Showing 129001 words to 132000 words out of 304903 words
wayarsa dake aljihu, ganin Number Baba Waziri yasa ya mike tsaye ya fice daga falon. Kasa ya dauko gaba daya sannan ya kara wayar a kunnesa da sallama. Bayan sun gaisa Baba Waziri ya
ce.
“Ban jika ba, tun da muka yi magana, idan Maijidda bata maka ka fada min wanda kake so, ba abu ne da zai dauki lokaci ba balle nai ta jiranka”
Shattima yayi shiru kamar ba Waziri ne a wayar ba, can kuma ya sauke ajiyar zuciya silently ya ce.
“Ina sonta Baba, amman dan Allah a tambaye ta idan ita ma tana so na, kar a mata dole”
“Mashallah, Allah ya hada kanku ya fada zaman lafiya sai ka fara shirye-shirye tun yanzu”
“Na gode Baba”
Ya furta sannan ya sauke wayar tare da sauke wani dog
on numfashi. Data kunna ya shiga wani side ya siye ticket din jirgin da zai tashi zuwa Katsina a gobe.
**
Shattima na fita falon, Iya ta shigo lullube da zane, tana shigowa ta fadi gaban Ammy tana zuba mata kirari bakin nan cike da goro, sai da ta k
alli ko'ina a falon ta ga Jekadiya ce kadai a falon sai Ammy sannan ta kara matsawa kusa da Ammy tana wasar hakora.
“Ranki ya dade, ina da magana”
Da gangan Ammy ta ki kallonta ba dan wulakanci ba sai dan nuna isa, daman can Allah ba hada jinin Ammy
da Iya saboda Iya ta fiye shiga hanci da kuddudumi ga salo irin na tsofin mayu, Ammy kuma bata son haka.
“Tau ina jinki”
Ta kalli Jekadiya tana dariya, kamin ta sake kallon Ammy.
“Daman wata yar shawara ce na zo da ita”
Sai kuma tai shiru k
amar mai tsoron fada. Ganin hakan yasa jekadiya ta ce.
“Iya ki bude baki ki yi magana, Ammy na saurarenki”
Iya ta juyo gurin Jekadiya tana yar dariya kamar ta kunya.
“Daman na ce wai akan Babban Mutum ne, na ce mi zai sa sai an tafi nesa”
Amm
y ta kalleta domin ta fahimci inda zancenta ya dosa tun kamin ta karasa, Jekadiya kuma gabanta ya fadi duk da ta san ba wai ta fada ne ta siffar gulma sai dai ta san Ammy ba zata jidadi ba ta fada mata abu kuma aji shi gurin wani.
“Wannan lauye lauyen
da kike ba zai fitar da ke ba, da kin fito kin fadi maganarki a fili da Ammy ta fahimta”
Iya ta shafa zanenta tana murmushi.
“Daman cewa nai me zai hana a hada Babban Mutum da yar'uwarsa? Ai ba sai an je can nesa ba an dauko bare tun da ga abu a cik
i gidan”
Jekadiya makis tai a gurin kamar an kama munafuki, ta rasa abun cewa. Ammy ta juyo da kyau tana kallon Iya.
“Eh lallai haka, jindadi yayi muku yawa ke da yarki, har hauka take raya muku wannan, shine dalilin shigewa Shattima da Zainab take?
To ai kalar zaren ba kalar yadin ba ne, kuma lalacewar takalmin sarki yafi karfin sakawa kafar bafade, Maijidda ce bare? Yar waziri ce nesa? Gata da sakin fuskar da ake muku a gidan nan ya muku yawa shiyasa har raini ya shiga ciki, har kike iya duban idon
a ki fada min wannan maganar, Iya wai ko kin manta waye ke?”
“Aa ina ya zan manta... A gafarce ni Hajiya salo na ne... Amin afuwa”
Iya ta fada da dariyar kunya, zuciyarta tab da tsanar Ammy sai kallon kurwarta take.
“To daga yau sai yau, ba ke ba
ko Zainab kar na sake ganin kafarta a falon nan, idan kina bukatar wani abu ko yin wani abu ki nemi iso karki sake shigo min falo, idan kika yi wasa ba a masarautar ba a yola gaba daya ma sai na canja miki zama”
“To Ammy ba za a kara ba ayi min afuwa a
gafarta min”
Ta farasa tana fashewa da kuka, ta mike tsaye rumgume da kunyarta ta fice daga falon, tana kuka kamar gaske.
Ammy ta kalli Jekadiya da duba na mamaki.
“Kin ba ni mamaki, ban yi zaton haka ba, amincewa da ke kuma farinciki abun da Wazi
ri yai yasa na labarta miki taya zaki dauki sirri ki baza a kunne Iya?”
Jekadiya ta rasa inda zata saka kanta, a take ta hau rantsuwa, tana labartawa Ammy yadda akai ta Iya ta ji.
