Showing 183001 words to 186000 words out of 304903 words
/>
aidai ita ya tsaya ya sauke gilashin motarsa, bata lura da shi ba har sai da ya kira sunanta.
“Falmata”
Ta kalli motar ganin shi ne yasa ta tsaya ba tare da ta ce masa komai ba, hannunsa ya mika ya bude mata dayan side din.
“Zagoyo nan”
Ba musu
ta zagaya tana dingishi, shi kuma ya bita da kallon tausayi har ta shiga motar ta zauna.
“Rufe”
Ta mika hannu ta janyo ta rufe.
“Ina wuni?”
“Lafiya kalau miya samu kafarki?”
“Faduwa nai”
“Wannan ba faduwa ba ne, karya kuma ba halinki ba
ne, Teema...”
Ta dago ta kalleshi ji irin sunan da ya kirata da shi.
“Baba ne ya dake ni”
“Saboda me?”
Bata boye masa komai ba, bata rage ba balle ta kara. Ajiyar zuciya ya sauke idonta ya cika da kwalla, for the first time ya ji ya tsani Baban
ta.
“Teema akwai wani abun da zan iya miki? Kina son naje na fadawa babanki baki son auren mutumen? Ko kuma kina da wanda kike so na je na yi magana da shi?”
Ta girgiza masa kai hawaye na zubar mata.
“Aa, ka min komai na gode”
Ya lumshe idonsa
ya bude ya kalleta.
“Me kika zo yi nan?”
Ta fada masa.
“Bari na kai ki duba Momy ta duba kafarki”
Ta yi shiru bata ce komai ba sai hawaye take, ribas yai ya juya da motar suka fita, tafiya suke bata ce da shi komai ba shi ma be ce mata ba sai k
allon fuskarta yake.
“Na rasa dan'uwana, 3 days back shi ne kadai dan'uwa namiji da nake da shi ya rasu sanadiyar hatsarin jirgin sama, ni kaina tun ranar dana bar ki a gidan Momy ban sake zuwa ba”
“Allah ya jikanshi”
Ta furta tana share hawayenta
, yayi shiru be sake cewa komai ba, sai dai har ga Allah yana jin sauka hawayenta a zuciyarsa.
A harabar gidan Momy ya faka motarsa, sannan ya bude ya fita tana ganin haka ita ma ta bude ta fita, ta bi bayansa, knocking yai after few seconds aka bude masa
kofar falon, sai yai ma Falmata alama da hannu cewar ta fara wucewa.
Bata masa musu ba ta saka kafarta cikin falon tana dingishi.
“Subhanallahi wani abun ne kuma?”
Momy ta fada tana kallon kafarta, Falmata ta mika mata gaisuwa ba tare da tace komai
ba.
“Wannan Step Mother din ta ce ta gano an koreta daga aikin shine tasa Babanta yai mata wannan dukan, and lastly wai ta ji yana maganar zai maida aurenta nan da sati daya!”
“Auren wa?”
Momy ta daki kirji tana kallom Sirleem da yai mata maganar
. Sai da zauna ita ma ta zauna sannan ya labarta mata zancen auren kamin ya biyo mata da abun da ya faru.
“Mai napep din ya dawo ya fada min ya daina ganinki zai je ya tsaya ya jira amman ba zata fito ba, yana fada min haka na raya cewar wata kila sun g
ano ne, ko kuma kin fada musu, na so na kira ka sai ga labarin rasuwar Talba ya same shi shiyasa da naje gaisuwar ban maka magana ba, yanzu miye mafita?”
“I don't know, na tambaye ta idan akwai wanda take so, tace babu”
Sirleem ya fada yana dagowa da
ga jikin kujerar da yake zaune. Momy ta kalleta wani irin tausayin Falmata ne ya shiga zuciyar Momy fiye da da, bayan wannan wahalar da ake bata sai kuma ace za a aura mata tsoho? Wata kila shi ma mutumen banza ne, da zai zo yana azabbatar da ita.
“Ke
baki da wanda kike so ne Fulani? Karki yarda a aura miki tsoho, karki yarda a aura miki wanda baki so, ki fada min idan akwai wanda kike so”
Falmata ta yi kasa da kanta kamar a zata ce komai ba, Momy da Sirleem suka zuba mata ido.
“Wanda nake so, ba
so na yake d aure ba”
“Taya aka yi kika sani? Ya taba fada miki ne? Kuma idan ba son aure yake miki ba me zai saka ya zo yace yana sonki?”
Momy ta tambaya.
“Ai kin san akwai masu son mace da son banza, bana aure ba, musamman irinta da ake ganin ka
mar idan an tabata ba za ayi komai ba”
Sirleem ya bata amsa.
