Showing 258001 words to 261000 words out of 304903 words

Chapter 87 - FULANI COMPLETE

/>
nu saman kai tana kalmar shahada, kowa na gurin sai da ya cika da tsananin mamaki, Baba Waziri ya girgiza kai.

“Azzaluma, ke da baki da gadonmu amman kin san ki yi kwadayin sarautar ku? Bayan duk hallacin da akai miki”

Ta motsa daker tana fadin.

“Suna ta yankana”

“Su waye?”

“Wadanda na cinyewa kurwa, ga su sun tsare ni suna ta yankana”

Ta shiga zana sunayensu a wahalce.

“Allah yasa su kashe ki, Azzaluma macuciya, macijiyar soshiya”

Baba Waziri ya fada cikin bakinciki da bacin rai.

“A ina kika rufe kurwar Mai Martaba?”

“Tana gida”

Ta fada kamar wanda ta kusa mutuwa muryar tai mata nisa.

“Tashi muje ki kwance ta”

“Ba kafa, kankarar maita ta min nauyi a ciki”

Ta fada daker tana numfashi a wahale. Sai Baba Waziri yas

a mutanen da suka mata duka su jata a kasa, bayan ya bada umarnin a shigo da mota har gurin kofar falon Hajiya Talatu.

Baba Waziri ya saka a ka dauko bargo kato aka rufa mata saboda feshin wutar da take, janta suka fara yi amman suka kasa janta sakamako

n wani uban nauyi da tai kamar dutse, sai da suka hada karfinsu suka hadu su biyar sannan suka iya daukarta suka fito da ita waje shi ma daker, a cikin wata hilos aka saka ta Baba Waziri da wasu muhimman mutane suka shiga wata motar, Ammy ta shiga motar ta

ita da driver ta sai da suna daf da fita sannan Baba Waziri ya kira Shattima ya labarta masa halin da ake ciki domin tun da akai jana'izarta akai gaisuwa 2pm tai sai ya bar gurin ya koma gidansa. Ko kamin su isa gidan Zainab da ke million quarters Shattim

a ya riga su har ya faka motarsa cikin gidan, sai dai be fito ba ya jira har suka karaso, Mai Gadin dai sai kallon ikon Allah yake ganin an zo da motoci ga Iya a bargo kamar wata mage.

“Shegiya kafira sai nauyi kamar namam wuta”

Daya daga cikin ssma

rin ya fada a yayinda da suke ta kokarin ganin sun fito da ita daga bayan motar dake bude. Daker da sudin goshi suka dauko da ita daga motar suka nufi kofar falon dake bude da ita, domin tun da mazan nan suka fita Zainab bata taba kofar ba ta nufi makota t

a zauna a can har sai Iya ta dawo.



“Wani guri?”

“Dakina”

Ta fada daker domin idon nata ya rufe bata ganin komai sai duhu, sai da aka kira Mai gadin sannan ya nuna dakinta ba dan yana da tabbaci ba, ana shiga dakin su ka tararda da shi a yamuts

e, sai da suka ja baya sannan suka jan bargon suka budeta har lokacin bata daina tartsatsin wutar ba, kallo kawai take ba dan tana ganin komai ba.

“Ku daga gadon ku dauko min kwarya”

“Gadon dake bude ko baki gani ne”

Dayan ya fada.

“To ku ba n

i kwarya”

Da kafa dayan ya tura mata kwayar dake can gafe aje, sai ta taba ta fara lalabe har ta kama kurwar ta shiga kwancewa, ganin kawai suke hannunta na kwance amman ba su ganin zaren da kuma abun da take kwancewar gani suke hannunta na ta yawo, sai

da ta gama ta daga hannun sama kadan saboda ciwon da suke mata ta jefa kurwa a nan kam sun ga zakara yayi sama sai ya bace. Ba dan suna maza ba da babu wanda zai tsaya a cikinsu, ita dai Ammy daman tana tsaye daga bakin kofa ne sai addu'a take, Shattima k

uma yana tsaye kusa da Baba Waziri.

“Ranka ya dade a kar ta?”

Dayan ya tambaya? Sai wani ya kama mishi.

“Lallai kam irin wannan bata da rana bata da amfani”

Sai Baba Waziri ya daga musu hannu.

“Aa ba za mu kasheta ba, ta je can ta ji da a

lhakin mutanen da ta kashe”

“Bayan Mai Martaba sai kurwar waye a hannunki?”

Shattima ya tambaya yana mata wani irin kallo na kyama da tsana, sai ta girgiza kai alamar babu kowa domin ta kai gabar da magana ma ba zata iya ba.

