Showing 36001 words to 39000 words out of 304903 words

Chapter 13 - FULANI COMPLETE

dakin. A

backyard ya fito ya tsaya yana ta kallon harabar gidan, zuciyarsa cike da tunani kala kala cikin har da makomarsu idan aka rasa Mai Martaba, and me ke damun mahaifinsa shi ya fi komai tsaya masa a rai, why baya son haske? Why baya son mutane?

Jin an dafa

shi ne yasa ya juyo a hankali sai suka yi ido hudu da Zainab, ta sakar masa murmushi tana tsosar mintin dake bakinta.

“Me kake tunani?”

“Ba komai”

Ya amsa mata yana juyawa fuskarsa ba yabo ba fallasa.

“Na binciko wani kauye, BANDALO a cikin K

atsina yake, ba  a san mutanen kauye sosai ba, ma fi yawa mutanen kauye Fulani ne makiyaya, sai dai ance akwai wasu Kabilu da yare kala kala a kusa da su, so i decided zan je can na yi aikina”

Juyowa yai ya kalleta.

“Hajiya tun daga Yola ki je har K

atsina?”

“Yeah aiki ne ai you know”

“Yeah amman kasar na cikin matsala tsaro kin sani ai”

“Okay zan yi magana da Ammy sai ta ba ni police su raka ni”

Ya dan tabe baki.

“Fine Allah ya bada sa'a”

“Amin excuse me....”

Ta fada tana kokari

n barin gurin rike da wayarta dake ring. Dakinta ta dawo ta manne da wayar a kunneta.

“Hey Baby ya kake?”

“Lafiya kalau, ya gidan... ”

Sun dauki kusan thirty minutes suna waya da Auwal mijin kawarta kamin daga karshe su yi sallama cike da saukin

juna. Zaune ta tashi tana wani irin shu'umin murmushi, ita kanta bata jin son Namiji kamar yadda take son Auwal ba, ko Maybe saboda ita ta nemo shi da kanta ko kuma saboda yana da kyau ne? Or maybe saboda ya waye kamar yadda take son namiji? Domin after ta

karbi Number shi kamin ta kira shi shi ya fara kiranta suka gaisa ina ya samu number ta shine abunda bata taba sani ba har yau, kuma bata tambaye shi ba.

Tashi tai ta fita daga dakin zuwa dakin Iya, ta tararda falonta babu kowa sai tv  hakan yasa ta w

uce dakinta kai tsaye, sai ta same ta zaune saman gado tana kokarin falla goro ta ci. Kusa da ita ta zauna cike da shauki.

“Iya gobe surukin ki zai fara shigowa masarautar nan ya mu gaisa me kike ganin ya dace na masa?”

Iya ta kalleta kallo na tsab

domin har hanjin cikinta tana gani da yadda jini ke tafiya a jikinta.

“Duk abunda kika shirya masa a dole ya so, wa zai ki abun masarautar nan?”

Ta saka duka hannayenta biyu ta dafa mahaifiyarta cike da nishadi.

“Na sani, kawai na rasa da me ya k

amata na tarbe shi ne, Wallahi ina son shi sosai”

Iya ta yi murmushi tana dauke kai daga barin kallon yar tata.

“Zainab har yanzu ba ki fara kwadayin aure a cikin masarautar nan ba?”

“Wannan karon da gaske aure zan yi, ba zan ma dauki lokaci ba”

Ganin Zainab bata gane inda ta dosa ba yasa bata sake ce mata komai ba akan hakan ba.

“Ba kya jin kunyar ki auri mijin kawarki? Ba ki son ki auri mijinki wai mijin wata? Ba ki so mijinki ya rayu da yayanki kawai? Kin fi son ki rayu da wasu yaya?”

Zainab ta mata kallon Mamaki.

“Ita fa ta saka mijin nan na gani na ji ya min to miye nawa a ciki? Ko matansa 99 da tara ni zan iya zama ta 100 domin ya cika yadda na ke son mijina ya kasance, ba ruwana da matarsa da yayansa, rayuwata zan yi da dabam it

a ma nata rayuwar dabam”

Iya ta tabe baki tana kallonta kamin ta girgiza kai.

“Har yanzu ba ki da hankali Zainab tun da baki fara tunanin gina kanki ba”

Ba ta ko jira iya ta karasa ba ta mike tsaye ta fice daga dakin, daman can indai irin wannan m

aganar ce basa jituwa da iya. Da kallo Iya ta bita har ta fice.