“Ke yanzu duk a cikin samarinki babu mai yi da gaske?”
Ya girgiza kai, alamar aa Momy ta sauke ajiyar zuciya, can kuma ta sake kallonta.
“Fulani zaki iya auren Ameer, yaron da kika g
ani ranar da kuka zo gidan nan wani baki haka?”
Falmata ta dago ta kalleta, Sirleem ma ya kalleta da sauri.
“Momy?”
Ta kalleshi.
“Na san me nake yi Sirleem i want to help?”
“Amman Ameer?”
“Yes”
“Ina da iko da Ameer duk da kasancewar ba
ni na haife shi ba, kuma mahaifinsa ba zai musa min ba”
“Makaranta fa yake yi yanzu kuma baya ma kasar?”
“Na sani, na san abun da nake yi Sirleem, idan ba Ameer ba muna da wata mafitar ne akan yarinyar nan?”
“No Momy gaskiya a canja wata shawarar
ba Ameer ba, Ameer yaro ne ba zai iya kula da ita yadda ya dace ba”
“Waye zai kula da ita yadda ya dace Tsoho?”
“Amman Momy ba ki yi tunanin kowa ba sai Ameer what if shi baya sonta?”
“Kai kana sonta? Zaka iya aurenta?”
Yayi shiru ya saka cewa
komai domin tambayar ta zo masa kamar saukar aradu. Falmata ta kalleshi zuciyarta na bugawa da karfi tana jin kamar ya amsa da eh, duk da tasan bata da kwarji da haifar da zai so a jikintaz gashi ita ba yar kowa bace balle tace ko dan arzirkin gidansu ko
sarauta wane ita.
“Ba ni da iko da kai Sirleem saboda Hajiya Balki tana nunawa kowa isa akan yayanta, ban isa na cilasta a ba saboda ita ko da kuwa ace ni din daga bangarenta na fito, balle kuma ina kanwar mahaifinka, kuma na san yadd Hajiya ta tsani ta
laka, ba zata saurara maka ba idan ka auri Falmata bayan ta zaba maka Nana a matsayin mata, ko da ace zan iya cilastaka Falmata ba zata samu jindadi a gefenka ba saboda Hajiya, zata ma iya cilastaka sai ka sake ta, yarinyar nn tana bukatar kula, mutumen da
zai bata ilmi ya kula da ita, idan ta auri Ameer zata dawo karkashina ne”
A take Sirleem ya datse maganar yana duban agogon hannunsa.
“Momy daman na biyo da ita ne ta fada miki abunda ya faru saboda kar ki ga bata zo ba, bari na wuce akwai abubuwan
da zan yi”
Wani kallon mamaki da rashin fahimta Momy tai masa, har za ta yi magana sai kuma wata zuciyar ta hana ta, ba tare da ta ce komai ba ta mike tsaye ta haye sama. Da kallo Sirleem ya bita sai da ta haye sama sannan ya kalli Falmata.
“Tashi mu
je”
Falmata ta mike tsaye ta ni bayansa har suka isa gurin kofar ya bude mata ta fara fita sannan shi ma ya fita. Sai da ya fara shiga motar sannan ta zagaya ita ma ta shiga yai ma motar key tare da danna horn tun kamin ya yi ribas. A wata kemis ka kait
a suka duba kafar suka bata magani tare da yi mata allura sannan suka fito. Be shigar motar ba ya tsaya yana kallonta.
“Zai fi ki hau Napep da ace na sauke ki a gidanku, wata kila za a iya kara miki doka ko?”
Ta daga masa kai alamar eh. Sai yaja wani
dogon numfashi ya sauke.
“Teema, ki yi hakuri da abun da zaki ji ko ki gani, kuma ki min afuwa ina son nai magana da mahaifinki gaskiya”
“Dan Allah karka yi maganar ka bashi da wani amfani a gurinsa sai ma kara jamin duka da zai yi, zan hakuri da du
k yanayin da zan samu kaina, na yarda wannan rayuwar a haka ita ce kaddararta, kuma na san Allah be manta da ni ba, zai min mafita inshallah, na gode da duk wani abu da kai min, cikin har da saurarena da bani lokacinka, bayan taimako na kudi da gudumawa da
ka bani Allah saka maka da alheri, ina son na bi zabin mahaifina, wata kila auren tsohon shi ne kwanciyar hankalina, na gane yadda rayuwata take tafiya, ba zan taba samun abunda nake so ba, kuma na hakura da komai zan rumgume kaddara”
Sirleem ya kasa c
e mata komai sai kallonta yake yana jin wani yanayi marar dadi. Ta share hawayenta.
