Showing 291001 words to 294000 words out of 304903 words

Chapter 98 - FULANI COMPLETE

ido.

“Wai Wai Wai Wai haba Baby”

Ya rufa tana sauke ta, sai ta tuna ance karka kuskura ta bata masa rai kuma idan ta bata masa rai ta duka ta bashi haku

ri tace ya yafe mata. Saurin dukawa tai kasa.

“Dan Allah kai hakuri ka yafe min”

Kallonta yai da murmushi, sai ya ji ta kara burgeshi, hannunsa ya mika mata sai ta rika ta mike tsaye tana tara yawu a bakin..

“Miyasa kika cigeni?”

“Bana son ka

zamta ne shiyasa kai kuma...”

Ta yi shiru bata karasa ba sai tai kasa da kanta, hannunsa ya saka ya dago kanta.

“Ba kazanta bace hakan yana nufi soyayya ne da rashin kyamar juna, idan na sha yawunki na yarda da tsaftarki kuma ina kaunarki ne matuka,

idan kin sha nawa hakan na nufin kin yarda da ni kuma kina kaunata, dan haka ki daina kyama”

Ta daga kai tana kallonsa fuska a yamutse, sai wani abu take ta ji tsabar kayan matan yar gidan mai fata da aka dura mata.

“Yanzu zubar da yawun”

Ta zuba

r da sauri daman abun da take nema kenan, tana juyowa sai ya kai bakinsa saitin nata.

“Kama ki yi kissing”

Ba dan ance kar ta masa musu ba, da babu yadda za ayi ya ce tai wannan kazantar ta yarda tai. Ta kama kadan ta dan yi kissing tana runtse ido

kamar mai shan magani, sai tai saurin cirewa ta kalleshi.

“Zan iya yin amai gobe?”

“Yeah Allah ya kai mu, oya cigaba”

Ba dan ranta ya so ba ta kusan kwashe rabin awa tana kissing dinsa sun tana kin hade yawun har ta fara hadewa tana jin kamar zat

a yi amai.

“Good”

Ya juyar da ita ta yadda ita da shi za su fuskanci madubin da yake bandakin.

“Kalli kyakkyawar fuskanci da dan karamin bakin nan”

Ta kalli kanta sai ya saka hannu ya cire sarkar wuyanta yai kissing din bayan wuyanta, sai kum

a gefen wuyanta na dama zuwa hagu. Ita kuma tai shiruuuuuu tana ta kallonshi ta madubi da tunani kala kala a ranta, ba yau ya fara kissing dinta ba Wasim ma ta taba kissing goshinta hannunta, amman ban da wuyanta amman shi har da wuyanta yake kissing kuma

ya saka ta sha yawunsa, tsoro ya fara kamata Allah dai yasa na jininta ya shanye ba ta cikin yawun, kuma wannan abun da yake mata abu kamar dan iska sai wani jarrrrr take ji. Hannunsa ya saka yana zirya da yatsansa a wuyanta yana kallonta ta cikin madubin.



“Yanzu alwala za ki yi sai mu yi sallah”

“Ina da alwala, sai da na yi alwala sannan akai min kwaliya”

“Okay ni bari na yi alwala”

Ya fada sannan ya sake kissing din wuyanta, wannan karon juyowa tai tana kallon fuskarsa, sai ya doko mata da fu

skar hakan yasa tai saurin rufe idonta kamar ta san idon zai sumbanta, sai ya dora bakinsa kan fatar idonta ya sumbance both eyes dinta da suke rufe sannan ya saka bakinsa a hancinta ya tsotse hancinta tasss, sannan ya sumbance shi ya dauke bakinsa.

“J

irana zaki yi?”

‘Kazami babban kazami hancin da ake cire majina ake kwakwata antoni shi yake tsotsawa, ina masa kallon mai tsafta ashe babban kazami ne’

Ta fada a ranta sannan ta bude idon ta kalleshi.

