Showing 162001 words to 165000 words out of 304903 words
a hannu yana tafiya k
amar baya son taka kasa, da sauri Inna ta mike tsaye ta tare shi.
“Malam dan Allah ko kai ne likitan ka taimaka mana?”
Kallonta yai na yan dakiko kamin ya kalli Bappa da shi ma ya mike tsaye, daga kam Bappa idonsa ya sauka akan fuskar Fadime da fusk
arta ta jike shakaf da hawaye. Be ji kamar ya san ta ba, ko ya taba ganinta ba kai tsaye zuciyarsa ta raya masa ita ce yarinyar da Ra'ees yaje nema masa, kuma ita ce yarinyar da ya kade a mota.
“Me ya faru?”
Ya tambaya yana kallon Fadime, yadda take
kallon direction dinsa sai ka rantse da Allah tana ganinsa, shi kanshi abun da ya zata kenan sai dai ya san kukan da take ba zai saka tai saurin ganeshi ba.
“Wannan yarinyar muka kawo asibiti, a duba idanuwanta”
Cewar Bappa yana matsowa da Fadime,
haka yake kiranta yarinya ko kuma yace Fulani be taba nuna yarsa ba ce, kara ma Inna ta kan nuna wani lokacin, sai a lokacin Shattima ya gane cewar bata gani, domin kallon da take mishi ba irin na normal mutane ba.
“Miya samu idon?”
“Wallahi ba mu s
ani ba, dazu da safe abun ya same ta”
Bappa ya fada yana kokarin tare Inna dake son dauko dogon labari. Hannunsa ya kai yana yawo da shi a fuskarta sai ya g bata motsa idon ba alamar bata gani kenan.
“Ku biyo ni”
Da sauri suka bi bayansa Fadime n
a rike da hannun Inna, yana gaba suna biye har y shiga office dinsa dake cike da sanyin ac da kuma kamshin tsadaden turarensa, sai da ya zauna sannan yai musu izinin zama, Bappa ya zauna daga can gurin kofa Inna da Fadime kuma suka zauna a kujerun dake gab
an teburin.
“Miya samu idon na ki?”
Inna zata yi magana ya daga mata hannu yana kallon Fadime.
“Komai be samu idona ba, haka kawai idona ya rufe ina cikin rubutu sai na ga duhu”
“Kin shafa wani a idon ne?”
“Aa”
“Wani abu ya fada miki a
idon ne?”
“Aa”
“Daman can idon yana miki ciwo ne?”
“Aa”
“Kina jin ciwo ko kaikayi a idon ne?”
“Aa bana jin komai”
“Me kike lokacin da abun ya same ki?”
“Rubutu”
“Wane irin rubutu?”
Ta ciro littafin daga cikin hijabinta ta mika ma
sa, sai ya kai hannu ya karba still yana kallonta.
“Ya kai awa nawa yanzu da abun ya same ki?”
“Yau da safe ne, ni ban san ko awa nawa ba ne”
Ya ya buda littafin ya fara dubawa rubutun hausa ne, sai dai tana good handwriting, kana ganin kasan tar
ihim rayuwarta ne take rubutawa domin be yi kama da gata ba ko novels. Farkon ya karanta sai kuma ya tsakalla tsakiya ya kuma duba inda ta tsaya sannan ya sake kallonta.
“Me kike ji yanzu a ido”
“Duhu kawai”
Ya dauko wata yar karamar fitila ya za
gaya gefenta ya matsa kusa da ita ya saka hannunsa ya bude idon ya haska, dayar ma haka yai mata sannan ya koma ya zauna yana kallon Inna.
“Am ina ganin likitan ido ya kamata ya ganta”
“To a ina zamu gan shi?”
“Ina zuwa”
Ya dauko wayarsa ya sh
iga contact dinsa, ya nemo number Habib. Cikin natsuwa ya aika masa kira ba bata lokaci yai picking.
“Hello Shattima”
“Doc Habib ka shigo yau?”
