Showing 75001 words to 78000 words out of 304903 words

Chapter 26 - FULANI COMPLETE

sannan ya sake kirga 10k ya m

ika mata.

“Wannan idan kin je ki samu wata sana'a ki rika yi”

Ta yi saurin girgiza kai.

“Aa idan aka gan ni da kudi da yawa za a iya dukana”

Sirleem be ce komai ba ya maida kudin wallet dinsa ya mike tsaye.

“Ka kaita gurin motana zan kira

oga na fada mishi”

“Okay”

Tare suka fito da Falmata ya nuna mata motar Momy.

“Ki jirata a can, idan ta zo ki fada mata unguwarku, kuma duk abun da tace ki ce eh haka ne”

Sai da yai maganar ne Falmata ta gane cewar sun iso Yola kenan, kamar ka

zar da kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi gurin motar da Sirleem ya nuna mata ta tsaya tana karewa gidan kallo.

AA POV.

Ganin bakuwar number yasa gabansa faduwa, duk kuwa da Nana ta fada masa cewar bata fada a gida ba, amman ya kasa natsuwa. Haka

yai ta kallon wayar har tai ringing ta gama sannan mike tsaye ta fito daga dakin Hindu ya nufi waje, a nan kiran ya sake shigowa sai da yai Bismillah uku sannan ya dauki kiran, jin muryar Nana yasa hankalinsa kwanta ba.

“Saurdauna”

“Na'am”

“Yauwa

kai ne, ya kake?”

“Ina lafiya”

“Kana ina?”

“Ina ina? Ina Yola”

Ya amsata yana juyawa ya gani ko wani na binsa, ko kallonsa.

“Ka zo gidanmu na fadawa Hajiya tace na kira driver, ka bashi key din motar”

Wani irin dadi ne ya lullube shi, ya

matsa kusa da wata transforma ya fada ta yana jin kamar ya rumgumeta.

“Da gaske Nana?”

“Wallahi da gaske, ka zo yanzu ka ji”

“To ina ne unguwarku?”

“Kasan Turaki area”

“Eh”

“To ka zo nan daga shigo kace ina ne gidan Mai Martaba idan kan

zo kace gurin Nana ka zo, sai ka kira line nan”

Wata kalar kabbara yai ya lumshe ido ya bude ya rumgume transforma da hannu daya

“Allahu Akbar yanzu Nana ke yar sarauta ce?”

Dariya Nana tai ta tashe wayar ba tare da tace masa komai ba. Wayar ya k

urawa ido yana tuna farkon haduwarsu, sai yaji abun kamar a mafarki, duba yai yaga babu mai kallonsa sai ya fadi yai sujada sannan ya mike tsaye yana gyara rigarsa.

“Shikenan Kakata ta yanke saka, na yi arziki malam”

Da sauri ya koma cikin gidan ya

canja tufafin jikinsa ya fito ba tare da ya fadawa kowa ba, ya fito ya tari mai achaba ya hau.

Ba a sauke shi ko ina ba sai Turaki area (Fake area) Unguwar masu arziki da naira unguwar da babu irinta kaf a fadin garin Yola, manyan gidanjen yake bi da kal

lo kamar be saba bi yana wucewa ta unguwar ba, wani karin dadi yake ji a ransa, yana sauka ya mikawa dan a chaban 500 yace ya yafe nasa canjin, cikin tsoro tsoro ya karasa gate din ya gaisa da masu gadin ya fadu musu gurin Nana ya zo, ba su yarda da shi ba

sai da ya kira wayar ta daga tai musu magana sannan aka barshi ya shigo.

Gaba daya rikecewa yai ya rasa ina zai bi ganin masarauta mai kama da wata unguwa, saboda fadi da girma gashi an raba ko'ina part part, kai tsaye ya nufi apartment din Hajiya yana

tafe yana jin wani dadi na daukarsa sai raba ido yake yana kallon amsu aikin dake kai da kawo da sauran mutane dake ta sha'aninsu. Bakin gate din ya tsaya ganin mota na fitowa a zatonsa Nana ce sai ya gata wata marar jiki ta tsaya daidai shi da motar.



Ya kai?”

“Na zo gurin Nana ne”

“Me zata maka?”

“Nine sabon driver da za a dauka”

Jurry ta kare masa kallo from head to toe sannan ta watsa masa wani banzan tsaki.

“Malam fita ka bamu guri ba za a dauke ka ba”

“Amman Nana tace na zo”



Nana ita take da ikon kanta i say out...”

Ya juya da sauri ya fice aransa yana fadin.

‘Wallahi ba zai yiyu na ga samu na ga rashi ba, dole ne sai an dauke ni’

***

Nana ta kwanta saman gadonta tana dariya, ba karamin dadi ta ji ba na samun number

sa da tai, daman kuma ta san ba zata mata wahala ba indai a line Hajiya ne. Duka numbers din da ta duba a call list tashi ce kawai ba suna.

