Showing 72001 words to 75000 words out of 304903 words

Chapter 25 - FULANI COMPLETE

daya, balle ay

i maganar mazaunai.

Wata uwar harara ta watsa masa, har ga Allah haushinshi take ji kuma da ace ba shi bane tabbas da mai raba su a yau sai Allah, amman tana tsoron tai masa wata rashin kunyar ko wani sherin yai mata wanda ya ci uban nata.

“Ina ta tu

naninki tun jiya”

Ya fada yana kokarin danne dariyarsa, domin babu abun da be sani ba na isa da tai da maciji a kanta. Ta masa banza tana son ta harare shi ba dama tun da tana tsoro. Ya mika mata guava hannunsa.

“Karbi ki ci”

Ta yatsina fuska alam

ar kyama, daman can bata jin ragin kowa ciki har da Babanta da Inna balle kuma shi. Dan karamin bakinta ta kurawa ido yana ta kallonsa sai ta soma jin halshenta na motsawa, ta kalle shi da sauri.

“Me ka min?”

Ba shiri ta rufe bakin jin muryata kamar

ta wani kwaro. Ta mike tsaye da sauri tana zaro ido.

“Wayyo Bapppa”

Kamar wani karamin kwaro na magana haka muryarta ta zama, zata ranta ana kare ya riko ta.

“Zaki min magana?”

Ta gyada kai da sauri hawaye na sauko mata, sai yai murmushi yana

kallon fuskarta yana jin kamar ya hade ta, duk wani motsi nata burgeshi yake. Bakinta ya sake kurawa ido sai ya halshenta ya sake motsawa bata bari ya kara ta sa hannu ta rufe baki tana fashewa da kuka, sai ya kara rike ta gam yana dariya domin fisge fisg

en take tana son ta subuce daga rikon da yai mata.

“Ki zauna idan ba haka ba, ba zan gyara miki halshen ba, kuma zaki tafi da shi gida a haka, zaki zauna”

Ta gyada kai da sauri, sai ya sake ta har lokacin dariya yake, ta zauna saman karamin dutsen s

ai ya mika mata guava daya bata dazun ta ki karba, kamin yace komai ta karba ta saka a baki ba ta ma wani tsaya taunawa da kyau ba ta hade.

“Na hade”

Sai ta ji muryar kamar duro, a take ta fashe da wani irin kuka, sai kuma tai saurin yin shiru ta ruf

e bakinta domin ita ma kanta tsoron muryar take, ji take kamar kukan da muryar ba a bakinta suke fitowa ba. Ta fara masa na kurame alamar roko tana nuna masa bakinta. Sai ta sake jin halshen ya motsa zata saka hannu ta rufe ya rike mata hannun. Wani uban i

hu tai shi kanshi sai da ya duke kanshi ya runtse ido saboda kyakyar muryarta har cikin kai take shiga.

Wani mamaki ne ya cika ta jin muryarta ta dawo daidai, sai tai dan murmushin tsoro tana kallonshi.

“Dan Allah da gaske kai ba aljani ba ne?”

Ya zauna kusa da ita yana ta kallonta.

“Ni mutum ne mana, bana fada miki muna tsafi ba”

“Na yarda...”

Ta fada cikin tsananin mamaki tana kallonsa.

“Miyasa kake kallo?”

“Burgeni kike”

Ya ansa mata still yana kallonta, sai ta nuna kanta.

“Kana so na kenan?”

Sai ya dauke kai yana murmushi, ita kuma ta ji kunya ta rufe ta, ai be kamata ta tambaya, idan yana sonta shi ya kamata ya fada, ba ita ba. Ta sinne kai kasa tana yan zanezane.

“Ba ni labari”

Ta dago kai amman sai ta kasa

kallonshi saboda kunyar maganar dazun.

“Ba ni da labari... ”

Ta yi shiru, shi dai sai kallonta yake can kuma tace.

