Showing 213001 words to 216000 words out of 304903 words

Chapter 72 - FULANI COMPLETE

da ta tambaya.

“Minene?”



“Na miki alkawarin ba zan taba cilastaki ba, ba zan taba miki abun da rai ki baya so ba, idan har baki so na, ko baki bukatar zama tare da ni, ba zan taba cilastaki ba, zan baki d

amar duk da kike so, daman dai na yi hakan ne saboda na tsiratar da rayuwarki”

Ya karasa yana kallonta har lokacin tausayinta yake ji. Ita ma kallonsa irin kallo na ban yarda a farke nake ba. Can kuma ta kalli jikinta.

“Na kasa yarda komai gaskiya ne

, na kasa yarda cewa kai na aura, na kasa yarda cewar nan din gidan aurena na ne, har yanzu ina jin kamar mafarki na ke, na yi zaton tsohon zan aura da gaske, na yi zaton rayuwa zata zo mi a wahale ne”

Ta lumshe ido hawaye a sauko mata.

“Ban cancanci

zama matar babban mutum kamar kai ba, duk da na san ka yi ne saboda ka taimake ni...”

“Kin cancanci auren wanda ya fini ma Teema, kina tarbiya ga hakuri kowa wane namiji mai mutunci zai so yayi dace da ke a matsayin mata”

Ya kai hannu ya kama hannun

ta ya rike yana murza yatsunta a hankali.

“Kina da kananan shekaru amman kina da tunani da hakuri kamar babba, rayuwarki na burge ni, a yanzu ma kin yi zaton ni din tsoho ne amman a haka kika zabi zama da ni ki rumgumi kaddararki, hakan yasa na kara jin

kin kwanta min a rai fiye da da”

Ya saka dayan hannunsa yana share mata hawaye.

“Kuka ya kare, bana son kina saka kanki a damuwa yanzu”

Ta bude idon still tana hawaye, shi da kanshi ya tayar da ita tsaye sannan ya suka ya dauke ta cak.

“Ashe m

a amarya ta bata da nauyi”

Fashewa tai da kuka, har lokacin bata jin ta koma daidai ba. Sama ya haye da ita ta zaunar da ita akan katon gadonta ya sumbanci goshinta.

“Kina da alwala?”

“Aa”

Zai sake wata maganar wayarsa tai ringing, sai ya saka

hannunsa aljihu ya ciro wayar ganin number Hajiya yasa gabansa faduwa.

“Hello Hajiya?”

“Sirleem kana ina?”

Ya dan yi jimm yana tunanin ko an labartawa mata wani abun ne, duk da ya san be fadawa abokansa ba balle wani ya fada har Hajiya ta ji, sai

amininsa shi ma dan yana da tabbacin ba zai fada ba ne.

“Ina gidana, kaina ne yake dan ciwo a nan zan kwana”

Yana jin lokacin data sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa masa da.

“Allah ya kara sauki, for now on bana son kana kwana a waje, kasan na sa

ba fada maka wannan ba sau daya ba”

“Na sani Hajiya, amman ba abun da kike zargi ba ne”

Ya fada yana kashewa Falmata ido daya, Hajiya bata son yana kwana wajen masarautar ne saboda Mansura, a tunaninta idan ba ya kusa da ita to yana kusa da Mansura n

e, duk kuwa da sanin cewar ba a Yola take ba, sai dai ta san wani lokacin tana zuwa Yola gurinsa, saboda Hajiya ta hana shi yin komai a Kaduna yanzu ba dan komai ba sai dan ya daina haduwa da Mansura.

“Shiga ki yi alwala bari na dauko mana kazar mu”

Ya fada yana jefar da wayar kan gado.

“Sirleem”

Ta kira shi sai ya juyo ya kalleta fuskarsa na ta annuri.

“Hajiya Nana take son ka aura, kuma Mansura ma tana sonka, kuma yanzu ka aure ni”

“Yeah...”

Ya furta sai kuma yai shiru ya dawo kusa da

ita ya zauna.