“Zan zauna a falo”

“Okay”

Ya furta idon

sa kamar wanda ke jin bachi, sai ya murza yatsun hannunta sannan ya sake ta ta fice. Tana fitowa taja masa kofar bandakin ta rufe, arba da tai da furnitures din dakin sai yasa ta manta da komai, ta shafa fuskarsa tana zaro ido.

“Yanzu nan dakina ne?aah

ahahaaaaaa”

Ta furta kadan kadan ta zauna bakin gadon tana ta mamaki yadda aka cika dakin da katon farin gado dan turkish da wardrobe kamar wata yar govno, hawa tai saman gado ta kwanta ta sauko ta nufi wardrobe ta shafa, tana jin motsinta sai tai sauri

n ta dawo bakin gado ta zauna ta kama jikinta ta marairace fuska kamar da gaske babu ruwanta. Bude kofar bandakin yai ya fito rike da babbar rigarsa ya dorata saman gadon sannan ya nufi wardrobe ya bude ya dauko mata hijab. Sai ta karba ta saka gaba ya tsa

ya ta tsaya daga bayansa kadan kamar yadda ya nuna mata sannan suka soma gabatar da sallah akan katon center carpet din da yake dakin, bayansu sallama yai musu addu'a sannan ya juyo ya kama kanta ta rike ya karanta mata addu'ar da annabi ya koyar da mu.

“Alhamdulillah wannan Allah da mu ka yi godiya ce ga Allah akan irin ni'imar da yai mana, ya hada mu ta sigar da ba mu yi zato ba, kuma ya daidaita mu ya shirya tsakaninku har muka kawo yau da aka daura aurenmu”

Ta gyada masa kai alamar gamsuwa.

“Na

yi mana addu'a kuma ina fatar ke ma kin yi mana”

“Eh na yi”

Yayi murmushi.

“Me kika ce?”

“Na ce Allah ya tsare mu daga dukan shari kuma ya ba mu yan biyu, kuma ya mana albarka”

“Yan biyu kike so kenan?”

Ta yi kasa da kai tana jin kunya,

to mi ya rage tun da ta yi aure a yanzu ai ba ta da burin da ya wuce haihuwa, ita ma ta zama uwa kamar kowa.

“Samun yan biyu ba sauki fa”

Ya fada yana kallon fuskarta.

“Ni dai ina so haka nan suna burgeni”

“Yanzu fada min yadda ake wankan hai

la”

Sai ta ji wata kunya ta rufe ta, wai ta fada masa ai da kunya kam ta ina zata fara.

“Fada min mana”

“Gaskiya ni dai ina jin kunya”

Ya kai hannunsa ya kama hannunta.

“Fatee na”

Ta kalleshi.

“Babu kunya tsakanin mata da miji, kuma

babu boyewa juna sirri, sannan babu yi ma juna karya, ni mijinki ne sirrinki komai nawa a yanzu na ki ne, haka ke ma sirrina ce, ko da wasa karki kuskura ki fadawa wani cewar mijinki yayi miki kaza ko taba miki kaza ko yace miki kaza kinji ko?”

“To fad

a min”

Ta fada masa kamar yadda take kuma kamar yadda Inna ta koya mata, ta fada daidai sai dai abun da bata sani ba shi ne yadda ake wankan haila haka ake wankan janaba.

“To ai yadda ake wankan haila haka ake na janaba”

“To minene ita?”

A taka

ice yai mata bayani duk da ya san ba lallai ta fahimta da kyau, har sai ya nuna mata, ita kam gaba daya ta gama tsinkewa da shi ganin yadda ya zage dantse ya fada mata abubuwa babu ko kunya, tashi yai ya nufi gurin da aka aje musu ledodi, ya dauko ya kawo

gabanta ya aje tana jin kamshin kaza ta fara hade yawu, sauka yai kasa ya shiga kitchen ya dauko plate da cup ya dawo dakin, da kansa ya zuba komai ya matsa kusa da amaryarsa ya kwanto da ita jikinsa ya dauki cinyar kazar ya kai mata a baki, kin bude bakin

tai haka nan kawai ta samu kanta da jin kunya. Be ce mata komai ba ya kai naman bakinsa ya tauna ya saka hannunsa ya dago kanta ya hade bakinsa da nata ya tura mata naman, tana son namam kaza over amman sai ta samu kanta da kyamar ci wannan.

