Showing 168001 words to 171000 words out of 304903 words

Chapter 57 - FULANI COMPLETE

dannewa, y

ana nuna musu kujerar da su kar barta. Inna ta kalli Bappa idonta na cika da kwalla.

“To ko sun sake dauke ta ne?”

“Su wa?”

“Aljanun mana”

“Aa kar ma ki kawo wannan maganar, haba dai”

Cewar Bappa yana kallon Malam Sule daya shigo yana tamba

yar Bappa.

“An ga yarinyar?”

“Ina fa”

“Na tambayi mutane sun ce an ga wani namiji fari ya fita rike da hannunta”

“Wani kuma?”

Bappa ya tambaya? Kamin ya juyo ya kalli Shattima.

“Ka san shi ne?”

“No, ban san shi ba, na fada muku a nan

na barta”

Ya dauki labcoat dinsa da wayarsa da keys dinsa ya nufi kofa sai suka biyoshi, fitowa yai ward din yana tambayar Nurse din da suke nan, sai sun suka bashi amsa daya.

“Ba mu ga shigarsa ba gaskiya, amman mun ga fitowarsa tare da ita, yana r

ike da hannunta har tana fadin gurin na da nisa ne? To ni n dauka kana ciki ma Wallahi”

“Ina yabi da ita?”

“Fita sukai ta kofar can, yana ssnye da kananan kaya bakake da facing cap ja, fari ne sosai ina ganin fulani ne dan'uwanta”

“Aa bata da wani

dan'uwan ba mu zo da kowa ba, sai dai idan aljani kika gani”

“Aljani kuma?”

Nurses din suka hada baki gurin fadar hakan suna kallon Inna da tai maganar tana kuka. Bappa ya daka mata tsawa da halshen fulantanci.

“Wai wane irin maganar banza kike

haka ne? Idan ma shi ya sace ta ai kin bashi damar kubuta,bana son shashanci Wallahi”

Fulatancin Katsina da na Yola akwai bambanci amman hakan be hana Shattima fahimtar abunda Bappa ya fada ba.

“Me zai saka na sace ta? Me zan yi da ita idan na sace t

a? Ina zan kaita? Wata kila akwai abun da kuke boyewa, wanda ni ban sani ba”

Bappa yayi shiru yana kallosa kamar mai tunani, shi dai kam be yarda wani ne ya shigo ya dauke ta, idan ma aljani zai dauke ta ai sai dai ace ta bata ba wai ace anga wani ya fi

to tare da ita ba, waya sani ko siyar da ita yai duk da be yi kama da mai yin hakan ba, amman sanin mutum ai sai Allah.

“Zan sanar da hukumar asibiti, za a ganta inshallah, ni ma hankali ba kwance yake ba yanzu aka kirani yaya biyu sun rasu, so duk abun

da ya kamata asibiti zata yi”

A nan Nurses din suka masa gaisuwa, shi kuma ya wuce da su Inna gurin hukumar asibitin ya sanar musu abunda yake faruwa, sannan ya sanar musu rasuwar yayansa saboda yana son ya wuce gida ya shirya komai tun yanzu, alam bara

m Bappa yace babu inda Shattima zai je sai an ga Fadime, Inna kam bata aikin komai sai kuka, kamin kace kwabo labari ya karade asibitin, a lokacin da bincike ya kai har gurin masu gadin asibiti sai su bada shaidar cewar tabbas sun ga shigowar shi da kuma f

itarsa tareda yarinya, a gurin da ake faka napep din haya ya nufa da ita ta shiga Napep din nan. A lokacin ne Bappa ya kara yarda cewar ba aljani ne ya dauke ta ba, likitan ne ya siyar da ita. Shattima ya rasa da wanne zai ji mutuwar yayansa ko kuma wannan

abun daya same shi? A dole ya koma office dinsa ya zauna after ya yi sallah la'asar. Yana nan zaune kiran Baba Waziri ya shigo wayarsa, ya dauka ko Baba Waziri zai masa gaisuwa ne ko kuma ya bashi hakuri, ashe wata mutuwar zai sanar masa.

“Ka yi kokar

i ka zo gobe da Safe, bayan yaya da ka rasa ka sake rasa dan'uwan, Talba ma Allah ya karbi abinsa”

Kamar an jefo masa aradu haka yaji maganar Baba waziri ta sauka kunnensa, ya mike tsaye da sauri ya cire wayar a kunnensa ya duba sunan mai kiran ya ga Ba

ba Waziri ne, ba zai masa wasa ba, ko ma zai masa ba zai masa ta mutuwa ba.

