Showing 216001 words to 219000 words out of 304903 words
wata mai aljannu.
“Shiyasa take cewa a boyeta karki ganta Hajiya
ta fada musu komai, ni ban ma gane kan wannan abun ba wayyo Allah na, na shiga uku idan Mai Martaba ya ji wannan abun tsine min zai yi, kuma masarautar ta karya da ni, garin Yola zai gagareni zama wayyon Allah na, ko mijin aure sai ya min tsaye Hajiya”
Hajiya ta kankance ido tana kallon Jurry, sai kokarin taro maganar take tana fassarawa da halshen da zata iya ganewa, domin yaren ya mata nauyi.
“Ban gane manufar wannan bokon ba, shiyasa be fada mana wacece Fadimen ba? Yarsa ce ko kuma me? And taya ta
zo gidan nan? Ko kuma bokan Hajiya ne muka je gurinsa ba mu sani ba?”
Jurry ta kara fashewa da kuka.
“Hajiya ba lokacin yin wannan tambayar ba ne, dan Allah ki tashi muje wani gurin tun abun be gama girma ba”
Hajiya ta mika hannu ta dauki wayarta
ta kira Hajiya Talatu, Hajiya Talatu na yin picking Hajiya Babba tace.
“Kina ina Hajiya Talatu?”
“Ina gida, lafiya dai?”
“Ba lafiya ba, asirinmu ya tonu, ki aika yanzu yanzu nan a dauko matar nan, gani nan zuwa”
“Innalillahi miya faru?”
“Ba
maganar waya ba ce, sai na zo”
Hajiya ta katse kiran sannan ta sauka kan doguwar kujerar da take ta nufi inda mayafanta suke ta dauka wanda yai kala da tufafinta ta yafa.
“Tashi share hawayenki, ki shiga mota zan yi magana da Mai Martaba yanzu sai m
u tafi gidan Hajiya Talatu”
Jurry ta zabura ta shiga bandakin Hajiya da gudunta ta wanke fuska ta fito tana gogewa da mayafinta ta fito falo a firgice, kana ganinta kasan bata cikin natsuwa jikinta sai rawa yake irin na barawo da mai kaya, tana isa guri
n motarta tai ta bude motar ta shiga tai ribas, kamin Hajiya ta nemi izinin Mai Martaba ta fito har Jurry ta fara jikewa da gumi duk da kasancewar ac motar a kunne yake.
Gidan baya Hajiya ta shiga fuska a daure tamau kamar wanda akai wa bushara da shiga
wuta, Jurry kam ido sai cika yake da kwalla, gaba daya ta bi ta rude, domin ta san wannan abun har ita zai taba. Kamar ta sato mutum haka ta rika gudu da motar tana sharar kwalla.
“Ki shiga natsuwarki mana, zaki tonawa kanki asiri”
“Asirina ya gama t
onuwa Hajiya, indai har ta fadawa kowa to ba abun da ya rage min, kowa zai rika kallona a matsayin yar da take son ta kashe mahaifinta, kuma ace ina budurwa yar sarauta har na san bin bokaye? Wallahi babu wanda zai aure ni Hajiya kuma Mai Martaba tsine min
zai yi”
Ta fashe da kuka tana duka sitiyarin motar da karfi, bata taba shiga tashin hankali irin na yau ba, duk wani abu da take tunani a da sai ya tarar na yanzu ya ci uban bata shiri ya zama har da tsonon asiri da bata suna da kuma lalata mata rayuwa
gaba daya. Ta yi horn ya kai sau biyar kamin mai gadin gidan Baba Waziri ya bude mata gate ta shiga, part din Hajiya Talatu ta faka motarta ta bude ta fita, ta bar Hajiya a ciki, iyakar kokarin da tai na boye fuskarta ne ta wuce dakin Hajiya Talatu ba tar
e da ta yi magana da yaran Hajiya Talatu da suke falon ba, cikin har da Haroon wanda dawowarsa kenan daga Abuja, kallo daya yai mata ya dauke kai ya maida gurin Hajiya Babba wanda ta shigo rike da waya tana dannawa.
“Hajiya barka da wuni”
“Ah Ah Haro
on sukar yaushe?”
“Ban dade ba, ya gida ya Mai Martaba da jiki”
“Jiki Alhamdulillahi”
Ta nufi dakin Hajiya talatu cikin taku na alfarma da kokarin danne damuwarta. Da waya makale a kunne ta shiga tana fadawa Kausar ta rufe mata dakinta ta manta ta
fito bata rufe dakin ba. Tun kamin ta zauna Hajiya Talatu ta saka salati tana dora hannu a kai saboda abun da Jurry ta fada mata
“Mun shiga ukun mu, Allah ni kaina idan Waziri ya ji wannan maganar aurena ya kare kenan, ba zai dubi yaya ko shekarun da a
kai a tare ba, akan Mai Martaba da Ammy baya jin asss bale kuma ya ji zance har da neman kisa? Gashi na je nemawa Mai jidda maganin hana auren? Wallahi kenan nan tawa ta karewa”
Hajiya ta tabe baki.
