Showing 171001 words to 174000 words out of 304903 words
Baba zai mata idan ya dawo da zancen auren da tai a yanzu sai ta rasa wanne ya
fi tayar mata da hankali.
“Umma dan Allah dan Annabi ki yi hakuri, Wallahi ba sata nai ba, kuma kudinki idan wata yai za a baki na rantse da Allah”
“Uban waye zai bani kudin? Ni zaki maida shashasha, uwarki ma a tafin hannuna take balle ke da aka hai
fo a gaban idona”
Ajewar Tumba sai tai daidai da shigowar Baba dake rike da fitila kasancewar unguwar ba wuta sai dan buhunsa daya saba zuwa da shi kasuwa, Falmata na ganinshi ta tashi da sauri ta nufi gurin da ake wanke wanke tana kuka, Tumba ma ta sa
ka nata kukan na munafurcin, daman tun da ta samu labarin take jin kamar tai kukan sanin cewar albashin ba zai samu ba.
ZAINAB POV.
Baya baya take tana kallon Wasim kamin ta juya da gudu ta shiga kofar falon, shi kuma ya cigaba da takowa yana nuf
o inda take ko kula Mai Gadin be yi ba dake masa magana yana fadin.
“Malam dakata a nan mana, lafiya dai?”
Shi kanshi mai gadi ya tsorata ganin matar gidan ma ta tsorata balle shi da yake tsoho, kuma be san abun da ya hada su ba, hakan yasa be yi gan
gancin taba shi ba, sai dai ya dage yana ta masa magana Wasim kam ko kallon inda yake be yi ba.
“A ina muke Wasim? Miyasa ake cewa ka dakata?”
Fadime ta tambaya tana lalabensa da dayan hannunta, jin kamar suna a wani gurin sabanin inda ya fada mata z
ai kaita. Ita dai tasan yace zai kaita gurinsu Inna sai kuma ya fito da ita harabar asibitin ya fita gate da ita suka hau napep yana fada mata wai Inna sun tafi wata asibiti, by pass ta ji yacewa mai napep din bayan an sauke su, mai Napep din ya wuce sai k
uma ta ji ya rike ta kamar suna tafiya a iska, kamin ta ji sun sauka ya kwankwasa gate din da suka shigo yanzu, ga kuma hayaniya ta biyo baya gashi sai tafiya suke.
“A Ina muke Wasim?”
Ta fisge hannunta daga rikon da yai mata ta tsaya cak kamar tana
ganinsa. Matsawa yai kusa da ita ya soma mata magana a hankali kamar mai rada.
“Wani guri inda zaki zauna kamin ki samu lafiya”
“Ban gane ba”
“Ciwonki bana asibiti ba ne, idan likitoci suka taba miki ido zai lalace ne kawai, kin samu makanta ne sa
boda na fitar da ke ba tare da izinin Babana ba, ba zai yiyu na maida ke garin ba, ba kuma zan iya barinki a gurin iyayenki a saboda kar su ja miki wani ciwon”
Nana da sai kuka da hawaye kamar ba ita ba.
“To a ina ka kawo ni?”
“Wani guri”
Ya fa
da sannan ya rika wuyan hannunta ya janyo yana forcing dinta tana takawa ba dan ranta na so ba, sai kuka take tana nadamar abun da ta aikata. Kamin ya karasa Iya ta fito rike da wuka, tana tambayar lafiya ganin Zainab ta shiga falon da gudu ta boya a daki
nta. Iya na ganin Wasim ta saki wukar hannunta fadi kasa, ta hade yawu da karfi cikinta yai wani irin hargagi da haniniya kamar fitinannen doki.
“Wasim...”
Iya ta furta tana ja da baya, nunfashinta har wani gargada yake.
“Wasim...”
Ta sake fur
tawa tana shiga falon da baya baya, Wasim kuma be fasa doso inda take ba, har ya shiga cikin falon ita kuma ta tsaya daga can karshen falon tana kallon.
“Ga ajiya na kawo miki”
Ya furta yana zaunar da Fadime kan kujera, jin muryarsa yasa Zainab ta b
ude kofar ta leko.
“Idan kin ga dama ki cinye, idan kin ga dama ki aje ta har sai na zo dauka, ki zo ta fiye da yadda kike so”
Fadimen na jin haka ta zabura ta mike tsaye.
“Ta cinye kuma na boni mayya ce kenan? Ni dai na boni na lalace, dan Allah
ka maida ni gida dan Allah innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Allah ka kawo min dauki wayyo Inna, wayyo Bappa kuna ina?”
