Showing 126001 words to 129000 words out of 304903 words
kafafauwanta suka fara lankwashewa kamar wata musaka. Nesa da Sarkin Wasim ya tsaya ya saki hannun
Fadime ya risina da kafarsa daya ya dukarda kansa ya kwashi gaisuwa.
“Barka da wannan lokacin Shugaba”
Ya fada da yarensu, a maimakon Sarkin ya amsa masa sai wata tsohuwa ce mai bakin zane ta amsa masa tana takowa zuwa inda yake tare da jero masa t
ambayoyi.
“Su waye wannan Shugabana?”
Wasim ya mike tsaye da kyau yana kallon tsohuwar kamar ba zai amsa mata ba.
“Yan garin nan ne, be zama lallai ki san kowa a garin nan ba”
Ya amsa mata da yarensu, kamin Liya ta nuna Fadime data magana da
yaren da su kadai suke ji.
“Na san wacan yarinyar, yana zuwa gurinta, a wani gari da yake yamma da garin nan...”
Fadime ta kara fito da idonta waje, duk da kasancewar bata san me Liya take fada ba amman nuna ta take, gashi ta ga Wasim ma a nan shi y
a risina a maimakon a risina masa, take mararta ta kara cika da fitsari, hannunta ta kai ta bugu Wasim yana kallonta ta soma masa magana a cikin ranta.
“Fitsari nake ji fitsari”
Ta fada a ranta tana mutsika masa ido tana masa alamar yadda zai gane.
Shi dai kam be fahimci komai ba hakan yasa ya maida hankalinsa gurin Liya.
“Ina magana tana magana saboda an daure mata ta yi yadda take so a masarauta, mi zai saka na fadi abun da ba shi ba a gaban Shugaba? Ya zama lallai sai kun san kowa a garin nan
ba, amman lallai ne kowa ya san ku”
Ya fada da yarensu yana watsawa Liya wani mugun kallo. Hannu Sarki ya daga sai tsohuwar taja baya ta nufi wani guri daya fi kama da bukka a cikin fadar, bata dade ba ta fito rike da ture wanda ke dauke da soyayyen nam
a, ta mikawa Zainab.
“Ci”
Ta fada da yarensu, Zainab ta kai hannu ta dauki yanka daya da sauri ba dan ta san abunda ta fada ba, jiki na rawa ta kai bakinta ta tauna ta hade, daga lokacin ne gaban Liya ya fadi ganin ba tai komai ba. Tsohuwar ta matsa
da naman kusa da Fadime.
“Ci”
Tana fadin haka Fadime ta kalli Wasim da sauri, sai ya amsawa tsohuwar da yarensu.
“Bata cin nama”
“Na yau ne kawai, kuma umarnin Shugaba ne, ci”
Ta karasa tana kallon Fadime, da sauri Fadime ta kai hannu ta
dauki yanka daya tana kuka ta kai bakinta, bata ko tsaya tauna shi ba ta hadiye. A take ta ji wani abu ya taso mata tun daga cikin cikinta ya nufo makoshinta, wani irin kaikayin bala'i ne ta ji a makoshinta, daga Wasim har tsohuwar da Sarkin da Liya kallon
ta suke.
“Wacan ta mu ce wacan bare ce”
Tsohuwar ta fada tana nuna Fadime, tana yin baya-baya, wani irin ihu Fadime ta saka ta rike makoshin tana kuka.
“Wayyo kaikayi wayyo Allah kaikayi”
Da sauri Wasim ya maida ita bayansa, yana kallon Mahaif
insa, Zainab kam mutuwar tsaye tai a gurin ganin ita ta ci be mata komai ba, amman ga Fadime rike da makoshi wasu yawu masu yauki na mata zuba kamar kubewa sai kuka take tana wani irin tari, tana yagar wuyanta da yatsun hannunta. Murmushin jindadi ne ya fa
dada kansa a fuskar Liya tana kallon yadda Fadime ke tari tana susar wuya cike da shauki.
