Showing 174001 words to 177000 words out of 304903 words

Chapter 59 - FULANI COMPLETE

guda daya da Allah ya bata, ko kuma rushewar burikanta? Abubu

wan nan uku sai suka taru suka tokare mata zuciya. A gidan ta wuni duk wani mai rabon yayi mata gaisuwar Hajiya Hansai yayi mata, washe gari ta bi jirgin safe zuwa Yola ita da wasu yan'uwanta hudu, sai da jirgin ya sauka yola ta kira direbanta ya zo ya dau

ke su sannan mutuwar ta fara tabata, bata yarda ta rasa danta ba har sai da motarsu ta nutsa kai cikin Masarautar, arba da fara yi da manyan manyan motoci na alfarma, ga taron mutane a harabar masarautar ban da cikin fada.

“Innalillahi wa'inna ilaihirra

ji'un Allah haka ka kaddaro min”

Ta furta tana fitowa daga cikin motar, matan da ke tare da ita suma kuka kamar ita, kallo sai ya koma akanta masu ganin tausayinta na yi musamman wadanda suka san mutuwa biyu akai mata ba daya ba. Tana shiga bangarenta

sai aka bare da sabon kuka, kamar a lokacin akai mutuwar babu jin komai sai kukan rashin mamaci, a lokacin ne ta fara jin kamar ace zata iya ta dawo masa da ransa, sai dai bata da rabon sake ganinsa ma, domin tun ranar da abun ya faru aka kai shi makwancin

sa ma gaskiya bayan an masa wanka da sallah kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Yaranta daga Karima har Juwairiyya da Kausar kuka suke sosai, su kansu sun san sun fi rashin dan'uwa kuma jigo a rayuwarsu.

“Na yafe maka Talba, na yafe maka duk ab

un da kai min a cikin rashin sani ko kuskure ko ganganci, Allah ya yafe maka ya karbi bakuncinka”

Shine abun da Hajiya take fada tana wani irin kuka na fitar rai.

“Jama'a kana naka Allah na nashi, ashe Talba ba zai yi aure ya aje yara na gani ba, ash

e rayuwar da Allah ya bashi ba mai yawa ba ce, Wayyo Allah mutuwa bata yi ba”

A gaba daya falon babu wanda be yi kuka ba, tausayin Hajiya ya kama su, sakon mutuwa kenan mai sanarwa jiki da ruhi da hana zuciyar walwala ta rike buri ta tarwatsa farinciki.



Gasuwar sai ta zama biyu, idan an yi ta bangaren Hajiya Babba sai a nufi gurin Ammy ayi mata nata, wasu kuma sai su fara yi ma Ammy sannan su iso bangaren Hajiya Babba. Hajiya Talatu ta dawo kusa da Hajiya Babba ta zauna tana ta bata hakuri da kalamai n

a kwantar da hankali.

Har akai sadakan ukun Hajiya bata iya cin komai ruwa da dan abu mai kamar ruwa kamar lemu ko fura, cikin kankanen lokaci kibar nan ta zube ta koma kamar ba ita ba.

FALMATA POV.

“Lafiya miya faru?”

“Komai ma ai ya fa

ru Malam, yarinyar nan ta zama abun da ta zama bata min komai sai keta, ga halayen banza data kirkirawar kanta, yanzu na tashi da kafafuwa naje gidan Inna wuro na fada mata idan ba a biya albashin ta kirani da kaina na karba ko kuma ta karba ta kawo min ba

sai an ba Falmata, ai sai ta bani bakin labari wai Falmata taje cikin gidan ta saci sarkar matar sarki ta miliyan uku, kuma ta saci yan kunnen yaran da take reno, shine fa suka koreta, amman da yake yarinyar ta kware a iskanci sai ta kama bakinta tai shir

u bata fada ba, ashe duk kwana kin nan wani guri take zuwa tana wuni ba gurin aikin ba, ina ganin mai napep din da yake zuwa yana daukarta shine yake zuwa da ita can wani guri suna shashanci, nan gaba kadan yarinyar nan ciki zata kwaso maka”

“Miliyan uk

u? Fulani ke yanzu kin san ki saci abun miyan uku? Ina kika kaita?”