  Wani irin dadi take ji zai zama driver ta domin har ga Allah yana burgeta kuma gashi yana jin maganarta komai ta

ce masa. After some minutes kiransa ya shigo wayar Hajiya dake hannunta ta daga tai magana da mutanen dake gate din sannan ta kashe ta mike tsaye ta fice daga dakin.

SHATTIMA POV.

Relaxing yai akan kujera yana busar da iskar bakinsa, manyan idanuwa

nsa na wani lumshi alamar bachi yake ji da kuma gajiyar tiyatar da ya gama a yanzu. Wayarsa dake gaban teburin ce tai ringing Sunan Hajiya Karama ne rubuce a gaban screen din, sai da ya dan matsa da kujerarsa baya sannan ya amsa.

“Hello Sis”

“Shatti

ma ya aiki?”

“Al-hamdulillah how is kids?”

“Suna nan kalau, on Saturday zan zo Katsina fa gurin aikin da na ce maka”

“Okay this Saturday?”

“Yeah na san dai ba zaka je asibiti ba ranar right”

Ya dan tabe baki kadan kuma yai shiru na wani loka

cin kamin ya amsa mata.

“Zan je da Yamma”

“Okay ni da safe zan shigo”

“Allah ya kai mu”

Ya fada bayan yayi shiru kamar ba zai ce komai ba. Aje wayar yai be kashe ba, daman can haka yake ko shi ya kira ka sai dai kai ka kashe, shi nashi aje way

a ne kawai. Ya mike tsaye yana murmushi yana kallon screen din wayar dake dauke da hoton yayanshi.

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

19

*Lit

tafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

Hannun rigarsa ya fara budewa sannan ya bude ya fara bude maballan rigarsa yana ta kallon kansa a jikin madubin dak

e gabansa. Dan murmushi yai kamar wanda ya tuna abu sannan ya juyo ya cire rigar gaba daya ya dora saman gadon ya dauko vest ya saka ya sauko kasa.

Kai tsaye kitchen ya wuce ya dauki cup ya aje sannan ya bude fridge ya dauko lemun tsami ya matsa a cup di

n ya bude durowar kitchen din ya dauko wata farar roba ya bude ta debi kanwa kadan ya zuba a cup din ya saka karamin spoon ya garwaye sai da lemun ya hade da kanwa sannan ya daga cup din ya shanye yana bata fuska tsamin na kai masa har cikin kai. Ra'ees ne

ya shigo kitchen din sai zuba kamshin turare yake.

“Shattima ni zan wuce”

Ra'ees ya fada daga tsayin da yaje bakin kofar kitchen din. Juyowa Shattima yai ya kalleshi, irin kallon nan na ina zaka je? Indai Shattima ne zai bude baki ya tambaye shi ba

sai dai kar ya sani, ba dan komai ba sai dan magana taba masa wahala, yana da nauyin baki furta wata kalar tafi komai yi masa nauyi a baki da jiki, abu ne mai wahala ka ganshi a cikin mutane ko da kuwa Ammy ce ko Zainab yana fira, sai dai yai shiru yai ta

saurarensu idan sun gama ya tashi wani lokacin kuma sai yi murmushi idan an fadi abun dariya idan kuma tambayarce zai iya ce maka eh ko aa ko ya girgiza kai. Magana ta fi komai yi masa wahala a rayuwa, gashi kuma likita haka nan dai yake ta fama kamar dol

e.

“Zan je kauyen kaita, akwai wani aiki da nake son yi a can”

Ra'ees ya amsa masa ba tare da ya jira ya tambaye shi ba, daman kuma ya san halin abokin nasa indai sai ya tanbaye shi ne sai a mutu a tsaye.

Shattima na son ya tambayeshi me zai je yi

a can kuma yaji ba ya bukatar wahalar da kansa, sai kawai ya tabe baki ya daga masa hannu.

“Safe trip”

“Thanks”

Ya juya ya fice daga kitchen din, kamin ya isa gurin motarsa Yayarsa ta masa kira ya kai uku domin mijinta ya shirya shi kawai ake jir

a. Da motarsa ya isa gidanta sai ya aje motarshi ya shiga motar mijin suka kama hanyar Kaita daga Katsina.

Suna tafe suna firar kasa da rashin tsoron da ake fama da ahi da yunwa, har suka isa, a cikin garin kaita suka yi sallah sannan suka yi tambaya aka

fada musu hanyar da za su bi ta kaisu garin Bandalo. Alhaji Tukur ne yake jan motar Ra'ees yana front seat, yana karewa garin kallon, garin Bandalo gari ne mai cike da burgewa, tun farkon shigowa garin zaka fara arba da manyan gonaki, domin garin ya kasu

kashi biyu ne, fulani makiyaya sai kuma hausawa da kusan sune rabin garin, daman fulanin irin masu yada zango nan ne a gari, yamma da garin ne bangaren fulani kana daukar hanyar da tai can zaka fara arba da bukoki da shanu da masu kiwon shanun gwanin burge

wa.