“Tauna ki

hade”

Bata iya masa musu ba, ta tauna naman ta hade, aiko yana kai mata yankan a karo na biyu sai ta bude baki ta ci, haka yai feeding dinta ya bata madarar ta sha ta koshi, sannan ya tashi ya dauko mata mayan bachi.

“To ka tafi waje sai na canja”

“Aa ba inda zan je bari dai na kashe miki wuta”

“To zaka rufe idonka?”

“Eh”

Ya fada yana cire rigar shaddar dake jikinsa, tana ganin kirjinsa da farar fatarsa sai ta yi saurin rufe ido.

“Innalillahi”

Kamar wanda bata taba ganin namiji ba

riga ba haka tai, duk ganin da tai ma Wasim a can baya ba riga ta manta da shi sai a yau, murmushi yai ya saka rigar bachinsa sannan ya canja wandon shaddar ma zuwa na bachi, ya nufi gurin da wutar dakin take ya kashe wutar dakin, jin motsinta a bayansa ya

sa ta bude ido.

“Ka ce zaka rufe idonka”

“Rufe idona yake”

Shiru tai tana jin yadda yake kokarin cire mata zip.

“Kai ni dai ka daina bana so, bana so Wallahi ko na fasa auren”

Murmushi yai duk da ya san bata ganinsa ya janye hannunsa ya nuf

i gadon ya zauna, sai da ta saka hannun tawulga ta ji ba ya gurin sannan ta cire rigar ta lalaba ta dauko ta bachi ta saka ta cire zanen lace dinta dauko wandon ta saka.

“Na saka ka kunna wutar”

Ya tashi ya isa ya kunna wutar ya tsaya yana kallon yad

da ta janyo bargo tana kokarin shinfidawa kasa.

“Me zaki yi?”

“Zan kwanta a kasa”

“Ni kuma fa?”

“Ka kwanta a saman gadon”

“Saboda gani dan iska ko? A kawo min Amarya kamar ke kuma na kwana a saman gado ke a kasa”

“To bari na hau gadon sa

i ka kwanta a kasa”

Yayi murmushi ya kashe wutar ya nufo inda take tsaye ya saka hannayensa yana shafata.

“Ba wani abu zan miki ba, zaki kwanta ne kawai ni ma na kwanta”

“Rantse”

Kamar saukar aradu haka ya ji rantsuwar da ta bashi, sai yaji wa

ta sabuwar kasala ta sako shi gaba.

“Idan baka rantse ba ba zan yarda ba”

Ta ture masa hannu.

“Wallahi amman a yau”

Ya rantse mata ne saboda bashi da niyar taba a yau, domin ya san halinta kuma ya san akwai gajiya a tare da ita kamar shi din

dai. Daukarta yai ya kwantar saman gadon ya kwanta bayanta yana dan shafata a hankali.

“Baby ba a fada miki ki yi min biyayya ba? Ba a fada miki ki yi duk abun da nace ba?”

“An fada min”

“To ki daina min musu, okay”

“Tau”

A hankali yakr sha

fata, can kuma ya tashi zaune yai mata addu'ar bachi ya tofa mata yai ma kansa, sannan ya sake komawa ya kwanta. Ya kai bakinsa saitin kunnenta a fara karanta mata Bakaqa murya can kasa, yana shafa ta har bachi yai gaba da ita.

Be taba ta har safe, sai

da rabin bachin nata a jikinsa tai yi, sai asuba ya tashe tai alwala shi kuma ya shiga yai wanka sannan yai alwala ya fito su kai sallah a tare, bayan sun gama suka sake komawa bachi, misalin 9am aka kawo musu abinci kala kala daga masarauta cikin manyan

kuloli na alfarma, da kamsa yai feeding din matarsa sannan ya shiga da ita bandaki sai aka fara drama ita ala dole ba zai taba ta.