Ta fara lalaben hanya tana ta kuka, sai ya rike ta ya motsa da ita kusa da shi.
“Ba zan yi komai dan na cutar da ke ba, ban bar m
aihaifina ya taba ki ba, ba zan bar kowa ya tabaki ba”
“Ka kawo ni gurin Mayyan mayya fa mayya kace wai ba za a taba ni ba, nama har gida”
Ta fada cikin kuka, tana kara rike shi da dukan karfinta. Fitowa Zainab tai gana daya a take da manta tsoron zu
wan Wasim da kuma mamakin yadda aka ya gane inda take, a da tana tunanin gurinta ya zo, sai dai kalaman da suke fita daga bakinsa yasa ta shiga rudani, Iya kawai take kallon.
“Hakan na nufi akwai wata alaka a tsakaninku kenan? Kuma hakan yana nufin kun
san juna, akwai abun da kike boye min, kuma akwai abun da kike aikatawa Iya...”
Iya ta kasa cewa komai idonta ya kade yayi ja sosai, gaba daya hankinta ya gama tashi ganin Wasim, ganin take kamar ba gaske ba ne, komai ya zo mata kamar a mafarki.
Fadime
kam ta kama Wasim ta rike gam ko motsin kirki ba shi da damar yi.
“Dan Allah karka bar ni nan, ba zan iya zama gurin mayya ba, wacece ita?”
“Ita din uwata ce, ki sake jikin dole a nan zaki zauna”
Ya kai bakinsa saitin kunnenta yana kallon Iya.
“Aa ni ba zan zauna ba, Wayyo Allah na, na boni na kusa mutuwa dan Allah karka bar ni nan”
Cewar Fadime tana kara fashewa da kuka, Zainab ma hawaye take tana kallon Wasim kamin ta kalli mahaifiyarta, dake kara shigewa jikin ginin falon tana jin kamar
ta bace bat.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, m
aganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman
turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bay
ani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
Ban taba sanin akwai masu kara
tu kara zube ba sai a jiya. Wasu suna karantu ne kawai amman ba su da tunani irin na mutane masu natsuwa da hankali. Zuciyarku bata raya muku sai dai na yi bincike sannan na fara rubuta littafin nan ba? Tunani be zo muku cewar idan sana'ar su Amo da Iya ce
sana'a mi zai saka na bayyana? Na tona asiri?
Na zabi na dauki jigon maita nai rubutu a kai ne saboda 55% din ciwon da yake damun mutane a yanzu mayu ne, kamar yadda na zabi Jigo a Gobena kan kalubalen da matan aure suke samu a gidan miji, da Zagon Kasa
kan matan da suke dadewa ba su yi aure ba, da kuma irin kalubalen da suke samu bayan auren, da irin mazan da suke auren yarinyar saboda dukiyar gidansu, sai Zaki kan matsalar cire wani sashe na jikin dan'adam ba tare da sanin mai shi ba, da sauransu. Sabo
da na zabi fallasa sirrin maita da yadda suke gudanar da abubuwansu da cutar da suke, sai a kira ni mayya? Hmmm abun dariya, abun da baku sani ba Wallahi ko 20% na sherin mayu ban fada ba, suna nan da yawa ga wandanda suke bincike sun san haka, ban fara ru
butun nan ba sai da nai bincike. Ban sani ba ko son rai ne ya raya muku jifata da wadannan mugayen kalaman ko kuwa hassada ce saboda na fallasa sirrin maita? Ko kuma tsantsar jahilci da rashin iya magana? Ko ma dai minene ni dai na bar mutum da Sarkin da b
aya bachi baya angaje, Allah kenan ina rokonsa ya saka min tun a duniya kuma yai mana shari'a da ku a ranar da gaskiya bata boyuwa.
Special thanks to my lovely fans, i sincerely thank you, friends and loved ones, for ur support and encouragement. Love y
ou to moon and back
💝
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
40
FADIME POV.
Wasim ya kai kunnensa saitin bakinsa a karo na biyu ya
rada mata.
“Idan na baki magani kin sha zaki yarda ki zauna?”
Ya fadi hakan ne kawai dan ya kwantar mata da hankali ba dan yana da maganin da zai bata ba, shi kanshi ba da shiri ya zo ba. Sai ta girgiza kai da sauri.
