai bachi kirki ba.

“Fada min damuwarki, me ke damunki Nana?”

Ya tambaya hankalinsa a tashe, ta yi shiru sai hawaye take.

“Fada min mana, kina da wanda ya wuce ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login