Showing 39001 words to 42000 words out of 304903 words

Chapter 14 - FULANI COMPLETE

hakura ta kwanta a gurin tana ta hawaye, ba hawayen kwana a gurin kadai ba har da hannunta da take jin kamar ya karye saboda mugun rikon da Baba yai ma hannun nata, ga kafarta da ya daure da karfen rodi ya tsuke mata kafar sosai.

Ba tai wani bachi kirk

i ba saboda kuka da ciwon hannu da kafa da kuma warin fitsarin dabbobin dake gurin, sai da rana ta fara fitowa sannan Tumba ta zo ta kwance ta.

“Na gode”

Falmata ta fada tana kallon Tumba da idanuwanta da suka kankance tsabar kuka da wahala, ba ta y

i zaton za ta kwance ta wuri haka ba ya dauka ko sai ta kwana biyu ko fiye ma.

“Tashi kije ki shirya ki tafi gurin aikin”

“To”

Ta fada jikinta na ta rawa wani irin sanyi take ji yana ratsata kamar zazzabi na son rufe ta. Duk yadda ta so tai wanka

kamin ta fara yin sallah sai ta kasa saboda hannunta bata iya komai da shi ga kafarta ma dingishi take, haka nan dai ta wanke jikinta sannan tai alwala ta shiga dakinsu ta saka wasu tufafin tai sallah ta fito tana jin jiri na dibarta ta durkusa a wahale t

a gaishe da mahaifinta.

“Baba ina kwana?”

Be amsa ba daman yana tsaye ne yana sauraren abunda Tumba take fada masa akan Khadija cikin tsawa ya ce.

“Babu ke babu Khadija daga yau, balle har ki je gidansu, na miki tsakani da ita”

“To Baba”

T

a amsa masa tana jin kamar ba zata iya numfashi ba, ga idonta sai ciwo yake, mikewa tai tsaye bayan ta gaishe da Tumba ta nufi kofar fita kamar wata musaka ta fice daga gidan. Da kallo Baba ya fita har ta fice sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali ta yad

da Tumba ba zata ji ya juya ya koma cikin dakinta.

Kai tsaye Masarautar Falmata ta nufa a ranta tana ta addu'ar Allah yasa su karbe ba, domin idan ba su karbe ta ba bata san yadda zata yi ba, kamar yadda ta saba sai ta gaishe da kowa take shiga ciki, sai

dai bata tsaya jiran su amsa tun da ko sun amsa idan ba su kwarai ba ba ji za tai ba. Sai da ta kawo gate din da zai sadata da bangren Ammy cikin rashin sa'a ta hango Iya tsaye ita da wasu matan gidan tana magana, a take jikinta yai sanyi, ta san ko kowa

zai ji rokonta ya karbi uzurinta ban da Iya, duk da baya san wacece ita ba amman ta lura da bata son ta tun farkon zuwanta gidan, bayan Iya akwai Zainab da Shattima su ma tana tsironsu ba ma kamar Shattima da shi ya kamata da kansa tana taba masa ya.

  J

i tai ba zata iya karasawa ciki ba ba kuma zata iya komawa gida ba, sai kawai ta koma gurin kofar babban gate na uku ta zauna tana ta kukanta marar sauti.

*****      *****       *****      *****

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Shi ne abun da

kowa yake fada, Ammy ta karbe ta daga hannun Baaba tana jirgizawa, amman babu alamar rai a tare da ita

“Hajiya a kira likita”

“Ko kuma a je asibiti kai tsaye ba”

Ammy ta hada hankalinta a tashe, Iya ce ta karaso gurin tana tambayar abun da ya faru

.

“Wallahi Luna ce, ta buga kwallowa, tana ta ihu ko da muka daukota jikin yayi zafi kamar wuta, daga nan bata sake motsi ba”

“Innalillahi”

Iya ta fada tana karbarta daga hannun Ammy.