“Ta mu ta kare zaki ce, ni kina tunanin idan Mai Ma
rtaba ya sani zama zai yi da ni? Korani zai yi ya barwa Ammy gida ita kadai, daman abun da take nema kenan, sannan na shiga a bakin duniya...”
Kamin Hajiya ta karasa Jurry ta jarba tana kuka.
“Ni kuma ba zan samu mijin aure ba, kuma Mai Martaba tsine
min zai yi, na zama zakka a gidan nan”
Hajiya Babba ta kalli Hajiya Talatu zuciyata da mugun nauyi.
“Na fada miki ki aika a dauko matar nna yau yau ba sai gobe ba, ta zo nan ta yi mana duk abun da ya kamata, haka mu kai wasa a baya har Falmata da Sa
rdauna suna mana tsaye a wuya, domin su na su duk mai sauki ne ba kamar wannan ba”
Hajiya ta ce.
“Ai kina kirana na kira matar da ta san gurin na ce ta bar abun da take ta dauki shatar motar kasuwa taje ta dauko ta, domin idan na aika tare da direba
wani karin tonon asirin ne, amman gaskiya wannan bokan ya iya munafurci, ta ya zai mana haka? Daga neman taimako?”
Jurry dai sai kuka take Hajiya Babba kuma ta nutsa a duniyar tunani tana ganin abun kamar ba gaske ba.
FADIME POV.
Sai da suka wuc
e take tambayar Jekafiya.
“Wacece wanda ta tambaye ni?”
“Ba ki santa ba”
Jekakadiya ta amsa mata a takaice haka take mata a duk lokacin da ta tambaye ta, ba ma ita kadai ba har wasu da ba Ammy ko Shattima ba idan suka tambaye wani abun gudun laifi
ko ace ka yi sai ta ba shi takaitacciyar amsa, hakan da Jekadiya tai ba karamin kufula Fadime yai ba, daman ta lura a duk lokacin da ta tambaye ta wani abun sai ta amsa mata kamar bata son amsarwa ko kuma ta takaita, cikin bacin rai Fadime ta bi ta har su
ka isa inda Sarkin gida yake ta gabatar masa da sakon Shattima, sai ya zabura da sauri ya ya shiga gaba suna binsa a baya har suka isa gurin da ya sauke su Bappa, shi da kansa ya shiga karamin falon da sallama suka amsa masa, suna bata cikin hakkinsa. Fadi
me na jin muryar Bappa ta fara kokarin sakin Jekadiya tana kiransa.
“Bappa...”
Kamin ya fito har Jekadiya ta kama hannunta ta shiga da ita cikin falon, ganin Fadime yasa idon Bappa cika da kwalla ita kam tu ni nata hawayen suka fara zuba sai hannu t
ake mikawa ta taba shi.
“Bappa... Kai ne”
Ta fada cikin kuka da shauki, sai ya amsa mata da yaren fulantanci yana kama hannunta.
“Fulani...! Har nan kika kawo mu? Fulani baki jin magana dubi yadda kika koma?”
Sai ta fashe da kuka tana taba fusk
arsa.
“Dan Allah Bappa ka yafe min, na yi dana sani kuma ba zan sake ba, Bappa idona na ya rufe bana ganin komai tun ranar idon be bude ba har yanzu, Bappa ba dadi bana ganin kowa, sai dubu kullum komai zan yi sai dai na yi lalabe”
Ta kara fashewa da
kuka sosai, sai lalaben fuskar Bappa take, Jekadiya na ganin haka ta juya ta fice tare da Sarkin gida.
“Ai rashin jinki ne ya ja miki, daman wanda be ji bari ba zai ji hoho... Ko ina ke ce Fadime ke ko tsoro baki ji”
Cewar Kawu dan iroro cikin fada
yana tsude hannu, Fadime na jin haka ta kama Bappa ta rike tana kokarin rumgume shi.