“Rabun da na ga bukka da idona ni har na manta”

Ra'ees ya fada yana kara bawa idonsa abinci, sai da su kai nisa sosai sannan Alhaji Tukur ya tsaya kusa da wasu fulani suka zaune gaban wani massalaci na kasa yana tambayarsu Malam Jauro.

“Dan

Allah muja cijiyar wani Malam Jauro Sama'ila”

“Kun zo gida, daga ina kuke?”

“Daga birni mun zo, gurin Matarsa ne Amo”

Wani bafullatanin mai tsaga a fuska ya mike tsaye.

“Muje na karasa da ku daman gidan Modibbo zan je”

A kafa yake tafiya su

kuma tana binsa a kasa har suka isa kofar gidansu Fadime, gidansa ne mai girma da aka zagaye da zana an share gaban idan tas ga kasar gurin ta kwanta kamar yashi. Malam Bala da kansa ya sallama cikin gidan sai Hajjo ta amsa masa ta fito ta gaishe shi tana

karewa mutanen kallo da yaren Fulatanci yake tambayarta ina Malam Jauro, sai ta fada masa baya nan ya tafi gona.

“To ga baki nan ki fadawa Amo, ni bari naje na kira shi”

Ya fada mata da yaren fulatanci, sannan ya kallesu yace.

“Zanje na kira shi

yanzu nan, yana gobarsa”

“To sannu da kokari mun gode sosai”

Duk suka fada Ra'ees har yana dan risinawa domin ya yaba sosai da yadda mutumen yake ta musu karamci.

Yana tafiya Amo ta fito baki har kunne tana dariya ta nufo su da hijabinta mai multi

colors tabarma rike hannunta Hajjo kuma na rike da kwanon ruwa dake cike da kindirmo. Icen dake kusa da kofar gidansu ta nufa ta shinfida kusu tabarmar a can, sannan ta karbi kwanon dake hannun Hajjo ta a gurin.

“Hannunku da zuwa Hannu da zuwa, kun sh

a hanya”

Ta hangame musu bakin nan nata mai cike da goro tana musu Sannu ga wata uwar dariya da take musu ta murna da ganinsu domin bata dauka za su zo din da gaske ba. Ra'ees ne ya fara zaunawa yana amsa gaisuwarta kamin mijin yayarsa ya zauna shi ma.

Da sauri Amo ta koma ciki gida da murnarta, ta nufi dakin Inna wacce ke zaune dakin tare da Fadime tun safe, saboda kukan da Fadime take ta yi, tun tana dan jin tsoron abun da ya faru jiya har ta fara dauriya tana lallashin yarta, duk kukan da Fadime tak

e na hawaye ne kawai bata yarda ta bude bakinta, gudun kar ta sake tsorota wani domin ita ma tsoron muryar take, gashi Bappa da Inna sun hata ta fita balle taje ko zata ganshi ta roki ya gyara mata nuryarta ta koma daidai.

Hankali Inna da Fadime be kar

a tashi ba, sai da Amo ta leko bukkar tace ga masu neman auren Fadime nan sun taho, Fadime kamar an mata allurar kuka haka ta ji, Inna kam sai tausayin Fadime ya kamata dan ta san yadda take daukin zuwa wannan ranar.

“To su gaisa da Malam tukuna mana”

“Eh na aika Hajjo ta kirashi yanzu”

Amo ta juya ta fita tana jin wani irin dadi marar misaltuwa, tasan a komai yanzu ita za a saka a gaba. Cikin hawayen Fadime ta mike tsaye tana nuna ma Inna tufafin jikinta da alama so take ta canja ta, tana son tai

magana tana jin tsoro muryar.

“To wai Fulani hakan zaki tafi musu kanar kurma? Komai sai dai ki da hannu?”