“Kishiyar Innata tace ta min miji a birni, amman har yanzu be zo ba”

“Aure za a miki?”

Ta yi shiru ita dai kam tana son aure

a rayuwarta, da za a mata auren ma a take da ta huta. Ta kalleshi

“Zaka iya min tsafi na gan shi? Ko ka kira shi ya zo?”

Yayi murmushi yana kallon cikin idonta.

“Kina son ki san mijinki?”

Ta daga kai ta sauri.

“Eh”

Ya mika mata hannun

sa.

“Kawo hannunki”

Sai ta miko masa hannun, ya dora saman tafin hannunsa yana kallon idonta.

“Washhhh sanyi hannu sanyi sanyi”

Ta fada tana saurin janyewa.

“To duk namiji da ya taba hannunki kika sake jin irin wannan sanyin shine mijinki”

Da dan bude ido tana kallon hannun nata.

“Da gaske? To mu gaisa”

“Idan kika ji sanyi a hannunki fa?”

“Shikenan kai ne mijin”

“Idan kuma ba kiji ba fa?”

“Shikenan ba kai ba ne”

Ya mike tsaye yana murmushi ya ciro guava a yar karamar ja

kar da ke kugunsa, sai tai saurin kai hannu ta taba hannunshi, saurin fisgewa yai.

“Tafin hannunsa zaki taba ko ya taba naki, idan tafin hannunki da hannun wani namiji su kai taba juna kika ji sanyi to shine mijinki”

Yana fadar hakan ya fara tafiya y

ana cin guava.

“Ina zaka je?”

“Garin mu”

Tayi shiru tana kallonshi.

“Miyasa jiya nan kai min tsafin maciji a nan ba a gida ba?”

“Ba ke kike ce a miki ba”

“Amman ai ban ce a nan ba, a gida na ce”

“Ina son ki ba ni nishadi ne shiyasa”

Ya fada yana ta kallonta. Sai tai dariya.

“Har da karyar aljanu nai nace sunan aljanina Sama'ila, kuma sunan Bappa na ne”

Shi ma dariyar yai, ya sake kai guava bakinsa sannan ya mika mara ragowar. Sai ta girgiza kai alamar a'a tana kyankyami, be

ce mata komai ba yai murmushi ya juya ya cigaba da tafiyarsa har ya haye saman dutsen ya dago mata hannu ita ma ta daga masa, sannan ta sauke tana kallon hannun na shi.

“Yana zuwa zan taba h.... ”

Bata karasa ba ta ji muryarta ta zama kamar ta shanu

wa saboda kara da munin sauti, da sauri ta rufe bakin ta fara hawa saman dutsen tana nemansa amman ko alamar sa bata gani ba, ta sauko a firgice ta nufi gida bata ko bi ta kan shanun ba.

  Kamar wacce aka koro haka ta iss gida, Inna na zaune da Rammu Fadi

me ta shigo gida babu ko talkami.

“Ke lahiya Fulani abun ya tashi kuma?”

Har ta bude baki tai magana sai kuma ta rufe bakin ta fara mata na kurame, tana nuna mata bakin nata. Inna ta taso da sauri tana fadin.

“Bude na gani”

Ta hangame bakin t

ana hawaye kamar ba ita ba.

“Ke babu komi ciki Fulani ya kai ne wai?”

Bata son ta yi magana Inna ta ji murya, ita kanta tsoron muryar take dan ji take kamar ba a bakinta take fitowa ba. Babu juyin duniya da Inna ba tai ba amman Fadime ta ki magana s

ai dai tai nuna. Shanun ma Hajjo aka tura ta dawo da su gida, hankali Inna duk yabi ya tashi, a zatonta Fadime ta daina magana ne, gashi ita kadai cikin gidan dan Amo bata nan kuma bata son kiran makota kar Bappa ya dawo ya hau ta da masifa, tun da komai c

ewa yake sirrinsu ba sai wani ya ji ba.