“Ina Zainab take?”

Shattima ya tambaya sai mai gadin yai hanzarin amsawa.

“Ta tafi makota saboda macijin da ta gani, bari na kirata”

Ya fita da sauri, cikin kankanen lokaci suka dawo tare da ita. Kasa cewa komai tai ganin halin da Iya take ciki ga kuma Shattima Baba W

aziri da Ammy tsaye da kuma yan uwan Mai Martaba.

“Ke ma kina maitar ne?”

Baba Waziri ya tambaya sai ta kalleshi ta kasa cewa komai hawaye suka sauko mata sharrrr kamar an bude fanfo. Shattima ya kalleta irin duban nan na kaskanci, sai Baba Waziri y

a ce

“Na baki daga yau zuwa gobe, ki dauki Iya ku bar garin Yola, idan ba haka ba duk abun da ya biyo baya ke kika ja, kuma idan muka sake ganin wani abu da ba mu yarda da shi ba, zamu nemo ku duk inda kuka shiga”

Lokaci daya Zainab ta runtse ido tan

a jin kamar mutuwa ta dauke ta huta da duniyar gaba daya.

“Boyewar da tai kuskure ne, sai dai be zama lallai ace tana maita ba, Baba ayi mata uzuri a kara mata sati so that ta siyar da komai na ta da yake garin nan ta bar garin”

Shattima ya fada yan

a kallonta.

“Shattima ina son ka sani, farin tuwon nan cikin bakar tukunyar nan ya fito”

Baba Waziri fada sannn ya fice a fusace, haka ma saura suka fice aka bar Shattima a dakin da Ammy dake tsaye jikin kofa.

“Kin ban mamaki Zainab”

Juyowa Z

ainab tai ta kalli Ammy.

“Kina da damar ki zargeni da komai Ammy, ba ni da kalmomin da zan hada na furta na wanke kaina, na san komai ne a kurarren lokaci....”

Ta yi saurin saka hannunta ta rufe bakinta saboda kukan da ya ci karfinta ta durkushe a k

asa ta fashe da wani irin kuka.

Shattima dauke kai yai ya fice daga dakin Ammy ta rufa masa baya tana hawaye.

FADIME POV.

Sai da ta ci abinci ta koshi sannan ta tuna da sallah.

“Malam ina zan shiga nai sallah”

“Muhseen”

Ya fada mata.

“Muhseen ina zan yi sallah dan Allah?”

“Biyo ni mu je”

Ta mike tsaye ta fara binsa, sai kuma ta dawo ta hada plates din da ta ci abinci ta dauka ta bi bayansa da su. Wani dakin ya bude mota.

“Shiga akwai komai a ciki”

Sai ta mika masa plate

din.

“To ka aje wannan a muhallinsu ni ban san kicin din ba, kuma ita wannan Mama Fulani za ta iya fitowa ta min masifa ko? Ka ce tana da masifa ai”

Ido kawai ya sakar mata yana mamakin yaushe yace mata Mama Fulani zata mata masifa saboda ta bar pl

ate, bata bi ta kansa ba ta duka ta aje masa plates din ta shigewarta dakin.

“Ni da mijina Malam sai kallona yake yi”

Ta fada da muryar da ita kadai zata iya ji, sannan ta tura kofar dakin ta rufe. Dukawa yai ya dauki plates din yana murmushi ya sauk

a kasa ya kai su kicin sannan ya sake hawowa sama ya shiga dakin Mama Fulani ko da ya shiga ya same tana ta masifa a waya, zaunawa yai a kam kujerar dake dakin yana taba wayarsa har ta gama sannan ya kalleta.

“Mama kin dauki abun nan da gaske what if y

arinyar nan karya take miki? Ko ma gaskiya ne idan baku da wata cikakkiyar hujja ba za su iya yin komai ba”

“Ashe ma ita Ammy ta san maganar, idan sun an shanye su mi masifa ta ba zata bar ni a shanye ni ba, Wallahi ba zan bar maganar nan ba ai har na s

iya tickets din tafiya gobe da yardar Allah, shi ma Waziri ina fada masa ya sa Iya ta tsallaka Maijidda wai abar wa Allah komai Maijidda ta riga ta rasu ka ji min shashanci”

“Mama dan Allah karki ce za ki shiga masarautar nan da masifa, mutuwa akai fa k

uma shi kansa Sarkin ba lafiya ce ta ishe shi ba”

“Karka kawo min wannan maganar babu wanda zan saurarawa rashin lafiyarsa ba su ne suka saka shi gaba ba”

“Bari dan ki ya zo yai miki magana ko za ki ji”

“Ba ruwanka Muhseen karka hada ni da Aliyu”

Mama Fulani ta da da tana daga masa hannu, domin Aliyu ne kadai sai Abbah mutanen da suke saka ta ta yi abu ko kuma ta hanu idan sun hana ta, Aliyu saboda kaunarsa da take yana wahala ya hana ta abu ba bar shi ko ya roki abu ta ki yi masa, Abbah kuma sa

boda ya zama cikakken namiji ne da baya daukar raini.

