Showing 120001 words to 123000 words out of 304903 words
ko
kuma yai mata, kayan su Khaleel da Aymana duk shi yake wanke wa, har girma yana mata idan yan kwarai na saman kai, ko kuma ya mata rabin girkin ita kuma ta karasa. Sai da ya fara dauraye tufafin yana shanyawa sannan ya dauko mata wani labarin.
“Anti i
na tunanin komawa makaranta fa”
“Makarantar lafiya? Ni ba ni da kudin biya maka makaranta yanzu, kai kuma ba aikin wahala kake so ba balle ka taimaki kanka”
“Ai wani aikin zan samu mai soka soon, zan gyara gidan nan na masa fenti na saka masa tayis n
a siyo miki gas, ke har makka sai na kai ki na siya miki mota, su Khaleet na saka su makarantar kudi, komai zai zama normal...”
Kallonsa tai.
“AA baka rabu da yarinyar nan ba ko? So kake ka jefa kanka a matsala ko?”
“Ni fa na rabu da ita bana tar
e da Ita sam sam sam”
“Ya dai kamata ace idan nai maka magana ka ji, idan na ce ka bari ka bari, ba ka da wanda ta fini a yanzu, baka da gata sai ni, kasan bamu da kowa sai Allah, idan ka shiga wani hali aka kama ban san ya zan yi ba, aje min wankina”
Ya kalleta a sanyeye.
“Ba maganar yarinyar nan ba ne Anti”
“Ni dai ka aje min wankina”
Ya cire hannunsa ganin da gaske take domin babu alamar wasa a maganar ta balle kuma a fuskarta. Wannan abun yake tsoro ya dade yana son labarta mata ko kuma
sammata wani abu amman yana tsoron abun da zata fada, domin shi kansa ya san ba shi da gatan daya wuce Antinsa a yanzu, ita ce uwarsa ita ce ubansa ita ce komai nasa.
“Ka rika taka tsantsa da rayuwa AA, neman kudi ba hauka ba ne bana son ka jefa kanka
a matsala, na rasa uwa n hakura, na rasa uba na hakura, na rasa miji na hakura, yanzu kam bana jin idan na rasa ka zan iya rayuwa, kai kadai ka rage min, ni ma ni kadai na rage maka, ya kamata ace idan na maka magana ka ji, ka san irin wahalar da muka sha
kamin mu kawo yanzu, kasan irin fadi tashin da nai kamin na samu na gina kaina, muna zaune cikin rufin asiri kana kokarin jefa mu a hadari?”
“Idan akan yarinyar nan Allah ya min arziki, ba fa akanta ba ne”
Uffan Anti bata sake ce masa ba, ta san akan
ta ne tun da har yai ma kansa addu'ar arziki. Ganin yadda ranta ya bace yasa ya tashi ya nufi gindin murhu ya fara saka itace zai hura mata wuta.
“Karka kunna wutar nan”
“Girki zan dora miki”
“Ba mu da abun dafawa kwado zan yi”
Ya kai hannunsa
ya taba aljihun wandonsa, yana da kudi amman ba damar ya bata tace ina ya samo ko kuma tace ba zata karba ba. Mikewa yai tsaye ya dawo bakin kofar dakinsa ya zauna yana kallonta, har ga Allah be jidadin yadda ya ga ranta ya bace ba, domin Anti Rabi ita ce
a matsayin uwa a gareshi duk wani abu da uwa take yi ma da, Anti Rabi ce tai masa lokuta da dama zata hanawa yaranta abu ta bashi, babu abun da zai nema ta ki yi masa sai idan bata da hali
“Da kin aje wanki gobe na karasa miki”
Ta masa banza, sosai
ranta ya bace ta san yadda AA yake da shegen son kudi, ba zai yi sata ba amman yadda ya lakewa yarinyar nan tana tsoro kar ya janyo musu abun da yafi karfinsu. Mikewa yai tsaye ya shige cikin dakinsa ya bude akwatinsa yana duba kayan da suka fi fitar da sh
i.
“Yarinyar nan ma da safe bata bar ni naje gidansu ba balle na kara samo wani abu”
Ya fada cikin jin haushi yana tuna kiran da tai masa dazu da safe ta sanar masa cewar ba zata je makaranta ba.
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sun
ansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa,
sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4am
are nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikaw
a ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
29
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank
, then send the evidence to 08036126660*
FADIME POV.
Zainab ta daga kai da sauri, domin ba karamin tsorata tai da tsawar da Wasim ya daka mata ba.
“Okay”
Ya matsa kusa da Fadime.