“Ba ki da mijin da ya wuce Shattima Zainab, ba zan yi zaman banza na kararda shekaruna a masarautar a banza ba, ina burin zama sukukar Sarki kuma ina da burin na juya masarautar nan ta yadd

a na ke so da bakina da kuma ikonki, dole ne Mai Martaba ya kwanta dama, Shattima ya hau mulki ki kuma ki zama matarsa Sarki, da ke kadai Shattima zai rayu, ke kadai sa ki haifa masa yaya, daga lokacin ne komai zai dawo karkashin iko na Ammy da kowa ya daw

o bin umarnina, idan har kika dage sai kin auri mijin kawarki to sai dai ke da kawarki ku rasa shi...”

Babu wasa a kalamanta kamar yadda fuskarta ta nuna, domin gaba daya ranta a bace yake da maganar da yarta ta zo mata da ita, tana ta nuna mata inda ga

bas take amman ta ki ta gane.

Mikewa tai tsaye ta nufi kofar dakin ta rufe da makulli ta dawo can karshen dakin ta hanye wata katuwar dorowa dake gurin ta daga carpet din ta fara tonon kasar gurin, ko ina na dakin tiles ne sai gurin ne kadai ke da masa h

akan yasa ta rufe shi da carpet kuma ta dora durowa sama.

  Sai da ta haka dan madaidacin rame sannan ta mike tsaye ta koma karkashin gadonta ta janyo wata kwarya ta bude kwayar ta dauko wani abu mai kamar mutun amman an nade da shi da zaren makauniya, h

ar da yan tsorayensa, ta dauko wata karamar wuka, sannan ta dauko lighter ta dawo gurin ramen ta tara abun ta kunna lighter ta fara kara shi, a take Luna dake dakinsu ta kwala wani irin ihu ta ta fara fisge fisge tana kuka iya karfinta. Iya ta yi saurin ja

nyewa hakan yasa tai shiru sai kuma Iya ta sake karata a take ta kara falla ihun tana kuka. Kashe lighter Iya tai ta tara abun ta saka wuka ta janka gurin wuya, ta cikin zaren jini ya fara zuba har ya bata mata hannu, sai da ta bari jinin ya tsare tsab san

nan ta rufe kasar ta gyara komai yadda yake, sannan ta shiga bandaki ta wanke hannunta ta wanke abun da ta wanke ta warware zare ta saka a cikin masai tai bi shi da ruwa, sannan ta dawo karkashin gadon ta dauko wani kwano mai murfi ta bude ta saka abun da

ta yanke mai lamniya kamar nama kuma ba nama ba ta saka cikin kwanon ta rufe ta mike tsaye ta maida kwanon mazauninsa sannan ta mike tsaye ta nufi kofar ta bude ta fita ta saka makullin daga waje sannan ta nufi bangaren Ammy.

FALMATA POV.

Ba karami

n dadi Tumba ta ji ba, da Falmata ta fada mata cewar sun ce sun hakura har ma ta yi musu aikin.

Sai da Falmata tai karyar sannan ta fara tunanin idan wata yai ina za ta samu kudin da zata bawa Tumba? Anya wannan karyar zata haifar da da mai ido kuwa? Ko

dai ta sake jefa kanta cikin wata matsalar ne? Idan kuma ta ce bata koma aikin ba za ta iya mata wani shekarin. A take ta fara tunanin ko dai ta koma ta ba su hakuri ko za su hakura? Idan ma ta je ba su hakura ba ya za ta yi? A take idonta ya cika da kwal

la ga yunwa sai cin cikinta take domin tun abincin da ta ci a gidansu Khadija da safe bata sake saka komai a cikinta ba har dare.

Duk kiran da Tumba take mata ba ta ji har sai da ta dauki abu ta jefa mata, ba dan tunanin da take kadai ba har da rashin

da take fama da shi a yanzu wanda har sai anyi magana kusa da kunneta ko kuma an daga murya sannan take ji. Zabura tai ta kalli Tumba hankalinta a tashe idonta kamar za su fito jikinta sai rawa yake.

“Tashi ki fita ana miki sallama na ce”

Ta fada da

karfi, da sauri Falmata ta tashi ta shiga daki ta dauko Hijabinta ta saka ta fita waje. Umar ne natsentsen saurayi kuma dan wanka, ba mai kudi ba ne amman yana da rufi asiri domin yana tsaron shagon wani mai saida kayan shaddodi a ciki yake samun na lalur

arsa. Dukan samari da suke zuwa gurin Falmata tana fitowa ne kawai saboda Tumba tana matsa mata ta fito din dan ta samo abun hannunsu wasu kuma saboda suna kunna mata wakar M2 amman ban da Umar Falmata tana son umar sosai ba dan wani abu na shi ba ba dan k

uma yana kunna mata wakar Sirleem M2 ba, no so ne dai na Allah.

Murmushi tai masa wanda ta saba masa a duk lokacin da ta fito sai ya kunna wayarsa ya haska fuskarka duk da kasancewar akwai hasken gulob a gurin. A take na sa murmushin ya kushe.