“Errugabea da, nire errua da ez dakiela ezer, tira egin nion”
“Bata da laifi, laifina ne bata san komai ba, ni na janyo ta”
Ya fada yana ta kokarin tare Fa
dime daga kallon da Sarkin ke mata. Hakan da yai kadai ya isa ya karantar da Sarkin cewar son ta yake.
“WASIM...!”
sarkin ya fada yana gyada kai a hankali tare da kara hade rai kamar bakin hadari, Fadime kam faduwa tai a gurin hankalinta na kokarin
bacewa saboda kai kayin bala'i da take ji a makoshinta, Wasim ya duka da sauri ya rike ta. Zainab na tsaye a gurin tana shafa wuyanta ba dan tana jin komai ba sai dan tambayoyin da take da su.
NANA POV.
Wani irin murmushi take tana kallon kanta
a madubi, ita kanta ta san ta yi kyau matuka red gown din dake jikinta ta haskata, daman can Nana ba mace ce mai son doguwar kwaliya ba, hoda ce kawai a fuskarta sai jan baki data shafa. Mikewa tai tsaye ta dauki purse dinta ta saka takalminta sannan ta n
ufi kofa tana takawa kamar wata Amarya. Ko da ta fito babu kowa a falon Ammy hakan kuma ba karamin dadi yai mata ba, sai ta nisa ta hanyar da Ammy take hana ta fita, da sauri sauri ta rika tafiyar gudun kar ta hadu da Ammy ta hana ta zuwa budan kan. Tana i
sa cikin fadar Ammy ta bude kofar ta baya ta fita. Daidai kofar AA ya faka motar, daman tun 7:40pm ya iso ya aika wata Hadima ta fada mata ya iso sai ta umarce hadimar ta fada masa ya dawo ta kofar fadar Ammy. AA na ganin Nana ya fito daga motar yai tsaye
yana kallonta, gaba daya ta sake ta masa mugun kyau kamar ba ita ba, abun ka da marar jiki sai sigar ta kama jikinta kamar wata yar tsana. Ita kanta kallonsa take domin yayi kyau fiye da kullum ba zaka ganshi ka ce direba ba ne dan masu kasa haka ya fito.
Murmushi ta sakar masa ganin yadda yake kallonta, sai shi ma ya mayar mata da murmushin ya bude mata gidan baya, saukowa tai a hankali ta shiga motar sai ya rufe ya bude mazaunin direba ya shiga ya zauna, sai ya samu kansa da rashin natsuwa har sai da ya j
uyo ya kalleta, be taba ganinta da kwaliya ba sai a yau, ashe haka take da kyau? Ya raya a zuciyarsa.
“Kin yi kyau”
Ya furta a fili yana jin wani irin girmanta na kama shi, duk sai yaji ta zame masa kamar ba ita ba ya ji nauyinta na sauko masa.
“
Na gode kai ma ai ka yi kyau”
“Thank Youu, ina zamu je?”
“X&L Hotel”
Ya juya yana shakar kamshin turarenta daya cika motar ya bata da na shi karamin turaren. Madubin motar ya saita ya juya ta inda zai rika ganin fuskarta sannan ya kunna wutar mota
r ya kunna ac. A hankali yake ta tuka motar yana satar kallon Nana ta madubin motar, a duk lokacin da suka hada ido sai ta saka masa murmushi. Daga ita har har shi babu wanda yai wata magana har suka isa.
X&L Hotel babbar Hotel ce a garin Yola, wanda man
yan mutane suke zuwa yin taro ko biki ko sauka idan ta kama, ko kuma shakawatawa.
A harabar Hotel din ya faka motarsa sannan ya fito ya bude mata ta fito.
“Zaka shiga ciki?”
“Ana bari a gashi?”