“No ina aikin yamma ne sai 4 zan shigo”
“Ina da patient da nake son ka duba min mai matsalar ido”
“Ba matsala a buda mata file kamin na zo”
“Okay”
Shattima ya aje wayar b tare da ya kashe ba, har sai da shi Doc Habib din ya kashe wayar. A natse ya kalli Bappa dake can baya yana fadin.
“Da yamma zai shigo, amman kamin y shigo za a bude mata
file, so that yan zuwa dubata kawai zai yi”
“Tau nawa ake bude file din?”
Bappa ya taba yana saka hannu a aljihu.
“No ba a nan ake budewa ba, bari na kira wata ta kai ku”
Telephone din dake gabansa ya danna ya kara a kunne.
“Zo”
Ya fada
sannan ya maida telephone din a muhallinta, ba bata lokaci sai ga wata kyakyawar budurwa ta shigo tana sanye da kayan nurse.
“A kira min Sule”
Ta juya ta fita, babu bata lokaci wani dattijo ya shigo sanye da uniform da alama shi ma ma'aikacin asibi
tin ne.
“File za a bude musu guide them pls ka yi musu komai”
“Tau ranka ya dade, ku ta zo muje”
Mutumen ya fada sannan ya nufi kofar fita, a tare Inna da Bappa suka mike tsaye Inna na kokarin kama hannun Fadime Shattima ya dakatar da ita.
“N
o Mama ki bar a nan, kuje ku dawo, zai zama mata wahala ne tun da ba gani take ba”
“To mun gode Allah ya rufa asiri”
Inna ta fada sannan ta bi bayansu Bappa da Sulen da suka rigata fita. Sai da suka fice sannan Shattima ya kalli Fadime dake zaune gab
ansa.
“Fada min gaskiya, miya samu idonki”
“Wallahi gaskiya na fada”
“Na fa san halinki ba ki jin magana”
“Ka san ni ne?”
“Eh”
“A ina? Wanene kai?”
Ta tambaya tana ta kyabce kyabce da ido, mikewa yai tsaye ya zagaya inda take ya kai ha
nnunsa ya kama hannunta da nufin kaiwa a fuskarsa ta lalaba sai tai wani irin jan numfashi kamar ta ga abun tsoro, sakamakon sanyin da ta ji a hannunsa ya gauraya da nata hannun, wanda hakan yai daidai da shigowa kira a wayarsa.
Saurin sakin hannunta yai
yana kallon kyakkyawar fuskarta da makantar bata rage ta da komai ba a kyau da haske, what if bata saba rika hannun maza ba? What if tsoron mutane take ji a yanzu tun da bata gani? Ya ma kamata ya rikata ne? Shi ne abun da yake tambayar kansa kamin ya nuf
i gurin wayarsa dake ringing ya dauka ya fice daga office din gaba daya.
Hawayene ya sauko a blind eyes dinta, zuciyarta ta hau bugawa da mugun karfi, jikinta ya hau bari, sai ta jimke hannun sosai kamar wanda aka cewa idan ta bude hannun zai fadi.
“
Wanene wannan? Wanene kai?”
Ta mike tsaye ta fara lalaben teburin kamin ta juyo ta ta fara tafiya da lalabe tana nufar inda take zaton kofa take, tafiya kadan ta ji ta ji ta taka mutum, sai ta dauke kafarta ta yi baya, ya mika hannunta sai ta ji mutum,
matsawa tai tana lalabe riga ce a jikinsa mai kamar ta sanyi, sai da ta lalabe kirjinsa tsab sannan ta kai hannunta gurin fuskarsa, hancinsa ta taba ta sauko gurin bakinsa sai kuma tai sama gurin idanuwansa, can kuma ta saka hannu biyu tana lalabar fuskar
gaba daya, dage tai ta lalabo kansa sai ta ji hulla a kan facing cap, dawowa tai gurin fuskarsa tana lalaben sai ta ji hawaye ya sauko a idon mamallakin fuskar, numfashinsa kuma na kara kusantota.