“Za ki jira ni nan zan je na dauko muku tufafin da za ku
saka da abun hawa saboda akwai nisa daga nan zuwa can”
“Ba zaka dade ba?”
Ya daga mata kai alamar Eh.
“Ku sauko ta nan kasa”
Ba musu ta bi bayansa, Zainab kuma ta bi bayan Fadime suka sauka ta dayan gefen dutsen Inda babu wanda zai gansu. Sai
da suka sauko sannan ya kalli Zainab ya ce.
“Ki boye camera ki da wayarki, karki yarda a san kina daukar hoto”
“Okay”
Ta amsa masa tana sauke jakar da camera take ciki.
“Amman idan aka gane za a mana wani abu ko?”
Fadime ta tambaya tana ji
n tsoron a ranta. Sai ya rage tsawo ya dawo daidai ita.
“Ba zan bari a taba ki ba”
“To ai kai ma za a iya maka wani abu saboda ka saba musu doka”
“Wa zai tana dan sarki? Sai dai Sarkin da kansa, amman bayan shi babu wanda ya isa ya taba Wasim a d
uniyar nan, idan kuma ina nan babu wanda ya isa ya taba ki”
Ba baki kadai Fadime ta bude ba har da ido da kunne da hanci, bata taba jin Wasim ya burge ta irin yau, tsabar mamaki har da hannu ta kai ta taba kirjinsa.
“Ashe kai dan sarki ne... Laaaaa..
Laaaa. Laaaaa”
Tana ta maimaita tana kallonsa, wani irin burge ta yai zuciyarta na raya mata shikenan ita kam kakarta ta yanke saka tun da Wasim Sarki ne ita kuma matarsa.
“Shikenan ma”
Ta furta sai kuma tai shiru bata karasa ba, Zainab dai sai
kallon Wasim take, yadda yake kallon Fadime kadai da irin tattausan murmushin da yake mata kadai ya isa ya sanar mata cewar son Fadime yake.
“Zan dawo yanzu”
Be jira cewarta ba ya nufi wata karamar hanya, ya fara tafiya da sauri-sauri tun suna hang
oshi har suka daina. Fadime ta zauna a gurin tana ta tunanin tafiya, tabbas tana son ganin garinsu Wasim amman tsoron da take ji yana kokarin hanata sukuni, ga shi yamma sai kara yi take. Zainab kam aikin gyara camera take ta yadda haske ba zai fita ba bal
le a gane tana dauka hoto, sai da ta gama da camera sannan ta dauko wayarta number Auwal tai dialing sai ta ji ta a kashe, sosai gabanta ya fadi, sai ta ji wani abu marar dadi yana ziyartarta. A hankali ta sauke ajiyar zzuciya, ta kashe wayar tana kallon s
ararin samaniya. Be yi 20 minutes ba suka hango shi tafe da rike da kaya a hannu dayan hannunsa kuma janye da wani gawurtaccen farin doki. Daga Fadime har Zainab mikewa sukai tsaye suna kallonsa har ya iso.
“Doki zamu hau?”
Fadime ta tambaya tun kam
yace mata komai, sai ya daga mata kai alamar eh.
“Ni gaskiya ba zan hau doki ba, zai je ya jefar da mu ni ban taba hawa doki ba”
Ta fada a shagwabe tana kallon dokin da fuskar tsoro.
“Ni na saba hawan doki ba zan bari ya jefar da mu ba, a idan m
u akwai dawakai”
Zainab ta fada tana murmushi daman can tana sha'awar hawan doki. Fadime ta kalleta tana aika mata tambayar da ta san ba lallai ne ta amsa mata ita ba.
“A can Yola kuna siyar da dowakai ne?”
“Aa suna gidan Sarauta ne”
Zainab ta
kalli Wasim da sauri jin amsar da ya bawa Fadime. Fadime ta wara manyan idanuwanta tana yi ma Zainab wani irin kallon burgewa jin an dangantata da sarauta.
“Taya kake sanin komai a kaina?”
A maimakon ya bata amsa sai ya sakar mata murmushinsa mai k
yau ya mika mata wata bakar rigar saki tare da gashin kaza.
“Je ki saka, wannan kuma ki laka shi a kanki”
Ta karba tana masa kallon mamaki, sai a yanzu ta kara tabbatar da cewar tsafin da ake fadar suna da shi ya wuce misali, daga ganinta har ya san
komai a akanta! Juyawa tai baya ta fara tafiya zuwa bayan dutsen, sai da ta wuce sannan ya mikawa Fadime nata.
“Ki saka wannan”
Ta karba tana dubawa.