“Wallahi ranki ya dade ban yi hakan da nufin labarta mata komai ba, a
gafarce ni, ni kaina murna ne yasa na fadi haka, ban yi zaton zata kawo wannan tunanin ba, Wallahi ba halina ba ne”
Ammy bata sake ce mata komai ba ta mike tsaye a fuce ta shige dakinta cikin mamakin yadda Iya ta iya karfin halin wannan tunanin, har ma
ta iya furtawa.
***
Iya na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe.
“Idan ba yi da lala ba ayi da tsiya, tsaya mu gani ida ita ma Maijidda ta mutu sai wacce kuma? Wata rana da kanki za ki zo kina rokon na taya ki nemawa Shattima auren Zainab,
ita kadai ce matarsa kuma da ita kadai zata haifa masa yaya, daga lokacin ne komai zai dawo na mu, ke kanki Ammy sai kin zama abar tausayi...”
Ta fada cikin wani irin zafin rai na jin zafin abun da Ammy tai mata.
“Tana jin kanta matar nan kamar ita
ce sarkin, ke kuma bari na gani zaki taya ni yake ko kuma ta gawa za ki yi”
Ta karasa tana janyo wasu sabbin tufafin a cikin wardrobe dinta, atamfa mai kyau da tsada ya janyo ta dora saman gado domin bata son gobe ta tsaya jiran komai.
Haka ta kwana
cikin bacin rai da sakesake kalakala a ranta, kamin garin Allah ya waye duk ta matsu, karfe tara ta shirya cikin atamfar data ciro jiya, ta dauki turare ta fesa sannan ta dauki jakar kudinta da makullin dakin ta fito, ta rufe dakin ta nufi kofar fita sai g
aisawa take da hadimai kamar ta Allah, kowa sai bata girma yake har ta isa gate din. Sai da ta fita daga unguwar gaba daya sannan ta samu Napep ta shiga tana fadin.
“Malam Unguwar Waziri”
Ta shiga ta zauna har tana kwafa.
31
*Littafin nan na
kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
AA POV.
Yana isa gurin ya nuna musu gate pass din sai suka bude masa kofar ya shiga, a inda ya san Nana ta zauna dazun
ya kalla sai ya hango babu Nana a gurin ba kuma kowa a har jakar da take fada babu, a take zuciyarsa ta raya masa yarinyar ta dauki jakarta ko kuma wata ta sata, kai tsaye ya nufi gurin yana ta rabon ido ko zai hango Nana. Gaban teburin ya tsaya yana ta sa
ke sake a ransa, be san yarinyar ba haka kuma be san inda zai sameta ba, wata zuciyar na raya masa ya aje sarkar a kasa yai tafiyarsa, sai dai kuma be zama lallai ta gani ba wani zai iya gani ya dauka, hakan kuma ba zai wanke Nana daga zargi ba, ba kuma za
i hana idan an bincike CCTV ta gurin ta nunata ba. Be raba dayan biyu ba, wata budurwar da ba zata wuce sa'ar Nana ba ta doso teburin tare da Amal, hankalinta a tashen.
“To wai ina kika aje jakar?”
Amal din ta tambaya tana duba gurin, sai yarinyar t
a amsa mata kamar ta fasa kuka.
“Wannan kawarki na bawa na ce ta rike min, ina gama karin kudin na dawo na ga jaka a bude ba sarka kuma ita yarinyar bata nan”
Jin hakan yasa AA ya dan matsa kusa da su.
“Malama ke kika jefar da sarka a nan?”
D
aga Amal har yarinyar dagowa sukai suka kalleshi, kamin su kalli Sarkar da yake nuna musu, yarinyar ta kai hannu da sauri ta karba.
“Wallahi ba jefarwa nai ba, sai dai idan sata kai baka samu damar fita da shi ba ka maido”
“No a kasa na ganta, na da
uka sai na rasa wa zan bawa”
AA ya fada da sauri yana kokarin kare kansa, Amal ta masa wani kallon rashin yarda.
“To me ya kawo nan bangaren mata ma? Kuma har ka ga sarka a kasa?”
“Believe me ban dauka sarkar nan ba”
Bata ko saurareshi ba ta n
ufi wajen securities din da suke kofar shigowa, AA ya ganin ta nuna inda yake yaji yawun bakinsa sun kafe, gabansa yai mugun faduwa, domin ba a taba zarginsa da sata ba, domin be tana daukar abun wani ba duk kuwa da kasancewar yana da son abun duniya. Tare
da Amal din securitin suka zo suna zuwa ba su tsaya komai ba sauka yi ma AA wani irin mugun riko. Hango hakan da Nana tai yasa ta dawo gurin da saurin, daman can gefe a tsaye ta kara waya a kunne kamar yadda AA ya fada mata ta yi, tsaye tai a gurin rike d
a wayar tana kallon AA.