“Maganar gaskiya, haduwar da nai da ke yasa na ji ba zan iya auren Mansura ba, saboda tana da bad habit, na yi iya abun da zan iya na raba da samari na kasa, na san tana so, amman tana mu'alama da wasu mazan, a iya tunanina idan na aureta

ba zata daina ba ni kuma ba zan samu aminci da ita ba, and every good man yana son ya samu mata mai tarbiya kuma yar gidan mutunci kamar ke...”

Ta yi masa da kanta.

“Nana fa?”

Ya tabe baki tare da daga kafadunsa.

“Na taba fada miki cewar hadin

Hajiya ne?”

Ta dago tare da daga masa kai.

“I don't think ina son Nana a raina, ina mata dai so ne irin na kanwa da yaya, amman bana soyayya ba, kawai dai na bi umarnin Hajiya ne, ita kanta Nana a yanzu idan aka tambaye ta za ta ce bata so na”

“A

mman idan Hajiya ta ji, Ammy da Shattima da Mansura da Nana zan shiga uku...”

Ya dora yatsansa a kan bakinta.

“Shiiii you talk to much, ki manta da kowa a yanzu, duk wata matsala da rigima ni ne zan shiga ba ke ba”

Ya mike tsaye.

“Bari na dauk

o abu downstairs”

Yana juyawa sai Falmata ta mike tsaye ta rumgume shi da baya.

“Wata kila idan na rumgume ka zan yardar kai ne, kuma zan yarda ba mafarki na ke ba”

Ta fada tana lumshe wasu hawayen da bata san na minene ba su ka sauko mata. Murmus

hi yai ya juyo ya rumgumeta.

“Kin cancanci fiye da haka Teema na”

Sakinsa tai tunawa da abun da tai da kanta na rumgumarsa abun da bata taba ba, murmushi yai ya fice daga dakin.

***

Hajiya ta sauke wayar tana kallon kular tuwon dake gabanta.

“Me yace?

Jurry ta tambaya.

“Baya jindadi a waje zai kwana”

“Okay”

Ta dauki plate din abincin da ta gama ci tare da mikewa tsaye har zata fice sai kuma ta juyo tana fadin.

“Yauwa Hajiya, na manta wai Kausar tace min lokacin da taje kai su

Hajiyar Zariya Gaisuwa a gurin Ammy ta ga wata yarinya makauniya tana fadar a boyeta kar Iya da Hajiya Babba su ganta, ina son na fada miki sai na manta”

Hajiya Babba ta juyo tana kallonta.

“Yaushe? Wacece?”

Wallahi ni ma ban sani ba, ranar da aka

kai su Hajiya dai su yi mata gaisuwa.

“Ko wannan yarinyar ce Falmata?”

“Ni ma haka nai tunani, amman kuma Kausar ai ta san Falmata”

“Kira min Kausar din”

Hajiya ta fada tana tashi zaune da sauri. Jurry ta amsa da to sannan ta fice rike da plat

e din. Bata dade ba ta sake dawowa dakin tare da Kausar tana dake ta danna waya suka zauna a kasa.

“Kausar”

“Na'am Hajiya”

Ya amsa mata idonta na kam waya.

“Kalle ni nan ki aje waya”

Kausar ta aje wayar tana kallon Jurry kamin ta kalli Hajiy

a a tunanin wani laifi tai.

“Wa kika gani a dakin Ammy?”

“When?”

Ta tambaya domin ita ta manta da zancen ma. Sai Jurry ta dafa kafadarta.

“Ranar da kika je kai su Hajiyar Zariya ba kin ce kin ga wata yarinya ba har tana fadar a boye ta kar Haji

ya ko Iya su ganta”

“Oh Eh me aka yi?”

“Kin san yarinyar ne? Ko Falmata ce?”

Hajiya ta tambaya.

“Aa ni ban taba ganinta ba, kuma ita fara ce sosai har ta fini haske Falmata kuma ai baka ce, kuma wannan bata gani har tana cewa wacece ni”

Haji

ya ta yi shiru tana nazari.

