Showing 66001 words to 69000 words out of 304903 words

Chapter 23 - FULANI COMPLETE

Isuhu ya matso kusa da ita ya haska fitilarsa yana ya fara karanta mata ayoy

in kona aljanu, tun da aka fara karatun Fadime take zaune guri daya tana saurare, idan ya karanta ya karanta sai yace

“Wanene?”

Sai Fadime tace

“Ni ce Fulani”

Tun yana yi yana tsayawa ya tambaye ta har ya gaji ya daina sai karatun kawai yake

mata, da Fadime ta ga abun nasa ba mai karewa ba ne sai ta fara lankwashewa tana burkice ido kamar da gaske aljannu ne suka zo.

“Muna aljanu gamu nan mun zo, mu ne”

“Ku suwa?”

“Mu aljanu”

“Miye sunanka?”

Ta dan yi shiru tana tunanin sunan d

a zata fada, can kuma ta fadi sunan Bappa.

“Sunana Sama'ila”

“Miyasa kika shiga jikinta?”

Mutumen ya tambaya.

“Saboda.....saboda... Muna son mu bada magani”

“A ina kuka hadu da ita”

“A daji..... ”

“To ku fita daga jikinta ko na kona

ku”

“Ba zamu fita ba”

Ta fada tana ta mulmula a kasa kamar wata mai aljanun gaske, sai mutumen ya cigaba da karatunsa da nufin kona su, Bappa kuma ya shiga dakinsa ya dauko bulalar dorina ya shada mata, a take tai saurin tashi ta zuba da gudu zuwa wa

jen shanun da suke gidan.

“Mun fita ba zamu sake dawowa ba”

Malamin yace.

“Karya suke haka suke idan suka ga ana kona su”

Bappa ya bita har can ya zuba nata wata bulalar yana fadin

“Ku fita daga jikinta yanzu nan”

“Bappa sun fita tun da

zun ni ce dan Allah ka tsaya”

Ina Bappa be yarda Fadime bace sai auna mata bulalar yake, tun tana fadin sun tafi har ta fara kiran Inna ta ceceta.

“Inna nice Wallahi ni ce dan Allah ki zo kar Bapppa ya akashe ni”

Inna ta zo da sauri ta rike bulala

r tana fadin.

“Sun fa tafi Fulani ce kake duka”

Sai a lokacin Bappa ya sarara mata bayan ta sha buloli da sunan aljannu.

HAJIYA BABBA POV.

Tsananin mamakin da yake fuskarta ya wuce misali, ta san Jarma ba zai mata karya ba, amman sam b

ata gane inda labarinsa ya dosa ba, Fadime Falmata Sardauna za su watse musu shiri?

“Wacace Fadime?”

Ta tambaya a fili tana kallon Jarma.

“Ni ma abunda na gagara sani kenan, balle kuma Falmata da Sardauna, amman ni ina ganin kamar Sardauna na Yol

a yake nufi”

“Sardauna ai yana da nisa da Sarautar nan, balle nai tunanin haka, idan na shi ne to su waye Falmata da Fadime?”

“Abun da na gagara sani kenan, kuma na yi wauta ko da yake tsoro ne a ya hanani tambayar ko me suke nufi, kuma ita Ammy ai

Zainab ne sunanta ba Fatima ba balle nai tunanin ko ita ce....”

Be karasa ba Hajiya ta daga masa hannu alamar yai shiru sai dai har lokacin mamaki be bar fuskarta ba. Kwankwasar dakin da ake take saurari kamin ta ji muryar Nana.

“Hajiya Hajiya....”

“Daughter ke ce?”

“Ni ce”

Hajiya ta tashi da kanta ta bude mata dakin tana kokarin kirkiro murmushi.

“Daughter na ya aka yi?”

Ta tambaya tana rike da kofar dan bata son Nana ta hango Jarma a dakinta, duk da ta san ya saba shigowa sai dai ru

fe dakin da makulli da akai zai saka shakku a zuciya.