“Ban dauka ba, a kasa na ganta Malam karka cikin mutunci a nan”
AA na rufe baki Yarinyar ta soma karyata shi.
“Wallahi karya yake sarkata a jakata na sakata”
Take police din ya tsinka masa mari ya fisgi rigarsa suka tur
ashi gaba, abun ka da abu a bainar jama'a sai mutane suka sako musu na mujiya, kallo ya dawo kansu. Mutuwar tsaye Nana tai ta rasa abun da zata yi idonta ya cika da kwalla ganin an tisa keyar AA gaba da sunan satar da ita ta aikata, gashi tun a gurin sun f
ara dukanshi, ta kasa cewa komai Amal kuwa sai kokarin labarta mata abun da ya faru take.
“Kin je can gurin waya kin bar jakar Rukayya ashe washe wannan mutumen ya hango sai zuwa yai ya daci sarkarta, mun kama shi sai fadin yake wai tsintarta yai a kas
a”
Nana ta kasa cewa sai kallon AA take har aka fice da shi daga dakin taron, kamar a sama Hajiya Babba ta dafa Nana domin sai a lokacin ta lura da ita, sai dai ita Nana ta lura da Hajiya tun farkon shigowarta.
“Daughter lafiya dai?”
Rukayya ce la
barta mata abun da ya faru, domin har lokacin Nana gani take kamar a mafarki ne komai ya faru.
“To sai ku yi hankali kuna sake jiki a ko'ina kuma kun san akwai inda ba mutanen arziki musamman irin wannan gurin”
Cewar Hajiya Babba kamin ta kama hannu
n Nana kamar gaske.
“Zo mu zauna a can”
Binta Nana tai kamar bawa da ubangidansa ta nufi inda Hajiya take ta zauna kusa da ita, kamar wacce bata cikin hayyacinta haka ta rika gaisawa da manyan matan da suke tambayarta ina Ammy, wasu abokan Ammy ne w
asu kuma na Hajiya Babba, hannunta na rike da wayar AA sai shafa waya take a hankali. Bata taba sanin wani abu mai suna tashin hankali ba sai a yau, bata taba jin nadama a aikata wani abu ba kamar wannan, he is innocent right? Ita tai causing komai, kuma y
a karbe ta ba tona mata asiri ba ya dauki laifin a kansa bayan ya san ba shi ya aikata ba. Bata san lokacin data mike tsaye ba, zata fara tafiya sai Hajiya ta rikota daman haka take nuna mata son munafurci har take ganin kamar ta fi son ta da Ammy.
“Da
ughter tafiya zaki yi?”
Nana ta kalli Hajiya idonta tab da hawaye, ta yi shiru sai kuma ta tuna Hajiya mai share mata hawayenta ne a koda yaushe.
“Hajiya ina son magana da ke”
Hajiya ta mike tsaye tana kai bakinta saitin kunne ta Nana a zatonta ma
ganar ta baki da baki ce kawai, sai Nana taja hannunta suka fita daga gurin, sai da suka isa gurin da AA ya faka motarsu sannan ta sake hannun Hajiya ta sunkuyar da kai kasa.
“Lafiya dai daughter fada min matsalarki”
Nana ta kalleta tana fashewa da
kuka.
“Hajiya wanda aka ce ya saci sarkar nan ba shi ya sace ta ba”
“Ban gane ba”
Cewar Hajiya tana kallon Nana da mamaki, zuciyarta na cika fal da farinciki jin furuncin Nana ta san wata kila zata fadi cewar ita ta saci sarkar wanda shi zai fi k
omai yi mata dadi a yanzu, saboda Ammy za a zaga ita kuma yabe ta na ganin tana son hada auren Nana da danta.
“Ni na sata.... Amman ban san miyasa n sata ba...ban san mi zan yi da sarkar ba...”
Hajiya ta kamo hannunta.
“To ya akai yace shi ne?”
“Ya fanshe ni ne, amman ba shi ya dauka ba, ni na dauka Hajiya ki taimaka masa kar a masa komai dan Allah, Wallahi Sardauna ba barawo ba ne na yarda da shi”
Hajiya ta ji wani abu ya sauko mata tun daga saman kanta har cikin kafafuwanta.
“Ke wa kik
a ce?”
“Sardauna”
Nana ta maimaita tana kuka sosai, domin wata kalar nadama ce ke rabarta.
“Ke sake fadi na ji”
Hajiya ta sake tambaya baki saki.
“Sardauna, Hajiya Wallahi ba barawo ba ne, dan Allah ki taimaka masa kar su masa komai saboda
da ni”
A take kallo ya koma sama, sai murnar Hajiya ta koma ciki, wani kalar fever ta ji yana sauko mata.