“Ba zan taba mantawa da kai ba, babban mutumen sananne yayi hidima da ni, ya taimaka min yayi mini gata kamar uba, Allah ya saka maka d alheri Sirleem kuma ina maka fata
n alheri sai wata rana”
Ta sauke kanta kasa hawaye na zuba.
“Ba zaki sake fitowa ba ne?”
“Bana jin za a sake barina na fito, sai dai na san ba za a hanani kallonka a waya ba ko a tv, ba zan manta da kai ba, na gode kuma dan Allah kai min godiya gu
rin Momy ita ma ta rike kamar ya, babu kyama babu nuna tsangwama”
Sai da ta share hawayenta sannan ta juya ta fara tafiya wasu hawayen na sauko mata tana jin kamar ta fasa ihu domin ta san ba zata sake ganin Sirleem ba sai a hoto. Da kallo ya bita ya ra
sa tunanin da zai fara? Maganar Momy ko kuma ya kyale ta tabi zabin mahaifinta kamar yadda ta ayyana? Kalamanta sun ratsashi, sun shiga zuciyarsa sun dada masa tausayinta. Sai da tai nisa sosai da inda yake sannan ta tari Napep ta shiga tana fada masa inda
zai kaita. Tun da ta shiga cikin napep din sai ta ji kamar ta samu gurin da zata fasa kurjin damuwarta ta ji sanyi, damuwarta ta soma mata aiken hawaye babu kakkautawa.
“Allah ka kwanar min da hankalina, ka saka min natsuwa a cikin zuciya da ruhina, na
tuba ka yafe ni ya Allah”
Shine kawai abun da take ta maimaitawa tana kuka sosai har Mai Napep din sai da ya juya ya kalleta, daidai inda aka saba aje ta ta bukaci ya sauke ta, ta fita ta zaro dubu daya cikin kudin da Shattima ya bata ta mikawa mai na
pep din ya cire kudinsa ya bata canjinta, ta karba ta kama hanyar gida, tana tafe tana dingishi dayan hannunta rike da ledar maganin da Sirleem ya siya mata, hawaye kuma be fasa mata zuba ba, kirjinta sai zafi yake tana jin zuciyarta kamar zata rabe gida
biyu.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin
sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren
sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zak
u iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
43
*Littafin nan na kudi ne biya k
i karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Bakin gate din gidansa ya tsaya yai horn sau biyu, mai gadin ya fito da gudunsa ya bude masa gate, a hankali ya shiga da motar ya faka a
yalwantaccen parking space din dake gidan. Sannan ya bude motar zai fita.
“Ina zaka?”
Ta tambaya tana kokarin kai hannu ta taba shi, be kula ta ba ya fita ya rufe ya zagaya side din da take ya bude mata.
“Fito mun kawo gida”
Ta mika masa hannu
nta alamar ya rikata ta fito, samun kansa yai da kallon hannun ya yan dakiku sannan ya mika mata nasa hannun ya riko nata, tafin hannunsa na shiga cikin nata sai ta tsaya cak ta fasa fitowar tana sauraren sanyi da take jin yana ratsa hannunta, a hankali ta
zame hannunta tai wani sukuku kamar ba ita ba, can kuma ta fara lalabe ta ta yunkura zata fito sai kanta ya bugu da motar.
“Careful...”
Yana kokarin taimaka mata ta fito, tsaye tai ta saka dayan hannunta tana taba goshin.
“Be yi jini ba...”
Y
a fada yana kallonta, bata ce komai ba, gaba daya yanayinta ya canja.
“Waye kai?”
Be ce mata komai ba ya janye ta jikin motar ya rufe motar.
“A asibiti na ji irin wannan sanyin da wani ya taba ni”
“Sanyin me?”
“Sanyi a hannuna, Wasim ya fada
idan na taba hannun namiji na ji sanyi to shi ne mijina...”
Wani kasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskar Shattima, ya kalleta yana jin tana kara kwanta masa a rai, saboda kiriniyarta da yadda take abubuwa babu kintsi, sai dai ya lura iya gaskiyar t
ake fada domin yanayinta ba bayyana.
“Ni ne na taba hannunki a asibiti, saboda batanki mahaifinki zai iya kaini kotu, saboda nemanki yake gobe gobe zan kaiki gida”
Ta yi shiru bata ce komai ba, sai murzar hannun take da dayan hannunta idonta ya cik
a da kwalla. Ganin hakan yasa Shattima fadada murmushinsa.