“Yes zan ce kai bodyguard dina ne”
“Okay”
Ya
rufe motar yana jindadi, daman can ya dade yana son ya shiga gurin domin ya dade yana jin labarin Hotel din sai dai be taba zuwa. A maimako tai gaba ya bi bayanta sai ta tsaya ta jera tare da shi, yadda ya ci ado ita ma ta ci sai abun ya bada kala kamar s
aurayi da budurwa, a tare suka doshi wata karamar hanya da aka kawata kamin su karasa wani saurayi ya kira sunan Nana, da sunan da Zainab take kiranta da shi.
“Baby”
Nana ta juyo tana arba da saurayin ta washe hakora ta doshi inda yake, AA kuma ya t
saya a gurin yana kallonsu, side hug tai masa suka gaisa.
“How are you?”
“I'm fine, kai ma ka zo biki”
“Yeah friend din mu ne zai yi aure, amman mu ba ciki zamu shiga ba, waya kawo ki Sirleem?”
Juyawa tai ta kalli AA a ganin be cancanta ta kir
a direbanta ba a yadda ya ci gayun nan.
“No wani ne”
“Okay sai mun hadu ciki”
Ya fada yana sannan ya nufi hanyar shiga gurin. Ita kuma ta juyo ta dawo gurin AA.
“Mu tafi”
“Ba zamu je din ba”
Ya fada yana watsa mata harara.
“Me akai?”
“Ya zaki rumgume wani kato da ba muharramin ki ba”
“To ai cousin dina ne”
“Ba cousin ba kwarkwata, bari na sake ganin kin rika hannun wani sai na fasa miki kai”
Ya karasa da kwafa ita kuma ta turo baki.
“To Wallahi zan ma koreka daga aikin”
Ya kwaikwayi muryarta yana yatsina fuska.
“To Wallahi zan ma koreka daga aikin”
“Kuma karka bi ni ciki, ba zan shiga ba”
“Wallahi sai na biki, sai na shiga, kuma muna shiga ciki kika ga wani kika masa magana sai na bata miki rai”
Ya fada w
ith serious face, yana kara hade mata rai kamar irin shi ne boss ita take aiki karkashinsa. Tana yin gana ya bi bayanta sai ta juyo tana turo baki.
“Ka daina bina”
“Sai na biki kuma ki kaiwa wani namiji magana sai na bata miki rai”
Wani irin abu
taji kamar ta saka kuka, sai kuma ta juya ta cigaba da tafiya yana binta bayanta har suka isa gurin. Bata nuna gate pass din ba sai kawai ta fada masa sunanta.
“Nana Aisha Abdallah Jari”
Da sauri ya bude mata kofar ta wuce AA ya bi bayanta yana fadi
n shi bodyguard dinta ne. Kato dakin taro ne da aka kawata da ado na zamani ga haske ko'ina kamar rana, mutane ta ko'ina kana ganin bikin kasan na manyan mutane ne. Kusa da kofar AA ya tsaya Nana kuma ta fara raba ido tana kallon mutane, ta nan ta hango Ha
jiya Babba cikin matan manya sai far'a take ana ta fira, can kuma ta hango kawarta Amal, da sauri ta nufi inda suke Amal din na ganinta ta rumgume ta tana murna kamin ta ja mata kujera ta zauna, duk abun da suke idon AA na kanta ita a tana yi tana satar ka
llonsa, tana son ta bar kujerar ta koma wata inda take hango wasu friends nata, da zarar ta mike tsaye sai AA ya bata mata fuska na babba da yaro sai ta koma ta zauna tana watsa masa harara tana turo baki. Sai da ya tabbatar ta natsu sannan ya fita daga gu
rin ya koma cikin motar ya zauna.
Kari aka fara yi ma Amarya wanda hakan yasa su Amal din tashi ita da kawayenta, suka nufi gurin Amaryar aka bar Nana ita kadai, wata kawar Amal din ce mai suna Rukayya ta dawo gurin ta aje handbag dinta ta cire sarkarta
ta zinari ta saka a jakar.