“Duk yadda akai yarinyar ta san ni, idan ba haka ba, me zai saka ta ambaci sunana? Ko kuma Ammy ce ta fada mata wani mummunan abu a kaina?”

“Maybe, to amman kuma ai har da Iya ta ambata. Hajiya kin san yadda za ayi? Bari n

a tashi na je na kaiwa Nana lace sai na dubata daga can”

Cewar Jurry tana kallon Hajiya. Sai Hajiya ta daga mata kai.

“Okay”

Jurry ta mike da sauri ta nufi wardrobe Hajiya ta bude ta dauko wani tsadadden lace sannan ta maida Wardrobe ta rufe ta nu

fi kofa.

Kamin ta isa bangaren Ammy har da hadawa da sauri kamar wanda aka cewa jeki gata a can ki gani, door bell din daya kamata ta danna sau daya ko sau biyu ta danna sau ba adadi kuma ta hada ta knocking. Cikin rashin sa'a Nana ta bude mata kofar, sai

tai tsaye kamar hoto tana kallon Nana, Nana na ganin hakan ta juya ta dawo cikin falon hannunta rike da apple daman can ba jituwa suke da Jurry ba, dama dama Kausar ko Karima amman Jurry bata shan inuwa daya da Nana. Shigowa tai cikin falon kamar yadda ta

saba ba tare da sallama ba, ta nufo kusa da inda Nana take zaune ta zauna tana ta rabon ido, babu kowa a falon sai Nana sai wata yar cousin din Ammy dake zaune dinning tana cin abinci. Tunani ne ya zo mata Rahila ce bakuwar da Kausar take fada ko kuma ita

ta zo tare da wata? Amman a iya tunaninta ai Kausar ta san Rahila, kuma ta ce wacan makauniya ce.

“Rahila yaushe kika zo?”

Cewar Jurry a kokarin ta na tantancewa, daga Nana har Rahila da aka kir juyowa suka yi suna kallonta, domin Nana ta san halint

a ganin mutum tai masa magana ba nata ba ne, sai idan kawayenta na na kusa ko kuma wasu na bangaren Hajiya, Jurry tana da wani irin hali na ji da kai ko ta sanka zata iya yin banza da kai ko kuwa ka mata magana ne.

“Yau Anty Jurry ina wuni?”

“Lafiya

Kalau ya gidan ke kadai kika zo?”

“Eh”

“Owk Ammy na ciki?”

Ta tambaya tana kallon Nana.

“No tana bangaren Mai Martaba”

Nana ta fada sannan ta mike tsaye ta nufi dinning din.

“Am Nana ga lace in ji Hajiya tace a baki”

“Ki aje nan na god

e”

Ta fada a cikin yanayin da bata saba ba, ada idan Hajiya tai mata kyauta da sauri take zuwa ta karba tana murna d tsalle.

“Kuma tace a kira ki wai kin daina zuwa bangarenta”

“Ki ce ina gaisheta, makaranta bata barina zama yanzu shiyasa”

Da m

ugun mamaki Jurry take kallon Nana, sai da ta isa dinning din ta zuba ma kanta abinci ta fara ci, sannan Jurry ta aje lace din ta fice.

49

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then se

nd the evidence via 08036126660*

Jirginsu na sauka direban Shattima na isowa, duk inda suka bi sai an kalli Shattima dake cikin shiga ta manyan kaya ga kuma Bappa da Kawu dan iroro dake biye da shi cikin shigarsu ta fulanin kauye, kana ganinsu ka ga f

ulanin ruga. Kawu dan iroro sai washe baki yake ganin a jirgi suka sauko abun da be taba tunanin zai faru, tun kam su karaso gurin motar Baba Adamu ya fito ya bude ma Shattima gidan baya a tunaninsa baya zai zauna kamar yadda ya saba. Sai ya ga sabanin hak

a ta hanyar nuna ma su Bappa mazaunin baya.