“Wayarki za ki bani sai na kira wanda na ce miki ina son ya zama driver na”

“To tsaya nan bari na dauko miki”

Hajiya ta rufe kofar ta dawo ta dauki wayar sannan ta koma gurin kofar ta bude ta

mika mata.

“Tafi da ita can idan kin gama ki bawa Karima ta aje min”

“Okay”

Ta karba ta juya cike da jindadi, dan ta san Number AA na cikin wayar Hajiya, saboda ta ari wayar shi ta kira Hajiya da line, duk kuwa da bata da tabbacin number tana nan

har yanzu ko an goge, ba dan zata iya ganewa number ba sai dan ta gwada sa'arta.

Bayan ta wuce Hajiya ta sake rufe dakin ta dawo ta zauna. Sai Jarma ya rage murya yace.

“Ashe Nana ta fara dan hali?”

Hajiya ta yi murmushi.

“Ai har abun da yaf

i dan hali sai Nana ta yi, matukar ina raye ƴaƴan Ammy ba za su taba albarka ba Wallahi har a abada kuwa, yadda take son ganin bakincikina ita sai na ga nata kukan”

Ta karasa tana wane kashe ido zuciyarta cike da kiyayyar Ammy.

*FULANI -i

t's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence to 08036126660 ƴan nijar za ku tura 500cf to +22790165991*

17

“Fulani ki jefar da tulun ta can sai ki gudu”

Cewar Inna cike da damuwa. Fadime ta girgiza kanta da ya kusa fa

shewa saboda ciwo, ga kukan da take idonta har ya kumbura.

“Aa sai na shiga gida”

Bappa ya nuna ta da sandar hannunsa.

“Wallahi baka kai min masizi cikin gidan, ka jafar da si ka gudu aka ce maka”

Ta kara fashewa da kuka, ta rasa yadda za tai

su fahimce ta, gashi jikinta ya gama mutuwa ga wani uban zafi da take ji, kukan har ya fara zuwa mata ba hawaye, a lokacin ne ta fara yarda ta fara bankwana da duniya, ta sanj Bappa ba zai bari ta shiga gida da maciji ba, ita kuma ba zata sauke shi ya cut

ar da ita ba.

Har rana ta soma dagawa ana abu daya, ita ta ki ta jefar da tulu, Bappa kuma ya ce ba zata shiga gida da maciji ba, aka rasa mai taimakonta duk wanda ya tunkaro ta sai ya ga kan maciji kato ya sako masa ido.

“Ina ganin abun da yafi aje

can garin su Ahmadu akwai wani mai majizai kira shi ya zo ya dauke mata wannan lalura”

Malam Adamu ya fada yana saka hannunsa ya kare fuskarsa daga hasken ranar da ke dukan su, domin rana ta bude sosai wanda hakan ke nuna biyu tayi ko ma ta gota. Fadime

na zaune kasa har ta fara wata ramar wahala, muryarta har ta dakishe ga wani uban gumi da take. A yanzu kam Inna ta yarda da mafarkin da tace mata tana yi har ta fadawa Bappa.

A dole dai da aka isa har garin hayin fari, aka dauko wani mutum nai wasa da

maciji akan ya zo ya dauke tulun.

A lokacin ne Fadime ta gane ashe tana da ragowar karfi, da mutumen ya tun karota sai ta mike tsaye ta fara tafiya wata hanyar tana kuka, hannunta daya na rike da tulun da ke saman kanta dayan kuma yana rike da zanenta d

aya kusan subucewa.

“Wallahi ba zan bayar ba, yace sai na kai shi gida”

Idan mutumen ya tsaya sai ta tsaya, idan ya tunkaro ta sai ta nufi wani gurin mutane kan kowa sai gudu yake.