“Zo muje na kai ki gurin su Inna”
Ya rada mata a kun
ne har lips dinsa na laba hijabinta lumshe ido tai hawaye ya sauko mata.
“Wasim...”
Ta furta domin ta gane muryarsa, wuyan hannunta ya kama ya fita da ita daga cikin office din.
FALMATA POV.
Tana cikin gyara dankalin ta ji kara door bell,
sai dai bata tai wani yunkuri ba har sai da ta ji an sake danna kuma an kwankwasa irin yadda tai, sai ta aje wukar da sauri ta fito falon, ganin babu kowa yasa ta nufi kofar ta bude cike da zumudi, domin ko ba a fada mata ba ta san Sirleem ne.
“Wow”
Ya furta yana fito da idonsa waje. Sai ta sakar masa murmushinta mai kama da dariya.
“Ina kwana?”
“Lafiya Kalau, ya kike har kin iso?”
“Eh”
Ya kara fito da idon waje, ganin be daga murya sosai gurin magana ba amman ta ji.
“Kin ji abun da
na fada?”
“Eh”
“Taya aka yi kika ji?”
“Na ji dai”
Ta furta cike da far'a, sai ya sako kafarsa cikin falon yana kallonta mamaki.
“Jinki ya dawo kenan?”
“Eh amman ba kamar da ba, ina jin maganar kamar daga wani daki ne?”
“Wow..... ”
Y
a furta yana jin kamar ya dagata sama ya juya.
“Soon zaki dawo normal inda kina amfani da maganin daman mai karfi ne sosai, I'm happy”
Ita ma ta yi dariyar jindadi, sai ya sakar mata ido hakan nan kawai take burgeshi, if you ask him miya kawo shi a
gidan yau he can't explain kawai dai ya ji yana son ganinta ne.
“Miya samu idonki?”
Ya tambaya ganin idon ya kumbura, sai tai kasa da idon ta kasa cewa komai.
“Ko an dokeki ne?”
“Aa”
“Then miya samu idonki? Karki min karya na san ba halink
i ba ne”
Dagowa tai ta kalleshi sai idonta ya cika da kwalla.
“Babana...”
Sai kuma tai shiru, a hankali tana wasa da yatsun hannunta. Yatsun ya kalla yadda aka jera mata su gwanin sha'awa, sirara ga akaifar fara fes.
“Ina Momy?”
“A nan na ba
rta da bakuwa kila tana dakinta”
Ta fada tana nuna upstairs. Sai da kalli inda yake nuna masa sannan ya kalleta.
“Me kike yi?”
“Dan kalin turawa nake gyarawa”
“Je ki cigaba bari na gaishe da Momy”
“Tau”
Ta buya sai ya fita da kallo har s
ai da ta shige kitchen din sannan ya nufi upstairs. Sai da ya fara knocking kofar sannan ya tura ya shiga, be samu Momy a dakin ba sai motsin ruwa da yaji a bandakin hakan ne ya tabbatar masa da tana bathroom din,jikin kofar y tsaya har sai da ta fito.
“Momy ina kwana?”
“Lafiya Kalau, yau gidan nan tun da safe”
Ta amsa shi tana kawardar fuska, bata son ya kalli fuskarsa saboda kukan da tai. Sai yai murmushi.
“Yeah kawai na biyo ne, i thought ko iyayenta sun hana ta zuwa”
“No ta zo tana kitc
hen ma”
“Eh ita ta bude min kofar ma”
“Okay”
Ya saki kofar yana kallonta kamar ya tambayi damuwarta sai kuma wata zuciyar ta hana shi, wata kalma bata sake shiga tsakaninsu ba ya juya ya fita daga dakin, har ya sauko kasa be daia kwankwanto da tun
anin damuwar Momy ba, duk da ya san a duniyar nan bata da damuwar da ta wuce ta neman haihuwa. Bakin kofar kitchen din ya tsaya yana kallon Falmata da yanka dankalin sala sala.
“Cutie..”
Ta dago ta kalleshi ba dan ta san abun da kalmar ke nufi ba, s
ai ta samu kanta da sakar masa murmushi.