“Bismillah Bappa ku shiga mota”

Shi kuma ya bude front seat ya shiga ya zauna, Baba Adamu ya fisge motar kamar yadda ya san Shattima na son tuki. Bappa be tabbatar da Shattima babban mutum be ne kuma dan Ba

bba mutum har sai da suka shiga masarauta, a nan suka rika kallon kallo shi da Kawu. Shattima da kansa ya sa a kira masa sarkin gida, sai ga shi ya zo da gudu ya zube gaban Shattima yana kwasar gaisuwa.

“Allah ya taimake ka, Allah ya kara maka lafiya”

“Sarkin gida ba bakina nan a basu masauki mai kyau”

“An gama dan sarkin da yafi wani sarki, an gama babbar giwa, Allah ya kara maka lafiya rai ya dade yai karko”

Uffan Shattima be sake ce musu ba, ya wuce abunsa bangaren Ammy, Bappa da Kawu kuma s

uka bi bayan sarkin gida kowa ne fuskarsa dauke da mamaki.

Kamar wani bako haka Shattima ya shigo cikin falon Ammy ya zauna yana dagawa Jekadiya hannu alamar amsa gaisuwarta da tai masa. Sai da ya fara kallon tv kamin ya kalli dakin yaransa, a idan ya s

higo sai ya fara zuwa ya duba su wani lokacin ma sakawa yake a dauko masa su a gidansa dake wajen masarauta. Ba karamin sosuwa zuciyarsa tai ba tunawa da babu yaran a yanzu. Mikewa yai tsaye ya saka hannunsa daya a aljihu ya nufi dakin Nana, kamar yadda ya

zata haka ya tarar Fadime na dakin zaune kasa hannunta a plate tana cin tuwon alkama da miyar ganye, kana ganin yadda ta bata fuska kasan bata son cin abincin.

“Waye a nan?”

Ta tambaya kamar an mata dole tana turo baki gaba. Samun kansa yai da murmu

shi sai farinciki da annashuwa suka baibaye masa zuciya. Sakin kofar yai ya fara takawa zuwa inda take.

“Shattima”

Ta fada tana washe hakora, sai ya tsaya cak yana kallonta a tunaninsa ta ji saitin tafiyarsa ne.

“Ga kamshin turarenka nan Wallahi k

ai ne”

Ta fada da dariya. Hakan yasa shi dariya shi ma ya karasa kusa da ita ya zauna a kasa kamar ita.

“Me kike ci?”

“Yeeee na gane kai ne, ina Bappa?”

“Na saka a kai shi masauki ya huta a bashi abinci tukuna sai na sadaku”

“Aa dan Allah ka

kai ni yanzu, dan ina son na ga Bappana”

“Gani?”

“No ji ina son na taba shi na ji”

“Yanzu muka shigo ki bari na huta su ma su huta”

“Aa dan Allah”

Ta fada tana kokarin saka masa kuka. Sai ya kura mata ido, daman ya san za a rina, wai an sac

i zanen mahaukaciya. Kamin yace komai har ta mike tsaye tana mika masa hannunta.

“Wanke min hannuna”

Ya daga kansa yana kallonta da dan mamaki irin mamakin yadda take masa abubuwa, wata kila soboda idonta na rufe ne ko kuma saboda halinta ne oho.

“Wa yake wanke miki hannu idan kin ci abinci?”

“Ni nake wankewa”

“Then why yanzu kika ce na wanke miki?”

“Saboda ka zo mana, kasan ai ina jindadinka”

“Really?”

“Yes”

“To je ki wanke sai na saka a kaiki”

Ta fara takawa tana lalebe, gani

n hakan yasa shi mikewa tsaye ya kama hannun nata suka nufi toilet din Nana. Da kansa ya kunna fanfo ya tara hannunsa ya saka nashi hannun yana murza mata a hankali.

“Wannan gidan na ku mai kyau ne sosai ko? Fanfo har a bandaki mu a kauyenmu ba mu da f

anfo ma sai rijiya”

Be ce mata uffan ba, har ya gama wanke mata hannun, sai ta mika masa dayan.