“Kin ga shikenan na kawo matata har gida”
“Aa ni bana son ka, Wasim nake so, shi nake son na aura”
Ya sake yin murmushi ya kai hannunsa a karo na uku ya riko hannunta har lokacin bata fasa
jin sanyin ba.
“Dan Allah akwai wani namiji a nan ka kira shi na taba hannunsa? Ina son na tabbatar”
“Idan kuma wasa yake miki fa?”
“Sai na tabbatar, ina son Wasim ina son shi, bana son ka bana son wani mutum”
To ni nace ina sonki ne? Ya tamba
ya a ransa, a fili kuma sai ya ce
“Gashi kuma idan na aure mace mutuwa take, duk matan da na aura sai sun mutu”
Ya karasa yana janyo hannunta su nufi entrance har din.
“Taka a hankali”
Ya fada yana kokarin taimaka mata ta haura gurin.
“Kai b
aka jin komai?”
Yayi shiru be ce mata uffan ba, har su ka hau gurin ya kai keys din dake hannunsa ya saka ya bude kofar. Sai ya fara shiga sannan ya janyo hannunta ta shigo, yana kokarin tura kofar ya rufe ta fashe da kuka mai karfi.
“Miya faru?”
“Dan Allah ka kaini gida gobe, zan fadawa Bappa gaskiya zan fada masa komai”
Ya kura mata ido, hawaye take wasu na bin wasu babu tsayawa.
“Na fada miki zan kaiki gida ai, and dole ne zan fadawa iyayenki gaskiya saboda su binciki waye Wasim din”
“
Mutumen kirki ne, ba mugu ba ne, yana so na yana min duk abunda nake so, zan fadawa Bappa wannan, zan fada musu gaskiya”
“Then share hawayenki, indai akan aurene, ba zan aureki ba domin ina da wanda zan aura a yanzu, ko da ma bana da ita, ba zan so kusa
miki a rayuwa na datse miki jindadi da walwala ba”
Ya fada yana kallon fuskarta, maganar yake har a zuciyarsa, idan ace za a aura masa Fadime tabbas ba zai ki ba, domin har ga Allah yarinyarta ta masa kuma zai so zama da ita, sai dai ba zai so ya auret
a ta rasa rayuwarta kamar sauran matansa ba.
“Wannan Wasim din ya dace, sai sha dariyarsa ya more, zai nishadantu da rayuwarki you cute”
Ya fada yana lakatar hancinta da murmushi a fuskarsa. Kalaman da yai mata ne yasa ta ji sanyi a zuciyarta har ta
share hawayenta.
“Zo ki zauna”
Ya zaunar da ita a kujera.
“Kin ce kina jin yunwako?”
Ta daga mishi kai da sauri tana kara share hawayen.
“Okay zan mana order abinci yanzu me kike so?”
“Yogurt da kaza”
Ta fada har tana hade yawu. Murmu
shi yai yana tuna wacan lokacin daya kadeta tace ya siya mata kaza da yogurt. Ya juya ya nufi upstairs yana lasa wayar hannunta.
“Ina zaka je?”
“Sama”
Jin abun da ya fada yasa ta dan tsorata.
“Sama kuma? Nan inda nake a ina ne?”
Murmushi yai
har yana daga kansa ya sauke.
“Seriously rabon da na samu kaina cikin nishadi irin wannan har na manta, ina da damuwa sosai a raina, amman haduwar da nai da ke a yanzu yasa kin mantar da ni komai, ina jin kamar babu abun da ya faru”
“Saboda me mi na
i?”
“Baki yi komai ba, saboda ba intentionally kike yi ba, rayuwarki ce a haka, and i like it”
Ya fada yana kallonta daga inda yake tsaye zuciyarsa cike da shauki. Fadime ta gyara zamanta tana saurarensa domin ta jidadi da yace he like it. juyawa yai
ya cigaba tafiya har ya haye sama ya shige dakinsa, Shaddar jikinsa ya cire ya saka kananan kaya sannan ya dauko wayarsa ya sauko kasa, ko da ya fito ya sameta tsaye a tsakiyar falon tana lalebe a hankali.
“Ina zaki je?”
“Ban jika ba ne shiyasa nak
e lalabawa”
Yayi murmushi ya karasa saukowa.
“Ya kamata a samo miki sanda ko? Ki huta da lalaben hannu”
“Aa bana son sanda ni warkewa zance, abun da mutum yake kira shi ke binsa, ni bana son muguwar sara, zan warke inshallah”
“Ni ma ai fatan wa
rkewa nake miki ai, amman sandar zata taimaka miki ne wajen gane abubuwa da kuma tafiya kamin