“Ayi sauri a tafi asibiti ai ba tsayawa za ayi ba”

Ammy

da kanta ta shiga ta dauko mayafinta ita da Baaba da Iya suka nufi asbitin. A lokacin ne labarin ya karade Masarautar kowa ya san abun da ake ciki ban da Nana da hankalinta be kai can ba, domin tana bangaren Hajiya kuma Hajiya ba ta yi magana a gabanta ba

ita kadai ce a falon tana ta kallon Tv duk da hankalinta baya wajen.

Ta kusan minti talatin a falon sannan ta taso ta dawo bangarensu, ta tararda manyan masu hidimar gidan zaune a falon cikin har da wasu kanen mahaifinta mata da suke zaune cikin masarau

tar, amman Nana bata tsaya ta kula kowa ba balle ma ta tambayi abun da yake faruwa. Kai tsaye ta wuce dakinta ta shige da rufo kofar ta hau saman gado ta kwanta, jikinta na bata ba lafiya ba amman ba zata iya tambaya ba.

Sai da ta ji hayaniyar na so ma ya

wa har da masu kuka sannan ta fito ta tsaya jikin kofar dakinta tana kallon Hajiya Karama dake kuka sosai ita da sauran matan, Shattima na zaune kan cushion kansa a kasa Iya kuma na zaune kasa tana kusar kuka kamar ba gobe. Sai a lokacin gabanta ya so ma f

aduwa, kar dai Mai Martaba ya rasu? Da sauri ta karasa fitowa ta nufo gurin da Shattima yake zaune ta zauna tana tambayarsa.

“Ya miya faru why kowa yake kuka?”

“We lost Luna”

Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba. A take ita ma ta fashe da kuka t

a riko shi.

“Ya How?”

Dagowa yai ya kalleta da idonsa da suka rine su kai ja, kana ganin kasan ransa a bace yake.

“Lokacinta ne yai”

“Ita take?”

“Tana ciki za a mata sutura”

Ya fada bayan ya nuna mata kofar da bakinsa, kallon kofar tai s

ai ta kwantar da kanta jikin yayanta ta fashe da kuka sosai. Kusan a falon Shattima ne kawai be yi kuka ba, sauran daga masu kuka suna ihu sai masu hawaye domin ko ba ka yi niyar kuka ba ganin yadda Iya da Nana da Zainab suke kuka dole ya baka tausayi ga k

uma Shattima da ya kasa kallon kowa ya kasa tashi daga gurin.

Sai da ana daf da za a fara mata sallah sannan Hajiya Balki ta shigo falon da Hijabinta da carbi a hannun tana kuka. Sai da aka fara shigowa gaisuwa sannan yaranta suka shigo suka zaune a fa

lon Ammy ana amsar gaisuwa da su.

Da dare Waziri ya tara kowa na gadan ya fada musu kar wanda ya sanarwa Mai Martaba da maganar mutuwar Luna. Kuma wannan zaman gaisuwar shi ne na karshe duk wanda ya zo sai dai yai musu ya tafi. A cikin daren Mama Fulani

ta dawo daga kauyen da tafi sakamakon wayar da aka buga mata aka labarta mata abunda ya faru.

Misalin ten Shattima ya shigo falon tare da wasu friends dinsa su kai ma Ammy gaisuwa sannan ya wuce da su bangaren Hajiya Balki su kai mata gaisuwa ita ma.

  Bayan sun fita Mama Fulani take cewa.

“Ni wannan abun har mamaki yake bani Wallahi, abu kamar ba banza ba”

Ammy ta kalleta.

“Wani lokacin ana munana zato, saboda an san akwai makiya kuma babu abunda basa iyawa, haka Waziri yake yawan fada wai

yana ganin kamar da sa hannun wani a lamarin gidan nan”

“Ya Waziri yana da gaskiya, ni kaina sai da mu kai maganar da shi, kuma maganarsa abun dubawa ce, tsakani da Allah da can ba haka ake ba, ki duba ki ga yadda suka mai da Mai Martaba ace kana sarki

babban sarki amman an maida ke a daki zaune komai sai dai a labarta maka iyalinka ma ba kowa ke shiga ya ganka ba?”