“Sis dan Allah zan bar jakata a nan ki kula min, sarkar tana damuna ne”
“Okay”
Nana ta amsa duk da bata san ba sai a lokacin. Yarinyar na barin gurin zuciyar Nana ta fara raya mata ta dauki sarkar, hannunta ya soma wani
irin kai kayi, wani abu ta soma ji ba dadi, har ta kai hannunta a jakar sai kuma gai saurin cirewa tana kallon jama'ar gurin da ba su kula da ita ba. Dagawa tai daga zaunen da take ta saka hannunta a kasa ta dannenshi amman bata ji ya daina mata kaikayi b
a, ba kaikai irin wanda aka saba ji ba kai kai yi a daukar abu wanda take jin a duk lokacin da so satar wa Ammy ko Mai Martaba kudi. Ciro hannun tai tana yarfarwa sannan ta kai cikin jakar ta dauko sarkar mai tsada ta saka a purse dinta ta mike tsaye da sa
uri ta fice daga gurin.
Sai da ta fito daga gurin sai kuma tai tsaye idonta ya cika da hawaye, bata taba abun da ba na Ammy ba sai da yau bata taba sata in public place like this ba sai a yau. Ji take kamar ta koma ta maida kuma tana jin tsoro. Takawa ta
fara yi ta nufi gurin motarsu, tana isa ta bude motar ta shiga gidan bayan. AA dake zaune ya juyo ya kalleta.
“An gama bikin ne?”
“Aa”
Ta amsa da muryar kuka, jin hakan yasa ya juyo da kyau ya kunna wutar motar yana kallonta, sai hawaye ya gani
a fuskarta.
“Ya akai?”
“Wani abu nai”
“Wani abu na mi?”
Ta yi shiru sai kuma ta ce.
“Sata nai na saci sakar wata kawar kawata”
Ba shiri AA ya zaro ido.
“Sata kuma?”
“Eh ai be kamata nai sata ba ko?”
“Then why kika yi?”
“I d
on't know i just feel like ina son nai, amman be kamata nai ba, kuma na san akwai camera a gurin zata nuna ni, kuma yarinyar ni ta bawa ajiyar jakarta”
“Nana me zai saka ki yi sata? Why, be kamata ace kina sata ba Nana baki bata sunan gidanku da mahaifi
nki, mi kika rasa ma da zaki yi sata? Why?”
“Ban sani ba, haka nan kawai nake yi”
Ta amsa shi tana kuka, wani tunanin ne ya zo masa kar dai ace kudin da take kashewa sato su take?
“Ina sarkar?”
Ta bude purse din ta dauko ta mika masa.
“Gas
hi”
Ya mika hannu ya karba.
“Akwai gate pass ne”
“Eh”
Ta ciro ta mika masa, sai ya karba.
“Ki koma ciki ki dauki wayarki sai ki samu gurin da babu mutane sosai ki kara wayar a kunne kamar kina waya, idan tai magana ki ce kin bar jakar ne ki
n je ki yi waya, zan shigo yanzu”
“Amman bani da waya Baba Waziri ya karbe”
Ya kika mata wayarsa.
“Rike wannan”
Ta Karba sannan ta bude motar ta fita ta nufi gurin tana share hawayenta gabanta sai faduwa yake. Da kallo ya bita har ta shige san
nan ya sauke ajiyar zuciya yana jin wani iri a ransa.
“So. That's mean kudin da take bani satarsu take yi? What's wrong with her?”
Ya furta yana ganin rashin dacewar hakan, sannan ya bude motar ya fita ta doshi guri.
FALMATA POV.