Baba ya fada yana dafa kirjinsa cike da mamaki da kuma tsoron kar ta ja masa zuwa gidan yari.

“Tace ai sun gane shiyasa suka karbe sarkar suka koreta, muna cikin zancen aka kirata wa

i yaran sun mutu”

A lokacin ne Falmata ta samu labarin rasuwar su Labib, a take ta ji wani irin tausayin yaran ya kamata har shakuwar da tai da su sai ta dawo mata sabuwa. Bata ankaro ba ta ji Baba yayi cikinta da duka, duka bana wasa ba domin katon ice

n girkin ya dauka ya rafka mata a kafafuwa, sannan ya shiga dukanta ta ko'ina gaba daya hankalinsa yayi mugun tashi, duk da bashi da tabbacin idan gaskiya Tumba ta fada masa, be tsaya ya saurari Falmata ba. Sai da yai mata lis da kuka kamar zai kasheta san

nan ya bar ta a gurin kwance ko motsin kirki bata iyawa.

“Ni dai Wallahi da zaka dauki shawarata kamata yai ka aurar da ita kawai ka huta, tun da mutumen yace baya son komai, ba sai an kai auren nan nesa ba, daman can saboda aikin nan ne yasa na zabi lo

kacin yanzu kuwa tun da ba aikin kuma gashi ta fara lalacewa ai ka aurar da ita kawai ka huta”

“Haka zan yi, idan ban yi haka ba ba zata bari hankalina ya kwanta ba, miliyan uku fa? Kiranshi zan yi a waya idan ya zo zan ce masa an canja lokaci”

“Eh W

allahi ni ban ki an maida shi nan da sati daya ba ma, a daura auren ya dauke ta can mu huta da fitina, tun har Allah ya hutar da kai yace baya son komai”

Baba ya nufi inda ya barar da jakar buhunsa ya dauka ya shige dakin cike da takaici sai huci yake.

A waje Falmata ta kwana saboda bata iya komai sakamakon dukan da Baba yai mata, gashi bata da gatan da wani zai rikata ya shigar da ita dakin ko ya kawo mata abun rufa, ta zazzabi ta kwana sai nishi take kamar mai shirin haihuwa, ko'ina a jikinta zafi y

ake mata, bata ko iya motsa kafarta ta dama domin a gurin Baba yafi dukanta.

Washe gari da safe Baba ya kira surukin nasa mai suna Malam Mansur, ya sanar masa yana son ganinsa, sai ya fada masa cewar ya tafi kauye gurin wani sha'anin sai dai idan ya dawo

zai zo. Da haka su kai sallama Baba be fada masa komai ba saboda ya fi son ganinsa face to face.

Da daker da shudin goshi Falmata ta samu ta shiga bandaki tai fitsari ta fito tai alwala ta shiga dakin tai sallah, sannan ta zube a gurin kwance ta fashe d

a sabon kuka tana tausayin kanta. Babu abun da yafi tsaya mata a rai kamar maganar auren da Tumba tai, wanda Babanta ya hau kai ya zauna, bata sani ba wata kila shi ma tsohon mai duka ne kamar Babanta, wata kila shi ma be da hali mai kyau, idan taje can wa

ta kila wata wahalar zata sha, a nan zai zauna da ita ko a kauye? Tana jin lokacin da Baba ke fadawa Tumba cewar kar ta sake bari ta fita daga cikin gidan ta ji wani sabon kuka ya zo mata, shikenan ba zata sake zuwa gurin Momy ba, ba zata sake ganin Sirlee

m ba, sai ta ji wani sabon bakinciki ya sallamo mata, wasu hawayen suka fara zubo mata.

SHATTIMA POV.