“To wa za ka yi zargi Fulani? Wasu dabam ko kuma a cikin masarautar ko a tsakaninmu, kanensa ko yan'uwa ko kuma matansa? Yanzu abunda ake

ta yayatawa a gidan nan wai har da sa hannu a cikin ciwonsa saboda ina son da na ya gaji mulki”

Mama Fulani ta rike baki.

“Iko sai Allah ke kuma”

“Wallahi hake ake fada ance na mallake masarauta ni na ke da ikon kowa sai yadda na yi, in ban da r

ashin tunani taya macen da zata auri mutumen tun tsufansa har kawo yanzu da yara suka girma sai kuma na ce wai ina son ya mutu a dora dana? Wallahi ni ban taba yi ma Shattima kwadayin sarautar nan ba, Shattima da be cika son damuwa ba ina ma zai iya da sar

auta? Yau ko babu ran Mai Martaba akwai kanensa masu so na nesa da na kusa, kuma sarautar yanzu ai ta sama waka sani waya sanka me ka tara me kake da shi, ni ban taba masa fatan hawan wannan sarautar ba ko can da balle kuma yanzu”

“Wallahi Hajiya karki

ce dan muna uwa daya uba daya nake wani zargi, Wallahi har ga Allah ba dan muna uba daya da jarma ba wallahi sai nake ganin kamar har da sa hannunsa a lamarin nan, saboda kwadayenyen mutum ne, kuma ya so a bashi sarautar nan tun tuni”

Ammy ta sauke ajiy

ar zuciya.

“Wani lokacin sai ka yi zaton da ba haka yake ba, mu dai mun bar wa Allah komai yai mana magani”

“Amman gaskiya a tashi tsaye nema masa na hausa”

“Ai an gwada, idan aka masa na hausar sai ki ga kullum abun na kara gaba har tsoro yake ba

mu, kuma kin ga idan an karbo ta nan ita ma Hajiya Balki ta gurinta tana karbowa sai ka rasa wanene na kwarai wanene mugun, shiyasa aka ce adaina ba shi gaba daya a cigaba da masa addua kawai”

“Allah ya kyauta”

“Amin”

Ammy ta amsa, sannan ta kai

hannunta ya janyo cooler abincin da ke gefen gadonta sai ga Nana ta shigo sanye da kayan bachi, ta zauna kusa da Ammy kanta a kasa.

“Ya akai?”

“Ba komai Ammy nan zan kwana”

“To sai ki kwanta tare da Gwaggonki, ni kin san dakin Mai Martaba zan kwa

na”

“Ni dai da ke nake son na kwana please”

“No ba zai yiyu ba Nana tsoro kike ji?”

Ta gyada kai.

“To kije dakin Zainab ki kwana ya miki”

Ta gyada kai sai kuma ya kwantar da kanta jikin Ammy. Ammy ta shafa kanta zuwa kafadarta.

“Kin ci

abinci?”

“Aa bana so”

“Gobe dai za ki koma school”

Ta dago kanta da sauri ta kalli Ammy.

“An samu sabon driver ne?”

“No School bus za ta zo ta dauke ki”

Ta bata fuska har ga Allah ita dai bata son zuwa makaranta.

“Ammy no please”

“B

a ni na saka ba Waziri ne, kamin ya bar nan ma sai da ya fada min zaki koma gidansa da zama idan an gama gaisuwa”

Da sauri Nana ta bar jikin Ammy ta koma jikin kanwar mahaifinta wato Mama Fulani.