“Ki saurare ni da kyau, babu abun da macijin zai miki ni zan zo

na karbi tulu sai ki gudu”

Bagarden ya fada a kokarinsa na kwantar mata da hankali, sai ta girgiza masa kai.

“Aa sai na kaishi gida”

“Waya ce ki kai shi gida?”

“Wani mutum ne, wani ne Wallahi”

Ta fada tana kuka cikin rashin kuzari domin ha

r ga Allah bata da wani zarafin kuka a yanzu. Cikin dabara mutumen ya fara takawa yana matsawa kusa da ita yana tambayarta.

“Wane mutumen a ina kika hadu da shi?”

“A can dajin, yace sai na kai shi gida idan ba haka ba, zai cijeni”

“Yaushe kika fa

ra ganin mutumen? ”

Bata bashi amsa ba ta ranta a na kare ganin yana tunkaro ta har ya mika hannu ya cafkota, tana gudu kan maciji yana rawa a tulu. Mutumen ya koma gurin mahaifinta.

“Abun da yafi kawai ka bari ta shiga da tulun cikin gida, ni kuma s

ai na bita idan ta jefar da macijin sai na dauke shi”

“A a ba za a shigar min da masizi cikin gida”

Daker aka lalaba shi ya yarda, sannan bagarden ya nufo ta ya tsaya nesa da ita yace.

“Ki shiga gidan sai ki jefar da tulun haka ya miki?”

“Eh”

Ta amsa tana mutsa kafafuwanta sakamakon zafin ranar da ke cizonta. A gaba aka saka tana tafe tana waige idan mutumen be biyo bayanta ba, sai da ta shiga har cikin gidan sannan ta jefar da tulun a tsakar gida ta juyo da gudu, mutanen da ke leke ma suka

auna da gudu ita da su aka rigen rigen kamar masu wasan boya. Abun da ya bawa Bagarden mamaki a lokacin da ta jefar da tulun sai tulun ya fadi kasa ya fashe da ruwan ciki babu maciji babu alamarsa. Ba shi kadai ba kowa sai da yai mamakin lamarin, wasu na

fadin ko dai ya shige wani gurin.

“Babu inda ya shiga a lokacin da ta jefar ai ina kallonta ruwa ne ya zubo a ciki, lallai ka bincike yarinyar nan akwai ifiranta dake tare da ita”

Bappa yayi shiru yana kallon tulun da ya tarwatse ga kuma ruwa a tsaka

r gidan. Ya san baya wasa da addu'a haka mahaifiyarta ita kanta Fadime be yi zaton zata wuni ba tare da ta yi addu'a ba.

“Zan mata karatu In-Sha-Allah, idan ma iskokin za su bar jikinta da yardar Allah”

Hannu ya saka aljihu ya dauko dari biyar ya mi

ka masa yana masa godiya sannan ya raka shi har gurin wanda zai kai maida shi gida akan babur dinsa. Bappa da kansa ya riko hannun Fadime ya shiga da ita gida a nan ta samu damar rafkewa masa tana lumshe ido, sai a lokacin ne ta san ta wahala, daker inna t

a dauke ta ta kaita bandaki ta wanke mata jikinta tas sannan ta rikota suka fito tare, doguwar rigar atamfa Inna ta saka mata ta shimfida mata tabarma waje, Fadime ta fito daga dakin tana tafiya kamar zata fadi, tana kwantawa saman tabarmar sai bachin waha

la yai gaba da ita, sai wani sauke ajiyar zuciya take.

FALMATA POV.

Falmata bata fito daga dakin ba sai da aka gama sallah magariba sannan ta fito tai alwala ta koma dakin tai sallah, gaba daya addu'arta na neman Allah yasa kar Baba ya doke

ta ne, tana cikin dakin aka kira sallah isha'i ta sake shimfida dankwalinta tai sallah sannan ta koma saman shimfidarta ta takure guri daya tana ta hawaye.

Naja sai dariya take mata tana Allah ya kara.

