Showing 9001 words to 12000 words out of 304903 words

Chapter 4 - FULANI COMPLETE

yankunne a kunnenta babu makeup a fusk

arta amman hakan be hana kyauta fita ba, kallo daya zaka mata ka san cewar jini daya ce ita da Shattima domin kamarsu ta bace kamar an tsaga kara.

“Ba a nan take ba”

Ya amsa mata with smile.

“A ina take?”

“Abuja”

“Abuja ai gurin zuwan mu ne

zan iya binka na kaini na ganta, tun ranar da ka fada min nake son na ganta har yau”

Ya zaro ido

“Ki bini? So kike ace na sace ki?”

“A a zamu je da sanin Ammy da kuma Hajiya kuma zan fada musu ba za su hana ba”

“Ba za su bari ba”

“To mu tse

re idan mun dawo sai mu fada musu”

Wannan karon dariya yai sosai.

“Nana ba ki da wayo”

“Ina da wayo mana, amman ai ina da hankali”

Ta fada ita ma tana dariya kamar shi.

“Fine, zan san abun yi ko dai na dauko miki ita na kawo ko kuma na bak

i address dinta idan kin shiga Abuja ki je ki ganta”

“Okay”

Ta fada tana daka tsalle, kamar ance ta daga kai ta gani, sai ta hango Sirleem a sama daga can bangarensu yana kallonsu.

“Idan kai tunani ka kira Ya Shattima ka fada masa sai ya fada min

ka ji?”

Tun kamin ya amsa mata tai saurin barin wajen ta koma sashensu.

Kai Doc Deen ya daga ya kalli Sirleem wanda ke watsa masa wani irin kallo na rashin kima, murmushi Deen yai ya bude motarsa ya shiga.

Daga backyard din da yake tsaye zuciyarsa

take wani irin tafarfasa ganin Nana da Yazeed da yai, ba tun yau ya lura a duk lokacin da Deen ya shigo  Masarautar sai ya tsaya yayi magana da Nana yake tafiya.

A fusace ya nufi bangaren Ammy zuciyarsa kamar zata fito tsabar kishi, cikin fusata ya tura

kofar falon ya shiga sai ya samu Shattima da Muhseen Zainab da Nana zaune a falon, dukan su kallonsa sukai ban da Shattima da yai kamar be san da shi a duniya ba, be damu ba ya soma gabatar da abunda ya kawo shi.

“Ke me kike yi waje da Deen?”

“Ina r

uwanka?”

Ta amsa masa ita ma tana turo baki gaba kamar za tai kuka sannan ta mike tsaye rike wayarta ta nufi hanyar da zata sadata da dakinta.

Zainab ta daga kai tana masa wani shegen kallo.

“Look at you Sirleem sai ka rika yin abu kamar wani fool

ya zaka shigo a gaban mutane kana tambayarta miye take a waje? Kamar wani ubanta”

Runtse ido yai ya bude cikin bacin rai ya ce

“Hajiya Karama babu ruwanki a cikin wannan maganar, idan ina magana da Nana ki daina saka min baki”

“Oh really? To ko du

kana zaka yi?”

Ta fada tana mikewa tsaye, daman can ita da shi ba sa shan inuwa daya.

Sai a lokacin ne Shattima ya daga ido ya kalleshi ya kalli Zainab.

“Please Hajiya Karama tafi dakinki”

“Amman....”

Bata karasa ba maganar ta makale sakamak

on kallon umarni da Shattima yai mata sai ta duka ta dauki wayarta ta fice daga falon. Shattima ya kalli Muhseen yana murmushi kamar ba shi ba yace.

“Muje sashena ka huta na san yanzu za a fara jera maka abinci dan gidan Mai Martaba”

A tare suka fic

e da Muhseen din aka bar Salim tsaye a falon kamar wani wawa.

FADIME POV.

Busar sarewar nan da take yawan ji a mafarki ta soma jiyowa tana tashi a hankali.

Kwantar da kanta tai jikin kafafuwanta tana sauraren yadda busar ke ratsa kunnuwanta tana

saukar da nishadi a zuciyarta busa ce mai ban tausayi mai saka shauki da dadin saurare, a iya lissafinta tana tuna mafarkinta ne shiyasa take jiyo busar, hakan yasa ta rufe idonta tana ta ganin mutumen nan mai busar sarewa na mafarkinta, a kullum idan tai

mafarkinsa baya yake bata bata taba ganin fuskarsa ba, yana daure da walki jikinsa babu riga.