Tashi yai yana dariya ya fito daga falon kamin ya karasa saukowa door bell din tai kara alamar akwai mutum abakin kofar falon, karasa yai ya bude kofar falon, sai yai arba da Aliyu Ataa na tsaye baya

nsa rike da babynta.

“Dan halak kaki ambato”

“Kenan gulma kake”

Aliyu ya fada fuska ba yabo ba fallasa kamar ba shi yai maganar ba. Muhseen yayi murmushi ya sakar musu kofar suka shigo. Kai tsaye Ataa ta nufi upstairs zuwa dakin Mama Fulani, Aliy

u kuma ya zauna a falon shi da Muhseen, a kan gadon Mama Fulani Ataa ta sauke babynta ta gaishe da Mama Fulani sannan ta sanar mata tare take da Aliyu, Mama Fulani ta taso cike da far'a suka sauko tare da Ataa, sai da suka zauna sannan Aliyu ya gaishe da M

ama Fulani, sannan ya kalli Muhseen ya ce.

“Ina Yasmin din?”

“Yasmin ko Fateema ko talkative”

Muhseen ya tambaya yana dariya, sai Aliyu ya masa wani kallo na rashin fahimta, kuma ba zai iya tambaya cewar be gane ba ko kuma miyasa ya ce haka ba, M

uhseen ya mike tsaye yana murmushi.

“Ni zan tafi gida, gobe karfi nawa zaki tafi?”

“Tara”

Mama Fulani ta amsa masa.

“Okay”

Ya nufi kofar fita, sai da ya fice sannan Mama Fulani ta ke dauko masa zancen abun da Fadime ta fada mata.

FADI

ME POV.

Sai da ta karewa dakin kallo sannan ta nufi kofar bandakin ta taba ta murda ta tura sai kofar ta bude, sai ga ta cikin karamin bandakin.

“Oh su kan yan birni sun ji dadi komai mai kyau ne, ji bandaki ne fa nan”

Ta fada tana karewa bandaki

n kallo, sannan ta fara tabe tabe tana murda fanfon har ta kunno ruwa, sai da ta wanke hannunta sannan ta tara ta sha ba dan tana jin kishin ruwa ba sai dan burgeta da abun yai wai fanfoa bandaki.

“Ashe haka irin na gidansu Shattima yake ko?”

Ta tamb

aya kamar wani ne a gabanta, da zai amsa mata, ta wanke fuskarta ya fi a kirga tana kallon kanta a jikin madubi.

“Barakalla Mashallahu”

Ta furtawa kanta sai a lokacin ma ta lura da kalar atamfar da ke jikinta.

“Allah na gode maka yanzu ina gani”

Ta dade a bandakin tana tabe tabe sannan ta yi alwalar ta fito. Kalle kalle ta fara yi ko zata ga hijab da abun sallah, sai ta ji kamar an jefo dutse a window dakin, da farko dan tsoro ta ji sai dai ba sosai ba, kadan kadan ta taka ta isa gurin window

ta daga lalulen ta leka bata ga komai ba. Sai manyan motoci da garden.

“Kai ashe gidan sama na da dadi hmm, sai ka hango komai a kasa”

Tana rufe bakin ana saka hannu a rufe mata bakin da karfi ta yadda ihunta ba zai fita ba, kamar wanda ya rufe mata

bakin ya san za ta yi ihu sai ta fara kokuwar juyowa tana ihun da sautinsa ya ki fita, juyowa yai ya ita ta fuskance shi. Bude ido tai kamar za su fito wani irin farinciki ya lullubeta da kuma dan tsoro a lokaci daya, a hankali ya dauke hannunsa daga bakin

ta yana kallonta fuskarsa da murmushi idonsa kuma cike da kwalla.

“Ya akai ka zo nan? Waya fada maka ina nan? Yaushe ka shigo?”

Be ce mata komai ba ya kai hannunsa yana shafa fuskarta, sai ta lumshe ido ta saka hannunta biyu ta rike hannunsa, tana j

in wani irin farinciki kamar ta rumgume shi.

_________

Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da

tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba,

muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku

labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.

Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.