“Wai ke kin yi dan ki barawa Umma suna ace bat

a baki abinci ko kuma ace tana cin bashin gari a shago sai gashi Allah ya toni asirinki kin dai ji kunya”

Uffan Falmata bata ce mata ba, dan bata ji abunda take fada ba, ko da ma taji ba zata tanka ta ba, domin yanzu ba ta kowa take ba sai ta Baba, gaba

daya jikinta ya dauki rawa sai wani tsam take ji kamar ana shada mata bulalar.

Kamar saukar aradu haka ta ji sallamar Baba a kunnenta, tana jin lokacin da Tumba ke labarta masa abunda Falmata take har da kukanta wai tana son bata musu suna.

“Haba

wannan wane irin abun kunya ne Fisabilillahi ace yarinya kamar Falmata zata je shago tace na ce a bani bashin gari kwaki, salon a zage mu ne ko kuma dan ta lalata kanta ne da irin tarbiyar da kai mata?”

Ran Baba yai matukar baci zuciyarsa ta soma bugawa

da karfi har wani huci yake.

“Ina Fulani take?”

“Gata can dakinsu, ni ina ganin idam ba albarka ka cirewa yarinyar nan ba ba zata taba hankali ba”

Tumba ta fada tana matsar kwalla kamar gaske. Jakar hannunsa ya aje ya nufi icen dake tsakar gidan

ya karyo ya nufo dakinsu, da sauri Naja ta shiga dakin Tumba ta dauko masa fitilarsa ta hannu ta mika masa kasancewar babu wutar nepa kuma dakin ba a kunna fitila ba. Hannunsa ya kai ya karbi fitilar ya shiga dakin ya maida kofa ya rufe, tana ganinshi ta

mike tsaye ta hade hannayenta jikinta nata rawa.

“Baba dan Allah ka yi hakuri ba zan sake ba, idan na sake ka kashe ni, ka yanka ni ka gasa nama na, amman yanzu ka min afuwa Baba dan Allah”

Tsaye yai yana kallonta idonsa suka cika da kwalla, tausayi

n yarsa ya cika masa zuciya, amman ba zai iya yafe mata ba idan be dake ba ya san Tumba ba zata ji dadi ba, shi kuma baya son bacin ranta.

Kama ana daga kafarsa dole haka ya isa inda take ya fara dukanta kamar dan dukanta kawai akai shi, yadda yake auna

mata lulalar a jiki sai ka rantse da Allah be tana jin tausayi a zuciyarsa ba. Sai da bulalar ta ƙalle sannan ya bude dakin ya fito. A lokacin Falmata bata ko iya kuka sai kakarin wani abu take kamar za tai amai.

A gurin ta kwana har safe, ta saba tash

i sallah azuba da wuri, wannan karon sai ta kasa sakomakon tsamin da jikinta da yai ga uwar yunwar da ta wuni da ita kuma ta kwana da ita, ga azabar ciwon duka ga na ciwon kai.

Har kusan bakwai Falmata bata fito daga dakin ba, sai da Tumba ta shigo ta h

au ta matsifa..

“Wai salon karki je aikin ne yasa kika fara wannan makircin, kika ki fitowa ki yi sallah ki yi aikin gida? Tun da kin ji ance za ki yuni can ko? Zan samu karin albashi”

Daker ta daga idonta daya da jinin ya kwanta a ciki ta kalli Tum

ba dan dayan ya like sakamakon bulalar data same ta a fuska.

“A a wallahi jikina ciwo yake bana iya tashi”

Ya fada kamar mai karyeyen harshe.

“Ke nan wannan ya anyi makira, Wallahi ko ki tashi ko na ci ubanki da kaina”

Ba dukan take tsoro ba d

an tasan duk dukan da Tumba zata mata a yanzu be kai wanda Baba yai mata ba jiya da dare. Hakan yasa ta koma ta kwanta a gurin, tana maida numfashi daker kamar mai nakuda. Kwafa Tumba tai ta fice daga dakin dan ta san ba zata iya tashin da gaske na ganin t

a mata warning da karin wani amman bata tashi ba, ita kanta ta san ba karamin duka Baba yai mata ba.