“Bappa dan Allah karka min fada, ka ga bana gani yanzu, dan Allah kar ka ga laifina, zan fada maka gaskiyar komai da komai Wallahi na rantse”
A gurin da take tsaye t
a zauna ta fara labarta musu abubuwan da suka faru na gaskiyar inda ta san ta yi karya sai ta fashe da kuka tace Bappa ya yafe mata ita ma ba da son ranta tai ba, duk abun da ta fada kwatankwacin abun da Wasim ya fada musu ne, sai karin wasu abubuwan da Wa
sim be fada ba domin ita zai ta fede daga biri har wutsiya, sai da ta kai karshe sannan ta tsaya tambayar Bappa tambaya mai nauyi.
“Bappa zaka bar ni na auri Wasim?”
Kamin Bappa yace komai Kawu ya kwatseta ta hanyar daka mata tsawa yana zaginta da ha
nnu kamar tana ganinsa.
“Ke arrrr Fadime, kina abu kamar ba ki sha nonon Fulani ba, duk wannan abun da ya faru da ke be isa ya saka ki natsu ba, ki yi hankali? Ke wace irin yace? Rashin kunya kiri kiri har kina tambayar aure? To shi Wasim din musulmi ne
aka ce miki? Kuma mutumen da danginsa suka miki haka kina tunanin za su yarda ki aureshi ne? Tsafe ki za su yi ko ma su kashe ki gaba daya”
Ta dafa zuciyarta da karfi tana zare ido.
“Na shiga uku... Bappa ai zai iya musulunta kuma dan sarauta ne ba
ka ga yadda ke masa ba”
Ta fada da iyakar gaskiyarta, domin ta gani da idonta irin yadda ake bawa Wasim girma a garinsu saboda yana dan sarki abun da ya kara mata son sa kenan a ranta, tana jin ita idan ta aure shi haka za ayi mata. Bappa ya sauke ajiya
r zuciya yana kallon yarsa, gaba daya ya rasa a wane muhalli zai saka Fadime, tunaninta har yanzu be bata ta fara jin tsoron ta nisanta kanta da Wasim ba sai neman aurensa take, kuma kai tsaye take fada masa haka abun da ya tabawa al'adarsu ta fulani.
“
Fulani natsu ki saurareni, kin girma ya kamata ace kina da hankali da tunani kamar sa'o'inki, ke yanzu mutumen da zuwa garinsu kadai ya maida ke haka har zuciyarki take miki shaa'war aurensa? Ki fara bari ki ga idon idan ya bude tukuna kika sani ko a haka
zaki zauna har abada? Sanadinayar abun da kika aikata Allah kadai ya san halin da kika jefamu, Shatu har da ciwo tai ke kuma kin zama a haka ni da Kawu da ba mu taba mafarkin zuwa yola ba gamu a gidan babba sarki a yola saboda ke, to ya isa haka nan idan k
ina yin hankali da tunani ki fara tun yanzu idan kuma ba zaki yi ba, ni na san maganinki?”
“Menene maganina Bappa? Ai shi Wasim din ba zama zai yi a garinsu ba, zan fada masa ya dawo garin mu ya zauna tare da mu, Bappa dan Allah”
Bappa ta ji kamar ya
dauke ta da mari sai kuma wata zuciyar ta hana shi ganin halin makantar da take ciki.
SHATTIMA POV.
Yana tura kofar dakin Ammy suka yi ido biyu da Baba Waziri, wani irin abu Shattima ya ji kamar ya fasa ihu ko kuma ya juya ya koma amman ba hali, y
anayin yadda ya ga Ammy na murmushi ya san ba zai wuce zancen aurensu da Maijidda ba.
“Waziri samun dan'uwa irinka abu ne mai wahala a wannan zamani, kwata kwata kai ta kanka kake ji ba ta dan'uwanka”
Cewar Ammy tana kallonsa da murmushin irin yadda
yake nunawa mai martaba da yayansa kulawa abun har mamaki yake bawa Ammy. Baba Waziri yayi murmushi.
“Ammy kenan, irin mu suna nan da yawa, ai ko'ina akwai mutanen kwarai, kuma rayuwar duniyar nan idan ba ka yi dan Allah da zumunta ba dan me zaka yi? Mu
na yi saboda yaranmu su ma su gani su koya daga garemu, a can ba mu san kanmu ko yayan mu sai yayan yan'uwa su ne namu na mu kuma su ne na su”
“Allah ya saka da alheri ya kara hada kanku kuma ya hada kan zuri'ar gaba daya”
Sai da Baba Waziri ya gama
magana da Ammy sannan Shattima ya mika masa gaisuwa yana kallon Ammy domin ta hanyarta yake gane labari mai dadi ko akasin haka, tsoronsa daya kar ace zancen aurensa ne Baba Waziri ke yi, tun da ya sanar masa tun a waya cewar ya fara shiri, Baba Waziri ya
duba Shattima duba bana wasa ba, irin duban nan na babba da yaro ya soma magana cikin dattijantaka.