Jin kamar a zahiri ake busar yasa ta bude idonta ta mike tsaye ta saki sandar korar shannun da ke hannunta, sai ta ji karar busar sarewar yana karuwa kamar ana

kusantota, waige waige ta fara yi sai kuma ta juya da sauri ta nufi gurin itatuwan masara ta kusa kai ciki domin a ciki take jin kamar busar na fitowa, tana tafiya tana juyawo tana ratsa shukar masara ta ko'ina, can kuma ta juyo sautin kamar a inda ta baro

ta juyo a guje ta dawo gaba daya hankalinta ya tashi domin bata taba jin busar a zahiri ba sai a yau, saman katon dutsen dake gaban shanunta ta haye tana hawaye tana waige waige ko zata hango mai busar ko kuma tabbatar da inda sautin busar ke fitowa amman

sai ta ji abun ya karade ilahirin dajin gaba daya, faduwa tai a gurin ta dafe kanta tana kuka domin a yanzu ta fara tunanin ba azahiri take jin busar ba a cikin kwakwalwarta ne.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ta furta tana kara runtse ido tan

a girgiza kai domin har lokacin bata daina jin busar sarewar ba, ta dade a gurin tsugune, sai da ta daina jin busar sannan ta mike tsaye tana kallon shanunta da ke kasa, a take saniya daya ta yanke jiki ta fadi a gurin tana shure shuren mutuwa, Fadime na g

anin haka ta sauko da mugun gudu ta nufi hanyar gida tana wani irin kuka na tashin hankali, @250 ta isa gida kamar wata mahaukaciya ta fada cikin gidan tana kururuwa.

“Inna Inna yau ma nagge guda ta fwadi, gata can tana shure shure Inna mutuwa za tai”

Ta fada da yaren Fulatanci tana haki kukan kuma ya ki ya tsaya mata. Da sauri mahaifiyarta ta aje tasar nonon da take ta nufo inda take ta rikata.

“Yau ko mun shiga uku da wannan lamari haka kullum za yi tai zama? Tafi ki fada ma Malam yana gonarsa”

Ta amsa masa ta yaren da suka fi gwarewa, a take Fadime ta tashi da gudu ya fice daga gidan zuwa gonar mahaifinta, Inna Amo ce ta fito daga bandakin lullube da bakin gane ta nufo tsakar gidan tana.

“Inna Fadime lafiya kike?”

“Nagge ce ta sake fad

uwa da sannu naggen Malam sai karewa suke Amo”

“Allah ya kyauta”

Shine abunda ta fada ta nufi bukkatarta tana koda tsatsagar hakora.

  Ko da Fadime ta isa ta fadawa Mahaifinta ya tafi tare da mutunensa da suke aiki tare sun isa a kuraren lokaci dom

in kuwa tuni saniyar ta mutu sauran kuma na tsaye suna kiwonsu. Faduwa Fadime tai ta dafe kai tana kuka, har sai da Mahaifinta ya tasheta tsaye.

“Haba Fulani komai ai na Allah ne? Ki daina wannan kukan”

“Bappa kullum fa idan na fita kiwo sai Nagge t

a mutu, ni kadai take ma haka”

“A a daman can haka Allah ya rubutu”

Ya amsa mata cike da karfin hali, sai daya daga cikin mutanen da suka zo tare da shi dayan ya ce.

“Malam da dai ka daina barinta tana fita kiwo da su”

Malam Jauro yayi murmush

i yana girgiza kai.

“A a babu abunda za a fasa, idan mutanen gari sun canfa ta ni ai be kamata na yarda a matsayi ne na mahaifinta, idan Fulani bata ji dadi a gurin iyayenta ba a gurin wa zata ji? Ko da duka sanu na za su kare ba Fulani ba zata daina z

uwa da su kiwo ba”

“To Allah Hukkumo sa'a”

Dayan ya fada cikin jin haushin be dauki shawararsa ba. Malam ya dafa kan Fulani ya ce.

“Ki cigaba da kiwon idan yamma ta yi sai ki dawo da su gida, annani?”

“Iyyiye”

Ta amsa masa tana gyara kai ha

r lokacin bata daina hawaye ba, kuma bata san ranar dainawar ba domin wannan matsalar ta shiga cikin jininta ta zauna ta hanata sukuni da walwala duk kuwa da irin ficen da tai a cikin kauye na amsa sunan yarinya daya tilo wacce ta iya turanci kuma ta iya r

ubutu da karatu a kauyen.

Sai dai wannan abun yasa mutane na tsoronta ga rashin farin jinin da yake damun mahaifiyarta, tun tasowarta har ta girma ta kawo yanzu babu namijin da ya taba nuna yana ra'ayinta balle har ya furta yana sonta, ko irin zuwa danda

lin da take sai dai taje wani lokacin dan ta kai sana'arta wani lokacin kuma dan tai kallo, domin ko da ta shiga tai rawa babu namijin da zai mata kari, sai dai tai wasa da yan 'uwanta mata duk kuwa da irin kyau da Fadime take da shi.