Jirgin safe ya bi, ya sauka a Yola in time sai dai ko da ya isa an yi ma yaransa sutura da kuma dan'uwansa har an bar masarautar da su. Ya

tarar da masauratar cike da mutane masu amsar gaisuwar da kuma amsu zuwa yi, manyan mutane suka rika zuwa gaisuwar, duk da kasancewar ba kowa ya san Talba ba, domin ba kasafai kake ganinsa a harkokin gidan ba.

Washen gari ranar da akai sadakan uku yana

zaune Dakin Ammy, bayan wasu yan gaisuwar sun fita, suna magana akan mutuwar Talba da yadda ta zowa kowa a bazata, Ammy ta dauko zancen yaransa Labib.

“Tun da yarinyar nan ta tafi sai su zama wasu marar lafiya, da ko har walwala suke suna wasansu, nan

da nan sai ciwo ya dawo sabo”

“Ina ta tafi?”

Ya tambaya ba tare daya kalli Ammy ba.

“Sata tai”

“Sata?”

Sai da Ammy ta dauki lokaci kamin ta labarta masa abun da ya faru.

“Ta taba daukar wani abu a nan kamin nan”

“Ba zamu iya ganewa b

a, tun da ba tsare ta ake ba”

“Amman an bata kudin aikin da tai?”

“Bata dawo ba ai, tun da suka tafi can bata sake dawowa ba, amman Jekadiya tace min wai Sirleem ya fita da ita har ya mari Juwairiyya”

Shattima ya sake kallon Ammy da mamaki yana tu

na wacan ranar.

“Sirleem”

Ya furta a hankali.

“Ammy baki yi tunanin akwai abun da zai iya saka yarinyar sata ba? Tana cikin halin rayuwa na san tahirinta, wata kila ta yi satar ne saboda ta taimaki kanta, Akwai inda sata ya halatta fa, Idan har da

gaske ta yin, wata kila kuma shari ne kawai”

“To wa zai mata sherin?”

“Sirleem mana, so that ya samu ta bar gidan, shi kuma yana da damar yin komai da ita ”

Ammy ta masa wani kallon mamaki.

“Ban san miyasa kake munanawa Sirleem zato ba, ko ba

komai yar'uwarka yake so ba, be kamata kana haka ba, kasancewarsa mawaki be rage shi da komai ba sai daukaka da suna”

“Ammay ba ki san waye Sirleem ba, yaron nan har rumgumarta yai before na tafi”

“Yaushe ya santa?”

A take mamaki ya cika Ammy domi

n ta san ba Shattima ba zai mata karya ba. Nana ce ta shigo dakin sanye da uniform din na islamiya cikin ladabi ta gaishe da Ammy kamar ba ita ba sannan ta mikawa Shattima gaisuwa, ya amsa da mamaki, sai ya ji ta burgeshi, a tunaninsa mutuwar da akai ne ya

sa ta natsu.

“Ammy zan tafi islamiya”

“To Allah ya tsare”

“Amin”

Har ta juya sai kuma ta juyo.

“Ya Shattima ka san Hajiya Karama bata gidan nan?”

“Nana ina ganin kamar kin fara hankali, taya zaki masa wannan maganar a yanzu?”

“Ammy ba

dadi gidan, na saba da ita kuma kowa ya saba da ita, be kamata ta tafi ba”

Shattima ya juyo yana kallon Ammy.

“Miya faru?”

“Zamu yi magana anjima”

Kai ya daga mata sannan ya kalli Nana da murmushin karfin hali a fuskarsa.

“Je karki yi latti”

“To, kuma Yaya ina son magana da kai idan na dawo”

“Okay”

Ta juya ta fita a natse kamar ba ita. Ba Shattima ko Ammy ta jidadin yadda yarta ta dawo mai natsuwa cikin yan kwanakin nan abun da ta dade tana nema.