“Falma

ta me ya samu fuskarki?”

Bakinsa da ke motsi kawai take kallo, kunnuwanta sun kasa jiyo mata muryar masoyinta a yau. A take ta rufe bakinta ta fara kuka marar sauti hakan kuma ba karamin daga masa hankali yai ba.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un

me ya same ki?”

Nan ma bata ji me yace ba amman tabbas magana yake.

“Bana iya jin komai Umar sai idan ka yi magana kwarai ko kuma ka yi kusa da kunnena... ”

Ta fada cikin kuka, sai ya nuna mata dakalin dake kofar gidan alamar ta zauna, after ta z

auna shi ma ya zauna yana kallonta cike da tausayawa.

“Me ya same ki?”

Ya fada yana kai bakinsa kusa da kunneta. Bata boye masa komai ba tun daga kan korar har dukan ta karasa tana kuka. Shi ma sai da idonsa ya cika da kwalla, sosai yake jin tausayi

nta da ace yana da hali a yanzu tabbas aureta zai yi ta raba ta da gidan ta huta, sai dai be da halin aure yanzu domin shi da iyayensa duka talakawa ne kusan ma shi yake taimakon iyayensa kuma dan abun da yake samu ba wani mai yawa ne sosai ba.

Ajiyar

zuciya ya sauke ya shiga gallery wayarsa ta kamo mata wakar Sirleem dan ya san ita ce kadai zata saka ta yin shiru a yanzu. Yana mika mata wayar ya saka hannunsa aljihu ya ciro airpiece dinsa ya mika mata, sai ta share hawayenta ta karba ta saka a kunne ta

na kallon wakar hawaye na sauko mata. Ta dauki lokaci kamin hankalinta ya tafi gurin wakar har tai murmushi.

Yau be bata kudi ba sai siyayyar kayan marmarin da yai mata, wanda ta saka ran ya bata kudin ta cire wani abu ta siye gari da suga ta sha domin

yunwar ta matsa mata fiye da kima a yau. A gaban Tumba ta aje kayan marmarin da ya bata Tumba tai mata na kurame wai ta dauki ayaba daya lemu daya, sai Tumba tai mata alama da ina kudi?

“Be ba ni ba”

Tumba bata ce komai ba ta dauki ledar ta shige da

ki. Falmata ta koma gefe ta zauna tana ci, babu komai a zuciyarta sai tunanin mahaifiyarta.

__________

Hope dai ba ku manta da Fadime ba ta kauye? Na ga kamar za ku rikice ne shiyasa na raba muku labarin biyu.

*

🐄🐄

FULANI

🐄🐄

*

By Khadee

ja Candy

*10*

FALMATA POV.

Haka ta kwana da ragowar yunwa a cikinta, washe gari tun da asubar fari Tumba ta fito ta fara kunna wuta a lokacin Falmata na waje tana alwala sallah asuba, baya ta gama ta shiga daki ta dauki hijabinta zata saka tai

sallah sai ta ji an rikota sakamakon kiran da ta yi ta mata bata ji ba.

“Karki sallah bari ki yi wanka”

Ta rada mata a kunne, ba ta isa tace mata bari na gama sallah ba, dan haka ta aje Hijabin ta fito bakin kofar dakin ta zauna tana ta kallon wuta

r da Tumba ke ta aikin fetawa tana tura ledodi, nan da nan ruwan sukai zafi sai ta dauko wani garin magani ta zuba a cikin ruwa ta juya shi sannan ta sauke ta tsirka mata da ruwan sanyi.

“Zo dauki ga shi nan ki yi wanka maganin tsari ne”

Tana maganar

tana mata alama da abunda take nufi irin yadda ake ma kurame. Falmata ta tashi daga inda take zaune ta dauki ruwan maganin ta shiga bandaki ta cire kayan jikinta ta watsa ruwan ta fito. Da hannu tai mata a alama da ta zo, sai Falmata ta aje bokitin hannun

ta ta karasa inda take tsaye, duba ta tai dan ta tabbatar idan ta yi wanka, ga kuma shaida ta gani maganin ko'ina a jikinta.

“To je ki yi sallah ma”

Nan ma alamar kurame tai mata, sai Falmata ta juya ta shige cikin dakin ta dauki wasu tufafin ta sak

a ta saka hijabinta ta fara sallah.

Bayan ta gama tai addu'ointa kamar yadda ta saba sannan ta fito ta gyara ko'ina na gidan tai wanke wanke, ba ta ko tsaya tambayar abincinta ba ta fice da zimmar zuwa gurin aikin karya.