Haka ta zauna a g

urin tana kula da shanun har rana ta raba sannan ta nufi sandarta ta dauka ta kora shanun suka nufi hanyar gida tana tafi tana rare wakarsu ta fulani kamar ba ita ce ta gama kuka dazun ba.

Ita ta kanta ta saka shanun a gurin zamansu sannan ta daure ko wa

nne ta dauki abun shan ruwansu ta debo musu ruwa ta kawo musu sannan ta fita daga wajen.

Bukkarsu ta nufa ta shiga ciki tana cigaba da rera wakar da take tun da ta turo shanun har ta kawo gida, tufafin Fulanin dake jikinta ta cire ta daura zane ta fito t

sakar gidan ta dauki wata karamar roba ta nufi tukuyar ruwansu ta debo ruwa a ciki ta nufi bandaki, sai da ta tube tufafinta sannan ta lura da kadangaran dake leke da windin da aka zagaye akai bandaki da shi suna a kai suna kallonta, bayan mutane abu na bi

yu data tsana yana kallonta kadangaru ne, dan ta lura har wani kada kai suke idan suna kallonta, abun haushi ma kallonta suke ba kakkautawa ko dauke ido basa yi.

Haka ta debi ruwan ta rika watsa musu suka fara gudu banda daya wanda ya tsaya yana kallonta

sai wani rausayarda kai yake.

Hakan yasa ta tsorata ta fara ja da baya tana cigaba da watsa masa ruwa, aiko kamar jira yake sai ya sauko da sauri yai cikinta, tsakanin ihunta da fallawa da gudu da kuma sakin robar ruwan ba a san wanda ya riga wani ba, k

amar bera haka ta shige bukkarsu har wani tsale take sama tsabar gudu da tsoro.

“Inna Kadangare ne ya bijoni”

“Ba dai zaki daina watsa musu ruwa ba ko? Wata rana sai kin watsawa aljani”

“Inna wannan ma da gudu yake, ba zan iya wanka a ciki ba”

Duk maganar da take da Inna ba ta dago ta kalleta ba sai aikin auna gi

ɗ

a take a kwarya, sai da ta mike tsaye sannan tai arba da yarta.

“Innalillahi Fulani a tsirara kike fa, zindir Subhanallahi”

“To Inna kadangaren ne ya biyo ni ai ba zan iya tsaya

wa daura zane ba”

Ta fada tana turo baki tare da sa hannu ta kare kirjinta wanda da shi da babu duk daya kamin ta nufi inda zane yake ta dauka ta daura. Sai da ta ga mahaifiyarta ta fito sannan ita ma ta fito waje tana labe bayanta kamar wacce zata sake

arba da shi.

“Ni ban ga komai a bandakin ba”

“To Inna ki tsaya na gama wanka tukuna sai ki tafi”

A bakin kofar bandakin Inna ta tsaya Fadime ta dauki robar taje ta debo wani ruwan ta tsaya daga baki-baki tai wankan ta fito da sauri...

*FULANI

-it's not free, if you want to subscribe pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

*

🐄🐄

FULANI

🐄🐄

*

By Khadeeja Candy

*-3*

FALMATA POV.

Bayan gama sallah isha'i Baba ya shigo gidan rike da yar leda

rsa, da sauri ta karasa ta karba tana masa sannu da zuwa, ya amsa mata can ciki yana dauke fuska kamar wanda baya kaunar ganinta.

Dakin Tumba ya nufa tana biye da shi a baya rike da ledar sai da ya shiga sannan ita ma tai sallama ta shiga ta aje ledar ta

juyo ta fito kamshin tsire na dukan hancinta, guri ta samu a saman tabarmar dake shimfide tsakar gidan ta zauna tana ta bitar karatunta na iziya. Hango mahaifinta ya fito daga dakin Tumba zai kama ruwa yasa tai sauri tashi ta karasa ta dauki butarsa ta zu

ba masa ruwa ta mika masa tana sirinawa kamar yadda ta saba.

Sai da ya shige bandakin sannan Tumba ta fito ta rike kofar dakinta tai tsaye tana watsa mata harara.

“Fulani dauki bokiti kije ke samo mana ruwa”

Juyowa Falmata tai ta kalleta da fuskar

tausayi tana jin kamar tace ta dauki bokiti taje ta debo wuta, har ga Allah bayan surfe deban ruwa ne abu na biyu data tsana, sai dai babu yadda za tai kullum sai ta yi surfen sai kuma ta yi deban ruwan abu ne da ya zame mata dole ko a ciwo ko da lafiya d

ole ne tai.

“Umma na debo ruwa dazun da safe fa sai da na cika komai”

Ta fada da muryar dake nuna rokon take a tausaya mata.

“Ba gabanki Naja tai wanki ba? Ruwan ya kare ko so kike mu tashi da safe babu ko na alwala?”

Umma na kai aya Abba ya

dauka yana daka mata tsawa.