‘Da can kai kake min wankan ne, sai wani maida ni kake jaririya kana ce min baby’

Ta fada a ranta tana dan turo baki, s

ai yai murmushi ya kai bakinsa ya sumbanci bakinta.

“Sarauniyar shagwaba, idan ba ki sonba zan cilasta ki ba, amman ni za ki min”

Ta bude baki

“Babba da kai?”

“Very soon zaki bukaci haka”

Ya fada sannan ya sa kai ya fice ya barta a bathroom

din, she a tsaye tana kallon bathroom din tana duba gashin kanta da lallenta kamin ta cire tufafin jikinta tai wanka.

Gidan ya wuni da mutane kala daga bangaren Ammy da kuma Mai Martaba, sai kuma su Inna da suka zo mata sallama, a nan ta fara sabon ku

ka tana jin kamar ta fasa auren, har tana cewa Inna wai akwai dakuna a gidan idan zata zauna, Farinciki ganin inda Fadime take zaune ya manta Inna wani zancen kewarta ta shafe komai a ranta tana ta hamdalla ga Allah.

Ba ta wani dade a gidan ba ta tafi t

are da direban da ya kawo ta, yan'uwanta da yan'uwan su Bappa da suka zo bikin kan a gidan suka wuni sai dare sannan sukai mata sallama. Ana sallah magariba Hajiya Mairo ta zo gidan ta kawo mata ragowar maganin matanta kuma ta fada mata yadda zata yi amfan

i da shi, Fadime bata ji kewar ta gaske ta kama ta ba sai da kowa ya watse aka barta a katon gidan ita kadai sannan ta fara kuka tana kewar su Inna da za su koma gobe.

Ana sallah isha'i Shattima ya shigo gidan, mai gadinsa ne ya shigo masa da ledodin d

ake hannunsa, ya aje a falo ya fice da sauri, Shattima ya dauki ledodin ya wuce sama, ya tura kofar dakin ya shiga, sai ya same ta kwance saman gadon tana kuka a hankali, aje lododin yai ya karasa inda take kwance ya sa hannunsa ya dago ta.

“Babyna ya a

kai?”

“Su Inna ne za su tafi gida gobe”

Rumgumeta yai a kirjinsa yana kissing din kanta.

“Haba Baby ba gani nan ba? Kuma idan an kwana biyun ai zamu je mu gaishesu, kuma za a kawo miki Hadimai a gida masu ta ya ki zama fa”

Ta dago kanta ta kal

leta.

“Da gaske?”

Ya sumbanci bakinta ya shafa fuskarka.

“Yes Baby”

Sai ta maida kanta a kirjinsa tai lamo, yana shafa bayanta gemunsa a saman kanta.

“Kin yi sallah?”

“Eh na yi sallah”

“To taso muje ki ci abinci”

“Ammy ta aiko man

a da rana da dare ma”

“Iyeee yar gatan Ammy, kuma ga kaza can na siyo miki muje ki ci”

Kamar jiya a yau ma shi ya ciyar da ita, banbanci jiya da yau, Jiya ya kyaleta yau kuma ba zai iya daga mata kafa. Azatonta irin bachin jiya da akai lami lafiya ba

komai, har da wani kara shigewa jikinsa take domin ta ji dadin na jiya, kyaleta yai sai ta ta natsu bachi ya soma daukarta sannan ya kai hanunsa yana shafata.

“Yau ba zaka min karatu ba?”

“Kina so ne?”

“Eh ina jindadi”

Yayi murmushi.

“To

zan miki wani sabon karatu da yafi wacan dadi”

“To”

Ta kara yin lamoooo a jikinsa tana jiran ta ji kira'arsa a kunnenta sai ta ji yana kokarin sa hannunsa cikin rigar bachinta.

“Minene haka?”

“Shine sai an tattaba mutum?”