Sai daf da magarina Bappa ya shigo gidan da yar tsarabarsa, daman a duk lokacin da yaje burni ya dawo sai ya musu tsaraba, Bappa irin mazajen nan ne da basa son shigowa gida hannu sake. Sai dai tashin hankalin da

ya tarar a gurin amaryarsa ya kawardar komai, domin kuka ya tarar tana yi kamar yadda Fadime ma take kuka. Bappa ya nufo Fadime cike da mamaki da kuma tsoro a lokaci daya.

“Fulani ba zaki iya magana ba?”

Kasa cewa komai Fadime tai sai hawaye take,

tsoro take kar tayi magana ta sake jin murya, ga kuma tsoron Bappa kar yace zai kira mai karatu ko ya daketa.

“Zan iya”

Ta fada da muryarta mai ban tsoro, gaba daya Bappa jin yai kamar muryar ta cika duniyar nan gaba daya, be san lokacin da ya jefar

da kayan hannunsa ba ya riko rigar Inna wacce ta kusa wuce da gudu ya dawo ta ita baya ya kara ma kafarsa giya.

FALMATA POV.

Tana zaune ya turo kofar dakin ya shigo hannunsa rike da takeaway da robar ruwa, mikewa tai tsaye da sauri tana kallon

sa, kallo daya yai mata ya dauke kai ya aje mata abincin ya fice. Bata bukatar ya fada ci zata yi a yadda take jin yunwa ko da guba aka saka a abincin zata iya cinsa. Naman kazar ta fara cinyewa rabon da ta ci nama har tun na sallah, shimkafar ma sai ta ji

kamar ta fi ko wace wane abinci dadi saboda bata cin abinci mai dadi a gida.

Ruwa kan kadan ta sha saboda ta riga ta cika cikinta da ruwan fonfon da ta sha na bandaki. A maimakon ta hau saman gadon ta kwanta sai ta kwanta a kasa, tana ta kallon pop bach

in yace mata ba dai shi ba, yadda ta ga rana haka ta ga dare, babu komai a cikin ranta tunanin kudin Tumba data taba idan ya maida ita gida yace guduwa tai ta san Baba zai iya saka wuka ya yanka ta ne, wasa wasa ta ji ana kiran sallah asuba, kamar yadda ta

i a jiya haka ta shiga bandakin tai alwala ta fito ta sake shimfida dankwalinta tai sallah. Tana cikin addu'a Sirleem ya turo kofar dakin ya shigo. Tea mai kauri ya aje mata da bread sai sake mikewa tsaye kamar dazun tana kallonsa.

“Dan Allah karka mai

da ni gida”

Uffan be ce mata ba, daman kuma be da niyar ce mata komai yana aje mata tea ya juya ya nufi kofa.

“Wallahi idan ka maiyar da ni Baba ya ji cewar na gudu sai ya yanka ni, kuma Umma sai ta kusa kashe ni saboda na taba mata kudi”

Daf da z

ai fice ta fadi haka, sai ya tsaya cak ya juyo ya kalleta, tausayinta ya kama shi how old she is da zata zabi guduwa da bar gidansu? Ko bata fada masa ba ya san ana azabtar da ita tun da har ta zabi barin garinsu da gidansu ta zo inda bata san kowa ba, amm

an rayuwarta yake ji kar ta aikata irin abun da Mansura ta aikata ya zame mata tabo, a kurciyarta zata iya lalata rayuwarta, amman idan tai hakuri da wahala zata ci riba kuma zata wuce kamar ba ayi ba.

Juyawa yai ya fice daga dakin, ita kuma ta zauna ta

fara kuka tana tunanin irin mugun dukan da Baba zai mata, bata tunanin zai barta ta rayu ma idan ko har ta rayu to sai dai ta zama musaka.

Misalin 6:30 ya sake turo kofar dakin, ya tsaya daga jikin kofar yana kallonta,  ya same ta a yadda ya fita ya bart

a, tana kuka kuma bata taba tea ba.