“Wannan ma ya taba tuwon”

Ya rika hannun ya wanke mata yana mamakin kansa, ko kadan baya son yi mata musu, baya son tai requesting abu ya hanata, sann

an baya son ya ga ranta ya bace.

“Sarautar nan gidan Babba ce ko? Ko karama?”

Be dai ce mata komai ba, surutun da take ne yasa Nana ta bude kofar bandakin ta leko sai ta hango Yayanta rike da hannun Fadime yana goge mata da tawul. Tsaye tai tana kal

lonsa da mugun mamaki shi ma kallonta yake kamin ya kamo hannun Fadime su fito daga bandakin.

“Yaya...”

Nana ta fada tana masa kallon mamaki. Sai ya kalleta.

“Nana me kika gani?”

“No ban ga komai ba”

Ta amsa masa tana zaro ido, sai ya juya s

ai kuma ta sake kiransa.

“Ya na ga kana wankewa Fateema hannun”

Juyowa yai yana kallonta fuska ba yabo ba fallasa.

“Zan iya sirri da ke?”

“Ba zan fadawa kowa ba, i mean ban ga komai ba”

“Good”

Ya juya ya nufi kofa sai ta bishi da kallon m

amaki har ya fice hannun Fadime na cikin nasa. Sai da suka fito sannan ya saki hannunta.

“Bi yo ni”

Saurarawa tai ta fara bin inda take jin takunsa har suka iso cikin falon.

“Jekadiya ki kai yarinyar gurin mahaifinta, sarkin gida zai fada miki ind

a yake”

Yana fadar hakan ya mike zuwa dakin Ammy. Jekadiya ta mike tsaye da sauri bayan ta amsa ta kama hannun Fadime suka fice zuwa neman Sarkin gidan, sauko suka downstairs tana rike da hannun Fadime har suka fita gate din zuwa inda ta san Sarkin gida

n yana zama. Jurry na tsaye jikin motarta tana waya idonta sanye da bakin gilashi ta hango Jekafiya da Fadime sun wuce, da sauri ta sauke wayar ta cire gilashin idonta ta kwalawa Jekafiyar kira.

“Jekadiya”

Jekadiya ta juyo da sauri tana amsawa, juyow

ar da tai sai ta juyo tare da Fadime da take rike da hannunta, tun kam su karaso inda Jurry take hankalinta yai mugun tashin, ganin Fadime. Tana ganin fuskarta ta gane ta kuma ta tuna inda ta taba ganinta duk da kasancewar wacan mai gani ce wannan kuma mak

auniya.

“Ina Ina zaki je?”

Ta tambaya numfashinta na rawa.

“Ranki ya dade aike zan isar”

Fadime na jin ance ranki ya dade sai ta saka duka hannayenta ta kama hannun Jekadiya ta rike.

“Okay wacece wannan?”

“To nima dai bana ce ba, domin ko

sunanta ban rike ba”

“Ke ya sunanki?”

“Fateema”

Fadime ya fada, sai jurry ta gyada kai.

“Owk Fateema kawai”

“Eh”

“Okay ku tafi kawai”

“Godiya muke”

Jekafiya ta fada sannan ta ja hannun Fadime suka wuce, Jurry ta juya da sauri ta ko

ma cikin gidan tana gudu kamar zata fadi, kamin ta isa dakin Hajiya har hakki take idonta ya cika da hawaye saboda tashin hankali, da karfi ta tura kofar dakin ta shiga wanda ya saka Hajiya yi mata wani kallo na mamaki ganin ta yi abun da bata saba ba.

“Juwairiyya?”

“Hajiya na shiga uku na lalace, asirina da naki ya tonu, Hajiya na ga yarinyar nan da Kausar take fada, Hajiya ashe ita ce a gurin bokan nan, yarinyar da muka gani gurin bokan nan tana tare da wani saurayi da ba shi da riga a lokacin da mu

ka je, Hajiya ita ce Fadime da ake fada, yanzu na ganta tare da Jekadiya na tambaye ta tace sunanta Fateema, na shiga uku Hajiya na shiga uku...”

Ta fadi kasa tana buga hannayenta kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login