“Talba fa kace Baba”

“Talba Shattima, wai yaje Abuja, jirgin daya biyo ya fadi”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ya furta yana sauke wayar daga kunnesa, Talba ne ka

dai dan'uwa namiji da yake da shi, how could he bear the lost of him kids and his only brother at the same time? The pain was almost more than he could bear. Yadda hawaye suka fara saukowa daga idonsa sai ka rantse da Allah saboda irin wannan ranar kawai a

ka halitto masa su, he couldn't bear the thought of losing them, be bude baki yayi kuka da haniniya yadda mata suke ba amman be iya tana hawayensa zuba ba, zuciyarsa kuma bata iya daukar nauyin ita kadai ba, har sai da ta rabawa wani bangare na jikinsa wan

da hakan ya haifar masa da zazzabi da nauyin kirji ga gumi, da wani sabon ciwon da suka sallamo masa.

Babu wanda ta fado masa a rai a wannan lokacin sai Hajiya Babba, saboda yasan yadda take son Talba fiye da duka yayanta, kuma Talba is the only male so

n da ta haifa da Mai Martaba, after ita ya tuna halin da Mai Martaba zai shiga idan ya ji wannan labarin. Ta sauri ya dauki tissue ya goge hawayensa ya kira number Baba Waziri ringing tai har ta katse be dauka ba hakan yasa ya kira number Ammy, a maimakon

ya ji muryarta sai ya ji muryar Nana ta amsa cikin kuka.

“Ina Ammy?”

“Ta tafi bangaren Hajiya Babba, Ya Luma da Labib sun rasu, Ya Talba ma haka”

Ta fada cikin kukan dake nuna da gaske kukan take irin kukan nan wanda baya jin rarrashi.

“Nana..

.”

Ya kira sunanta sai ta amsa masa da muryar kuka.

“Na'am”

Sai kuma ya rasa abun da zai fada mata ba, shi kan shi yana bukatar wanda zai fada masa wasu kalamai da za su sanyaya masa zuciya, duk wani karfi hali da dakiyar zuciya a yau ya neme su y

a rasa.

“Nana ki fadawa Ammy kar ta fadawa Mai Martaba”

“Ya gaba daya gidan kuka ake, i don't want to lost someone again, I'm scared”

Kasa ce mata komai yai ya aje wayar wayar saman teburinsa ya lumshe ido, duk wanda zai ce yana jin tsoron rasa w

ani a gidan a bayansa yake, tun yana rasa mata yana jin tsoro har abun ya soma zame masa jiki yanzu kuma yaya ya rasa da kuma dan'uwan.

Sai biyar har da yan mintuna ya bar office din ya nufi gurin da ya san ya bar Bappa da Inna da kuma sauran ma'aikatan a

sibitin. Ko da yake ya tarar an tafi da su zuwa police station domin bada cigiya bisa ga shawarar da hukumar asibitin ta bayar, sun fada masa sai idan anyi bincike ba a gano inda take ba sannan yake da damar shigar da kara ko kuma daukar matakin daya dace

akan yarsa amman for now ya fara zuwa ya sanarwa hukuma ayi bincike har gidanje redio za a saka cigiyar.

Shattima be bar asbitin ba har sai da ya rubuta takardarsa ta neman transfer, domin a yanzu ya yarda da maganar Baba Waziri cewar Familynshi suna b

ukatar shi a kusa da su.

FALMATA POV.

Sai da suka gama karyawa sannan Momy ta shiga ta shirya ta nufi gurin aikinta, ta bar Falmata ita kadai a gidan bayan ta fada mata ta dafa duk abun da ranta yake so da rana. Tana zaune falon tana kallo har 1

2 na rana, can kuma ta tashi ya fara gyara falon, domin tun shigowarta da suka gama karyawa Momy bata ce mata ta gyara komai ba, bayan kuma ta dauke ta ne aiki saboda haka, wata kila tana jin kunyar yi mata magana ne. Ita kuma hankalinta be bata wannan ba

sai a yanzu, sai da ta gyara falon tsaf sai ta nufi upstairs, bata karasa dakin Momy ba ta tsaya cak tunawa da tai da abun da ya faru, a wacan karon bata tunanin halin Momy zai zo daya da na su, sai dai be kamata ta shiga ba tun da ba ita ta bata umarni ba

.

Juyowa tai ya sauko kasa ta nufi kitchen din ta wanke kayan da suka ci abinci da su, sannan ta yi share tai mopping, ta maida komai a muhallinsa sannan ta fito falon, ta zauna ta cigaba da kallonta, sai da aka yi sallah sannan ta ta tashi a nan kuma ta

rasa inda zata shiga tai alwala, domin bata san kan dakunan ba, kuma a ganinta be kamata ta shiga ba tare da izinin Momy ba, fitowa tai waje tunawa da masarautar ma akwai Garden, inda take alwala wata kila Momy ma tana da ita, sai da ta gama zagaye gidan d