“Fito muje”

Mikewa tai tsaye ta nufi kofar hawaye na sauko mata kamar dan irin wannan ranar kawai ta tanade su. Bata ce me zata ce masa ba, tun da har ya kasa sauraranta ta san ba zai fahimce ta ba, a yanzu ba ta d

a wanda zata karantawa damuwata balle ya nade mata kuncinta. Ta yarda a gidansu bata da gata, a nan din ma bata da gata. Da kanshi ya bude mata gidan gaba ta shiga ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga mazauninsa ya ja motar.

Tun da ya fara tafiya

wata kalmar bata shiga tsakaninsu ba, daji take kallo tana share hawayenta lokaci zuwa lokaci, ta sadakar kuma ta yardar da kaddarar da ta rabo da gida, ta yarda wata kaddararce take bibiyarta a yanzu na fadawa wata damuwa. Tun yana tukin tana kallon titi

har bachi ya sallama mata ita kuma ta amsa masa cikin sauki, daman tun jiya basu hadu ba. Sai da ya tabbatar da bachin nata ya yi nisa sannan ya faka motarsa gefe ya fita ya zaya gefenta ya bude mata a hankali kwantar mata da kujerar ya rufe, kamin ya daw

o motar ya ciro wayarsa ya kira Mansura bugu daya ta dauka.

“Sirleem ina yarinyar nan ta kwana?”

“Tun jiya na saka ta a motar Yola”

“Ina ta kiranka baka dauka ba tun jiya, kuma ka san zan samu”

“Shiyasa na kira ki yanzu”

Ya fada yana kallon

Falmata ta cikin farin gilashin motarsa, bachinta take hankali kwance kamar wacce bata da damuwa. Ta saka hannu ta share hawayen idonta.

“Kana ina kai”

Ya daga kansa yana kallon katon dajin.

“Somewhere.... Anjima zan kira ki”

Be jira cewarta

ba ya yanke wayar ya maida aljihu ya zagaya ya shiga motar ta cigaba da tukinsa. After every deep breath sai ya kalli Falmata wacce ke ta ranko bachi har ya shiga garin Yola.

Kai tsaye ya nufi GRA, a gaban wani katon gate ya faka motarsa sannan ya fita y

a doshi gate din yai knocking, babu bata lokaci mai gadin ya leko.

“Ranka ya dade kai da kanka kake buga gate”

Sirleem ya dan yi murmushi.

“Allah yasa Momy dai tana ciki”

“Yanzu yanzu ko ta dawo”

Mai gadin ya fada yana matsa masa daga kofa

. Sai da ya danna key mota yai ta shiga lock sannan ya shiga cikin gidan. Kato gida mai yanayi da na turawa domin babu hayani sai kukan tsuntsaye dake saman itatuwan da suka zagaye harabar gidan su kai masa ado, ga wasu manyanna alfamar. Entrance din ya ha

u ya isa gaban kofar yai knocking.

Wata kyakyawar mata ce ta bude masa kofar fuskarta dauke da murmushi matar zata yi 40 to 42 years tana sanye da farar atamfa, sai farar t labcoat dake saman atamfar.

“Celebrities ganinku sai da ticket, sai kuma idan

kun so kawo ziyara”

Dan murmushi Sirleem yai ya naso kafarsa cikin falon mai cike da sanyi ac.

“Ba ma ziyara na kawo ba ni alfarma na zo nema”

“To yau kuma a gurina”

“Na san ke kadai zaki min ai”

Ya fada yana kokarin zaunawa.

“Yanzu ya

nzu na dawo daga aiki, lemme go and change”

Sai da ta aje masa lemu da ruwa sannan ta nufi upstairs ta shiga dakin farko. After like thirty minutes ta fito sanye da Hijab din dake nuna alamar sallah ta gama, sai da ta sauko kasa ta zauna sannan Sirleem

ya kalleta yace.