“Miyasa kuke saka wannan kayan da kuma gashin kaza?”
“Kayan saki muke sakawa ba ma saka iri
n tufafinku, saka gashin kaza kuma yana nufin marar aure, duk mace da kika gani da gashin kaza a kai to bata da aure ko da kuwa tsohuwa ce”
Ta kalleshi tana yar dariya.
“To su mazan da basa saka riga su ma ba su da aure?”
Dariya yai mai sauti ya
juya mata baya.
“Canja kayanki”
“Ba zaka juyo ba?”
“Eh”
Ta shiga cire rigarta sannan ta kwance zanen tana yi tana kallonsa.
“Kar fa ka juyo”
Be ce komai ba sai murmushi yake duk kuwa da kasancewar bata ganinsa. Sai da ta cire tufafin ji
kinta ya rage daga ita sai dan karamin saket din ciki sannan ta shiga kokarin saka rigar, wanda hakan yai daidai da fitowa Zainab a inda ta boya tana saka tufafin, tun da ta doso inda suke yake ta kallonta har ta iso, ba karamin kyau rigar sakin tai mata b
a, daman bakin abu ko a bakar fata yana kyau balle ita da take fara sol, sai ta fito sak kamar yar garin, ga gashin kanta daya sha gyara ya kwanta bayanta gwanin sha'awa. Rigar ta tsaya iya guiwarta ne kasancewarta doguwar mace, ba kamar Fulani ba da bata
kaita tsayi ba abun ka da wanda be gama girma ba, ga kirjinta babu komai, sai dan abun da ba a rasa ba, Fulani irin yan matan nan da basa da cikar gaba sai dai hakan be rage ta da komai ba. Tsabanin Zainab da kirjinta yake cike gwanin sha'awa.
“Na gama
”
Fadime ta fada tana kokarin laka gashin kazar a kanta, juyowa yai ya kalleta sai ya ga ta masa kyau fiye da ko yaushe, daman kullum cikin kayan fulani yake ganinta, yau kuma gata sanye da kayan saki da suka karbeta suka mata kyau suka kara fito da has
ken fatarta.
“Kin yi kyau kyakkyawa”
Ya furta tare da kai hannu ya karbi gashin kazar ya laka a mata a kai, sai ta kara kyau sam ba zaka ganta ka ce ba yar garin ba ce domin babu abun da ya banbanta da su. Juyawa yai ya matsa kusa da Zainab ya karbi
gashin kazar yana kokarin saka mata a kai. Kusantota da yai sai ta ji wani irin faduwar gaba wanda yake neman danne mata numfashi, har sai da ta lumshe ido, abun da bata taba ji ba saboda namiji ya kusance ta ko Auwal da take so bata jin faduwar gaba idan
ya matsa kusa da ita. Bayan ya saka mata ya matsa baya gurin Fadime.
“Zaki iya hawan dokin?”
“Ina tsoro”
Ta amsa masa a shagwabe tana masa wani kallo da manyan idonta kamar zata fito da su waje, hakan da tai sai ya ji ta kara burgeshi.
“Zan h
au na rike linzamin ke kuma sai ki hau bayana ki rike ni”
Zainab ta fada tana kokarin saka camera a jikinta, wayarta kuma tana cikin karamin aljihun wandonta.
“Kin yarda”
Ta tambaye Fadime, shiru tai kamar mai tunani sai kuma ta daga masa kai ala
mar eh ta yarda. Wuyan hannunta ya rika, ya nufi gurin dokin da ita, Zainab na ganin haka ta dauki jakarta ya bi bayansu, sai ya gyara sirdin sannan ya mikawa Zainab hannunsa. Kallon hannun tai ta sai kuma ta kalleshi sannan ta mika masa nata hannun ya rik
ata ta hau, a maimakon yai ma Fadime yadda yai ma Zainab sai ya cira Fadime da duka karfinsa ya dorata saman doken.
“Wayyo wayoo shiiiiii”
Ta fada jin ta a saman doki abun da bata taba ba kuma bata taba saka rai ba. Duka hannayenta ta saka ta rike Za
inab gam kamar wacce aka cewa idan kika sake ta zaki mutu.
“Asssha esssh essssss ashhhhhhh”
Shine abun da take ta fadi ta rufe ido gam. Shi kam kallonta kawai yake cike da burgewa.
“Kai ina zaka hau”
Ta tambaya ba tare da ta bude idon ba.
“A kafa zan je”
Ta bude ido da sauri.
“To ai shi dokin be san hanya ba”
“To ni kai zan bi”
Ta fara kokarin saukowa.