“Mama Fulani dan Allah ki saka baki bana son zama gida

n Baba Waziri Wallahi”

“Ya Waziri ai daman ba shi da dadin zama da yara ba ke kadai ba duk yara ba son zama gurinsa, zan masa magana ya bar ki zauna nan sai ki cigaba da karatunki”

“Eh dan Allah”

Nana ta fada cikin kuka tana daga mata kai. A dakin

ta kwanta duk firar da Mama Fulani da Ammy suke tana ji ta labe sosai kamar mai bachi alhalin idonta a bude yake.

Misalin sha biyu Ammy tai ma Mama Fulani sallama ta sannan ta leka Nana.

“Nana...”

“Na'am”

“Ba ki bachi ba? Tashi ki je dakin Zai

nab ki kwanta, ko nan kike so?”

“A a zan je can”

“Goodnight”

Ammy ta fada tana shafa bayanta, har cikin ranta take kaunar yarta, sai dai dabi'un da Nana take yasa basa jituwa da Ammy har Nana take ganin kamar Hajiya ta fi Ammy son ta. Sai da Ammy

ta fice sannan Mama Fulani ta fashi ta shiga bandaki, da sauri Nana ta mike tsaye ta bude wardrobe Ammy ta inda ta san tana aje kudi ta fara mata bincike, tana yi tana kallon kofar bathroom bata samu komai ba yasa tai saurin rufewa ta fice daga dakin da sa

uri. Zainab na zaune gaban system dinta tana duba wani aiki Nana ta kwankwaso kofar dakin.

“Waye?”

“Hajiya Karama ni ce”

Jin muryar Nana yasa ta tashi taje ta bude mata kofar.

“Baby”

Ta kirata da sunan da take kiranta da shi.

“Na'am na

n zan kwana”

“Tos shigo”

Ya matsa nata daga jikin kofar, sai da Nana ta shig sannan Zainab ta rufe dakin ta dawo ta zauna a inda take tana hamma. Nana ta cire talkamin kafarta ta kwanata saman gadon tana ta kallon zoben zinarin da Zainab da aje kan b

ed side drawer.

          Washe gari aka tashi gidan kowa shiru shiru ba ma kamar Ammy da Zainab, Ammy ta tsorota da mutuwar Luna ne sai take ganin kamar so min tabi ne zata iya rasa mijinta, gashi kwana biyun nan sai mafarke take da bata gane kansu. Z

ainab kuma ta damu da mutuwar kuma ta damu da halin da Shattima zai shiga duk da ta san ba zai nuna ba amman abun yana nan cikin zuciyarsa.

Kowa yana falon suna karyawa ban da Ammy dake kitchen tana hadawa Mai Martaba nasa abun karyarwa dabam. Kadan kada

n Nana take cin abincin tana sanye da uniform dinta sai satar kallon Shattima take da ya ke ta kurba tea shi a hankali. Sirleem ne ya shigo falon be yi sallama ba sai da ya iso dinning room din, Shattima ne kadai ya amsa masa Zainab kam tai kamar bata gan

shi ba.

“I'm sorry for your lost Allah ya yasa masu ceto ne my condolences please”

Ya mikawa Shattima hannu, Shattima ma ya miko masa nasa suka gaisa.

“Thanks”

Shattima ya fada yana kallon Ammy wacce ta fito daga kitchen din tana murmushi.

“Sirleem”

“Na'am Ammy barka da tashi ya hakuri?”

“Al-hamdulillah”

“Allah masu rahama”

“Amin Thank U”

Yana kokarin juyawa Nana ta mike tsaye da sauri ta ce.

“Ya Sirleem dan Allah zaka sauke ni makaranta?”

“No School bus zata zo ta da

uke ki”

Ammy ta amsa mata, Nana ta bata fuska kamar zata fasa kuka. Sirleem be ce komai ba ya juya ya fice daga bangaren gaba daya, daman saboda yai ma Shattima gaisuwa ya shigo, saboda jiya be masa gaisuwar saboda baya son fitowa cikin mutane.