Tara da
yan mintuna yaran su kai bachi amman tana zaune a dakin domin cika umarnin Shattima da jekadiya ta fada mata sai 10 zata tafi gida, ko kadan bata jidadin hakan ba, sai dai bata isa tai musa ba balle ta tsaba, ta sani suna mata haka ne saboda kawai bata da
galihu, saboda tana aiki karkashinsu. Wannan abun kadai ya isa yasa ta kara kaunar Sirleem a ranta, ko ba komai ya tausaya mata, ya nuna mata kulawa kuma ya taimaketa. Sai da goma tai sannan Jekadiya ta shigo dakin.
“Za ki iya tafiya yanzu, direba na
waje yana jiranki, daga gobe har kullum zai rika zuwa daukoki misalin 7am”
“Tau na gode”
Ta fada tana risinawa sannan ta mike tsaye ta fice daga dakin. A natse ta shigo falon Ammy, al'adar ta ce indai akwai mutane a falon ba zata fice ba sai ta taje
ta gaishesu. Hakan yasa ta karasa gaban Ammy ta kwashi gaisuwa sannan ta risina gaban Yarima ta mika masa gaisuwa. Kara ma Ammy ta amsa shi kam ban da kallonta komai be yi ba, babu alamar amsar a tare da shi. Mikewa tai tsaye ta nufi kofar fita, fitarta da
kamar minti daya ya mike tsaye ya nufi backyard din falon Ammy, tsaye a gurin yana kallon yadda ta nufi motar, da kuma Sirleem daya fito daga bangarensu ya doso inda take.
“Ina wuni, Malam dan Allah kai ne aka ce zaka kai ni gida?”
Falmata ta tamba
ya tana leken Baba Adamu dake gaban motar.
“Eh ni ne”
Ya amsa mata, sai ta matsar da kunnenta kusa da shi.
“Dan Allah sake fada bana ji sosai”
“Eh ni ne”
Ya fada da karfi.
“Tau na gode”
Ta mike tsaye tana jin alamar mutum a bayanta,
da sauri ta juyo sai tai arba da Sirleem.
“Gida zaki je?”
Ya rada mata a kunne yana murmushi.
“Eh wannan zai kai ni gida”
“Ina maganinki yake?”
“Gashi”
Ta fada tana kokarin fiddo da hannunta cikin hijabin, bata karasa ba ya kai hannuns
a cikin hijabin ya karbi maganin ya dora saman motar yana amsa gaisuwa da Baba Adamu ke masa, sai da ya fitar da maganin na digawa sannan ya rika fuskarta ya ja hijabinta baya ya fito da kunnuwanta ya kwantar da kanta ya diga mata maganin a kunne daya, ya
saka mata kada sannan ya sake digawa a dayan kunne ya saka mata kada kana na rufe maganin.
“Karki yi wasa ki rika amfani da shi kullum, ta fada min magani ne mai tsada ta siya miki”
“Inshallah, na gode Allah ya saka da alheri”
“Never mind”
Ya
fada yana fadada fuskarsa da murmushi sannan ya bude mata bayan motar, ta shiga ya rufe ya daga mata hannu, ita kuma ta juyo tana kallonsa ta bayan motar har suka fita daga harabar sannan ta juyo ta zauna daidai tana jin wani irin abu a zuciyarta mai wuyar
fassara, abun da bata taba ji ba sai a yau, abun da ba zata iya fadar ga kalarsa ba balle yanayinsa, idanuwanta ne suka cika da kwalla sai ta rumgume hannayenta ta lumshe ido.
**
Sai da suka wuce sannan Shattima ya bar backyard din ya dawo cikin fa
lon ya zauna kusa da Ammy.
“Ni kam sai nake ganin kamar Sirleem ba son Nana yake ba”
Ammy ta kalleshi.
“Kamar ya?”
Ya daga kafadunsa, alamar haka nan dai.
“Idan baya son ta ai ba zai nuna ba, tun da ba dole aka masa ba, ya dai rage kula t
a ne kamar baya, saboda kun saka masa ido”
Be sake cewa komai ya ciro