“Aa ni ban yarda ba”
“Idan
kina can zasu taba miki ido ne, kuma da zarar hakam ya faru kin rasa idon gaba daya kenan shiyasa na kawo ki nan”
“Zan fada musu kar su taba idon, yanzu kam Wallahi gaskiya zan fadawa Bappa ba zan sake boye komai ba”
Rasa yai yadda zai yi da ita, ba
zai maida ita a can ba, domin ya san sai iyayenta sun taba idon nata, duk da ya san abu ne mai wahala ta yarda ta zauna a nan ko da tana gani balle bata gani.
“Iya ki ce min wani abu mana”
Maganar da Zainab tai yasa ta Fadime ta kara kame Wasim ta r
ike kamar ta shige cikinsa ta kara fashewa da kuka.
“Kana jin mayun biyu ne, Wallahi raba za su yi”
Kallonta Zainab tai cike da takaici kamin ta dauke kai ta nufi kofar fita daga falon ta fice gaba daya. Sai da ta fita sannan Iya ta kalli Wasim cikin
tsoron mutuwarta ta ce.
“An min sako ne?”
“Ba a miki sako ba, zuwan kaina ne amman duk ranar da akai miki sako, kin sani na mutuwarki ne Iya, kuma be zama lallai ki san hanyar da sakon zai rikeki ba, ban san miyasa kika zabi zama dabam da mutane ba,
kin ki ki amayar da kankarar maitar dake cikinki, kina ta bibiyar halittarki kina ci”
“Ban ci kowa ba, face na kusa da ni, iyalin wani mutum na ke bibiya, na cinye mata yanzu kuma na cinye yaya, maitar da nake ta cikar buri ce Wasim ba ta cinye duk wan
da be ji be gani ba, kowa yana da dalilinsa na yin maita, wani saboda ya samu amfanin gona, wani saboda yai arziki, wata saboda kishiya ko makiya, har yanzu mutanen da nake ci wadanda suke shan gabana ne suna kokarin tare min cikar buri”
Ta fada jikinta
na rawa, Uffan Wasim be sake ce mata ba, ya zauna a kujerar dake kusa da shi Fadime na rike da shi.
“Kai ka makantar da ni?”
“Me zai saka nai miki haka? Baki yarda ba zan iya bari a cutar da ke ba?”
“Zaka iya Wallahi tun har ka sace ni ka kawo ni
gurin mayya”
“Bana da gurin aje ki ne sai nan, idan na koma dake garin mu wata karim fitinar ce, daman na fada miki matukar na fitar da ke b tare da izinin Babana ba wani abu zai iya samunki, amman kika dage akam sai na fito da ke, kin ga abun da hakan
ya haifar saboda kin dage, a yanzu ma idan kika dage zaki rasa idonki har a bada, idan na fada miki abu ki rika yarda da shi, ki saka a ranki Wasim yana kaunarki, ba zai bari wani abu ya taba ki ba, ba zai taba cutar dake ba”
Ya fada hannayensa duka bi
yu shimfide a fuskarsa, yana mata maganar cikin kyakkyawan lafazi da kwantar da hankali.
“Daga danginki ma ban bari an taba ki ba balle daga ni? Ki yarda da ni Fateme Wasim ba zai taba cutar da ke ba”
Hawaye ya sauko a blind eyes dinta.
“Amman Inn
a da Bappa za su yi ta nemana, kuma ba zan samu natsuwa a gidan mayu ba, miyasa zaka tafi to? Ka tsaya a nan mana”
“Zan tafi na nemi gafarar mahaifina ne, ba zuwa zan yi dan na zauna ba, ina son ki dawo kamar da”
Ta sassauta rikon da tai masa tana ku
ka.
“Yaushe zaka dawo anjima ko gobe?”
“Anjima ina dawowa zan dauke ki na maida ke gidan iyayenki”
“Idan zan yi fitsari waye zai kai ni?”
Wasim ya kalli Iya
“Ita”
Iya ta girgiza kai da sauri tana matsewa jikin ginin. Fadime ta fashe da wa
ni irin kuka.
“Idan ka dawo ka ga na mutu, kace Bappa da Inna su yafe min, kuma ka fada musu gaskiyar abun da nai”
“Zan dawo na same ki lafiya, duk wanda ya ci ki, ya ci mutuwa”
Ya sumbanci goshinta.
“Bude baki”
Ta bude sai ya saka yatsunsa
biyu ya cikin bakinta a saman halshenta ta lakato yawun saman halshen ya bude nasa bakin ya shafa a halshensa. Sannan ya mike tsaye a hankali ta yadda ba zata iya jin motsinsa ba ya fara takawa da baya baya tana kallonta har ya fice daga dakin.