“Fada min Baba ne ya taba ki?”
Ta maida kanta gurin abun da take kamin ta sake dago kan ta kalleshi.
“Ya.. Ya..”
Haka kalmar ta makale a bakinta ka kasa fitarwa, karasa yai kusa da ita ta duka yana kal
lonta, kamshin turarensa ya cika mata hanci.
“Ya me? Feel free ki fada min damuwarki, ba ki son ni ma na rika fada miki damuwata ina neman shawararki?”
Ta kalleshi.
“Ni”
“Eh, fada min me Baba yai?”
“Aure zai min...”
Ba numfashinsa kadai
ba har bugun zuciyarsa sai da ya tsaya cak na yan dakiko, can kuma ya sake tambayarta kamar wanda be ji da kyau ba.
“Aure?”
Ta daga masa kai.
“Saboda me?”
“Ni ma ban sani ba”
Daga haka ta kwashe abun da ya faru ta fada masa.
“Wai mi ya
ke damun iyayenki ne? Wannan step mom dinki bata da imani? Taya zata goyi bayan babanki ya aura miki tsoho? A shekarunki? Mutumen da baki ma sani ba?”
Ita dai bata ce komai sai hawaye take.
“Kuma ke yanzu aurenshi zaki yi?”
“Na riga na roki Allah
, idan auren alheri Allah ya ba ni ikon yi ma mahaifina biyayya idan kuma ba alheri ba ne Allah ya musanya min”
Duk sai ya ji tausayinta ya kara kamashi.
“Ban baki shawarar aurensa ba? Zaki ruguza rayuwarki ne kawai”
Ta kalleshi hawaye na mata zu
ba.
“Ina kallonka a mutum mai kima da daraja, da za a bani da da duniya zan bi ina rubuta sunanka a ko'ina, saboda kwarjinka ya cika idona, amman ba zaka ba ni shawarar bijirewa umarnin mahaifina ba, kamar yadda baka bani shawarar na gudu na bar gida b
a”
“Ko da hakan zai cutar da ke? Rayuwarki nake magana ba tawa ba, ban ce ki bijirewa umarninsa ba, kuma ban baki shawarar auren tsoho kakanki ba, rayuwar aure is the last life da mutum yake da, idan ka dace ka dace, idan kuma ka samu jarabawa to rabin
rayuwar duniyar ba zata maka dadi ba”
“To guduwa zan yi?”
“Ban ce ki gudu ba”
“Ce masa zan yi ban amince ba?”
“Ban ce ki ce haka ba?”
“To me zan yi?”
Ido ya kura mata.
“Kina da wanda kike so?”
Ita ma idon ta sakar masa, kamar mai t
unani can kuma ta sunkuyar da kai.
“Aa ba ni da kowa”
Mikewa yai tsaye yana juyowa sai yai arba da Momy dake kokarin shigowa kitchen din, at that time wayarsa dake aljihu tai ringing. Ciro wayar yai sannan ya fice daga kitchen ya kara wayar a kunnen
sa.
“Hello”
“Hello kawai kamar ba ka gane mai magana ba?”
“As how”
“Ya ka saba kirana?”
“Hey listen...”
“I'm not listening, ko dai ka zo Kaduna ko kuma na zo Yola, saboda magana ce mai muhimmanci I'm pregnant”
“As how you're pregnant
wani abu ya taba shiga tsakaninmu ne?”
“I don't care, ko ka aureni ko na bata maka suna, ba zai yiyu na gina ka ba, wata karamar yarinya ta karbe min kai, you always telling Maman ka ce bata son aurenmu amman yanzu na gane ba ita bace kai, saboda kana s
oyayya da karamar yarinyar kuma har a cikin gidanku, and ba zai yiyu ace mamanka bata sani ba”
Mansura ta fada daga dayan bangare.
“Wow... Awesome... Haka zuciyarki ta raya miki? Kin manta waye Sirleem a gurinki? Yarinyar da kike dorawa laifi babant
a auren dole zai mata so what's your problem?”