“Shattima ka yi hakuri, ban nemi shawararka ko izininka ba na tsayarda rana karshen watan nan, na san idan na tsaya neman shawararka zaka fara kawo wasu
kabli da ba'adi ne, kuma ina jin na isa da kai shiyasa nai haka”
Shattima yayi shiru be ce komai ba, sai dai har ga Allah be son wannan hadin da Baba Waziri yai tsakaninsa da Maijidda, ya san tana tsoron ta aureshi ta mutu kamar sauran matan, kuma ko d
a babu mutuwa ba lallai ne a samu kwanaciyar hankali a tsakaninsu ba, domin shi be taba kawo ta a ransa ba, ita ma kuma bata taba kawo shi a ranta ba, ko da ma ace sun taba irin yadda Hajiya Talatu taka kin Ammy abu ne mai wahala ta bar su su yi zaman lafi
ya balle kuma ga wannan jarabawar da take tare da shi.
“Ba ka ce komai ba”
Baba Waziri ya fada jin yayi shiru ya kasa furta komai, ga fuskarsa bata nuna jindadi ko akasin haka ba. Shattima ya dago ya kalli Ammy sannan ya kalli Baba Waziri ya ce.
“
Baba ita Maijidda ta amince? Idan har bata amince ba dan Allah kar ayi mata dole, ni akwai wanda zan iya nema a hadamu...”
Ammy ta watsa masa wani kallo mai kama da harara, Baba Waziri ma kallonsa yake.
ZAINAB POV.
Cikin abun da be fi kwana b
iyu ba, ta rame ta koma kamar marar lafiya, ko da yake za a iya kiranta da marar lafiyar amman ta zuci ba na jiki ba, damuwar da take ciki ya mata yawa, idan ta fara tunani sai ta rasa ta ina zata tonke. Ta ya zata tuna cewar mahaifiyarta ce ta kashe mijin
da zata aura ta ji sanyi? Ta ya tunaninta zai tsaya akan abun da mahaifiyarta ta aikata na kashe mutanen da basu mata komai ba face kyautawa hankalinta ya kwanta? Ta ya zata tuna yadda rayuwa ta zo mata a birkice a haife ta bata hanyar sunna ba kuma ta ji
dadi? Anya farinciki zai sake kusantarta? Sai a yanzu ta gane darin dukiya da kyau ko isa ba shine farinciki ba, kuma a yanzu ta yarda ba komai kudi suke iya siya ba, domin da ace kudi suna siyen komai da ta siye wata uwar ta canja iya, da ta siye wani uba
n ta canja wacan da yai cikinta a tasha wanda ko sunansa ba ta sani ba.
Barin jikin window tai ta saka hannunta ta share hawayen da suka zubo mata, sannan ta nufi kofar dakinta ta bude ta fita, a falo ta samu Iya tsaye tana gyaran zane da alama fita z
ata yi domin har ta sanya hijabi.
“Ina zaki je?”
Zainab ta tambaya daga jikin kofar dakinta da take tsaye, sai Iya ta dago ta kalleta.
“Unguwa”
“Unguwa gurin me? Shekaranjiya kin fita jiya ma kin fita kullum sai kin fita, amman wannan fitar da
alama mai muhimmanci ce shiyasa kika saka sabon kaya”
Iya ta daura zanenta tana kallon Zainab da mamaki.
“A da can baki min irin wannan sa'idon, ke da na haifa kike da damar fita ki yi yadda kike so balle kuma na haife ki? Ni ce uwarki fa karki manta
”
“Na san ke ce uwata ai, na san ke kika haife ni haihuwar da bata min rana ba, enough is enough Iya! Ki bar Ammy da iyalanta su huta, ki bar Shattima yayi rayuwa kamar kowa, mutanen nan ba su miki komai ba sai karamci da kyautatawa, idan ma tsoron kik
e asirinki ya tonu miyasa kika aikata tun farko? Wallahi idan baki kyale su ba Iya sai na aikata abun da baki taba tunani ba”
Ta karasa cikin kuka mai karfi hawaye na sauko kamar dan ta kadai akai yi su, juyawa tai da sauri ta koma dakinta tana kukan da
ita kanta ba zata iya fadar na wanene a cikin danuwarta ba, kamin ta karaso gurin gadonta ta hango Wasim tafe sanye da kananan kaya kamar wacan karon, banbancin wacan dress din da wannan wacan black ne wannan kuma red T-shirt da blue jean sai hular sanyi
da ya rufe fuskarsa da ita ma red ce.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi
da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna h
adin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari
, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
50
*
Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300