“I think mutuwar nan ta taba Nana”

“Ba mutuwa bace tun kamin mutuwa ta koma haka, abubuwa da yawa sun faru baka da labari, marasa dadi, ina ganin natsuwar bata Allah da annabi bace”

“Miya faru?”

Sai da Ammy ta labarta masa abun da Nana tai sannan ta biyo masa da zancen Zainab. At

first dariya abun ya bashi duk da kasancewar yana cikin yanayin marar dadi.

“What if Iya ta fara rudewa ne Ammy? Kin san dai Zainab ba zata turo ta ta fadi haka ba, i think tana da wanda zata aura ma ai”

“Na ji ance ya rasu ai, kuma idan ita Zainab b

ata nuna mata ba, iya ba zata zo ta same ni da maganar ba, kuma dan rainin hankali sai suka tattara suka bar gidan, ni za su nunawa isa da zuciya? Miye masarautar nan ba taiwa Zainab ba da Iya?”

“Amman da su akai amsar gaisuwa ai shiyasa ban gane cewar

sun bar gidan ba”

“Suna zuwa ne dai”

“Bana tunanin Zainab zata yi haka, ta dauke ni ne kamar dan'uwanta, tana yawan fada min damuwarta da duk wani abu daya ta so mata”

“Sake mata da kai da yawa shiyasa har ta fara tunanin sonta kake”

Ya sake

yin murmushi domin shi kam abun dariya yake ba shi.

“Wata kila tayi hakan ne saboda karamci, a halin da nake ciki yanzu ai ba ko wace uwa ce zata bani auren yarta ba”

“Haka ne”

Ammy ta amsa wani tunanin na zo mata, miyasa Iya zata kawo tallar Zai

nab a gurinsa bayan ta fi kowa sanin halin da Shattima yake ciki? Amma Waziri ma yana kokarin yin haka, wata zuciyar ta raya mata. Mikewa Shattima yai tsaye yana saka hannyensa aljihu ya fito daga dakin.

“Jekadiya a nemo yarinyar nan”

Jekadiya ta da

ga masa hannu da sauri alamar girmamawa.

“To za a nemo ta”

Ta amsa ba dan ta fahimci yarinyar da yake magana kai ba, kuma kwarjininsa ba zai barta ta tambaya ba.

“Yarinyar da tai renon su Labib”

Sai da ya kara gaba kadan sannan ya furta hakan

ba tare daya juyo ba, yai ficewarsa abinsa. Yana fita Jekadiya ta fice ita neman Inna wuro.

Kasa ya sauko har lokacin mutane shigowa suke suna gaisuwa, hakan yasa shi zabar zuwa garden ya kebe kansa, a dya daga cikin kujerun da suke gurin ya zauna yana ko

karin ciro wayarsa, arba da yai da hotunan yaransa da suke screem din yasa jin wani iri, kewa da wata sabuwar kaunarsu ta sauko masa a kirji, sai a yanzu yake kara jin bakinciki rasa su da yai, sai dai babu wanda ya isa yaja da hukuncin Allah yadda Allah y

a tsara haka ke tabbatuwa. A hankali yaa sauke ajiyar zuciya lumshe ido ya bude ya busar da iskar bakinsa.

Ku yi hakuri daga yanzu sai dare zan rika posting inshallah saboda wasu uzuririka da suka sha gabana, ni kaina ba haka na so ba Wallahi. Ay

i min a fuwa dan Allah

🙏

41

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Yana zaune garden din har la'asar, sai da ya ji kiran sallah sannan y

a mike tsaye ya fito daga garden din, a fanfan masallaci yai alwala kamar sauran mutane sannan ya shiga cikin masallacin ya daidaita sahu tare da sauran talakawan gidan.

Bayan sun sauke nauyin sallah la'asar ya addu'a sannan ya fito ya nufi bangaren Mai M

artaba. Yau ma kamar ko yaushe yana zaune falo, sai dai wannan karon yana tare da Waziri ne da alama suna tattauna wata maganar ne. Da sallama Shattima ya shigo ya zauna a kasa yayinda iyayensa suke zaune akan kujera.