“Dauki kije debo ruwa aka ce sha-sha -sha kawai”

Ya karasa yana daure zariyar wandonsa karen sigari a bakinsa. Kamar wacce tai arba da mutuwarta haka ta nufi inda bokin ruwan yake ta dauka da sauri jikinta har rawa yake ta

shiga dakin da suke kwana ita da naja ta dauko hijabinta ta saka ta dauki bokintin ta fice daga gidan tana ala ala kar ma tai numfashi da karfi mahaifinta ya ji.

Sai ta fito daga cikin gidan sannan ta shara hawaye, ina zata je debo ruwa yanzu cikin dar

e? Ta san ko wane gida a yanzu sun rufe rijiyarsu, gashi babu wuta balle taje bohol domin idan babu wuta to bohol din baya aiki.

Hanya ta mike tana tunanin wace rigiyar zata dosa, hawaye na ziryo mata, da karfi da yaji dazun Umma ta hana ta deban ruwan t

a wanke mata surfe amman ta bar Naja yar gata tai wanki da ruwan yanzu kuma sai ace ita ce zata je ta debo wasu. Hawayen idonta ta share ta nufi gidansu kawarta Khadija, tun a bakin kofar gida take sallama amman babu wanda ya amsa ta sakamakon kure volume

da sukai da wakar fitattacen mawakin nan da Falmata tafi kauna fiye da komai da kowa a duniyar nan, wato Sirleem M2. A take ita ma ta bi sahu cikin yaran makota da suke zaune bakin kofar dakin Maman Khadija suna kallo, ba ta ko bi ta kan neman Khadija ba t

a zauna saman bokitin ta fara bawa idanuwanta abinci, a take murmushin ya gauraye fuskarta ranta yai fes kamar ba ita ba, daman can haka take indai tai arba da wakarsa ko hotonsa wani irin dadi take ji saboda burgeta yake kaf a mawakan duniya babu wanda ta

ke so irin Sirleem har wani shauki take ji idan ta tuno wakarsa.

“Ke”

Khadija ta dafa ta aje butar hannunta da ke nuna cewar daga bandaki ta fito.

“Ina kika fito da bokita da daren nan?”

Falmata bata kula ta ba sai da wakar Sirleem ta kai kar

she kaf sannan ta juyo tana kallon kawar tata kamar wacce ta dawo daga hayyacinta.

“Me kike cewa?”

“Oh na shiga uku ni Khadija wato tsabar son wakar M2 har baki ji abunda nake fada ba”

Dariya Falmata tai.

“Wallahi ina son M2 sosai Khadija ya

iya waka sosai yai ta hausa yai ta turanci har kasashen waje ance yana zuwa yai waka kuma kin ga dan Yola ne ai dole mu so shi ko?”

“Ke dai kike sani, dan yana dan Yola aka ce miki zama suke a garinsu ne, yawanci kasashen turawa suke zuwa ko Abuja su za

una”

“Khadija kin san me? Da ace na yi boko na iya rubutawa da karanatawa ko? Da nima na rika koyon wakokinsa ina yi”

Cewar Falmata tana dariya har kyakyatawa.

“Lallai Falmata abun na ki babba ne, ina zaki je da dare ke da ba a barin kina fita?”

A take yanayinta ya canja murmushi da far'ar dake fuskarsa ta gushe tunawa da duniyar kuncinta, cikin rashin kuzari ta labartawa Khadija abunda ya faru sannan ta dora da.

“Dan Allah muje ki kara ni idansu Binta tun da kawarki ce kila Mamanta zata ya

rda na debi ruwan ko maya biyu ce dan Allah”

“Gaskiya dai tsakani da Allah Falmata Umma tana cutarki, shi kuma Baba ya zama wani iri duk abunda tace shi yake amfani da shi, yadda fa iyaye suke da hakki akan yayansu su ma yayansu suna da hakki akansu, ni

kam da ma ke aka kai kauye aka bar kanenki nan wannan wahala ta miki yawa Falmata”

Ta zaro ido.

“A a ke idan su Aisha n suke nan ai wahala za su sha sosai tun da su kanana ne, kara dai ni da nake da girma yanzu ni dai muje ki rakani”

“Ga ruwa can

a jarka je ki deba ki yi uku da bokitin ki”

Kamar ta dauki kawar tata ta goya haka ta ji dan dadi, da sauri taje ta bulbula ruwan ta cika bokinta ta kai gida ta sake dawowa ta kara wasu har sai da tai bokiti uku sannan ta hankalinta ya kwanta. Bayan ta

aje bokitin a mazauninsa ta nufo kofar dakin Tumba kamar mai labe ta tsaya daga bakin kofa murya can kasa tace.

“Ga ruwan nan na debo”

“To Allah yai miki albarka Fulani ya baki miji na gari”

Tumba ta fada da far'arta, Falmata dai bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login