Sai kusan tara Falmata ta samu kuzarin mikewa tsaye ta fito daga dakin tana jin jikinta na mata mugun tsami, daker ta cika buta da ruwa ta dauka ta nufi

bandaki, tufafin jikinta ta cire ta dauko soso da babu sabulu ta fara goge sai ta ji wani azaba kamar tana likawa jikinta wuta. Da sauri ta aje soson ta saka maida tufafin ta wanke fuskarta ta fito waje tai alwala ta shiga dakinsu tai sallah tai addu'a sa

nnan ta fito sanye da hijabinta ta nufi tukuyar ruwa ta bude ta cika kofi ta sha, sai ta ji cikinta ya tsuke ya fara murdawa.

Daker ta karasa bakin kofar Tumba ta leka.

“Umma zan je aikin”

“Da dai karki je, yar iskar yarinya kawai Allah in baki

yi hankali ba sai na saka Babanki ya tsine miki albarka”

Bata ce komai ba, ta sanda kanta kasa ta juyo ta fara tafiya.

“Ki tafi gidan Asabe ki kai mata wannan”

Ta juyo ta shiga har cikin dakin ta karbi kudin da Tumba ta mika mata. Ko ba fada mata

ba ta san ko kudin adashe ne da take zubawa duk wata 5k wanda a cikin kudin zancen da ake bata da kuma kudin Baba take samu ta zuba tun da ba wata sana'a take ba.

Falmata na tafiya tana juya kudin a hannunta zuciyarta na raya mata abubuwa da dama, a t

ake ta ji wani kuzari ya kara mata, tana tafiya mutane na tambayar abun da ya same fuskarta sai tai musu shiru kawai ta wuce.



Bata hanyar da zata sadata da ta gidan Asabe mai adashe ba sai ta dauki hanyar titi wacce hanya daya ce da hanyar zuwa gurin

aikinta.

Sai da tai nisa sannan ta tari Napep ta hau.

“Ina za a kai ki?”

“Tasha”

“Tashar da ake zuwa wani gari”

“Wane gari za ki je?”

Ta yi shiru kamar mai tunani, bata san garin da zata ce ba, hasalima ita bayan kauyen Babansu sai na Ma

manta sai kuma na su Tumba bata san wani guri ba.

“Maiduguri ko Kano ko Kaduna? Ko Kauye?”

“Ka... Ka... Kadun... Na.... ”

Ta fada muryarta na rawa sai waige take tana jin kamar an biyoyata.

“Dari uku zaki bada”

“To muje”

Mutumen ya kunna

napep dinsa ya hau titi ya fara tafiya yana kara sautin kidan dake tashi. A tsorace take har suka isa babbar tashar ta mika masa kudinta ta fita daga napep din ta shiga cikin tashar.

Tana tafe tana waige waige har ta isa gurin manyan motocin. Masu nema

n passengers na ta aikinsu sai tambayar inda zata je suke.

“Kaduna”

Ya fada ba dan tasan hanyar da za a bi a tafi can din ba.

“Zo ga mota nan mutum biyu ake jira”

Ta bi mutumen dake nuna mata motar, sai da ta shiga ta zauna sannan suka fada ma

ta kudin motar ta cire ta ba su, tana kokarin gyara zamanta ta hango wata mai abinci a gafen wata mota, sai ta fita cikin tsoro zuciyarta sai bugawa take.

“A bani shinkafa da miya”

“Na nawa?”

Ta mika dari biyar din dake hannunta.

“Na 100”

“A leda ko a plate?”

“A leda”

Falmata ta amsa tana ta kallon hanyar shigowa tashar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login