a fadinsa amman bata ga Garden ba, sai dai ta hango fanfo a gurin da tankin gidan yake, gurin ta nufa ta bude fanfon tai alwala ta dawo cikin falon ta shimfida dankwalinta tai sallah, bayan ta gama ta tashi ta shiga kicin din, sai ta rasa me zata girka, Mo

my ta bata umarnin da girka duk abun da take so, amman bata fada mata inda kayan abincin suke ba, kuma tana tsoron kar tai bude bude tai laifi, magi man kuli, albasa da sauransu ta ga inda Momy take ajewa, shimkafa da sauran kayan masarufi ne bata san inda

zata buda ta gansu ba. Har ta juyo da zimmar fitowa daga kitchen din sai kuma wata zuciyar tace ta mata ta bude karamar kofar kicin din mana, domin kofa biyu ne a kicin din data store da kuma ta fita wajen gidan, sai kuma kitchen cabinets da suke rufe, su

ta fara budewa kamin ta nufi kamar kofar ta bude, sai tai arba ba babba daki mai cike da kayan abincin kala kala. Wasu an bude wasu kuma suna a rufe, rufewa tai ta nufi inda kayan miyar suke ta deba ta zuba a turmi ta daka sannan ta kunna gas ta dora tuku

nyar da take kyautata zaton zata wadatar ta zuba mai ta soya... A natse ta hada komai na jallof sai dai bata yi karabanin saka nama ko kifi ba duk kuwa da kasancewar ta ganshi a firizar dake kicin din.

A gurin ta zauna ta tsare girkinta har sai da ya da

hu sannan ta sauke ta kashe gas din, dan karamin plate ta dauko ta zuba nata, ta dauko wata kula ta zubawa Momy, ta sake dauko wata ta zubawa Sirleem duk da bata da tabbacin zai dawo ko akasin hakan, haka nan dai take son ya zo ya ci girkinta.

Sai da a

binci ya sha iska sannan ta dandana, tana jin yayi daidai ta daka wani tsalle ta dire tana jin wani irin dadi, ta dauki abinci ta fito falo ta zauna ta saka abinci a gaba ta ci abunta ta koshi, sannan ta koma kicin din ta wanke plate din ta aje ta dauko cu

p ta kunna fanfan ta tara ruwan ta sha, sannan ta aje kofin ta dawo falon ta zauna.

Momy bata dawo gidan ba sai kusan la'asar, a lokacin Falmata na kwance a kasa tana bachi, Momy kamar ta sani ta saka makulli ta waje ta bude kofar ta shigo, sai da ta ka

wo tsakiyar falon ta tsaya tana kallonta, ta takure guri daya tana ta bachi, irin yadda marasa galihu suke yi, hakan yasa tausayinta ya kara shiga zuciyar Momy, a ganinta kamata yayi ace tana gaban mahaifiyarta ko kuma gidan mahaifinta, amman tana a nan ra

kube tana bachi.

“Fulani”

Momy ta taba ta, sai ta farka a firgice, ganin Momy yasa ta tashi zaune.

“Sannu da zuwa Momy”

“Yauwa, ki hau kam kujera mana ki kwanta ya zaki kwanta a kasa sanyin tiles din ai sai ya shiga jikinki ga kuma sanyin ac”

“Tau na gode”

Ta mike tsaye ta hau saman kujera ta kwanta, Momy kuma ta hau sama ita da tufafin aikinta, bata sauko ba sai da tai wanka ta shirya cikin wasu tufafin kuma ta sauke nauyin sallah, la'asar sannan ta sauko kasa, ta shiga tashin Falmata.

“Tashi ki yi sallah la'asar”

“Tau”

Falmata ta mike tsaye.

“Ki shiga dakina akwai bandaki a ciki ki yi alwala idan kin fito akwai carpet a gurin sai ki yi sallah”

“Tau na gode”

Momy ta bita da kallo har ta haye sama ta shiga dakin. Sannan t

a busar da iskar bakinta ta nufi kitchen, ba karamin mamaki tai ba ganin Falmata ta yi girki, duk da ta san ta fada mata ta girka abun da take so, gas Momy ta kunna ta dauko tafassashen naman dake firgin ta soya sannan, ta soya kwai ta zuba saman shimkafar

sannan ta zubawa Falmata nata dabam a plate ta dauko ta fito kicin din, ko da ta fito Falmata ta sauko tana zaune kasa tana kallo.

“Ungo ga wannan ki ci nasan dai kin ci abinci ko?”

Falmata ta saka hannu biyu ta karba.

“Na gode Allah ya saka da a

lheri”

“Daga yau idan zaki girki ki rika saka nama, wa ke da abincin kula daya?”

“Ya Sirleem”

Ta amsa kanta a kasa tana jin kunyar da bata san dalilinta ba. Momy ta yi murmushi.

“Ai yana da wahala Sirleem ya dawo yanzu, kin ba mai gadi?”