“Ba zaki iya tafiya a kafa ba, ki zauna nan”
“Zaki iya ganin abun tsoro, ba irin tafiyar da kike tunani zan yi ba”
“
Tau”
Ta fada cikin muryar kuka, sannan ta gyara zamanta saman dokin.
“Zan iya tafiya da jakata?”
Zainab ta tambaya tana nuna masa jakar dake kasa, amaimakon ya amsa mata sai kawai ya dauko jakar ya mika mata.
“Takak takak”
Ya fada yana kal
lon dokin, kamar jira yake sai ya fisgesu da mugun gudu kamar za su fadi. Wani irin ihu Fadime ta saka tana ta kyakya da muryarta mai shiga kunne ta rufe ido gam ta kankame Zainab. Da kallo ya bisu yana murmushi.
“Fateme”
Ya furta sannan ya kalli ha
nnunsa ya sauke ajiyar zuciya. Tun da dokin ya fisgesu be tsaya sai gudu yake kamar zai jefar da su, ba su isa bakin kofar garin ba sai da aka kira sallah magariba. Wani abun daya bawa Zainab mamaki ganin Wasim bakin kofar garin yana jiransu bayan sun baro
shi a can baya. Daidai shi dokin ya tsaya sai ya rika shi ya shafa kansa, sannan ya nufo inda Fadime take yana rikata ta fasa ihu domin har lokacin idonta a rufe yake.
“Shiiiiiiiiiii ni ne”
Jin muryarsa yasa ta bude idon, wuyansa ta rike har ya sauk
ar da ita, sannan ya mikawa Zainab hannu a karo na biyu ta rika ta sauko tana karewa kofar garin kallo. Katuwar kofa ce da akai ta ta manyan itace an yi ma kofar kwaliya da wani abu mai kyali kamar zinari.
“Wow”
Ta furta tana kara kallon yadda mutan
e suke ta hadahadansu babu wanda ya kula da wani. Be ce musu komai yai gaba ita da Fadime suka bi bayansa, yawancin mazan garin dukansu suna daure da walki sai dai kalar na kowa daban, masu riga a cikinsu kalilan ne, matan dake wucewa kuma wasu suna sanye
da gashin kaza a kai wasu babu. A zatonta karami gari ne da ba zai kai garinsu Fadime ba ma, sai ya zo akasin tunaninta ashe wata duniyar ce ta dabam mai zaman kanta, wani gurin kasuwa wani abun gidanjen kasa wasu gidanjen zana. Wani mai mangalar dawakai n
e ya faka a gabansu, sai Wasim ya umarce su da su hau, ba musu suka hau har shi, dawakin sukai gaba da su, wata unguwar da dabam suka dosa Zainab dai sai rabon ido take. Daidai bakin wata rumfa mai kamar ta shago ya sauke su, Wasim ne ya fara shiga cikin r
umfar sannan Fadime dake ta makalewa jikinsa kamar zata shige masa, yadda taga kowa ba riga yasa ta kara tsorata jikinta sai rawa yake.
A inda suke suna nesa da mutane sosai kuma ba kowa zai lura da su ba, kasancewar duhu ya fara dauka.
“Zaki iya dauk
ar hotonki daga nan”
Wasim ya fada masa yana kokarin janye tafin hannunsa da Fadime ke son kamawa ta rike, domin jin take kamar wani ne zai zo ya sace ta.
Zainab ta fiddo camera ta fara daukar hoton, garin be kara burgeta ba sai da hudu ya soma sosai,
a lokacin ne mutanen garin suka soma kunna wutar ice, wasu kuma aci balbal, sai ko'ina ya haskaka gwanin sha'awa, masu gida suka kunna wutar icen daga waje, ya haska kofar gidansu ga kuma hasken farin wata daya haska ko'ina, a kusa da su ma wani ya kunna,
cikin natsuwa Zainab ta shiga daukar hoton, abun da yake nesa zooming take ta dauke shi hoto.
“Sauke camera ki”
Ya fada da sauri hango Liya ta doso inda suke, cikin sauri Zainab ta boye Camera, Fadime kuma ta kara matsawa kusa da shi. Daga Zainab h
ar shi har Fadime kallon Liya suke har ta iso, tsayawa tai kallonsu, ba zata iya cewa ba yan garin ba ne kasancewar suna sanye da irin tufafinta, sai dai abun da bata taba ganin ba Wasim da mata, ita kanta da take yar'uwansa ba yawo yake so yi da ita ba. T
a san kuma be da budurwa a duk fadin garin, hakan yasa mutane