“You're my problem, idan ba ka rabu da yarinyar ba, i swear to God zaka ja mata matsala, ka san ni Sirleem”
“Yeah and you know me too”
Ya katse wayarsa yana mamakin yadda Mansura ta kasa masa uzuri.
After Sirleem ya fita daga kitchen din Momy ta dauki dankalin ta saka a fanfo ta wanke, sannan ta kalli Falmata.
“Matsa kusa ki ga yadda ake kunna gas din”
Falmata ta matsa kusa da ita sosai tana kallo har ta kunna, ta kashe sannan ta sake kunn
awa.
“Kin ga yadda ake yi?”
“Eh”
“Good dauko kwai a firjin din can ki fasa min ki saka magi da yaji da albasa sai ki kunna wannn bangaren ki soya, ai kin iya soyar kwai ko?”
“Eh”
Momy ta bita da kallo, gaba daya rasa na zaba tsakanin burint
a maganar Hajiya Umaima da kuma bijewa zuciyarta. Tabbas gaskiya Hajiya Umaima ta fada this is last chance da take da shi, this is the only hope da za tai fatan cika burinta? Amman a sirinsa ba tare da sanin Falmata ba ko kuwa da saninta? Idan ta sani zata
aminta ne? Idan kuma tai mata a boya zata sake yarda da ita? Anya ya dace ya jefa rayuwarta cikin matsala bayan wacce take ciki? Ya zata kalli Sirleem nme zata fada masa? Wane hali zata kara jefa Falmata? Anya lokaci yayi da zata aikata haka? Yaushe ma ya
rinyar ta zo? Amman idan ba tai a yanzu ba sai zuwa yaushe za tai?
Haka ta jerowa kanta tambayoyi man da ta dora saman wuta yana ta soyuwa bata sani, ba, can kuma wata zuciyar ta bata amsa.
‘Duk abun da zai faru indai har na samu biyan bukata! Koma
i zai zo da sauki, zan dauki dawainiyarta zan tallafi rayuwarta, na yi mata duk abun da take so’
Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Falmata dake numa mata man yana konewa.
“Oh Sorry hankalina yana can wani guri”
Ta fada da murmushi a fuskarta, sa
nnan ta fara zuba dankalin tana kallon yadda Falmata take soya kwan kamar daman can shi ne aikinta.
“Fulani baki yi karatu ba ko?”
“Eh ban yi ba”
“Kina son ki yi?”
“Eh amman yanzu ai a yi girma sosai”
“No ba a girma da karatu, zaki iya shig
a a haka kuma idan kika maida hankali har jami'a sai ki je?”
“Jami'a? Karatun da ake zama likita?”
Maganar likita da tai yasa Momy ta tuna cewar ai bata ji sosai.
“Yes, Fulani yanzu kina ji da kyau ne?”
“Eh”
Ta amsa tana murmushi. Momy ma t
a yi murmushi.
“Mashallah haka ake so, daman ina sa ran haka saboda maganin mai tsada ne kuma yana aiki sosai, Allah kara lafiya, sauran makaranta na nema miki ko?”
Falmata ta kalleta da sauri.
“Makaranta?”
“Eh ko baki so?”
“Ina so sosai i
na son idan na ga abu na karanta ko na rubuta, ina so sosai”
“To zan nema miki inshallah, har jami'a idan kina so zan sama miki, ni ma kuma ina fata idan na nemi abu wajen ki ba zaki min ba”
“Me kike so Momy?”
“No ba yanzu ba, wata rana dai”
“I
nshallah zan miki ko minene, ba zaki same ni mai butulci, ko dan Sirleem kin cancanci komai a gareni”
Momy ta mata wani kallo. Kamar tai magana sai kuma ya fasa ganin Sirleem ya dawo kitchen din.
“Baka wuce ba?”
“Eh yanzu dai zan wuce”
“Ba zak
a tsaya ka karya ba?”
“No thanks”
Be tsaya jiran abun da zata fada ba ya juya da