Tana tafe tana nemawa kanta mafi

ta, ta sake komawa gidansu Khadija ko kuma dai ta koma gurin aikin ta sake ba su hakuri? Domin idan wata yayi Tumba zata tambayi kudinta na albashi to me za ta ce mata? To idan ma ta koma za su karbe ta ne? Sai ta rasa wanda za tai, daga karshe dai ta yank

e shawarar zuwa gidansu Khadija domin har ga Allah ita yanzu tsoron zuwa gidan can take, abun da bata sani ba Naja na biye da ita a baya tana lekenta kamar yadda Tumba ta saka ta. Sai dai ita bata lura ba har ta shige cikin gidansu Khadija. Yau kan bata sa

mu Khadija a gidan ba dan ta tafi islamiyar safe kasancewar yau Sunday, Maman Khadija bata tsaya komai ba ta zubo mata abinci, Falmata ta zauna ta ci sai da ta koshi sannan ta nemi guri ta kwanta tai ta bachinta. Sai kusan azahar sannan Khadija ta tashe ta

, firgigit ta mike tsaye dan lokacin komawarta gida yayi har ma ya dan gota.

Duk yadda Maman Khadija da ita Khadijar kanta suka so Falmata ta tsaya ta ci abinci sai ta ki gaba daya hankalinta ya tashi kar ta koma late Tumba ta doketa.

“Ko na zuba mik

i a leda?”

“Idan ta gani zata iya min fada”

Duk da rada Khadija take mata maganar. Bata jira abunda Khadija zata sake cewa ba ta fice daga gidan hankalinta a tashe, da sallama ta shiga gidan Naja ta amsa mata tana tabe baki.

“Ashe idan an tura ki

aiki gidansu Khadija kike zuwa kina zaunawa ko? Ai na biki dazun na gani”

Naja ta fada cikin daga murya ta yadda Falmata zata iya jinta. Wani irin bugawa gabanta yai da karfi, da zaro ido tana kallon kofar dakin Tumba sai ta nufo gurin Naja ta riketa.

“Dan Allah Naja karki fada, dan Allah ki rufa min asiri”

Tana rufe baki Tumba na fitowa daga dakinta ta tsaya bakin kofa rike da kunkuru tana hararar Falmata, da sauri Falmata ta mike tsaye ta fashe da kuka, a take tsoro ya kamata ta rika ganin kamar

Tumba dukanta za tai sai ta fara ja da baya baya tana ganin Tumba ta motsa ta fice daga gidan da sauri. Komawa tai gidansu Khadija ta zauna, a can ta wuni har dare ba ta fada musu abun da yasa ta gudo ba, sai dai suna ganin yadda hankalinta ya tashi sun s

sn ba lafiya ba. Sai bayan sallah isha'i Naja ta zo kiranta, cikin rashin kuzari ta tashi suka fita daga gidan tare tun kan su karasa gida ta fara kuka.

Suna shiga cikin gidan fara rabawa jikin gina tana kallon mahaifinta dake watso mata harara.

“Gat

a nan ashe idan an turata aiki gidansu Khadija take shiga, yau aikin komai ba tai ba can ta wuni, ni dai dan Allah ka yi mata tsakani da yarinyar ba ma yarinyar kirki bace Wallahi”

Tumba ta fada tana narke murya kamar gaske.

“Wato Falmata duk abun d

a za a fada miki ba kya ji ko? Kullum sai kin tsiro wani bakin hali ko?”

Bata ji abunda Tumba ta fada ba amman ta ji abunda mahaifinta yace shi da yake da tsawa yake mata magana.

“Zo nan....”

“Baba dan Allah ka yi hakuri sun kore ni kuma ina tsor

on komawa gidan da? Allah kai hakuri gobe zan je”

Ta fada cikin kuka.

“Zo na ce....”

Ta fara tafiya tana kuka tana kallon Tumba tana jin kamar ta taso ta zo ta cece ta, irin yadda mahaifiyarta take mata idan za a doke ta, gabansa taje ta tsaya ta

rika hannunta ya murde iya kar karfinsa sai da ta fasa wani irin ihun ta fadi kasa.

“Wayyo Baba Wayyo Baba dan Allah kayi hakuri, ka yafe min Baba karka kashe ni dan Allah”

Sakin hannun nata yai ya rika hijabinta yaja ta daga inda take kwance har g

urin da tumakinsu suke daure, ya kwance igiya daya ya daure mata kafa tamau, zai juya ta riko kafarsa.

“Dan Allah Baba ka yi hakuri, karka ba ni na kwana a cikin tumaki dan Allah Baba”

Kasa juyowa yai kuma ya kasa tafiya har cikin ransa yake jin kuk

an yarsa idonsa suka cika da hawaye, amman sai ya ji ba zai iya mata komai ba bayan haka, fisge kafarsa yai ya fice daga gurin ya barta tana ta kuka. Tun tana kukan tana kiran sunansa tana bashi hakuri har koma kiran Tumba tana bata hakuri daga kashe sai t

a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login