A haraba
r gidan ya samu Zainab tsaye tana kallon gate kamar mai jiran shigowar wani, hawaye sai sauko mata suke. Zuwa yai daidai ita ya tsaya sai ta juyo ta kalleshi, for the first sai ta ji bata jin tsoronsa sai ma kwarjinsa da ya cika mata ido.
“Ya akai ka ga
ne gidan nan?”
“Ta hanyar zaren da na daura miki a hannu”
Ta dago hannunta ta kalli zaren.
“Kana da alaka da ni kenan, shiyasa ka gane cewar ni jinin Iya ce”
“Na gane ke jinin iya ce saboda na gaisa da ke, ba dan na san asalin cewar ke jinin ba
ce”
“Sai yanzu na gano dalilin daya sa kace na ci naman nan, kuma na ci be mun komai ba, amman baka fada min ka santa ba”
“Ta taba baki labarina? Ko ta taba baki labarin tahirinta a can?”
Ta girgiza kai alamar a'a.
“Bata fada min gaskiya ba, k
uma ban san dalilinta na yin haka ba, tunanina yana tafiya ne akan abun da ta shimfida min a kwakwalwa, shiyasa ban damu na zafafa bincike ba...”
Ta ja wani dogon numfashi ta sauke, ta kalleshi.
“Amman da gaske tana maita?”
Ta tambaya cike da farg
aba da kuma tsoron irin amsar da zata fito daga bakin Wasim. Shi ma kallonta yake na yan dakiku kamin ya daga mata kai.
“Abun da ya rabota da garin kenan, saboda mu bama maita kuma ba mu yarda mu zauna da maye ba, ko da jininmu ne”
Da sauri ta daga k
anta sama sai kuma ta sauke kasa tana hawaye, ji tai ina ma ace bata tambaya ba, wani irin kuka ne ya zo mata sai tai saurin rufe bakinta. Wasim ya cire hular kansa ya kai hannu ya janyo Zainab sai ta dora kanta akan kafadarsa ta fara rara kukanta a hankal
i, Fadime ma tana can cikin falon tana yin nata. Sai da Zainab tai kuka sosai sannan ta daga kanta daga kafadarsa.
“Im sorry”
Ta fada still crying idonta har ya fara ja, be ce mata komai ba yana ta kallon kyakkyawar fuskarta, har sai da ta sake kall
onta.
“Ki kula min da Fateme saboda ke ta shiga wannan halin”
Juyawa tai ta kalli kofar falon da take jiyo kukan na Fadime, juyowa tai da zimmar yi masa magana sai ta ga babu kowa a gurin. Da sauri taja baya gabanta yai mugun faduwa.
HAJIYA BABB
A POV.
A lokacin data fadi ba Suma tai ba, faduwa tai a kasa saboda jikinta ya kasa daukarta zuciyarta kuma ta buga irin bugun da ba a son zuciya tana yi. Da sauri aka dauke ta aka dora akan gado aka nufi ICU da ita, ba karamin kokarin likitocin su kai
ba kamin su samu taimaka mata komai ya dawo normal, sai da suka mata allura mai karfi sannan ta samu tai bachi.
Wata yar kawunta aka bari tana jinyarta, su kuma yaran yayarta suka dauki gawar Hajiya Hansai suka tafi da ita gida, sai da suka isa sannan s
uka samu labarin rasuwar Talba, a lokacin ne suka gane dalilin faduwar Hajiya, a take aka tashi wasu family zuwa Yola domin yin jana'iza.
Haka Hajiya ta kwana ta wuni bata san inda kanta yake ba sai washe gari, shi ma ta farfadi ne kawai ba dan tana jin
wani kuzari ko lafiya a jikin ba.
Bata komai sai kallon mutane da kuma bin dakin da kallo, idan ta fara tunanin abun da ya faru sai ta ji tunanin ya mata nauyi kamar zata soma, sai da suka bata magani suka mata allurar sannan ta samu sa'ida sai dai duk da
haka bata iya kuka ko yin magana idan tana bukatar wani abu sai dai ta nuna da hannunta, ba dan ta kurmance ba sai dan magana tana mata nauyi a baki yanzu, bata aikin komai sai sauke numfashi da karfi kamar wata mai tsoho ciki. The following day suka sall
ameta, sai ta koma gidan Hajiya Hansai cikin yayanta ana ta mata gaisuwa, abun sai ya zame mata biyu ta rasa da wanne zata ji mutuwar yayarta wacce ita kadai ta rage mata ko kuwa na danta namiji