“Saurayinki ne?”
“Aa shine sabon direbana”
Nana ta fada har muryarta a shakewa, jikinta sai bari yake irin na wanda kuka yake cinta sosa
i. A take Hajiya ta saka salati.
“La'ilaha illala muhammadu rasulullah sallalahu alaihi wassalam, ki ce ni na siya da kudina”
Nana bata kula zancen ba balle har ta gane inda ta dosa, wani irin dogon numfashi Hajiya ta ja ta sauke tana kara nanata su
nan.
“Sardauna...”
Jin hakan yasa Nana ta rike hannayenta.
“Hajiya dan Allah ki taimaka kar a masa komai”
Hajiya ta jata jikinta ta rumgume tana rarrashinta kamar gaske.
“Daina kuka yanzu zan kira Babanki Jarma na fada masa ya binka inda a
ka kai shi”
Tana fadin hakan ta saki Nana ta nufi gurin motarta, Nana ta bi bayanta da sauri. Direban Hajiya na hangota ya fito cikin motar ya bude mata gidan baya, kamar daman abun da take jira kenan tana isa ta shiga gidan baya ita da Nana shi kuma ya
tashi motar. Nana ta kwanto jikin Hajiya hawaye a sauko mata, can kuma ta dago hannunta tana ta kallon tafin hannun ita kanta bata dauka bayan Ammy da Mai Martaba da take yi ma sata ba zata iya yin wata a public place like this, kuma sarka. Ta jimke hannu
n wasu hawayen a sauko mata. Ganin hakan yasa Hajiya ta ciro wayarta a jaka ta nemo number Jarma, sai da wayar ta dade tana ringing sannan ya daga.
“Hello Jarma”
“Hajiya barka da dare”
“Dan Allah yar wata muka samu, wani yaro ne yai sata a gurin
bikin da muka zo na yar Faro Ambassador, shine police suka tafi da shi, to ina son ka saka a binciko mana wane police station aka kai shi”
“To yayi, amman kin yaron ne?”
Hajiya kamar tana jira ta amsa da karfi.
“Eh sunanshi Sardauna, shine sabon d
ireban Nana”
Daga dayan bangaren Jarma ya amsa da kuzarinsa.
“Sardauna fa kika ce Hajiya?”
“Eh a taimakawa daughter na kar ta shiga damuwa, gani tare da ita, zan kira ka anjima”
Bata jira abun da zai ce ba ta kashe wayar tare da kai hannunta t
a taba Nana.
“Ki daina kuka ai komai zai zo da sauki tun da na fadawa Jarma”
Nana ta rumgume Hajiya tana jin wani irin son ta a ranta, domin ta tabbatar da Ammy ce ba zata mata haka ba. Apartment din Hajiya direban ya faka motar, sai Hajiya ta fito
rike da hannun Nana ta nufi cikin gidan da ita, har cikin dakinta ta kai ta kwantar.
“Kwanta a nan ki huta”
Ba musu Nana ta kwanta a gurin, Hajiya kuma ta karasa ciki ta aje jakarta ta fice daga dakin rike da wayarta. Tashi Nana tai zaune ta kunna P
ower button din wayar sai ta samu wayar a pattern da katon hoton AA a din daya cika screen din wayar, wani irin tausayinsa ne ya kara sauka a ranta, ji tai kamar bata da natsuwa idan bata san halin da AA yake ciki ba, hakan yasa ta mike tsaye ta bi bayan H
ajiya.
Hajiya ta na fitowa daga dakin, ta shiga second room dinta ta rufe ta kira number Jarma, wannan karon bugu daya ya dauka.
“Jarma”
“Hajiya”
“Jarma a nemo inda yaron nan yake, maganar bokan ta tabbata sunanshi Sardauna”
“Hajiya ai n
i abun ya bani mamaki, ace har kin san shi”
“Ni ma sai yanzu nake saninsa, amman ni na siye macijin da hannuna, domin ni na dauke shi aiki ba tare da sani ba, kuma ba tare da na yi bincike ba, ina cikin tashin hankali Jarma ka nemo yaron nan”
“Dole z
an saka a nemo shi ai, ba ke dai ce a matsala ba har da ni”
Jarma ya amsa daga dayan bangare.
“Kuma idan an samo shi, ka fada min da wuri, a juyar da case dinsa daga sata zuwa kisan kai, a tura shi gidan kaso, ko nawa ake ashewa zan kashe, ka shigo
da safe zamu yi, domin dole ne mu koma gurin mutanen nan kar abubuwan su kara mana yawa, ina murna Nana ta fara dan hali sai kuma abu ya juye min haka”
“Gaskiya kam ya kamata mu koma garin nan daga can ma sai su sanar da mu wacece Fadime ita ma kar ta r
ibance mu”
“Haka ya kamata, muna ta