“Wata yarinya ce na hadu da ita a Kaduna, ban ji labarinta ba amman a yadda na fahimta tana shan wahala ne a gurin rikon nata ko gurin Babanta, saboda tace min mamanta ta rasu, kuma ta gudo ne daga gidansu zuwa Kaduna, bayan kuma bata

san kowa a can ba, so idan na kyale ta a can rayuwarta zata iya lalacewa shiyasa na zabi dawo da ita gida saboda yar nan Yola ce”

Iya nan ya tsaya yana sauke numfashi a hankali, tun kamin ya gama labarta mata abubuwan ta soma jin tausayinta.

“Allah

mai iko ina yarinyar take?”

“Muna tare a mota, ina son kije gidansu ne tare da ita, ki ce ke kika kadeta kuma hankalinta ya gushe sai yanzu ta farko ta fadi gidansu kika kawo ta, saboda ta nuna min idan ta koma gida Babanta ya ji cewar ta gudu zai yanka

ta, kuma ta taba kudin ko waye i don't know zan tambaye ta kudin sai na bata”

“Allah mai iko, wasu suna neman haihuwa wasu kuma suna wulakantawa”

Momy ta fada cikin rashin dadi rai, Sirleem yayi murmushi yana kallonta cike da tausayinta, kamin ya mik

e tsaye.

“Bari na shigo da ita”

“Okay”

Fita yai daga falon, ko da ya isa gurin motar ya tararda ta farka tana ta kalle kalle, unlock din motar yai sannan ya bude side dinta.

“Fito”

Ta fito kamar daman can umarnin take jira, be yarda ya shig

a cikin gidan ba sai da ya saka ta a gaba, ita dai tafiya kawai take ba dan tasan a ina take ba a Kaduna ko kuma a Yola? Ina zai kaita? Shine abun da take ta tambayar kanta, rage tafiya tai har sai da ya sha gabanta sannan ta bi bayansa suka shiga cikin fa

lon.

Wani irin kallo Momy take mata na tausayi, karamar yarinyar kamar wannan ace zata gudu ta bar gida? Ta jefa rayuwarta a hadari?

“Sannu zauna nan”

A maimakon Falmata ta zauna a kujerar da Momy ta nuna mata sai ta zauna kasa ta sinne kai gabant

a na faduwa, bata ji me tace mata ba amman ta san alama take mata da ta zauna.

“Ya sunanki?”

Momy ta tambaya, Falmata kan bata ma san tana yi ba dan kanta a kasa yake kuma ba ji take ba.

“Bata ji sosai sai kin daga muryar”

Sirleem ya amsa mata

, sai tausayinta ya kara kama Momy, ta dan daga muryarta ta sake tambayarta.

“Falmata”

Ta amsa ta ba tare da ta kalleta ba.

“Sannu Mamana”

Momy ta fada cike da tausayawa sannan ta mike tsaye ta nufi kitchen, cornflakes ta hada mata da madara

sannan ta dauko wani plate da zuba mata fruits ta dawo falon ta aje a gabanta.

“Yanzu na dawo aiki ban dora komai”

A nan ma Falmata bata jira tace mata dauki ki sha ba, dan yunwar da take ji ta musammance, sai ta dauki cup din ta cire cibin ta aje t

a kafa kai ta sanye shi dika, wani irin dadi ta ji har cikin kanta domin bata taba shan cornflakes ba. Tausayinta ne ya cika Momy har ta rasa me zata ce sai kallonta take kamin ta kalli Sirleem.

“Ka kaita ciki ta yi wanka ta huta”

“No Momy Hajiya na

jirana, na fi son a kaita gidansu sai tai can”

Ya kalli Falmata.

“Nawa ne kudin da kika taba?”

“Dubu biyar ne”

Ta amsa masa muryarta na rawa, sai yasa hannunsa aljihu ya ciro wallet dinsa ya kirga 5k ya mika mata,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login