Daga

bangaren Ammy ya koma bangarensu, sai ya tararsa falon ba kowa tsabanin dazun da ya bar kanensa suna karyawa. Kai tsaye yai nufi bangaren corridor da zai sadashi da dakin Hajiya. A hankali yake takawa har ya isa kofar dakin, yana kokarin kai hannunsa ya t

ura sai ya ji shi a rufe.

“Hmmm ai na jidadi Wallahi an rage mugun iri, sauran su bi baya mu huta, da sannu mugun abun su zai koma musu ai, kin ga idon shi wai? Da wannan makirar sai kuka take kamar yarta”

Shiru yai yana sauraren muryar mahaifiyar

sa. Can kuma ya ji ta ce.

“To shikenan bari na duba yanzu”

Fasa kwankwasa kofar yai ya juyo zuciyarsa cike da tambayoyi kala kala. Da wa Hajiya take? A waya take magana ko da wani? Be shiga dakinsa ba ya sauka downstairs. Ya nufi gurin motarsa tun k

an ya karasa ya danna key hannunsa, yana isa ya bude motar ya shiga, be san inda zai je ba at this early morning, but haka nan dai ya tashi jikin nasa ba dadi yau, haka yasa kowa ya karya shi yana gefen falon zaune.

*

🐄🐄

FULANI

🐄🐄

*

By Khadeeja Ca

ndy

*11*

A hankali ya fara driving din da dayan hannunsa dayan kuma yana shafa fuskarta da ke annuri kamar wani sabon ango. Tun ka ya karasa babban gate din ya hango wata duke ta rufe kanta wanda hakan ke muna alamar kuka take. Very slowly ya kara

sa kusa da gate din, ya mika hannunsa ya dauko facing cap dinsa ya saka ya dauki bakin gilashinsa dake cikin motar ya saka, sannan ya sauke gilashin motar yana kallonta, kuka take a hankali wanda in baka saurara sosai ba zaka iya ji ba.

“Ke...”

Ya k

irata da muryarsa mai dadi sauraro, sai dai yanayin da yai mata kiran ba zata iya ji ba, saboda ita din ba ta da lafiyar kunne a yanzu.

“Hey....”

Still bata dago ba dan bata san ma yanayi ba. Be sake na uku ba ya data gilashin motarsa ya cigaba da dr

iving dinsa sanyin ac motar na ratsa ko'ina na jikinsa. Kamin ya karasa babban gate din wayarsa tai ring, cikin very low volume, hannunsa ya sa ya ciro wayar daga aljihunsa yana dubawa yai arba da Mansura. Murmushi yai kamin yai picking call din da Bluetoo

th din dake kunnesa.

“Hey Baby”

“Baby kana ina?”

“Gani zan fito daga gida”

“Ina zaka je?”

“I don't know kawai na ji bana son zaman gidan ne”

“Baby i miss you”

“Miss you too, on wednesday zan dawo Kaduna”

“I can't wait ina jin kamar

na biyoka yanzu, i miss everything about you, your smell, your hug, your smile and everything, ina jin kamar idan ka auri wata ba ni ba zan iya mutuwa”

Ya karshe maganar da muryar da ke nuna tana daf da fashewa da kuka, sai tausayinta ya kara shiga zuc

iyarsa.

“Even if na auri Nana still zan aure ki, Hajiya ta yarda na auri Nana first then na auri duk wacce nake son aure daga baya, and i promise you....”

Sai kuma ya kasa karasawa what if yai mata alkawari kuma ya tsaba? What if Hajiya ta hana shi

aurenta gaba daya?

“I know lokaci zai zo da zaka kasa daga kirana ma, but no matter what ina son kasan cewa ina kaunarka Sirleem, Hajiya tana son ka auri Nana ne saboda Nana ta fi ni kyau, ta fini kurciya ta fini asali ta fini komai, na san idan ka aure

ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login