5

9

*Khadeeja Candy*

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Lumshe ido yai ya bude har lokacin idonta a rufe suke tana murmushi.

“Fate

me..”

Ya kira sunanta da muryar da bata taba jinsa da ita ba. Hakan yasa tai saurin bude idon sai tai arba da hawaye da ke sauka fuskarsa. Take hamkalinta yai mugun tashi.

“Miyasa kake kuka? Me ya faru? Ko dan an taba min ido?”

“Aa”

“To me ya

saka ka kuka?”

Ya kai dubansa gurin rigar da ke jikinta sannan ya kai hannunsa ya kama hannunta ya dora saitin kirjinsa.

“Ban kwana na zo na yi miki”

“Ina zaka je”

“Babu inda zan je?”

“To miyasa kake min bankwana? Ko mutuwa zan yi?”

Yayi

murmushi wasu hawaye na sauko masa.

“Aa, bankwana na har abada”

“Mutuwa zan yi? Ko jirgin zai yi hadari damu mu mutu?”

Ya girgiza mata kainyana yawo da idonsa a fuskarta.

“Zan miki bankwana ne, irin na tafiya ba na mutuwa ba, zan tafi garinm

u ja zauna tare da yan'uwana, ke kuma na bar ki da na kin yan'uwan?”

Take ta ji wani iri sai a bata fuska kamar ta fasa kuka.

“Me na yi?”

“Ba ki yi komai ba, ba za ki taba min komai ba”

Ya fada sannan ya kama tafin hannunta ya saka cikin na sh

i.

“Saboda wannan...”

Wani irin jan numfashi tai cike da tsoro, ba tsoro na ganin wani abun gudu ba, sai dan tsoro na sanyin da bata ji ba a hannunsa.

“Miyasa ban ji sanyin ba?”

Ta tambaya cikin tashi hankali. Sai ya bata amsa cikin kuka marar

sauti.

“Saboda bani ne mijin ba”

Fashewa tai da kuka ta rumgume shi da sauri.

“Aa kai ne, kai ne Wallahi...”

Hannunsa ya saka ya banbanreta daga jikinsa ya kama fuska hawaye na sauko masa.

“Da gaske ba ni ba ne, ba ki taba hannun wani na

mijin kin ji sanyi ba?”

Ta yi shiru tana kuka irin kukan dake shigewa cikin zuciya saboda bakinciki da zafinsa.

“Ka kara zuba min to”

“Idan zan zuba miki sau dari ki rike hannuna sau dubu ba za ki ji komai ba, saboda ba ni ba ne”

“Amman ni ai n

i ce ni dai ina sonka haka nan”

Ya sake rumgume kankan, sai ya lumshe ido hawaye na sauko masa.

“Karka bar ni dan Allah, kai kadai na ke so, bana son kowa ni da kai na saba”

“Za ki saba da kowa ma, domin kina da shiga rai, kina burge wanda ya fah

imci rayuwarki”

Ta dago tana kallonsa.

“Miyasa to zaka bar ni? Mi na yi?”

Bude idonsa yai ya kalleta.

“Saboda, addina da na ki ba daya ba ne, al'adata da ta ki ba daya ba ce, kuma ba ne mijin ba, domin ba ki ji sanyi a hannuna ba”

“Ai ba d

ole sai na ji sanyin ba, Dan Allah Wasim ka daina min wasa”

“Ba wasa ba ne, dole ta sa ni kaina ba dan na so ba ne, idan ban rabu da ke ba, Idonki ba zai bude ba, kuma da yanzu ba ki dawo hayyacinci ba, mahaifina ya dage akan dole na rabu da ke, idan ba

haka ba ba zai bar ki ba”

“To ka aureni a haka mana, Wasim dan Allah... Ina son idon ya rufe sai mu yi auren dan Allah”

Ta durkushe a gabansa tana fashewa da kuka.

“Ba za ki ga ne ba ne, idan na yi haka b zaki jidadin rayuwar ba, ni ma kuma ba z

an so haka agareki ba”

“Na gane baka so na yanzu? Saboda bana jin magana ko? Saboda ina ta yawan magana ko? Na bari daga yau ba zan sake ba, ko na ji maganar ta zo zan yi sauri na rufe bakina, dan Allah kai hakuri Wasim ina sonka, ni dai ina sonka”

J

uya mata baya yai ya dafe kansa yana ta hawaye, duk yadda za ta ji ya san b kai kwatar yadda yake ji ba, domin shi ya fara kamuwa da kaunarta, kuma ita zata iya samu wanda zai kula da ita ya biye rayuwarta ta manta da shi amman shi kamin ya samu haka abu n

e

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login