Fadime. Ta dan turo baki ta fice daga bukkar ta nufi bukkarta ta dauko atamfar dake can masa ghana must go, ta tube rufafin jikinta ta debi r

uwa ta shiga bandaki. Sai da ta kori kadangaran da ke gurin dan kar su sako mata ido suna kallon tsiraici sannan ta cire zanenta, sama sama tai wanka ta fito tana ta ayyana yadda mutumen yake a idonta, bata ma tsawa shafa mai ba ta saka atamfar ta daura da

nkwali ta dauko mayafi ta dora a saman kai, ta dauki karamin madubin ta kalli kanta. Dan murmushi tai kamar ba ita ce take kukan tun safe ba har rana. Can zuciyarta ta bata cewar ta shafa hota ai yan birni ne, da sauri ta kwance kullin hodar ta kasa dake c

ikin farar leda ta dagali kadan ta shafa ta shafa janbaki, abun ka da farar mace sai tai kyau sosai pink janbakin ya haskata ita kanta sai da tai murmushi. Ta dauko talkaminta na sallah ta saka ta fito tsakar gidan ta zauna, Inna na kallonta ta saki murmus

hi ganin yadda yarta ta fito Ma-sha-Allah, daman can Fadime akwai iya kwaliya ba kamar ta sauran yan matan kauyen ba.

“To kwalli fa”

Inna ta fada tana kallonsa. Sai Fadime tai murmushi kamar ta bude baki tace ai su yan birni basa saka kwalli kuma ba

dama tun da muryarta ta zama abun tsoro, duk da bata da tabbacin muryar tana nan har yanzu ko kuma ta dawo normal a yadda take, abun haushi ma muryar shanun bata fita kadan kamar an saka loudspeaker haka take shiga kunne mutane.

Gaba daya Fadime kasa nat

suwa tai taje jikin zanar tana lekensu sai dai bata ga fuskar ko daya daga cikinsu ba kasancewar sun bata baya ne suna magana da Bappa da wani abokinsa. Wani irin tsalle ta buga tana jin kamar ranar za a kaita dakin mijin. Amo de na zaune bakin tata bukkar

tana murmushi a ranta tana ayyana ko kwana nawa Fadime za tai kamin ta mutu, ta dayan bangaren kuma tana ta mamakin yadda jiya ma wani abun ya same ta na sauyawar muryar kamar yadda Inna ta fada mata, dan ita dai bata nan komai ya faru.

Yanzu kam ta far

a gasgata cewar Fadime ta hadu da aljanu domin su kadai zasu iya cire nata wutar sai kuma maye irinta ko mai tsafi, wata kila shiyasa ita ta kanta ta nemo mata miji, ko da yake mijin ma daga gani maye ne kamar ita ko zai iya cin kurwa Fadime ko kuma zata g

agareshi ne kamar yadda ita ma ta gagareta?

‘Bari na gani yanzu za a sake cirewa’

Ta fada a ranta sannan ta mike tsaye ta shiga cikin bukkarta, ta mika hannu a karkashin gadon ta na kara ta dauko wata yar karamar tukunyar kasa wacce ke rufe da jan k

yalle ta bude kyalle ta kai bakinta ta fara kiran sunan wani aljani tana masa kirari kamin ta fadi bukatarta sannan ta kai kunnenta tana saurare. Can ta sake kai bakinta.

“Bakin bunsuru zan yanka maka”

Sannan ta aje tukunyar wacce aljaninta na maita

yake ciki ta maida ta karkashin gado, ta sake janyo wata tsohuwar roba mai murfi ta bude ta dauki wata yar karamar soyayyar kurwa ta kai baki, har wani lumshe ido take tana shude yatsan hannunta.

“Saratu kam akwai dadi”

Ta fada tana kokarin maida r

obar a inda take, sai davta gyara komai tsaf sannan ta mike tsaye ta fito, a tsakar gida ta samu Bappa tsaye yana nunawa Inna kudin da suka ba shi.

“To gashi nan since ase goro”

A take ta ji ranta ya bace akan me zai fara nunawa Inna bayan itace uwar

gida, sannan ita ta kawo ma Fadime mijin nan, sai dai bata yarda ta nuna musu komai ba ta washe baki tana murna kamar gaske.

“To Fulani tashi kije ku gaisa”

Bappa ya fada. Abun ka da mai nema sai tai zumunt ta mike tsaye, jikinta sai rawa yake zuciy

arta na bugawa da karfi, tana son ta tambayi Inna idan taje me zata fara cewa kuma tana gudun tai magana aji muryarta bata sani ba ko har yanzu muryar tana nan.

“Karki musu magana Fulani, duk abun da suka ce miki sai dai ki daga musu kai ko ki yi dariya

, idan suka tambaye ki ki nuna musu wuyanki wuyanki ke ciwo”

Inna ta fada, sai Fadime ta gyada kai ta sinne kai kasa tana dan jin kunyar Bappa, har tafiya sai da Fadime ta sauya ta fara irin na yan zamani a hankali take takawa har ta isa inda suke, tana

kokarin zaunawa a saman shimfidar ta tuna cewar bata saka turare ba, gashi dai yan birni suna son kamshi tun da su ma taji sai kamshin suke, sau daya ta kalli Ra'ees ta dauke kai dan ta fi sa ran shi ne mijin nata ganin ya fi kurciya. Da hannu ta gaishe s

u irin yadda kurame suke yi sai suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login