“Aa



“To ki zube a wata kula tana nan rawaya ki zubawa a ciki ki kaiwa mai gadi”

“To”

Ta mike tsaye ta nufi kitchen din ba dan ta jidadin yadda Momy tace a bawa mai gadi ba, domin ba dan shi ta zuba ba, sai dai babu yadda ta iya dole ta bi umarninta,

juye abincin tai a kular da momy ta fada mata ta dauka ta fito da shi.

“Ki bar kofar a bude ba sai kin rufe ba”

“Tau”

Ta amsa sannan ta nufi kofar ta wangale ta fita, kamar wacce bata son tafiya ko take bakincikin a bashi abincin haka ta isa inda

yake ta gaishe sannan ta aje masa abincin.

“Momy tace na kawo”

“Tau Allah yayi albarka”

“Ameen”

Ta juyo ta dawo falon cikin rashin dadin rai. A inda ta zauna dazun ta sake zama ta fara cin nama sai da ta cinye tsokokin sannan ta fara cin kwan,

shi kam kadan ta ci ta ji ya isheta ba dan bata son kwai ba sai dan cikar da cikinta yai, sakamakon abincin data ci dazun.

Tana zaune a gidan har dare, sai duk ta ji ta takura, sai ta ji tafi sakewa a masarautar duk kuwa da kasancewar a nan Momy tafi

sake mata fuska da komai ba, amman acan tana wuni da su Labib suna rage mata kewa, kuma a can tana fita ta zagaya har garden din tana wasa da su, a nan kam wuni tai kallo, duk yadda take da son kallo sai ta ji a gudireta.

Ta inda abun ya zo mata da sauki

ana kiran magariba sai ga mai daukarta ya iso ya aiko mai gadin kiranta.

“To gata nan zuwa”

Momy ta amsa masa sannan ta kalli Falmata tace.

“Tau sai ki je yana kiranki, kin koshi dai ko? Na ga ma baki ci tuwon da yawa ba, ko baki son miyar shuwa

ka ne?”

“Aa ina so, na ci ai ya ishe ni”

“To Allah ya tsare hanya”

“Ameen na gode sai da safe”

Ta fada sannan ta nufi kofa tana gyara Hijabinta, duk abunda ya faru a masarauta Momy bata da labari hakan yasa Falmata bata san komai ba. Bata tare

da tsoro ko fargabar komai ba ta shiga gidansu bakinta kumshe da sallama, daga Naja har Tumba aka rasa mai amsa mata, Tumba ta ranka uban tagumi tana kallon kofar kamar mai jiran shigowarta.

“Makira... Macijiyar soshiya...yar bakinciki, ke wannna da dak

e nai kishi dana shiga uku.. Da yanzu ina can gidanmu ina zawarci”

Gaban Falmata ya fadi jin irin kalaman da Tumba take jifarta da su, sai ta tsaya cak tana kallon Tumba da fitilar touch light take haskawa. Sai ta rasa dalilin wannan kirari da Tumba tai

mata, domin bata san ta aikata wani laifi ba kamin ta fita, sai dai inda sabo ya kamata ace ta saba da abun da ake mata a gidan, domin ko bata da laifi ana kakaro shi a dora mata.

“Daga gidan uban wa kika?”

“Daga gurin aiki”

“Gurin aikin ubanki,

makira annamimiya, barauniya”

Jikinta ya fara bari zuciyarta ta shuga bugawa da mugun karfi.

“Gurin wasu mazan kike zuwa kenan?”

“Aa Wallahi daga gurin aiki nake”

Ta fada da muryar dake nuna kuka na kusanto, Tumba ta dauki butar dake kusa da it

a ta jefa mata iya karfinta tana jin kamar ta saka wuta ta kone ta, Falmata ta kauce da sauri tana kuka.

“Shegiya mai bakin hali, yar gadon mugun abu, ke dai ba burinki ki saka a bakinciki ba? To Wallahi sai dai ki ganshi a dakin tsohon nan da zaki aura

, barauniya kawai ashe an koreki gurin aiki shine kika ki fada kina yawon bin maza? To bari ubanki ya dawo, sai na fada masa komai kuma Wallahi na ba zan iya zama da ke ba, kara ya aurar da ke kawai na huta da bakinciki, da kuma zubar da mutuncin da kike m

ana, ba zan iya jira nan da wata hudu ba, ai bakincikinki kasheni zai yi ya zo a canja shawara, kara ya aurar da ke kar ki dauko mana cikin shege, ina jiran wata yai a bani kudi sai kawai na ji wani bakin labari, da yake kin yi gadon makirci sai kika kama

zancen kika rufe, kika samu lasisin bin maza ko?”

Falmata ta fashe da wani irin kuka jikin ta sai bari yake tsakanin kalaman da Tumba take jefarta da su, da kuma irin duka da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login