Sai da ya fara gaida Baba Waziri san

nan ya mikawa Mai Martaba tashi gaisuwar.

“Omar ya hakuri?”

“Alhamdulillah Mai Martaba”

“Ayi ta hakuri, rayuwa tana zuwa haka daman, abubuwa biyu sun zo maka a lokaci daya, rashin dan'uwa da kuma yaya, amman idan kai hakuri sai ka ga komai ya wuce



“Inshallah na gode Allah kara girma”

“Ameen”

Waziri ya amsa sannan yana murmushi, Shattima ya mike tsaye tare da yi musu sallama sannan ya fice. Sai ya fito ya saka hannunsa aljihu ya ji babu keys din motarsa sai a lokacin ya tuna da ya bar su a

dakin Ammy. Ba dan yana son zuwa ba babu abun da zai maida shi part din daukar keys saboda mutanen dake shiga shi kuma ba mutum ne mai son hayaniya ba, da kallo. Gashi kuma bayan son kowa ya tuka shi da sai ya kira Baba Adamu, hakan nan ya daure ya koma b

angaren Ammy din. Be kalli kowa a falon balle ya lura da mutanen da suke ciki duk kuwa da irin gaisuwar da ake mika masa, sai da yai knocking sannan ya tura kofar a hankali ya shiga. Wata kawar Ammy ya samu a dakin tare da Ammy suna gaisawa.

“Shattima

ya aka ji da hakuri?”

Cewar Matar sai ya amsa mata a takaice.

“Alhamdulillah”

“Allah ya masu ceto ne”

“Amin na gode”

Har ya dauki keys din zai juya Ammy ta kira shi.

“Shattima”

Sai ya juyo ba tare daya amsa ba.

“Yarinyar da kace a

kira tana falo”

“Okay”

Ya juya ya fita, har ya iso tsakiyar falon be daga ido ya kalli kowa ba.

“Jekadiya yarinyar ta same ni waje”

Ya fada ba dan yana da tabbacin Jekadiya tana wajen ba, sai dan ya san ko bata nan dole a nemota a fada mata sa

konsa, sai kuwa aka yi sa'a tana gurin ta amsa da to tare da yi ma Falmata a lama data mike tsaye, Falmata ta mike tsaye daker tana dingishi ta bi bayan Jekadiya suka fita daga bangaren, daker da wahala ta sauko stairs din saboda kafarta da bata ko son mot

sawa, haka ma da zata hawa sai da tai ta wai wai sannan ta samu ta haye har ta shiga cikin falon ita da Inna wuro.

Iyakar inda zata iya hange sai da ta duba ita da jekadiya amman ba su ganshi ba, gasu tsaye a rana suna ta duban inda yake ba su gashi ba,

shi kuma isa ta hana shi yi musu wata alama da za su ganshi, ya hakimce cikin motar sai kallonsu yake, Jekadiya bata sa ran yana gurin motarsa ba, idan ma yana can wace daga ciki? Can dai wata zuciyar ta raya mata taje ta duba ko yana gurin ko kuma Garden

duk da ta san be cika zuwa gardn din gidan ba.

“Zo mu duba nan”

Ta nufi gurin Motacinsa da suke fake a dabam da sauran motocin gidan, ta hanyar kukan motar da ta ji a kunne ne ta gane cewar yana cikin bakar motar, sai ta ja ta tsaya ita da Falmata h

ar sai da yaga dama ya sauke gilashin motar. Da hannu yai mata alama da ta tafi sai ta juya ta koma inda ta fito, Falmata kuma ta sirina a gaban ganbun motar idonta a kasa, gabanta sai faduwa yake domin bata san dalilin kiran ba.

“Me ya samu kafarki?”

Ya fada yana kallon saman kanta daga inda yake zaune cikin motar. A tunaninta be kamata ta fadawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login