“Eh haka ake yinsa



Ya janta ta yi sama sosai sai ya saka bakinsa cikin nata yana kissing a hankali, yana kissing yana shafa bayanta sai wani yarrrr yarrrr yarrrr take ji tana jin wani bakon lamari na kusantarta, bata hana shi kissing din ba saboda ta san ba zata iya ba,

kuma bata son gantsara masa cizo kamar na jiya. Ya dade yana ta bautawa bakinta sannan ya cire bakinsa ta dan samu salama, tashi yai zaune ya cire rigar bachinsa sannan ya koma ya kwanta yana shafa ta tare da jan hannunta ya kai kirjinsa sai ta ji shi bab

u riga, da sauri ta janye hannun ta tashi zaune.

“Ni bana son haka?”

Hannunsa ya kai ya nuna bedside lamp ta yadda zai iya ganin fuskarta ita ta samu ganin ta shi. Hannunsa ya kai yana shafa gefen fuskarta sai wani lumshe ido yake.

“Minene”



Karatun da zan koya miki ne ai”

“Aa ni bana so”

“To zo ki kwanta”

“Zaka kara ai”

“Ba zan kara ba”

“Sai ka rantse”

Ya fara janta, kallonta yai ya ga a bakin gaskiyarta take nufi domin har gyara zama tai wanda hakan ke nuna ba zata kwanta b

a matukar be rantse ba.

“Wallahi, amman Baby ba a son yawan rantsuwa, ni kaina ba a saka ni rantsuwa kawai dai ina miki ne saboda ina kaunarki, ki daina haka”

Bata dai ce komai ba ta koma ta kwanta a jikinsa domin tana jindadi ta kwanta a kirjinsa.

“Ka min karatu?”

“Babba ko karami?”

Shiruu tai tana tunani Qira'a ita ce karama wacan shine babba, zuciyarta ta ayyan mata, sai ta ce.

“Karami”

Murmushi yai ya kai bakinsa saitin kunnenta ya soma karanta mata wani bangare daga Suratul Baqar

a, sai ya tabbatar bachi ya dauke ta sannan ya matsa kadan ya raba jikinsa da nata ya sauka saman gadon yana kallon fuskarta.

“Rigimammiya”

Ya fada yana murmushi ya dan kwanto saman gadon yai kissing dinta ya shafa fuskarta a hankali, sannan ya mike

tsaye ya fice daga dakin. Kasa ya sauko ya kunna tv ya kai volume din kasa gaba daya, sannan ya hada ma kansa tea ya zauna yana ta sauraren yadda jininsa yake gudana domin ya saka ma ransa zai yi kuma be samu damar hakan ba. Ya dade a zaune har kusan 1am

bachi be ziyarce ba, daman can idan irin haka ta taso masa cikin dare abu ne mai wahala ya iya yin bachi, 1:30am ya kashe kallon ya dawo dakinta ya shiga bathroom yai alwala ya fito ya saka jallabiya ya shimfida prayer mat ya fara nafila, sai kusan 3am ya

sake komawa saman gadon ya kwanta ya ja Fadime jikinsa yana ta kallon fuskarta.

“Na auri shagwababbiya kuma yar rigima dole na yi hakuri”

Ya fada murya can kasa yana sa dayan hannunsa ya ja hancinta.

“I love you”

Ya furta yana kissing din gos

hinta sannan ya rumgume ta tsantsan yana addu'ar nemo inda bachi yake.

Washe gari ma shi ya rigata tashi sai da yai alwala sannan ya tashe ta, sai ta soma wani lankwashe tana mike kamar ba zata iya tashi ba, daman ko a gida haka take wani lokacin ida

n Bappa ya tashe ta tai sallah, sai dai yana ganin ta fara haka sai ya tsaula mata carbi ko ya watsa mata ruwa dole ta farka da sauri, Inna ce mai hakurin tashinta har sai ta gama mikar ta tashi.

Shattima na ganin haka ya san bachin ne ya saukar mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login